Showing 36001 words to 39000 words out of 94205 words
yi mata daurin mayu ana dukanta, ihun da Baffa ya yi
yasa hankalin jama'a dawowa kansa, Jauro ya yi murmushin gefen baki kafin ya matso kusa da Baffa
yana magana yana daga murya
77
HAUSACINEMA.COM
"Hakika bai kamata ace daku za a haɗa baki a munafurci mutanen yankin nan ba, (yana yi da sarki
chubaɗo da mai unguwa ori) sannan kai kuma Magaji idan ka manta na tuna maka,kaine kace min duk
ranar da na gano AZIMA DA AZIZA MACIZAI NE kaine wanda zaka bani takwabin da zan kashesu! Dan
haka yau sunan Aziza gawa,ita ma Azimar da ta bar yankin nan da ace tana nan da yau gunduwa-
gunduwa zamuyi musu" murmushi Baffa ke yi hawaye na zuba a idonsa yana yiwa Jauro wani irin kallo
wanda ko idonsa baya kiftawa, Jauro ya kuma cewa
"Shin zaku yarda ku rayu da macijiya mai kisa a cikinku?" jama'a suka amsa da a'a, Jauro ya kuma cewa
"Idan kuwa hakane ku ci gaba da dukanta har sai ta mutu!!" Sarki Chubaɗo da mai unguwa Ori suna
dakatar da jama'a amma ina kamar kara ingizasu akeyi, wani ne da ya daga wani babbar sanda ya
roɗawa Aziza a kai jikake kwasss!! Wani ihuuu Baffa ya kuma yi ganin yadda sandar ta shigi Aziza dan har
sai da ta girgiza, Baffa ya kalli Jauro cikin jan ido ya ce
"Karka bari na nuna maka waye asalin Magaji!!"
"Zan so hakan" Jauro ya fadi yana dariya, ci gaba da dukan Aziza mutane suka yi, wani gurnani Baffa ya yi
mai taken muryan zakin dawa, sannan ya rintse ido ya haɗa wani guguwa mai cike da barkono ya kwashi
jama'ar da suke dukan Aziza ya watsar dasu, a take ya yi tsalle daya yaje gabanta yasa hannu ya shafe
igiyar da suka daureta igiyar ta tsinke, sannan Baffa yasa hannu ya shafe mata inda suka ji mata ciwo ya
kamo kafadunta cikin daga murya ya ce
"AZIZAAA!! NA YARDA DA KEEE!! INA SO NE KI BAR YANKIN NAN!! BANA SO SU KASHEKI ALHALI 'YAR
UWARKI TA BAZAMA GARI! INASO KIJE KI NEMOTA SANNAN KI DAKATAR DA ITA,IDAN HAR KU KA HADU
KIKA GA B'ARNARTA YA YI YAWA NA MIKI IZINI KI KASHETA ITA DA BANJU!! IDAN KUMA KE MA TAKI TA
ZO KARSHE DAMA BA ZAMA MUKA ZO YI BA,IDAN KUMA KIN SAMETA KU DAWO! NINA SAN TA INDA
ZANYI MAGANIN BANJU!! AZIZA TAFIIIII!!" girgiza kai Aziza tayi tana wani irin kuka alaman ba zata iya
tafi ta bar Hajja da Baffa ba, rai b'ace Baffa ya kara cewa bar yankin nan na ce Azizaaaa!! da gudu Aziza
ta yankin jeji dan barin yankin kwana, Jauro ya yi yunkurin binta Baffa ya ce
"Kana bin bayanta zan mata umarni ta kasheka! Ka godewa Allah Aziza ce ba Azima ba ce! Da sunanku
gawa gaba daya!! Ni zaku yiwa haka! Sabida su waye yanzu nake fuskartar wannan bala'in!!?"
Cikin gari ya nufa inda ya kaita asibiti mafi kusa, yana shiga ya ce a bata taimakon gaggawa,inda wasu
nurses suka hau masa iskanci a kan ba zasu karbeta ba, hannu yasa a aljinun wandonsa ya ciro wallet
dinsa ya bude ya ciro ID Card dinsa ya nuna musu, suna gani suka hade gefe suna sorry sir, ya ce
78
HAUSACINEMA.COM
"Baku da tausayi ko kaɗan! haka ku ke yiwa jama'a da haka idan yazo da ƙaran kwana sai marar lafiya ya
mutu amma kune sanadi! An san likitoci da tausayi dan haka ku gyara,ina mai wannan asibitin ina son
magana da shi idan har yana kusa" jiki na rawa suka ce bari su nuna masa office din, har bakin kofar
office ɗin suka kaisa, ya kallesu su biyu ya ce
"Ku fara duba yarinyar nan kar ta mutu ina zuwa bari nayi magana da shi zan zo nayi mata dressing da
kaina"
"Ok sir" suka fadi shi kuwa ya shiga ciki da sallama.
Amsawa wanda aka yiwa sallama ya yi, ya kalli wanda ya masa sallamar ya ce
"Bismillah ƙaraso ga waje zauna mana" ƙarasowa ya yi cike da jin kansa ya zauna,sannan ya miƙawa Dr
din hannu suka gaisawa, Dr din ya ce
"Amma ban gane ka ba daga ina? sannan baka yi kama da marar lafiya ba"murmushi ya ɗan yi na gefen
baki, sannan ya miƙa masa ID dinsa,yana dubawa ya kallesa ya ce
"Doctor?" ya yi murmushi yana gya ɗa kai, tashi ya yi da sauri yana fadin
"Allah dai yasa sa'a ce ta sameni har office zaka fara aiki a hospital dina" shi ma tashi ya yi tsayen ya ce
"A'a ko ɗaya wlh,ai ni ba a nan yola nake da zama ba,ina zama a kd ne akwai aikin da ya kawoni ne,tun
jiya ma ya kamata ace na bar yola to ashe tsautsayi ne ya tsayar dani dan na buge wata yarinya ne da
mota shine na kawota asibitin,inaso nayi treatment dinta sai mu wuce dan bana so na ƙara kwana a
garin nan"
"Ya Subhanallah! tana ina yarinyar? muje sai ka dubata ai ba komai"ba tare da ya sake magana ba ya bi
bayan Dr har izuwa dakin da aka kwantar da Aziza, suna shiga ya hau dubata ya ga bata mutu ba, kayan
aiki yace a ba shi ya fadi abubuwan da za a ba sa aka kawo masa sannan ya hau dubata,ya mata su
allurai ya sakawa kanta bandage ya mata komai sannan ya ɗora mata ruwa, ya duba agogon dake daure
a hannunsa ya ga sha ɗaya, ya kalli Dr ya ce
"Tnk u so much Dr on my way" ya faɗi tare da kokarin daukar Aziza, Dr ya ce
"Haba Doctor ka bari mana ko zuwa gobe sai ka wuce idan ta farka,ga shi kace baka santa ba,duk yadda
akayi inaji irin fulanin rugan nan ne, yanzu idan ka wuce da ita kd alhali ba yar kd ɗin ba ce fa?" shuru ya
79
HAUSACINEMA.COM
yi yana nazarin maganarsa kuma gaskiya ne tunda a nan ya sameta miye hujjarsa na tafiya da ita? Kawai
ya barta idan ta farka taji sauki sai su sallameta ta koma inda ta fito, da wannan tunanin ya ce Dr ɗin ya
ba shi acct number ya masa transfer'n kuɗi ya kula da ita idan ta warke sai su sallameta,haka kuwa aka yi
bayan ya masa transfer ɗin nan ya fito da sauri ya shiga mota ya tayar yaja ya bar asibitin, har ya fara
tafiya ya ɗan yi nisa sai yaji hankalinsa bai kwanta ya tafi ya barta ba,ko ba komai shi ya bugeta sannan
bata farfaɗo ba ya tafi ya barta anya ya kyauta kuwa? Saurin juya kan motar ya yi ya koma asibitin, yana
zuwa ya ce a ba shi ita kawai, Dr ya ce
"Haba Doctor baka yarda damu bane?"
"No ba haka bane ba wai ban yarda daku bane,kawai ban yarda da shawaran da zuciyata ta bani bane na
in tafi in barta alhali ban san a wani condition zata farka ba that's why, amma yanzu zan tafi da ita,idan
ta farka lafiya taji sauki zan sa a maidata gidansu" da haka yasa hannu ya dauketa tare da drip ɗin da ya
ɗora mata, har yanzu tana bacci, ya gyara bayan motarsa ya kwantar da ita ya ajiye drip ɗin a gefenta
yana duba agogo tare da auna tym din da ruwan zai ƙare" da sauri yaja motar yanayi yana duba tym.
Horn ta yi a wani madaidaicin gate da sauri gateman ya zo ya buɗe yana zuba mata kirari, hannu ta daga
masa sannan ta danna hancin motar cikin gidan,tana parking ta fito tana fitowa ita kam ma ta manta da
ta saka mutum a bayan both cikin gida ta wuce tun kafin ta shiga take kwalawa Lantana kira, da gudu
wata 'yar dattijuwar mata ta fito ta zube a gabanta ta ce "gani Hajiya Zubaida"
"Oh dan iskanci dama kinaji ina ta faman kwala miki kira amma ba zaki iya amsawa ba sai dai ki wani fito
da mugun gudu sai kace ana gasan tsaren karnuka, ki fa kiyayeni kiyi hankali!, ina Hajiya?"
"Tana ciki"
"Hajiya! Hajiya! Hajiya!" ta hau kwalawa Hajiyan kira.
80
HAUSACINEMA.COM
An ɗau kusan mintuna uku kafin Hajiyar ta fito tana hamma tana matsa ido alamun bacci take yi kiran
Zubaida ne ya tayar da ita
"Zuby me ya faru?"
Zama ta yi tana fadin
"Wlh Hajiya sai na ci uban baban mai aikin nan, kin san wai har da kai karar mu police station wai mun yi
'yarsa duka a bi masa kadi"
"To yanzu ya aka kare?" Hajiya tana tambaya tana zama kusa da inda Zubaidan ta zauna,ta ce
"Na basu kudi nayi gaba abina,kee! Lantana kawo min ruwa mai sanyi" tashi tayi da sauri tana fadin to,
sannan Zubaidan itama ta tashi ta shige wani daki wanda yake nuni da nata ne, kaya ta shiga canzawa ta
ga ko gyara mata dakin ba a yi ba, da sauri ta cire na jikinta ta watsar dan haka dabi'unta yake, ta saka
wani riga iyakarsa guiwarta sannan ta fito tana masifa tana zama
"Haba Hajiya ashe ba a gyara min bedroom dina ba?"
"To Zuby wa zai gyara? Masu aikin duk sun gudu sai Lantana ce kawai ita kuma aiki ya mata yawa" tsaki
ta ja tana shirin faɗin yanzu wa zai gyara mata daki sai ta tuno da ta sa mutum a bayan mota, tashi tayi
da ɗan sauri tana fadin
"Wayyo na manta da wan can bagidajiyar bafulatanan" a haka ta fita riga iya guiwa kai babu ɗan kwali
sai uban attachment, Azima kuwa tana kwance a both a macijiya hankalinta kwance tana bacci, jin kara
ne ya sakata buɗe ido tayi saurin komawa mutum,tana zama mutum tana bude both din ta kalleta a
wulakance ta ce
"Fito" a hankali Azima ta fito tana gyara mayafinta tana tafiya tana lankwasa kamar yadda take tafiya a
yankin kwana.
Shiga parlourn sukayi, Zuby ta ce
"Hajiya naji dama kina neman mai aiki to gata nan, a hanya na tsinceta, sai ta ɗora da aikin da Kuluwa ke
yi" Hajiya ta kalleta tana toshe hanci ta ce
"Ya sunanki?"
81
HAUSACINEMA.COM
"AZIMAA!" ta faɗa da kaushin murya dan duk tana kula da yatsine fuska da toshe hancin da Hajiya ke yi.
"To dubu biyar zamu dinga baki a duk wata, zaki dinga share-share da goge-goge,inada yara guda uku, ga
Zuby nan akwai Yayarta mai suna Baby sai kuma Babban ɗana namiji yayansu kenan, sunansa Munir dik
basu nan sun fita idan suka dawo zaki gansu, ke ce zaki dinga gyara musu bedroom dinsu!" Azima dake
duƙe ta ce
"Hajiya miye shi badorom din?" Zuby ta ce
"Hajiya ƙidahuma ce daga jeji take taya zaki mata turanci,keee Bagidajiya ana nufin daki,nasan bukka ku
ke kira a can jejinku" cije baki Azima ta sake yi, jin yadda zuciyarta ke tafasa idan bata tashi ba komai zai
iya faruwa,hannunta ta kalla ta ga ya fara sab'ulewa yana zama blue saurin ajiyar zuciya ta koma yi dan
zuciyarta ta yi sanyi, Zuby ce ta sake kwalawa Lantana kira ta amsa da ta zo tace mata ta tafi da Azima ta
nuna mata yadda zata yi wanka ta bata wasu kaya da turare dan Azima na wari,sannan idan ta nuna
mata ta taho ta saka musu turaren wuta, Lantana ta amsa tana kamo Hannun Azima suka shige daki,
suna shiga Hajiya ta ce
"To ita haka zata dinga rufewa mutane fuska a gida?"
"Hajiya manta da wannan kin san bata taba shigowa birni ba,dan haka bata waye ba"
"Kuma hakane fa" cewar Hajiya, Zuby ta ce
"Wai ina Munir da Baby suka je ne?"
"Wa ya san musu" share zan can suka yi suka kamo wata hirar,da Lantana suka shiga daki ta kalli Azima
ta ce
"Baiwar Allah zauna ki jirani kinji bari naje na saka musu tiraren na dawo" ta fita da sauri, buɗe ido
Azima tayi tana fadin
"Babu wanda ya isa ya zageni ya tafi a banza ba tare da nayi masa hukunci ba! Babu shi!" ta faɗa tana
lankwasa yatsun hannunta, an dauki mintuna sha biyar kafin Lantana ta shigo, ta ce
"Azima ko?" Azima ta sunkuyar da kai tana fadin
"E" a sanyaye kaman wata ta kwarai, Lantana ta kama hannunta suka shiga bayi,ta haɗa mata ruwan
wanka ta dauko soso da sabulu da shampoo dan ta ga tana da ga shi mai tsayi, ta ce
"Na wanke miki kan naki naga gashin naki da tsayi sosai" Azima ta gyaɗa kai, Lantana ta bata fallan zani
ta ce ta cire na jikinta ta ɗora, ba musu Azima ta cire kayanta ta ɗora fallan zani lantana ta jiƙa mata
82
HAUSACINEMA.COM
kayan a ruwa tace zata wanke mata su, sannan ta bata kujera ta zauna, Lantana na fara kwashe gashin
Azima tayi saurin lumshe ido dan bata son Lantana ta ga kwayar idonta.
Shampoo sosai Lantana ta zuba a kan Azima amma ta ga idan har ta juye ba isa wanke mata kai zaiyi ba,
haka yasa ta dauke ledar omo sai da ta zuba ya kai kwankwani ɗaya da rabi kafin ta fara dirzan kai Azima
wanda yake fitar da datti, sun kai mintuna talatin tana wanke mata kai kafin gashin ya fito baƙi da shi ga
tsamtsi yayi fess!Lantana ta yi murmushi ta ce
"To kiyi wanka,bari na baki waje" har Lantana ta kai bakin kofa sai ji tayi Azima na faɗin
"Miyatti Inna" karo na farko da ta fara yima wani ɗan adam godiya a rayuwarta, murmushi Lantana ta yi
ta fice, sai a lokacin tunanin 'yan yankin kwana ya faɗowa Azima a rai,dariya ta hau yi tana fadin
"Ko ina Macijiya Aziza sarkin tausayi oho! Watakila sakaran tana can an kasheta a jeji! Ko da yake ba
zasu iya kasheta ba! Amma nasan shanuwar tana can suna jibgarta" ta karasa maganar tana haɗe rai,
wanka ta yi sosai ta dirje jikinta ta fito, sai da jikinta ya bushe ta kuma saukowa da gashin kanta kafin ta
fito ta samu Lantana ta ajiye mata fallan zani da t-shart da su mai da turare, kayan ta saka, sannan ta
dauki kum ta sharce gashin kanta ta zubo da wanda yake rufe masu gefen fuska sabida kar ana ganin
kwayar idonsu, gashin ya sauko har ƙirjinta, kallon kanta ta yi a madubi ta ga ta yi kyau,murmushi ta yi,
sai ga Lantana ta shigo
"Wa Subhanallahi bi'ahsanul Khaliƙin!" cewar Lantana Azima ta sunkuyar da kai, Lantana ta ce
"Zo muje na nuna miki ayyukanki" Azima ba ta kuma magana ba ta bi Lantana a baya, nunnuna mata
komai Lantana ta yi har da dakin Baby da dakin Munir, Azima ta ce ta gane, sannan Lantana ta ce
"Yanzu ki fara gyara dakin Munir dan bai da mutunci ko kaɗan duk wulakanci Baby da Zuby suna bin
bayan Munir ne, idan ya dawo ba a gyara masa daki ba ya ganki bazaiyi la'akari da cewa ke sabuwar
zuwa bace ya yi ta kwallo dake"
"DA KUWA KO ƘASHINSA BA ZAN RAGE BA!" Lantana ta ce
"Iyeeee!!?" sauri saita kanta Azima ta yi ta ce
"Inna je ki kawai zan gyara yanzu" fita Lantana ta yi,Lantana na fita Azima ta bi lafiyar gado ta kwanta
dan tayi wanka mai dadin da bata bata yi ba taji bacci takeji.
83
HAUSACINEMA.COM
Karfe sha daya saura ya shigo kd bai wuce gida ba ya wuce asibitinsa da ita, har yanzu kuma bata farka
ba,bai damu ba tunda ya mata alluran bacci mai karfi ne, bayan ya mata komai ya ba wasu nurse mutum
biyu kula da ita wanda zasu yi nyt duty, kafin ya wuce gida.
A wani katafaren gate yayi horn da sauri aka zo aka buɗe masa, ya shiga ya yi parking din motarsa, da
fari ji ya yi kamar ya shige part dinsa dan ya gaji,amma kuma gwanda ya shiga ya yiwa Mom sai da safe,
da wannan tunani ya yi babbar parlon nasu da sallama,kanwarsa Sultana tana zaune wacce ba zata wuce
18 ba tana kallon wani horror seris film tana jin sallama ta miƙe da gudu tana fadin
"Oyoyoo BROS NAWAZZ!"
Saurin juyowa Azima ta yi ba tare da ta dago ba
Ya yi murmushi ya CE
"Yan mata magana nakeyi fa" da saurita matsa gefe ta hau tafiya tana sake rufe fuskarta, shi kuwa binta
ya hauyi yana kan yi mata magana,da ya ga ba zata tsaya ba ya sha gabanta, cije bakiAzima ta yi tana
hade rai,babu abunda ta tsana kamar a sha gabanta,Cikin murya da yake nuna taji haushin takura mata
da yayi tace
"Malam wai lafiya?"
Dariya ya hau yi jin yadda kalar Hausarta ta ke fita, a ransa yake fadin "wow! Wannan daga ganinta
bagidajiya ce daga jeji take,bari nayi mata wayo, ko Allah zai sa na shana da ita daga dawowata!"