Showing 33001 words to 36000 words out of 94205 words

Chapter 12 - Azima-Da-Aziza-Macizai Ne Complete

20 Jul 2024

37841

ya sauke duk wata baiwa tasa ya binne bayan yasha wahalan kama aljanu da mayu ya kullesu!! Ya
sauka ne a kan matsayinsa da yake da shi bayan ya kashe Banju! Amma har kwanan gobe! kai ba ma
kwanan gobe kawai ba! HAR GABAN ABADA BABU WANI GARKUWAN FULANIN YANKIN KWANA SAMA
DA MAGAJI! SANNAN BABU WANI MAI MAGANI SAMA DA MAGAJI! Har ta Garkuwan fulanin yankin
kwana na yanzu da Magaji yake tunkaho"

Garkuwan fulanin kwana na yanzu ya fito ya ce

"Tabbas hakane, da taimakon Magaji Bawa na zama Garkuwan fulanin kwana shi ya maidani mutum,
gaskiya baku kyauta ba" wasu ne jikinsu ya fara sanyi ganin haka yasa Jauro ƙara tattaro sauran
munafurcinsa dan shi baya so ace mutane su banzartar da maganarsa idan ba haka ba ba zai cika burinsa
ba,baya so yaji sunan Magaji na daukaka! yafi so duk yankuna yadda ake kiran sunan Magaji Bawa!
Magaji Bawa! ya kasance shi Jauro Mai Maganin yankin kwana shi ake kira ba wani Magaji Bawa ba, ace
shine shahararsa ta kai inda yake so kuma yake bukata, saurin cewa ya yi

"Babu wani borin kunyar da za ayiwa mutane an dai cutar dasu! Wa inda aka kashe musu yara su ce
mai? Sannan tunda daɗewa Magaji yasan yaransa Macizai ne amma ya boyewa mutane bai gaya musu
dan yanzu yana da mugun nufi a ransa!"

"Magaji baya da masaniya a kan cewa AZIMA DA AZIZA MACIZAI NE taya idan ya sani har zai barsu su yi
kisan kai!? Da kake maganar su na kisa Aziza bata taba kisa ba,akasari ma ita dabi'un Magaji ne tattare
da ita, ku a tsammaninku da Azima ce har kwa fara yi mata abunda ku ka yiwa Aziza? Inaaa! Da kafin mu
iso wlh sai dai gawawwakinku!" cewar Baffa Mandi, jauro ya ce

"Owoohh! Kenan da saninku ma kamar yadda na faɗa! Jama'a kuna dai ji ko? An zalinceku an
munafurceku an kashe muku! Kuma ta yadda zaku gane Magaji ya san yaransa Macizai ne shine basu
zuwa bikin gargajiya ta al'adun fulani wanda ake gabatarwa duk shekara, sabida sun san a lokacin ana
amfanin da magungunan macizai! Sannan......"

"Ya isheka haka Jauro!!" Baffa ya katse Jauro jikinsa na rawa, ya tako ya zo gabansa ya ce



72
HAUSACINEMA.COM


"Da ace da sanina yarana macizai ne da tuni na dauki mataki wani zancan 7ake yi yanzu ba wannan ba, a
da nace maka muddun ka gano yarana macizai ne nina maka lamuni ka kashesu! Amma tunda na gano
cewa ku ɗin ba mutane bane dabbobi ne wanda shanu ma sun fiku hankali ko da Azima da Aziza sun
dawo yankin kwana duk wanda ya yi gigin taba min yara a lokacin zan basu umarni su kashe min koma
waye!! Sannan ka zuba ido ka gani, zan maida yarana mutane ko da kuwa hakan zaiyi sanadiyar
mutuwata, a yau kuna zaginsu macizai kuna ci min mutunci, amma ku sani ko nace kai jauro ko sani,
MAGAJI BAWA KAFIN ALLAH NE BA KAFIN MUTUM BA! KO DA ACE MISALI BANA RAYE! AZIMA DA AZIZA
SAI SUNANSU YA BUGA TAMBARI A YANKUNA BA MA IYAKAR YANKIN KWANA BA! KAMAR YADDA NA
MAHAIFINSU NI MAGAJI BAWA NAYI! NA MAKA WANNAN ALKAWARI! BAIWA DA FARIN JININMU DAGA
ALLAH NE KA ZUBA IDO KA GANI JAURO!!!" Baffa na gama faɗi ya bar wajan tare da daukar Hajja suka yi
gida yana tunanin tashin hankalin da Hajja zata farka da shi, da fari yara macizai yanzu kuma babu su ma
kwata-kwata, amma ya zata yi dole su rungumi kaddara.

Bayan Baffa ya bar wajan Sarki Chubaɗo ya kalli Jauro ya ce

"Ka dai ji kunya wlh! Da ace nima tsoron kar nayi abun kunya ba wlh da yau a yanzu na koreka daga
yankin kwana, ku kuma idan dai Jauro ne gaku ga shi,in dai ba a mutu ba to ba shakka ba a daina kallo
ba, ba fata nake muku ba amma na tabbata akwai jarabawa,sannan Allah ba azzalumin bawansa bane,
duk wani abunda ya sameku karku sake kuce zakuje wajan Magaji ya taimaka muku! kuje wajan Jauro ya
taimaka muku, wannan umarnina ne a matsayina na sarkin wannan yankin!! Idan kuma na ga akasin
abunda nace mutum zai fuskanci mugun hukunci!" Chubaɗo na gama faɗi ya yi gaba ya bar su a tsaye a
wajan, wasu jikinsu yayi sanyi inda nadama ta kamasu wasu kuwa zuciyarsu kamar busashshen itace!.

Azima kwananta biyu tana tafiya kafin ta fito bakin titi, tana fitowa wani guɗa ta yi da dogon harshenta,
duniya sabuwa! Tana nan tsaye a kan titi da lullubi tana tunanin hanyar da zata fara dosa, nan ta yanke

shawara kawai ta bi dogon titi ta ga iyakar karewarsa, haka ta hau tafiya a tsakiyar titi tana murmushi,
kamar daga sama sai ga wani mota ta yanko da gudu amma sai ganin yarinya ya yi tana tafiya akan titi
sai horn yake danna mata amma a banza! Azima kuwa tunda farkon fitowarta kenan ba fahimta tayi ba,
da kyar mutumin ya taka burki ya fito a motar gami da daka mata tsawa "keeeeeeee!!" wani tsayuwa
Azima tayi tare da ware blue eye dinta, babu wanda ya taba mata irin wannan ihun, a hankali ta kara jan
mayafinta ta rufe fuska sannan ta juya a hankali kanta a duke, mutumin kallon sama da kasa ya mata
yana yatsine fuska dan ya ganta da shigar fulani ba mamaki irin kidahuman nan ne na jeji dan haka cikin
izgilanci ya hau ta da zagi.

"Ke wace iriyar bagidajiya ce da ana miki horn amma da shike kin fito a cikin jeji baki ganewa
kwakwalwarki a toshe yake kina tafiya a kan titi banza ballagaza daƙiƙiya ƙidahuma tunkiya!!" hakika
zagin ya soki zuciyar Azima, zaro ido ta yi tare da yaye mayafinta rai b'ace cikin hausar da babu sosai a
kan harshenta ta ce

"Ba dai tunkiya ba, sai dai MACIJIYA!" ta faɗi tare da komawa macijiya ba ta jira ya gama firgita ba ta kai
masa sara a wuya nan ya fadi kasa yana shure-shure,komawa mutum ta yi tana dariya ta ce



73
HAUSACINEMA.COM


"Kaina mutum na farko da na fara kashewa daga fitowata,hakan na nufin cewa zan sha jini da yawa
kenan sabida mutanen cikin gari basu da ɗa'a,ni kuwa AZIMA MACIJIYA bana daukar wargi!" ta faɗi tana
murmushin gefen baki ta leƙa cikin motar ta wargaza ta ga kuɗi ta kwashe duk da bata san amfanin me
zasu mata ba, ta ci gaba da tafiya, ta yi tafiya sosai inda ta iske tasha wanda yake cike yake da jama'a a
hankali ta ƙutsa kanta cikinsu tana ji ana ambatar sunayen garurruka, garin da taji ya mata masauki a
kunneta shine KANO TUMBIN GIWA KO DA MAI KA ZO AN FIKA! murmushi ta yi ta kara nanata
KANOranta, sannan ta afka mota ta nemi can baya ta zauna tana murmushi yau burinta ya cika ta bar
yankin kwana.

Kuɗi aka fara karba aka zo kanta, ana cewa kawo kuɗinki nan kuwa ta cire ta miƙa ba tare da tayi
magana ba ko tasan nawa ta bayar ba,duk da zuciyarta na raya mata da sun isa kanon da zasuje
zatakashe mutanen da suke motar!.

Bayan yan wani lokaci ƙalilan mota ta tashi daga tasha ta hau tafiya, inda Azima ta ji ta gaji dan gani take
yi motar bata mata sauri,amma ance biyan bukata yafi dogon buri dan haka ta kara rungume hakuri.

Basu da isa kano ba kuwa sai magriba, ganin tsananin girma da faɗi da cikowa irin na garin kano yasa taji
ma ta fasa kashe mutanen da tayi niyyar kashesu, ta shagala da kalle-kalle ta ji ana mata magana ta
bayanta

"Barka dai 'yar fulani"

Ko da Salti ya isa gida ya kwashe kaff yadda yaji su Sarki Chubaɗo da mai Unguwa Ori suka tattauna ya
gayawa Baffansa, a hankali Jauro ya mike yana murmushi ya ce

"Salti,tun da kake kwaso gulma baka taba kwaso mai amfani ba sai yau, jeka dole nayi maka kyautar
shanuwa daya" da sauri Salti ya miƙe yana murna ya fice,Jauro ya dungule hannu yana dukar iska ya ce

"Lokaci ya yi da zan fatattaki Magaji Bawa, ka fi ni a komai kyau,martaba,baiwa,kyakkyawar mata
Jumala,ga kuma yara kyawawa! kai kana gani ka fi kowa ne! zargin da nake yiwa yaranka ya tabbata,
wato ma har b'oye-b'oye ake yiwa mutane ana munafurtarsu kar a gaya musu gaskiya, to ni nan zan
bayyanawa jama'a su waye Azima da Aziza!" ya faɗa yana murmushin mugunta.




Kamar yadda Malam Shadi ya faɗa da daddare ne ya yi bincike mai zurfi dangane da matsalar su Azima
da Aziza,inda ya hangi gagaramin matsala mai rikitarwa inda tausayin yaran ya kamasa dan kuwa da
wuya a samu maganin warakarsu.

Da washe gari bayan sun idar da sallar asuba ana gaggaisawa bayan sun gama gaisawa Malam Shadi ya
kalli Baffa sai kuma ya duƙar da kai, Baffa ya yi murmushin yaƙe wanda yafi kuka ciwo ya ce




74
HAUSACINEMA.COM


"Malam Shadi karkiji komai gaya min ko ma miye ne,ni musulmi ne kuma nayi imani da kaddara mai
kyau da marar kyau, ka gaya min kawai"

Jinjina kai Malam Shadi ya yi ya ce

"Tabbas ni shaidan hakane Magaji, wato a gaskiya ba zan boye maka ba, samun lafiyar Aziza yana tattare
ne da Azima, domin kuwa wanda yake da alhakin abun ya ja Azima basu yankin kwana balle a musu
magani, kai ko da Azima bata bar yankin kwana ba da wuya a samu wanda zai yi jahadin taimaka musu"
goge gumi Baffa ya yi ya ce

"Malam Shadi ka gaya min kai tsaye kawai zan fi ganewa,dan a yanzu ji nake kamar kirjina zai tsage
zuciyata ta faɗo kasa"

Malam Shadi ya gyara zama ya ce

"Dole sai sunyi aure kafin Banju ya rabu dasu, barin ma Azima ita ce wacce take bukatar taimakon
gaggawa, sannan wannan miji da zai auresu sai ya sadu da Azima kafin Banju ya fita a jikin Azima, idan
Banju ya bar jikin Azima a cikin kaso dari mun yaƙesa kaso sittin, idan aka yi sa'a idan Banju ya fita a jikin
Azima, Aziza zata iya samun lafiya,idan kuma bata samu ba ita ma dole sai wanda ya aureta ya kusanceta
kafin makarin sihirin da Banju ya mata na siddabarun maidata macijiya ya karya"

"Ma'asabamun musibatin Qalu Innalillahi wa inna ilaihirrajiun! Innallahi wa inna ilaihirrajiun! Innalillahi
wa inna ilaihirrajiun!" shine abunda Baffa da Baffa Mandi da Arɗo suke iya nanatawa suna fifita da
hannunsu,Arɗo ya girgiza kai ya ce

"Tabdijam kawai Allah ya jikan Azima da Aziza, dan kuwa na tabbata babu namijin da zaiji cewa su
macizai ne ya taimaka ya auresu har mu sa ran zasu samu lafiya"

"Kuma dole wanda zai aure su zai fuskanci ƙalubale kafin ya kusancesu,sannan bayan ya kusancesu zai
iya kamuwa da mugun ciwo amma ba ina nufin ba zai warke ba amma tabbas zaiji a jikinsa,idan an samu
damar hakan zaka iya kara kashe Banju a karo na biyu" hawaye ne Baffa ya hau yi yana kan tasbihi ga
Ubangijin talikai, Baffa ya ce

"Tabbas da ace na dinga ganin tashin hankalin nan na b'arna da ta'adin da Azima ke yi da ni da kaina zan
kasheta! to amma yanzu tana ina? Me take yi? Su wa da wa zata kashe!? Akwai tambayoyi dayawa a
raina wanda babu wanda zai amsamin" Baffa ya hau kuka Arɗo da Baffa Mandi suna rarrashinsa, Baffa
Mandi ya kalli Malam Shadi ya ce

"Malam Shadi, yanzu ya maganar raba Aziza da Bahula?"

"A gaskiya Mandi ni a ganina a shawarce, kar a raba Aziza da Bahula, tinda bata cutar da ita, sannan ko
an raba Aziza da Bahula Aziza fa ba zata taba komawa mutum ba, ni a ganina tunda Banju yana son



75
HAUSACINEMA.COM


kanwarsa Bahula sannan yasan cewa tana rayuwa a jikin Aziza dole wata rana zai dawo, karku manta
kamar yadda Azima da Aziza suke 'yan biyu haka ma Banju da Bahula suke 'yan biyu, zamu iya samun
dawowa da Azima gida ta hanyar Bahula dake jikin Aziza,ni a ganina kar a raba Aziza da Bahula a barsu
tare idan ya so aka samu wanda zai yi jahadin aurensu bayan an raba Azima da Banju sai a raba Aziza da
Bahula"

"Tashin hankali wanda ba a sa masa rana" cewar Arɗo yana kan rarrashin Baffa dake kuka wi-wi, da kyar
suka rarrashi Baffa ya samu ya tsaida hawayen idonsa sannan ya miƙe yana yiwa Malam Shadi godiya ya
ce masa zasu wuce yau, Malam Shadi ya ce

"Ba damuwa Magaji,karka damu Allah zai shiga cikin lamarin" Baffa bai iya ya kara cewa kala ba, Malam
Shadi ya miƙa masa wani ganyen magani ya ce

"Wannan idan ka je ka haɗawa Aziza,ita kuma Azima Allah ya dawo da ita cikin gaggawa, bari nasa a kira
muku Azizan sai ku wuce" su Baffa Mandi da Arɗo suka yiwa Malam Shadi Godiya sannan suka fito a
tare,bayan an kira Aziza ta fito Baffa ya kama hannunta idonsa jajur ya ɗorata a kan doki, Aziza tunda ta
ga yanayin Baffanta tasan cewa kwai gagarumin matsala, haka sukayi sallama da Malam shadi cikin
amince suka kama hanyar yankin kwana.

Sai da lokacin sallar azahar ya gauta kafin suka iso yankin kwana kai tsaye gidan Arɗo suka nufa, Hajja na
zaune tayi zugum Yawuro ta ajiye mata kwaryan nono a gabanta amma haka nonon ke kallonta, Yawuro
ke fadin

"Haba Jumala! Dan Allah ki sa wani abu a cikinki mana, ga jikinki da zafi, kiyi hakuri mana haba dan
Allah" hawaye Hajja ta goge ba tare da ta cewa Yawuro Uffan ba, sallamarsu Baffa ne yasa Hajja ta dago
da sauri ta sauke idonta a kan Aziza da ta shigo kanta a sunkuye, duk irin kunya na Hajja amma da sauri
ta tashi ta rungume Aziza wacce itama ta saki kuka take ji a ranta da ace kisan kai ba haramun bane babu
abinda zai hanata bata sha guba ta kashe kanta ba, kuka sukeyi sosai sai da Inna wuro ta dakatar dasu,
sannan Inna wuro ta hau tambayarsu ya suka yi a can yankin ja'o ɗin, Baffa Mandi ya ce "babu amfanin a
boye muku, gwara a gaya muku gaskiya" Ardo ya ce "tabbas dan wannan ba abun boyewa bane" nan
Arɗo ya kwashe yadda suka yi da Malam Shadi ya gaya musu, wani mahaukacin zare ido Aziza ta yi jin
bala'in da suke ciki wai sai sunyi aure an sadu dasu kafin su warke! Wa ma zai auri macizai!? Barin ma
wanda zai auri Azima ya ji labarin kisan da Banju ya yi tayi a jikinta ai ma babu mai aurensu,in kuwa dole
sai hakane sun zama annoba a cikin jama'a barin ma yanzu da Azima bata nan.

Sallallami su Inna wuro da Yawuro suke yi suna tafa hannuwa yayinda Hajja ke girgiza kai tana fadin ita a
maido mata da yaranta tana wani irin kuka, Arɗo da Baffa Mandi suka ce Baffa yazo su je wajan Sarki
Chubado da mai Unguwa Ori su gaya musu halin da ake ciki,a tare suka fita aka bar Hajja da kuka ita da
Aziza, su Inna Wuro suna rarrashinsu.

Bayani dalla-dalla suka yiwa su Sarki Chubaɗo da mai unguwa Ori yadda Malam Shadi ya shaida musu,
Sarki Chubado ya ce



76
HAUSACINEMA.COM


"Tashin hankali, gaskiya Banju ya mana illa dayawa, amma ina da shawara mai zai hana a gayawa
mutanen gari halin da ake ciki, idan ya so sai a nemi wanda zai auresu ko da ba zai zauna dasu ba dai da
sun samu lafiya sai ya sake su!"




"Nima na fara wannan tunanin a raina ranka ya dade,amma abun dubawan a nan shine wa zai auresu?"
cewar mai unguwa Ori, tattaunawa suke yi sosai ta yadda za a shawo kan matsalar amma duk inda aka
dafa babu mafita, su na nan suna kan shawara sai ga Sanda da mugun gudu kamar wanda yake gudu a
iska yana zuwa gabansu sarki Chubaɗo ya zube yana haki, Sanda jika ne ga Yawuro, Arɗo ya ce

"Sanda mahaukacin ina ne kai? Wannan gudu da ka zo a haka sai kace an kawo mana farmakin yaƙi miye
haka? Meke faruwa?" kasa magana Sanda ya yi illa hanyar gida da yake nunawa da kyar ya furta "ADDA
AZIZAAA!!" da sauri Baffa ya ce

"Me ya samu Azizan?" ya fada yana miƙewa tsaye, Sanda ya ce

"Baffa Jauro ne ya gayyo duka mutanen yankin nan wai zasu kashe Adda Azima da Adda Aziza wai
macizai ne sune suka dinga kashe-kashe sune suka kashe su Ilu mai maganin Maciji dasu Jarman Macizai
da Innu Maciji, yanzu haka ma sun saka wuta a gidan Arɗo ƙarami" da sauri su Chubado suka miƙe suna
salati tare da al'ajabin ina Jauro yaji wannan maganar? Baffa Mandi ya ce

"Kafff yankin kwana da kewayenta babu munafuki sarkin gulma sama da ɗan Jauro Salti, to amma taya
akayi ya ji wannan maganar?" Sarki Chubaɗo ya ce

"Yanzu babu lokaci maida magana muje kar su kashe Aziza" da gudu Baffa ya yi gaba idonsa har yana
rufewa, ya rasa matsalar dake tsakaninsa da Jauro,bai san me ya tarewa Jauro ba a rayuwa da baya
sonsa baya kaunarsa sam.




Ko da su Baffa suka isa, sun samu gidan Arɗo karami na ci da wuta, ga Hajja a sheme a kasa an fasa mata
kai, Aziza kuwa sun ɗaureta a jikin bishiya sai dukanta suke yi duk sun fasa mata jiki, a ranta take kalman
shahada dama su kasheta kawai ta huta da wannan rayuwar, ihuuu Baffa ya yi ganin matarsa kwance a
sheme a kasa an fasa mata kai ga 'yarsa da aka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login