Showing 66001 words to 69000 words out of 94205 words

Chapter 23 - Azima-Da-Aziza-Macizai Ne Complete

20 Jul 2024

37850

153
HAUSACINEMA.COM


"Nawaz labarin Azima da Aziza da baffansu da kauyensu abun tausayi ne mai cike da zallar al'ajabi" cikin
taushin murya Mom ta hau zayyanawa Nawaz labarin Aziza bata boye masa komai ba kamar yadda Aziza
ta ba su haka ta bai wa Nawaz, mom tana gama ba shi labarin ya dago yana fadin

"Wlh mom yawancinabun da kika faɗa min ina ganinsa a mafarkina, tun ranar da na bugeta a mota na
kawota kaduna tun daga ranar na daina bacci kirki,mom ina yawan ganinta a siffar macijiya tana kuka
tana neman taimakona!" jinjina kai Mom tayi ta ce

"Ba mu san me Ubangiji ya boye tsakaninka da Aziza ba Nawaz, amma inaso muyi wani jahadi wana
Allah ya zama silar shigarmu aljanna, Nawaz har zuciyata ina jin Aziza,yarinya ce mai hankali da natsuwa
da sanin ya kamata duk da tana da kananun shekaru amma tana da hankalin manya da imani da kaddara
ga tawakkali da miƙa wuya,kuma dama abunda akeso kenan ga musulmi mumini ko mumina, Nawaz
sultana zata bar gidan nan kwanan nan, dan Allah ina so kayi jahadi ka AURI AZIZA!!" dummm!! gaban
Nawaz ya bada ya kalli Mom da sauri, Mom ta gya ɗa kai tana fadin

"Tun kana yaro ban taba cewa ina neman alfarma ka kasa min ba, ina so ka taimaka ka auri Aziza, ka
zamo silar warkewarta, duk wanda ya zama silar farin cikin mutum daya Allah zai zama silar farincikinsa
a ranar da babu wani mai gata sai fiyayyen halitta, Nawaz kana da ilmi duk abunda zan gaya maka ka
sani sai dai na kara yi maka tuni, idan ka auri Aziza ka zamo silar warkewarta hakika zaka saka mutane
dayawa ne farinciki, zaka fidda UWA da UBA daga ƙunci, da sauran yan uwansu, wlh har zuciyata na
aminta" kallo fuskar Aziza Nawaz ya yi, hakika daga fuskarta zaka san cewa tana jin jiki

"NA AMINCE MOM! ZAN AURETA!" da sauri Sultana tazo ta duƙa ta rungumesa cikin murna, "da gaske
yaya zaka aureta!? Wayyo dadi wlh nayi farinciki"

"Allah ya maka albarka Nawaz" cewarmom tana shafa kansa.




Nan suka zauna a dakin har sai da aka yi sallar la'asar kafin suka fita da niyyar sallah, nawaz msallaci yaje,
bayan sun idar ya jima yana kwararo adduoi a kan wannan lamari da yake gani tamkar a mafarkin da ya
saba ne.




Bayan ya dawo part dinsa ya wuce, ya dauki wayarsa ya ga miss calls din amininsa,kiransa ya yi ya daga
yana tambayarsa ya jikinsa,Nawaz ya amsa da sauki shima yana masa ya gajiyar hanya, Al'mazeen ya
amsa da alhamdulillah ya kara da fadin ya jikin Aziza, alhamdulillah Nawaz ya fada, sun ɗan jima suna



154
HAUSACINEMA.COM


magana inda Nawaz yake ji ko ya gayawa Al'mazeen? Daga baya kuma ya fasa har suka gama wayar
sukayi sallama.




Sai wajan shidda Aziza ta farka sultana ta taimaka mata tayi alwala tayi sallah a zaune kamar dazu, bayan
ta idar tayi addua sultana ke gaya mata sadda ta suma mom ta gayawa Yaya Nawaz komai, a lokacin da
sultana ke gayawa Aziza Nawaz sun shigo shi da mom, kuka Aziza ta saka tana fadin

"Shikenan zai koreni! Dan Allah Anty Sultana ki ba shi hakuri kar ya koreni, wlh da na samu Azima zan
tafi da kaina,tafiya na har abada ba zai sake ganina ba in sha Allah" rasss! gaban Nawaz ya buga jin tace
zata tafi na har abada, a hankali Nawaz ya juya ya fita ganinyadda take kukan duk sai yaji babu dadi yana
danasanin abunda ya mata, tayi mugun karya masa zuciya.




Mom tace

"Injiwa yace zai koreki a gidan nan? Bana so na ƙara ji kince zaki bar gidan nan na har abada, dan kuwa
kina nan a gidan nan har abada In sha Allah,kinji ko?" Aziza ta gya ɗa kai tana kuka.




Da washe gari tana kwance tana fama da kanta,bata san ta yadda zata samu furen huriri ba, da ace ta
samu da tuni an wuce wajan, turo kofar akayi da sallama, jin muryan mai sallaman yasa gaban Aziza
bugawa, murya na rawa ta amsa, karasowa yayi a hankali ta dago idonta ta kallesa a tsorace, ta gansa da
plate a hannu, mamaki ne ya kamata, zama yayi a gefen bedside'drower fuskar yau da sassauci, murya a
can kasa ya ce

"Ya jikin naki?"




155
HAUSACINEMA.COM


"Alhamdulillah, ina kwana?"

"Tashi kici abinci ki sha wannan rubutun, wani babban aminin Daddyna ne malami ne wajansa naje jiya
da daddare na masa bayani a kan matsalarki, yace na baki wannan zakiji dama-dama duk da ba lallai
bane ya dauke miki abunda kike ji gabadaya ba, amma zakisamu karfin jiki" mamaki ne ya ƙara kamata,
amma bata da lokacin tsayawa mamakin, a hankali ya dagata ya jinginata da pillow, ya dau spoon ya ɗibi
abincin ya kai mata shi saitin bakinta, tsananin mamaki ya hana Aziza buɗe baki taci dan ji take kamar
mafarki takeyi, ganin yadda jikinta ke rawa yasa Nawaz furta kalman

"I'm sorry Aziza" a sanyaye, sake yin ƙasa da kanta Aziza tayi gabanta na ci gaba da bugawa, muryarsa
taji yana kara fadin

"Na sani, na cusa miki tsorona a zuciyarki, am sorry once again" kuka ta fashewa da shi, ya ɗan rintse ido
ya ce

"Kamar na gaya miki bana son kuka ko?" ta gya ɗa kai

"To meyasa kikeyi?"

"Na...ba...ri" ta fada murya na rawa,

"To kici abincin" ya fada yana bata a baki cike da tausayinta, bata wani ci sosai ba ta ce masa ta koshi,
cup ya dauka ya tsiyaya mata rubutun ya bata tasha tana sha taji kanta na wani mugun juyawa, ba
jimawa ta zube ta hau bacci, ganin tayi bacci yasaka shi tashi ya fita,a parlour ya samu Mom da sultana,
zama ya yi kusa da mom, ta ce

"Allah ya maka albarka Nawaz, Allah ya faranta maka duniya da lahira" a tare suka amsa da amin shi da
sultana.




Ko da ta farka taji jikin nata da dama-dama,dan kuwa ta miƙe da kafafunta har tana iya tafiya, jirin ne dai
bai daina dibarta ba.




156
HAUSACINEMA.COM




Bayan kwana biyu taji sauki alhamdulillah amma lokaci zuwa lokaci jiri na zubar da ita, tsakaninta da
Nawaz kuma yanzu babu tsangwama, sai tausayawa, har mamakinsa take yi,ita dai ba zata gushe ba tana
yiwa su mom addua.




Bayan sati daya da dawowar Al'mazeen kano komai ya canza a gidan, Azima ke zuba mulki son ranta, ga
shi yanzu tana kwatowa Al'mazeen yancinsa a cikin gidan, duk wani guba da maganin mallaka idan aka
zuba masa a cikin abinci sai dai azo a samu Azima ta juyewa karnuka abincin, su Hajiya Lawiza da Hajiya
Luba sun rasa yadda zasuyi da Azima, ta bangaren Al'mazeen kuwa a sati ɗayan nan kacal ya shaƙu
matuƙa da Azima dan har zuciyarsa yake jinta, shi mutum ne mai son kulawa da soyayya amma bai samu
ba, sai ga shi rana tsaka ya samu a wajan mai aiki dan ba karamin kulawa da shi Azima ke yi ba.




Kamar yadda Azima bata son dogon magana haka ma al'mazeen, amma su kan zauna suyi hira, inda take
gaya masa ai itama bata da kowa duk an kashesu, idan Azima na magana ya kan ji muryan Aziza, duk da
ba wai ya taba ganin fuskokinsu sosai bane, dan itama Azima duk shaƙuwan nan bata buɗe fuskarta,
bayan dawowarsa da kwana uku taso guduwa ta bar gidan amma haka ta kasa har ya kai sati daya,inda
takeji kafafunta sunki amincewa da barin gidan.




Yau ma kamar kullum ya shirya zai tafi asibiti, yana kan saukowa kasa har ya zo step din karshe sai ga
Hanan, tana ganinsa sarai ta bangajesa briefcase dinsa ta faɗi, amadadin ta tsaya ta ba shi hakuri sai
tana shirin rab'awa ta gefensa ta wuce, Al'mazeen cikin haushi ya ce

"Kee Hanan! Baki ga abunda kika min bane! Zo ki dau jakata ki bani"

"Wlh Al'mazeen sauri nake yi inaso naje na gwada wannan memoryn ne" ta faɗa tana shirin hawa sama
taji an wani fizgota ta baya, ta ma zata Al'mazeen ɗin ne amma tana juyowa ta ga Hajja Azima wacce yau


157
HAUSACINEMA.COM


tayi shigan riga da wando idonta sanye da wani black shadow, Al'mazeen ne ya siyo mata jiya
kasancewar itama ta masa karya da cewa ai idonta na ciwo.




fuskarta a haɗe da ka ganta sai tayi maka kama da irin bosawan film din indian nan, ashar Hanan tayita
kalli Azima sama da kasa tace

"Wato na kauye ya shigo gari ko?"




"Ki duƙa ki ɗau jakarsa ki basa sannan ki ba shi hakuri" Azima ta faɗa cikin murya mai nuna umarni take
badawa ba shawara ba.




"Lalala! Wlh ni ba irinsu Hajjaju bane, da zaki dinga yab'a musu magana kina juyasu kina basu umarni
kina gasasu! Wlh ni karyaki zanyi! dan ni bana son raini!"




Hannunta Azima ta kama ta murɗe Hanan tasa ihu, Azima ta cije baki tace

"Kinga ni nayi miki kama da wacce take son raini? Tun kafin ki san wacece asalin Azima dau jakarsa ki ba
shi sannan ki ba shi hakuri!"




Maman Hanan da Maman Beenah da beenah da Hanif ne suka sauko jin ihun Hanan.




Nan suka ga Azima murɗe da hannun Hanan Al'mazeen na cewa da Azima a kan ta saki hannun Hanan,
ita kuwa tace ba zata sake ba, sai Hanan tayi abinda ta sakata,jin wuya yasa hanan cewa zata yi yadda
Azima tace, sakinta Azima ta yi ta duka ta dau jakar ta ba shi ta ce

"Kayi hakuri"




"Kayi hakuri wa?" Azima ta faɗa a tsawa ce.




158
HAUSACINEMA.COM




"Kayi hakuri Al'ma...." dauketa da mari Azima tayi har saida Hanan ta kai kasa,Azima tace

"Hamma! Daga yau idan na cire su Hajiya duk gabadaya Hamma Mazeen zaku na ce masa tunda ya
girmeku, maza gaya masa!"




"Kayi hakuri Hamma Mazeen" Hanan na faɗi ta hau sama da gudu, Maman Hanan da Maman Beenah da
Beenah suka bi bayanta, Al'mazeen ya haɗa rai yace

"Ina bakijin maganata? Ina cewa ki saketa amma kinki ko?" turo baki tayi tace

"Ba komai nake yi daukawa ba,kuma ma ai sabida kai nayi" tana gama fadi ta fice tana tura baki ta bar
shi tsaye, murmushi Almazeen yayi ya fice ya tafi office.




Ko a office din ya kasa aikin kirki tunanin Azima kawai yakeyi, wayarsa ce tayi kara yana dubawa ya ga
Alisha,guntun tsaki yaja,yau kusan sati tin dawowarsa kano take kira baya dagawa.




"Yanzu me zamuyi wa wannan yarinyar dan tana son fin karfinmu?" cewar Maman Hanan, Maman
Beena ta ce

"Shegiyar taga kudi duk yadda akayi sonsa takeyi"

"Abunda za ayi muyi mata sharrin sata na san shi da kansa zai koreta, dama yau su Summy da Sady zasu
zo ko?"




"E sunce ma sun kusa isowa".



159
HAUSACINEMA.COM




(Summy da Sady, kannan Hajiya Lawiza da Hajiya luba, wanda suke so su aurawa Al'mazeen).




Da kyar ya tattaro jarumta jin yadda kafafunsa suka yi sanyi ya shiga parlourn, ya samu Al'mazeen zaune
yana cin abinci, zama shi ma ya yi Sultana ta zuba masa ta tura masa gabansa, amma tunani yasa ma yaji
abincin ya fita kansa, Aziza kuwa tin sadda ta ba wa driver sako ta maqale ta kasa shiga gidan ganin yayi
babakere a bakin kofa, sai da ya shiga ta siɗaɗo a hankali ta shige dakinta da gudu,tana shiga ta zube a
gado ta saki kuka, ba jimawa Sultana ta shigo ta sameta tana kuka ta ce

"Subhanallahi! Aziza lafiya me ya faru?"

Cikin kuka ta dago ta ce

"Anty Sulty Hamma Nawaz ya ga idona"

"Mtswww! To sai me dan ya ga idonki?"

"Wlh tsoro nakeji kar ya koreni, dan naga yana mini kallon tuhuma kamar yasan wani abu a kaina"

"Kinga Aziza dan Allah ki kwantar da hankalinki ki samu natsuwa kinji? Babu abinda zai faru,na san me
zanyi, kuma ma ai idan ya san wani abu a kanki ai ya rage mana aiki, balle ina ma zai sani? daga wajena
sai wajan Mom,kuma Mom da kanta ta kwabeni tace kar na gaya masa ta san ta yadda zata gaya
masa,na tabbata mom bata gaya masa ba,dan da ta gaya masa zata gaya min, dan haka ki dai na damun
kanki" rarrashinta Sultana ta yi har ta samu tayi shuru, kafin suka koma hiran karatu.




Da kyar Nawaz ya yi cokali uku a abincin ya tashi, Al'mazeen ya ce

"Dude ka ce yunwa kakeji amma ka kasa cin abinci i hope dai komai lafiya?"

"E lafiya,ina zuwa" ya fada yana ficewa, part dinsa ya koma ya kwanta a dogon kujera, hakika idonta
babu bambanci da wanda yake gani a mafarkinsa, wai wacece wannan yarinyar nan ne kam? Ya zama
dole ya tambayeta ita wacece sannan miye haɗinsa da ita,idan ma mayya ce to wlh shi namansa da
ɗaci,kuma sai ya danna mata kashedi ta fita rayuwarsa ya huta, ya kara jan tsaki.




160
HAUSACINEMA.COM




Bayan Al'mazeen ya gama cin abinci ya koma part din Nawaz ya samesa yana kwance a dogon
kujera,zama ya yi a 1siter yana fuskantar Nawaz ya ce

"Dr lafiya kuwa?"

"Nml, kawai kaina ke ɗan min ciwo"

"Ayya sorry, to ka sha magani mana"

"No ba yanzu ba, bari na gani zuwa dare idan banji dai-dai ba zan yiwa kaina allura ko kuma ka min"

"Ok, Allah yakara sauki"

"Amin" Nawaz ya fada yana lumshe ido, wayar Al'mazeen ne ya sake ƙara, Nawaz ya bude ido yana jan
dogon tsaki

"Mtswwwwww!!! Wannan mayyar ce ko!?"

"Meyasa kake ce mata mayya bayan kasan ita zan aura?"

"Wlh Allah ya sawwake maka da aurar wannan kakar taka, duk da nasan bana son yarinya karama amma
ina zaka kai Alisha? ni fa wlh na rasa meke damunka, duk matan duniya ka rasa wacce zaka zab'a ka aura
sai Alisha? Ga uban saka gashin doki a kai, ga ƙarin farce, ga saka gashin ido, ga rashin kunyar taunar
cingam, gabakidayanta ma wlh zube take da karuwai! Dan Allah ka bar batun auren Alisha!"




"Haba dan Allah Nawaz ya isheka haka mana! Kai kullum baka da aiki sai kushe Alisha? A tsammaninka
dadi nakeji idan kana kusheta? Shuru fa kawai nake yi" Al'mazeen ya faɗa ransa a haɗe, Nawaz ya yi
tsaki ya ce

"Aikin banza! Abunda kai ma ba sonta kake yi ba, dan an kusheta miye naka na jin haushi,wlh da ace
kana son Alisha yadda nake kusheta da mun jima da rabuwa da kai"girgiza kai Al'mazeen ya yi ya ce

"Mace ba zata rabamu da kai ba Nawaz, idan na rabu da kai waye zai dinga supporting dina? Plss karka
kara fadin haka, abunda yasa nake son auren Alisha ita tana sona sosai,kuma ina sa ran zata bani




161
HAUSACINEMA.COM


kulawar da na rasa da soyayyar da ban samu ba" ya karasa fadin idonsa na canza kala,ganin haka yasa
Nawaz matsowa kusa da shi ya zauna a hannu kujera ya riƙo kafadarsa yace

"Karka fadi haka, In sha Allah Aminina ya kusa fara dariya, ka tsaya kuma ka gani,mahakurci mawadaci,
na fadi dai-dai?" Nawaz ya fada yana murmushi tare da miƙawa Al'mazeen hannu, shima Almazeen
murmushin ya yi yana haɗa hannunsa da na Nawaz sannan suka rungume juna.




Yau wuni zunbur Aziza ta yi a daki ta ki fitowa, bayan sallar isha'i gabadaya suna zaune a parlour suna
hira, Aziza kuma na daki tana rike da book amma a zahiri ba karatun take yi ba,tunani takeyi na yadda
idan mom ta gayawa Nawaz cewa ita macijiya ce ya zai dauki lamarin, tayi nisa sosai a tunani taji an turo
kofar da sallama, amsawa tayi tana ɗaga idonta ta sauke a kan Mom, Mom ta ce

"Lafiya kuwa yau kika wuni a daki Aziza? Ko wani abu na damunki shine kika kasa gaya min?" murmushin
yaƙe Aziza ta yi ta ce

"A'a Mom, yau din ne dai nake ɗan jin zazzabi amma ba sosai bane"

"Subhanallahi! Ai saiki faɗi ba wai ki zauna shuru a daki ba, gamu da likitoci har biyu a gida, bari nayi wa
Nawaz magana ya zo ya dubaki, ko allura ya miki" zare ido Aziza ta yi sai kuma ta koma ta hau narai-
narai da fuska, Mom ta ce

"Ai ba zaki zauna da ciwo ba" Mom ta fita tana ambatar sunan Nawaz, wanda suke lissafin bikin sultana
shi da Almazeen

"Na'am Mom" Nawaz ya amsa yana maida hankalinsa ga mom

"Nawaz dan Allah zo ka duba Aziza kayi mata allura, ashe bata jin dadi ne shiyasa ta wuni yau a daki"
Sultana ta ce

"Ya Salam! Aziza akwai zurfin ciki wlh,nan fa dazu babu kalar tambayarta da banyi ba amma tace min
babu komai, dan Allah Bro Nawaz muje ka dubata"

"To ba ga Al'Mazeen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login