Showing 48001 words to 51000 words out of 94205 words
mun kara daukar mai aiki dan ya tanadi kudin biyanta
ita ma"
"Ah to shine magana ai,idan bai kashe mana kudin ba munyi wadaka yadda muke so ma wa zai yi ma
wa? Tunda Uwar da Uban duk sun mutu" Maman Beenah ta yi murmushi ta ce
"Ai muyi kokari da ya dawo mu haɗa masa kannanmu ya aura dan mu ci gaba da tatsarsa"
"Wannan magana taki haka take, Hadiza shiga da wannan ki nunnuna mata abunda ya dace, su dakuna
zata dinga gyarawa, dakin su Hanan da Beenah da Hanif sai kuma namu dakunan, sai idan AL'MAZEEN ya
dawo zata dinga gyara masa nashi dakin dan haka har part din Al'mazeen zaki nuna mata amma ba
yanzu ba"
"Tukunna ma ya sunanki?"
"AZIMA BANJU!" cewar Azima kanta a duƙe
"To kin dai ji aikin da zaki dinga yi mana ko? Za a dinga baki dubu goma a wata"
"Na gode sosai" cewar Azima, Maman Hanan ta ce
"Kuje da ita Hadiza"
"To Hajiya,Azima zo muje ki ga dakinmu" da kyar Azima ta miƙe dan tun lokacin da aka kira sunan
Al'mazeen ta nemi natsuwarta da karfin halinta ta rasa, a zuciyarta take tambayar kanta waye shi
Al'Mazeen din? dole ta ga waye shi dan daga kira sunansa sai jikinta ya yi sanyi? anya zata iya zama a
106
HAUSACINEMA.COM
gidan kuwa? daga fara saka kafarta a gidan tayi tuntube da faɗuwar gaba,yanzu kuma an kira suna
zuciyarta ta tsinke, jin babu kuzari a gangar jikinta yasata b'allan gashin kanta ta sa a baki ta lumshe ido
tukunna taji ta dawo dai-dai, Hadiza ce ta nunnuna mata abubuwa dasu dakunan da zata dinga gyarawa
a sama da kasa,amma bata haura da ita part din Al'mazeen ba, kasancewar an ce mata ba yanzu za a
nuna mata ba,Azima kuwa tace ba zata iya jira ba ko da yaya ne sai ta shiga part din ta gani.
Yau kwanan Azima biyu a gidan,kuma cikin ikon Allah babu wanda ya shiga hidimarta kamar yadda bata
shiga tsabgar kowa, sunan wanda ake kira da AL'MAZEEN shine ya tsaya mata a rai, ga shi bata san part
dinsa ba,kuma ba zata iya tambayar su Hadiza ba,dan bata son yawan magana , Beenah har kyautar kaya
suka mata,kuma babu wanda ya taba yi mata magana a kan rufe fuskarta da take yi kasancewar ansan
kunya gado ce ta fulani, ko Hanif da yake namiji baya shiga hidimar Azima,idan kuma gyaran daki ne tana
shiga zata hura iska ta bakinta dakin shi da kansa zai gyara kansa,idan ta shiga daki ko minti goma bata yi
zata fito da an shiga za a gansa fesss! shiyasa daga Maman Hanan har Maman Beenah suke jin dadin
zama da Azima,ita kuwa Azima yanzu tunanin kisa ya fita a ranta sai son ganin waye AL'MAZEEN.
A kwana biyu kuwa Aziza ta ɗan sake dasu Mom da Sultana barin ma Sultana da bata nuna mata ƙyama
tana janta a jiki, ranar da ta cika kwana biyar a gidan ganin jikin nata da sauki sosai yasa Sultana zuwa
wajan Mom tace Mom ta basu kudi zata kai Aziza wajan gyaran gashi, Mom tayi murmushi sannan ta
bata kuɗi ta ce driver ya kai su.
107
HAUSACINEMA.COM
Bayan sun je shagon salon din za a buɗewa Aziza fuska ta hanyar kwashe mata gashi tayi saurin saka
tafin hannunta a fuskarta dama da kyar ta yarda ta cire hijabinta, dariya Sultana ta sa tana fadin
"Duk rowan da kike mana na ganin fuskarki yau dai dole ki bude" da kyar mai salon ta lallaba Aziza tana
kwashe gashin Aziza tayi saurin rufe idonta gam, kan aka hau wanke mata kai ɗin, Sultana na zaune a
gefe wayarta ta yi ƙara tana dubawa ta ga Brother da sauri ta daga tace
"Assalamu alaikum, Brother ina kwana?"
Daga can ya sauke ajiyar zuciya ya ce
"Lafiya lau Sultana ya kuke? Ina Mom? Na kira wayarta bata ɗaga ba,ki gaya mata yau ina hanya"
"To Brother sai dai nima na kirata a wayar"
"Sabida me? yau ba saturday ba ai ba skull, ko kina skull din ne?"
"A'a Bro ina shagon salon na raka Aziza ne a wanke mata kai" jin sunan da ta kira yasaka shi katse wayar
da sauri, dan tun ranar da ya buge yarinyar nan yake mafarkin tana neman taimakonsa,tun abun baya
damunsa har ya koma damunsa, da fari ya yi tunanin ko dan ya bugeta ne amma a yanzu ya kasa
fahimtar halin da yake ciki, da ya ji Mom tace ta dauketa aiki har cikin ransa bai so ba amma dai bai ce
komai ba.
Sultana kuwa mamakin katse wayar ya yi tayi,daga baya kuma ta ce
"Uhum Yaya kenan" wayar Mom ta kira bata ɗaga ba itama, ta kalli mata mai salon din ta ce
"Dan Allah Anty ki gama mata da sauri zamu tafi gida Yayana wai yana hanya"
"Ai gashin nata ne dayawa wlh ga tsayi ga cika tabarkallah Ma sha Allah!" Sultana ta yi murmushi.
Kusan mintuna talatin aka kwashe ana wankewa Aziza kai idonta kuwa yana lumshe ko da wasa bata
buɗe ba, bayan an gama ne aka busar mata da kai din aka shafa mata mayuka masu kyau da ƙamshi aka
taje mata shi sannan aka sa ribbom aka daure mata shi, Ma sha Allah! shine Abun da Sultana ta faɗa ta
ciro wayarta tana daukar Aziza hoton wacce ta yi saurin maida hijabinta tana rufe fuskarta,bayan Sultana
108
HAUSACINEMA.COM
ta biya kuɗin mai salon suka mata godiya suka fice tana ta yabon kyawun Aziza da dogon gashinta,ita dai
Aziza tana murmushi ne kawai sama-sama,bayan sun shiga mota Sultana ta ce
"Yanzu mu fara biyawa mu karbo kayanki na wajan tela, yawwa dama ina so na tambayeki,kin iya
karatu?"
Aziza ta gya ɗa kai ta ce
"Nayi sauƙan al'kur'ani mai girma a kauyenmu, sannan na karanta litattafai da dama,na iya rubutu kamar
irinsu ko da wasika idan Baffanmu zai rubuta idan rubutun tayi masa yawa ina tayasa rubutawa amma
ba da irin rubutunku ba, da harafin su Alif kamar ajimi haka"
Sultana ta ce
"Ahh Ma sha Allah ki ce malama ce" ta faɗa a mamakince dan kuwa ta sha mamaki ɗin sosai, murmushi
Aziza ta yi ta ce
"A'a ina dai kan neman ilmin"
To shikenan zan koya miki karatun hausa da turanci ta yadda zaki iya duka,idan har kina ganewa da wuri
zan cewa Yayana ya nema miki skull mafi kusa da saurin ganewa,sannan matsalar idonkin nan ya nema
miki medicalglass"
"A'a Anty Sultana karki gaya masa,ki bari kawai idan kika koya mini ma ya isa, idona kuma haka yake
haka aka haifeni dan Allah ko wa Mom ne karki ce mata komai" Sultana ta yi murmushi ta ce
"To shikenan"
Bayan sunje sun karbo kayan suka koma gida a daki suka samu Mom, Mom tace "sannunku da dawowa
'yan matana har kun dawo" Aziza ta duka kasa Sultana kuma ta zauna a gefen gadon Mom, ta ce
"E Mom mun dawo barka da gida, dazu muna shagon salon Yaya ya kirani wai yana hanya mun kiraki
baki daga ba"
109
HAUSACINEMA.COM
"E munyi waya da shi daga baya,kema na kiraki bai shiga bane, lokacin da ya kirani ashe na tashi na bar
wayar a parlour shiyasa, yanzu dai ku tashi kuje ku gyarawa Yayan naku dakinsa, idan kun gama sai ku
shiga kitchen" dan mom bata yarda da lalaci ba dan babu irin girkin da Sultana bata yi shiyasa da shike
basu da yawa a gidan kuma ba yara garesu ba shiyasa mai aiki daya kawai suke dauka, suka amsa da to,
Aziza ce ta fara tashi ta fita, Sultana ta ce "zo muje part din Yayan" tayi gaba Aziza na binta a baya, suna
fita sai ga wani ɗan ƙofa madaidaici Sultana ta buɗe suka shiga,parlour a kasa har da step wani sashene
mai zaman kansa a wajan tabbas an tsara parlourn ya tsaru, Aziza matowa tayi da kallon parlour,idonta
ne ya sauka a wani pic babba a parlourn shi daya da kuma wani a gefe su biyu, dukkansu fuskarsu babu
murmushi,tabe baki Aziza ta yi,dan ita bata ga abum gyara a wajan ba,ganin yadda take kallon hoton ne
yasa Sultana fadin "wannan shine Babban Aminin Yaya baya da wani sama da shi, a tare suke a america
tare suka yi karatu gabaɗayansu kuma likitoci ne, karki ga fuskarsu haka a haɗe barin ma yadda kika ga
na Abokin Yaya,to wlh yafi Yaya Nawaz sauƙin kai,kawai dai shi magana ce bai cika yi ba da dariya,amma
idan kina neman zafin zuciya kika samu Yaya Nawaz kin gama" jinjina kai Aziza tayi ba tare da tayi
magana ba,suka hau sama yadda k'asan ya tsaru haka ma saman ya tsaru haka de ta dinga bin Sultana
har suka gama suka saka masa turaren wuta sannan suka wuce kitchen suka hau girki, dama Sultana na
koyawa Aziza yanayin girkinsu,duk abunda ta koya mata sau daya kuma cikin ikon Allah ta riƙe kenan
babu mantuwa, idan tazo yi kuma sai tayi wanda yafi na Sultana daɗi, haka suka yi girki a tare suka gama
duk da ba wani hira sukeyi ba,tunda Sultana ta fahimci Aziza bata son yawan magana yasa itama bata
takura ba,ita kuwa ba zata fahimci tashin hankalin da take ciki bane,bata fata su gano cewa ita ba
mutum bace macijiya ce har su rabu tinda zama dasu na wucin gadi ne, bayan sun gama girki Sultana ta
ce
"Aziza je kiyi wanka ki canza kaya, sai ki kwanta ki huta idan kika huta da dare sai mu fara karatun ko?"
"Dazu fa kafin muje wajan wankin kai nayi wanka"
"E na sani,ai ita tsafta bata yawa sai dai tayi kaɗan, zaki dinga yi ne dai-dai gwargwaɗon iyawarki,kuma
gwara ki saba da shi tun daga yanzu dan bamu sani ba watakila Mom ta samu surki a nan garin"wani
wawan faduwar gaba ne ya ziyarci Aziza ta sake maimaita kalman sirki a ranta, da kyar tayi murmushin
karfin hali ta amsa da to a sanyaye sannan ta wuce daki,itama Sultana sama ta haura, Aziza na shiga daki
ta wuce toilet, tana shiga ta maida kofa ta rufe ta rintse idonta ya sake komawa fari, fatar jikinta ma fari
yana sab'ulewa, daga ƙasarta ta fara rikiɗewa nan ta zama rabi mutum rabi macijiya sannan ta zauna a
gefen bath din wanka ta hau kuka, tunowa da maganar Arɗo da Baffa Mandi, na cewa ba zata warke ba
har sai sunyi aure, kuma ita warakanta yana tattare da Azima wacce bata ma san a wani duniya Azima
take ba, sai bayan da ta gama shan kukan nata kafin ta yi wankan ta fito.
110
HAUSACINEMA.COM
Sai huɗu Nawaz ya samu damar isowa, ko da ya iso wajan Mom ya nufa nan take masa sannu da zuwa
tare da fadin
"Nawaz sai yanzu?"
"Wlh Mom motata ce ta ɗan samu matsala a hanya sai da aka mata gyara"
"Subhanallahi! Karfen nasara babu tabbas Allah ya kara kiyayewa"
"Amin Mom bari na samu na ɗan watsa ruwa sai na fito na ci abinci,ina Sultana?"
"Ba mamaki tana dakinta,bata ji shigowarka ba ai da ka ganta da gudu" murmushi ya yi kawai ya
fice,part dinsa ya shiga ya samu na tashin kamshi bai tsaya wani bata lokaci ba ya yi wanka ya shirya ya
fito, ji yayi ba zai iya komawa babban parlour ba dan haka ya kira Sultana ta kawo masa abincin part
dinsa.
Hakika wannan mafarki ya tayar masa da hankali, ko da ya farka da washe gari jikinsa a mace, da kyar ya
gama shiryawa ya fito ya yiwa Mom sallama da shike driver ne zai kaisa ya dawo, shiyasa zasu yi fitar
wuri, bayan sun gama sallama da Mom suka rakasa har bakin mota, sai ware ido yake yi inda zan hangi
Aziza amma bai ganta ba, kallon Sultana ya yi ya ce
"Ina Aziza ne?"
"Ina ga tana dakinta bari na dubota"
"Noo leave her" ya faɗa yana jan murfin mota Mom tana kan yi masa addua yana amsawa da amin,
Mom da Sultana basu koma cikin gida ba har sai da motar ta fice a gate gabadaya aka ja gate din kafin
suka koma,ko da suka shiga Sultana ta wuce dakin Aziza ta sameta zaune tana ninke kayan Mom da ta
wanke, Sultana ta ce
"Aziza baki fito kinyiwa Yaya Allah ya kiyaye hanya ba har sai da ya tambayeki wlh"
"Ayye ban san ya fita ba da shike ina nan ina ninke kayan Mom ne" ta faɗa ba tare da ta dago ba, alhali
taji sadda suka sauƙo dasu Mom har sadda ya shiga mota duk tana tsaye tana leƙensu ta window, sai da
ta ga motar ta fice a gidan kafin ta koma daki, Sultana ta ce
111
HAUSACINEMA.COM
"To ke miye haɗinki da kaya ina Buba yake?"
"Wlh jiya ne yaji ciwo a hannu shiyasa na karba kayan na wanke"
"Subhanallahi! Allah ya kiyaye gaba amma ai sai ki faɗa ba wai ki wankesu da kanki ba da an nemo mai
wankewa,yanzu dai ki gama ɗin sai ki zo muje Mom ta aike mu karbo kulolin azumi wanda ake abincin
sadaka dasu gidan wata kawarta a nan malali"
"To Anty Sultana bari na karasa gani nan zuwa"
"To kiyi sauri ki shirya, saura kuma wlh ki zunduma hijabin kin nan, dan Allah ki nemi abaya ki saka ki
yafa gyale akwai gidan da zaki rakani mu shiga tare Mom ta bamu sako ma a gidan" da to Aziza ta kara
amsa Sultana, Sultana tana fita Aziza ta sauke ajiyar zuciya tana fadin "Allah ya kaika lafiya Hamma
Nawaz, ba mamaki ba zaka dawo ka sameni ba" ta fada tana mai lumshe ido, saurin kwashe kayan ta yi
ta kaisu dakin guga, sannan ta koma ta shirya shap-shap tasa doguwar abaya baƙi ta dauki ash'color din
gyale taja gashin kanta ta nannaɗesa ta daure a tsakiyar kanta ta dau hula ta saka kafin ta dauki mayafin
ta yi lullubinta kamar kodayaushe,ko da ta fito parlour Mom da Sultana suna parlour Mom tana kara ba
wa Sultana saƙo, itama ta yi shigar bakin abaya, tana fitowa Sultana ta ce
"Yawwa ko ke fa" murmushi kawai Mom tayi ta ce
"Ma sha Allah 'yan matana, Allah ya kawo miji na gari,kodayake ma yanzu kam sai dai nayiwa 'yata Aziza
dan ita Sultana rana kawai za a saka"
A sanyaye Aziza ta ce
"Lahh Anty Sultana shine baki gaya mini ba? To Allah ya kaimu Allah ya sanya alkhairi" Mom ta amsa da
amin Sultana kuwa ta dukar da kai tayi tana murmushi,bayan Mom ta gama basu saƙon ta ce
"Dan Allah karku kai magriba,Sultana karki ga dan Nawaz baya nan ku kai magriba kin san dai ko da wani
lokaci kiran waya yake yi,da ya kira kuma zai ce ina kike, dan haka kuyi ku dawo"
"In sha Allahu Mom" suka faɗa suna ficewa, duk inda aka aikesu nan suka je, har gidan surakanan
Sultana, a gidan kuwa wani ƙaninsa ya ga Aziza sai kallonta yake yi, har sai da ya biyo Sultana yana faɗin
"Anty dan Allah wannan fa?"
Murmushi Sultana ta yi tana faɗin
"Kanwata ce,kana ciki ne?"
"E wlh Anty ina ciki"
112
HAUSACINEMA.COM
"Lallai kam to sai ka gayawa Yayanka"
"To Anty shi da baya kasar ki kirasa ki fara gaya masa,kinga ma sai a haɗa bikin da naku"
"Ahh lallai Walid baka da kunya, wato ma a haɗa da namu?"
"E mana Anty,kodayake ma ku da ba a saka ranar ba, sai a fara namu kafin Yaya ya dawo ke kuma kin
gama skull kafin nan kema kin kara girma Anty" ya faɗa cikin tsokana, Sultana ta ce
"Wlh Walid ka rainani,zan haɗaka da Yayanka kuwa"
"Allah ya baki hakuri Anty,ni dai dan Allah ki fara min kamu"banza da shi Sultana ta yi ta shiga mota ta
cewa driver yaja su tafi,basu tsaya ko ina ba sai gida,suna isa Mom ta musu sannu da dawowa tace musu
idan sun huta su shiga kitchen suyi girki suka amsa da to.
Da washe gari sai dare Mom ta samu damar yin waya da Nawaz ya shaida mata cewa ya isa lafiya, Mom
ta ce
"Ma sha Allah haka akeso,Allah ya taimaka ka gaishemin da son"
"Zaiji Mom,ina Sultana?"
"Suna can daki ita da Aziza suna karatu, dama kuwa ni ina son yi maka magana a kan yarinyar inaso zan
nema mata makaranta, tana da kaifin basira, wlh basu kai sati da fara karatu ba amma karka ga yadda
kanta ke ja,abun mamaki" Shuru Nawaz ya yi na dan wani lokaci har sai da Mom ta kuma cewa
"Nawaz bakaji me nace bane?"
"Naji Mom duk yadda kikayi dai-daine,Allah ya baki lada"
"Amin Nawaz" hira suka ɗan taba kafin suka yi sallama da shi.
113
HAUSACINEMA.COM
Bayan sati biyu