Showing 3001 words to 6000 words out of 94205 words

Chapter 2 - Azima-Da-Aziza-Macizai Ne Complete

20 Jul 2024

37835

saurin jiyo abu.

Kallon Aziza da kyau Hajja ta yi kafin ta ce

"Me ku ke zuwa yi kullum ne a rafin jimulo?"




7
HAUSACINEMA.COM


"Ba komai Hajja kawai rafin akwai dadi ne, ga iska mai dadi, Hajja kin manta sadda kike kai mu muyi
wasa?" murmushi Hajja ta yi ta ce

"Eh na tuna, yanzu dai je ki kirawo Azima ku zo kuci abinci"

"To Hajja, Baffa ya fita ne?" Aziza ta tambayi Hajja kamar bata san Baffan ya fita ba, Hajja ta ce

"Eh ya fita kin san ai jiya yace yau Jarman macizai zai zo, yace min idan yazo zai zo ya kiramu muje
gabadaya ayi gwaji" Aziza ta jinjina kai tana fadin "to Hajja bari naje na kira Azima kafin Baffa ya dawo"

"To a dawo lafiya,ki tabbatar kinyi lullube da kyau fa"

"To Hajja" Aziza ta fada tana ficewa jiki a sanyaye, tana fita da gudu ta yanki rafi inda tasan Azima ba
zata wuce can ba.

Tana zuwa ta sameta kwance a kusa da rafi.

Hannnu tasa ta janyota ta ce

"Kin kashesa ko Azima? Na ce kin kashesa ko!?" dariya ta kyalkyala cikin amo marar dadin sauraro ta ce

"Ai na gaya miki Aziza sai na kashesa!"

Rike kai Aziza ta yi ta ce

"Me kika so ki zama ne kam Azima?"

"Bana son ganin zaman lafiya a wannan yankin! Na fi so ayi ta b'arin jini! Ina so na haɗa maƙotan
yankunan nan faɗa, duk wani mai kama macizai wanda za a yi masa aike ya zo yankin nan sai na kashesa!
Kin ga daga nan za a fara yaƙi tsakanin yankuna da yankuna, sannan dama akwai y'ar tsama tsakanin
yankin kwana da yankin tudu da kuma yankin Ja'i nasan kuma dole mai unguwa zai bukaci taimakonsu,
duk wanda aka turo ni kuma zan kashesa! Na tabbata daga lokacin zaman lafiya ya kare, Baffa shine
jarumi na farko a wannan yankin wanda da shi aka yi gwagwarmaya kinga kuwa ba mamaki a wajan
yaƙin a kashesa!"

Zaro ido Aziza ta yi tana kallon Azima kafin ta ce

"Na rasa dalilinki na son ganin bayan Baffa! A yadda na fahimceki, ke ba ki ƙi kowa ya mutu ke ki rayu ba,
idan kika samu dama na tabbata za ki kashe Baffa"dariya Azima ta kyalkyale da shi tana kewaye wajan
kafin ta koma ta haɗe rai sosai ta ce

" AI BA YAU BANE KAWAI NA SHA GWADA HAKAN!ko a yanzu na samu sarari sai na kashe Baffa! Ko kin
manta na sha yunkurin kashesa!? Lokuta da yawa ke ce kika katse min burikana! Ga shi ke ban san ya



8
HAUSACINEMA.COM


zanyi dake ba! Ke ta biyu na ce! Ba zan iya kasheki ba! Sabida duk muguntar gubana naki yafi nawa!
Kuma ina sonki yar uwata! Da ace nike da karfin dafin da kike da shi da na jima da shafe wannan yankin
kakaf dinta!" Azima ta fada tana daga hannuwanta sama.




Aziza ta girgiza kai ta zauna a kasa tare da fashewa da kuka ta ce

"Azima ba zan taba bari ki cutar da Baffa ba,ko da kuwa zaki iya,ni dai a gaskiya inaji a jikina kamar ni da
mutum ce! Ban san a garin yaya muka zama macizai ba, miye dalilinki na son kashe Baffa Azima!?" Aziza
ta faɗa tana haɗa kai da guiwa tana ci gaba da kuka,duk sadda ta kalli jikinta ta ganta a macijiya tana jin
zafi a zuciyarta, ta yi nisa sosai a kuka ta ji wani irin murya na namiji wanda yake abun tsoro an bata
amsar maganarta.




" ZUNUBIN DA BAFFANKU YA AIKATA NE YAKE BIBIYARKU!, TARE DA GOYA MASA BAYAN DA JAMA'AR
YANKIN NAN SUKA YI!" da sauri a matukar firgice Aziza ta dago tana waige ta ga daga ina ne maganar ya
fito? Amma bata ga kowa ba illa Azima dake wasa a cikin rafi kana ganinta zaka san tana cikin nishaɗi, ta
zama macijiya ta koma ta zama mutum.




Sauri tashi tsaye Aziza ta yi tana waige a fili ta kara furta kalman da ta ji "Zunubin da Baffanmu ya aikata?
Me Baffanmu ya yi kuma?" tambayoyi ne maqil a ranta amma babu mai bata amsa, ko dai zata je ta
tambayi Baffa ne? Kai amma kuma idan ta yi haka za a gane su ɗin ba mutane bane, riƙe wuyanta ta yi
jin kamar zuciyarta yana shirin fitowa bakinta, kallon Azima ta yi ta ce

"Azima ki zo muje gida"

"Tare muka zo dake ne?"

"Idan ma ba tare muka zo ba Hajja ta ce mu dawo tare yanzu, kar Baffa ya dawo...." Aziza ba ta karasa ba
Azima ta fito tana fadin

"Ke komai ki ce Baffa?"

"To idan ban kira sunan Baffana ba sunanki zan kira?" murmushi Azima ta yi ta ce

"Yau bana jin yin faɗa dake, dan yau ina cikin farin ciki, nasan idan sako ta iske sarkin yankin jimo an
kashe masa Jarman Macizai me kike tunani zai faru Aziza?"




9
HAUSACINEMA.COM


"Ban sani ba!" Aziza ta faɗa a ƙufule ta yi gaba, ita ma Azima a macijiya ta hau bin bayan Aziza, yau
tsananin takaici ya hana Aziza ta cewa Azima ta koma mutum, Azima kuwa da gangan take wani abun
dan Aziza ta mata magana.

A macijiya ta shiga gidan Allah ya so Hajja na bandaki, zama Aziza ta yi ta buga tagumi, Azima kuwa
bukka ta shige, bayan Hajja ta fito ta ga Aziza da tagumi ta ce

"Ah Aziza kun dawo?" shuru Hajja taji dan Aziza ta yi nisa cikin tunani, sai da Hajja ta tabota tukunna ta
dawo hayyacinta ta ce

"Na'am Hajja magana kike yi ne?"

"Tunanin me kike yi haka Aziza?" murmushi Aziza ta k'wak'ulo ta ce

"Abunda yake faruwa a mahaifana shine yake tayar min da hankali Hajja"

"Karki ce zaki saka hakan a ranki,addua ita ce mafita,duk abunda ya yi tsanani maganinsa Allah" kuka
Aziza ta fashe da shi ta rungume Hajja ta ce

"Dole ne na saka a raina Hajja! Idan mun san abunda ya faru yau ba bamu san me zai faru gobe ba
Hajja!" sosai Aziza ke kuka yayinda hankalin Hajja ya tashi, Azima ce ta fito daga bukka dauke da abinci a
hannunta zama ta yi ba tare da ta kalli Hajja ko Aziza da ke kuka ba,abincinta ta hau ci hankalinta
kwance, Hajja ta kalli Azima wacce ta jima da gane ita damuwar wani bai dameta ba, ta ce

"Azima meke faruwa da yar uwarki!?"

Cikin halin ko in kula ta ce

"Oho mata! Tana son ɗorawa kanta damuwar da bata da mafita a kansa, ta ga zata iya ne, Hajja ki daina
damun kanki a kanta!" Hajja zata yi magana sai ga Baffa a fujajan ya shigo ko sallama babu, da sauri
hankalin Hajja da Aziza ya koma kan Baffa akasin Azima da ta yi kamar bata san da shigowarsa.

"Baffan yan biyu lafiya kuwa na ganka a cikin wannan yanayin?"

Sharce zufa Baffa ya yi ya ce

"Jumala ina kuwa lafiya! Ku zo muje gaban gari ana neman dukka mutanen yanki, kin san an kashe
Jarman Macizai kuwa?" hannu Hajja ta zuba a kirji tare da fadin

"Ma'asabumin Musibati qalu Innalillahi wa inna ilaihirrajiun! An kashe jarman macizai to waye
kashesa!?"




10
HAUSACINEMA.COM


" MACIJI! SARAN MACIJI NE A JIKIN JARMAN MACIZAI!" Baffa ya faɗa yana sauke idonsa a kan Azima
wanda hankalinta sam baya kansu, Hajja ta ce

"Ba ri na dauko mayafina mu tafi gaban gari din" Hajja ta karasa maganar tana shigewa bukka, Aziza
kuma tana gyara mayafin kanta hankalinta a tashe! Baffa ya ce

"Ke Azima? Ana gaya miki mahaifarki babu lafiya amma kina zaune hankalinki kwance ba tare da kin
nuna damuwarki ko a fuska ba kina cin abinci! Za ki tashi ne ko sai na saka sanda na roɗe miki shingen
kafafunki nan masu kama da fuffuken sauro!" Baffa ya faɗa yana yin kan Azima da sauri ta tashi tana
huci tare da juya baya, hanyar randar kasan dake tsakiyar gidan taje ta ɗibo ruwa a kwarya tare da fakan
idon Aziza ta watsa dafi a ciki, sannan ta juyo tana kallon Baffa a ranta take fadin

"Ba zan taba samun salama ba idan har ban kasheka ba!"tunkaro Baffa ta yi har ta zo gabansa tana tura
baki ta ce

"Baffa na ga alama kan ka ya dau zafi kaɗan sha ruwa zuciyarka ta huce! Baffa ita fa damuwar duniya
bata karewa barin ma idan mutum yasa hannu ko nace mutane suka sa hannu suka jawo bala'i wa kansu,
sannan dole akwai abunda ku ka aikata ma wasu yake bibiyarku! Dan haka Baffa a koma a yi tunani da
kyau, ga ruwan ka sha" ta mika masa tana sunkuyar da kai kasa sai kace wata ta Allah, shuru Baffa ya yi
yana son yayi tunani a kan maganar da ta fada amma tashin hankalin da suke ciki ya ƙi basa damar haka,
hannu yasa ya karbi ruwan caraf idon Aziza ya sauka a kan ruwa ta hangi dafi, cikin azama ta ce

"Baffa wani ruwa kuma zaka sha? Ka manta Azima ita bata damuwa da damuwar wani? Kawo ruwan nan
Baffa" Aziza ta karba, wani kallo ne Azima ta bi Aziza da shi jikinta har na tafasa tsananin takaicin abunda
Aziza ta yi, Aziza na karban ruwan da gangan ta yi tuntube ruwan ya b'are kwaryar kuma ta riɗata da
dutse ta fashe, cije baki Azima ta yi, idonta ya kara rinewa tana shirin tunkaro Aziza wacce itama ke
kallonta ko gizau bata yi ba, Hajja ce ta kara katse mata hanzari ta fito tana fadin

"Yi hakuri Baffan yan biyu! Na zubar da wake ne na tsaya kwashewa shiyasa ban fito da wuri ba,muje"
gaba Baffa ya yi Aziza ta bisa a baya, Azima ta zo fita Hajja ta ce

"Ina mayafinki?"

"Ba zan saka ba! bana jin saka wa Hajja! Raina a b'ace yake karki min maganar wani mayafi!" daskarewa
Hajja ta yi jin amsar da Azima ta bata,ita ma Azima bata san lokacin da ta faɗi badan bata taba yiwa Hajja
magana haka ba,ganin Hajja ta tsaya tana kallonta ne yasa ta cewa "yi hakuri Hajja bara naje na
dauko,kuyi gaba zan zo a baya" Hajja dai bata iya cewa komai ba illa bayan su Baffa da Aziza da ta bi
wanda sun yi gaba abunsu.




Su na kan tafiya Aziza ta ce



11
HAUSACINEMA.COM


"Baffa?"

"Na'am Aziza yaya ne?"

"Baffa baka taba bani labarin kafuwar mahaifata ba, kullum kana cewa an sha gwagwarmaya da aljanu
da mayu, amma baka taba bani labarin kalar gwagwarmayen da ku ka sha dasu ba"

"Yo to banda abunki Aziza ana cikin wannan tashin hankali kina maganar labari? Abunda ya kafu sama da
shekaru hamsin? Ki bari Allah ya bamu ikon dakatar da wannan ambaliyar wutar masifan dake tunkaro
wannan yankin" shuru Aziza ta yi ba tare da ta sake magana ba, da haka har suka karasa gaban gari inda
cincirindon fulani suke tsaye kowa ka gari hankalinsa a tashe, har anyiwa jarman macizai jana'iza an
binnesa.

Ana ta shawaran yadda za a rubutawa sarkin fulanin yankin jimo sakon cewa an kashe jarman macizai
wanda yankuna sun san shi jarumi ne, idan ka cire yankin ja'i da yankin tudu za a iya cewa babu wani
jarumi wanda ya shahara a kama macizai sama da jarman macizai, amma a yankin Ja'i akwai wanda har
aljanun macizai yana kamawa tsananin shahararsa wanda har laƙabi ake masa da INNU MACIJI, daga shi
kuma sai na yankin tudu wanda shike takawa Innu Maciji baya wato IRO MAGANIN MACIZAI daga shi sai
wanda aka kashe na yankin jimo wato JARMAN MACIZAI, lokacin da aka raba kambun girma na wa inda
suka shahara a kama macizai aka ba wa INNU MACIJI lamba daya, aka ba wa IRO MAGANIN MACIZAI
lamba ta biyu sai kuma JARMAN MACIZAI lamba ta uku, har ta Ilu mai Macizai da Azima ta kashe na
yankin kwana shine aka ba wa lamba ta shidda, sannan aka rabawa na ƙasa dasu, tashin hankalin da
yankin kwana ke ciki shine rashin jituwar da basu da shi da yankin tudu da yankin ja'i, barin ma yankin
ja'i tsatstsauran gaba ce daɗaɗɗiya, dan kuwa an sha gasan kisa a tsakani, yankin tudu kuwa dan sarkin
yankin ne ya zo yankin kwana ya yiwa yar yankin fyaɗe bai kyaleta ba har sai da ya kasheta! Hakan ce
tasa ARƊO ya bada umarnin a kashesa shi ma,aka gille masa kai aka turawa mahaifinsa da shi daga nan
gabar ta soma, yanzu taya zasu fara neman taimakon Yankin Tudu ko kuma yankin ja'i? Yanzu dai ba shi
bane tashin hankalin, tashin hankalinn shine yadda zasu fara tunkaran yankin jimo da sakon an kashe
jarman macizai.

Su Baffa sun iso ana kan shawara ba a tsaida mafita ba, sai da Baffa ya karaso aka sake yin shawara a kan
a rubuta sako a tura mutum huɗu da suje yiwa yankin jimo ta'aziyya tare da rigan Jarman Macizai wanda
yake jina-jina da jini, sannan ayi musu bayanin abunda ya faru bai kai ga yin aikin da yazo yi ba aka iske
gawarsa, tare da sakon ban hakuri iri da kala daga wajan mai unguwan yankin kwana da kuma sarkin
fulanin yanki kwana tare da Arɗo, hakan ce ta kasance aka tura mutum huɗu izuwa yankin jimo, tare da
kayan Jarman Macizai da kuma dokinsa da takwabinsa.

Aziza na tsaye a gefe da lullubi hawaye ne cike a idonta,ba dan komai ba illa su na zuwa wajan aka fara
darewa ana matsawa babu wanda ya tsaya kusa da ita.




12
HAUSACINEMA.COM


Azima kuwa za ta zo yau ne gobe ne shuru, har aka gama tattaunawar da za ayi Azima bata zo ba.




Bayan an fara watsewa Arɗo ya kira Baffa gefe ya ce

"Magaji? A gaskiya ba zan boye maka ba, ka binciki yaranka! Barin ma wannan yarinyar taka Azima,jiya
an kawo min wani magana a kanta, bana son na tsawaita zargi dan babu kyau, sannan jikokinane kasan
dai ba zan so abunda zai cutar dasu ba, amma ya kamata mu san abunyi,kasa ido sosai a kansu, bana so
na kirawo Jumala dan duk abinda za a gaya mata ba yarda zatayi ba, sannan bayan sallar isha'i za a zauna
ayi tattauna a faɗar mai unguwa, zamu je neman alfarma a yankin tudu" da sauri Baffa ya ce

"Arɗo yankin tudu kuma?"

"E Magaji, yankin tudu bamu da wani mafita wanda ya wuce hakan"

"To amma Arɗo kana ganin anya Sarkin Tudu zai sauraremu? Ko ka manta abunda ya shiga tsakanin
yankinmu da nasu ne? Ɗansa yazo ya yi laifi a yankin nan an masa hukunci hakan ne ta haifar da gaba
mai tsauri a tsakani, bana tunanin Sarkin yankin tudu zai yarda Iro Mai maganin macizai zai zo
taimakonmu, kana gani duk wasu masu kama macizai da muke dasu a yankin nan sun mutu, a gaskiya
inajin tsoron abunda zaije ya dawo, kar bamu gama da wani yaƙin ba mu sake kunna wani, a gaskiya
bana so duk shawaran da za ayi ace za a bukaci taimakon yankin tudu da yankin ja'i"

Nauyayyiyar ajiyar zuciya Arɗo ya sauke ya ce

"To Magaji mai zai hana kai ka maida hannun agogo baya?"

"Bangane ba Arɗo?"

"Ina nufin ka dawo yadda kake a da dan mu taimaki yankinmu, Kayan aikinka da kaje ka binne kaje ka
hakosu saboda......" girgiza kai Baffa ya hau yi yana ja da baya, ya ce

"A'a Arɗo na riga da nayi alkawari ba zan sake ba, har kwanan gobe ban manta da kuskuren da na aikata
bisa tsautsayi a baya ba, abun shekara ashiri amma a yanzu gani nake yi yanzu abun ya faru, Arɗo ba a
son raina na kashe BANJU ba, na kashesa ne sabida shafe mutanen yankin nan da ya fara, sannan idan
baka manta ba yace zai dawo daukar fansa a kaina da mutanen yankin nan! tunda na kashe Banju nayi
alkawari na dai na! duk wani abu wanda na gada daga gareka da kakanni! Dan Allah Arɗo a bar wannan
maganar"




13
HAUSACINEMA.COM


Dambe suke yi sosai a tsakaninsu ba ji ba gani, yayinda Azima ta yanki Aziza a gefen wuya,nan ta koma
mutun ta faɗi kasa, ita ma Azimar rabi mutum rabi Macijiya ta zama tana kallon Aziza ranta a haɗe
idonta ya kara rinewa zuwa blue, a hankali Aziza ta miƙe tsaye tasa hannu ta karkaɗe jikinta ta juya
baya,ta sa hannu a gefen wuyanta inda yake zubar da jini ta lumshe ido, kamar ƙiftawar ido da bismillah
ta shafe wajan, sannan ta daga hannunta sama ta haɗa wani guguwa mai karfin gaske ta turawa Azima,
Azima bata ankara ba taji anyi sama-sama da ita, sai da taje can sama kafin ta faɗo timm! Da kasa nan ta
koma mutum, a hankali Aziza ta juyo tana kallonta yau fuskarta babu fara'a, haqiqa dan faɗa su na faɗa
amma basu taba dambe ba, bar su a cacan baki.

Saurin tashi Azima ta yi ta sake komawa macijiya ta yi hajijiya ta tada ƙura ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login