Showing 84001 words to 87000 words out of 94205 words
ta rasa yadda zata yi, Mom tace
196
HAUSACINEMA.COM
"Nawaz Al'mazeen ku kama matayenku ku saka su a mota, bari na yiwa Umma magana (Umma yaya ce
ga Mom wanda itace zata tsaya a karasa biki a kai sultana dakinta) har zasu fita sultana ta fashe da kuka
tace
"Aziza! Za ki dawo? Kiyi min alkawari zaki dawo?" itama Azizan kuka tasa suka rungumi juna, Nawaz zai
ja Aziza mom ta daga masa hannu alamun ya barsu, dagowa Aziza tayi tace
"Ban san me zance miki ba Antyna...."
"Shiiiii! Yanzu kece Antyna tunda da auren Yayana a kanki" murmushi Aziza tayi hawaye na zuba a idonta
tace
"Ba a canzawa tuwo suna, ke ɗin antyna ce wacce nake ji da ita sosai, da fari zan fara neman gafararki!
aurenki guda amma ta sanadina da yar uwata ba a miki shi yadda ya kamata ba, kiyi hakuri ki yafe mana,
ga shi zamu kara tafiya da mom,mu kuwa me zamu ce muku? Sai dai mu muku fatan Allah ya muku
sutura ranar lahira, dan kuwa kunyi mana a duniya"
Sake rungumeta Sultana tayi ta ce
"Ni kam alhamdulillah! Naji dadin aurena,dan kuwa an daura tare da Yayuna, sannan karki damu da
batun tafiya da Mom, Umma tamkar mom take har ma taso tafi mom, lafiya za a kaini gidana,ni dai
fatana dan Allah kiyi hakuri ki dawo a kan lokaci,kinji?" share hawaye Aziza tayi ba tare da tayi magana
ba dan bata sa a ranta zata dawo ba, Nawaz ne ya kama hannun Aziza ya jata ya rabasu da sultana suna
kuka suna komai, mom ce ta rufe musu fuska kowa ya kama matarsa a haka suka sauko jama'a sai guɗa
ke tashi, da manyan motoci biyu zasu tafi wanda zai juri wahala da afkawa jeji mai gudu, mom da Hajiya
Luba Maman Beenah kenan ba dan taso ba haka aka sa ta shiga mota,Maman Hanan kuwa cewa tayi wlh
ba zata je ba, da kanin mahaifinsu Nawaz Alhaji Karami da Malam Yunusa abokin Mahaifin su Nawaz.
Al'mazeen da Azima suna zaune a bayan mota Nawaz da Aziza suna zaune a gaba,mota daya suke su
hudu Nawaz ke driving, Azima tamkar gunki haka ta koma, lokaci zuwa lokaci Al'mazeen zai waiga ya
kalleta, sunyi nisa Al'mazeen yace
"Aziza? Hope dai Azima lafiya take?"
Gya ɗa kai Aziza tayi a sanyaye tace
"Lafiya take Hamma Mazeen, kawai na kafar mata da dafi ne idan ba haka ba sunanku gawa dan Banju
zai kasheku! Ni ba zata iya kasheni ba, kuma kafin ace nayi kokarin yin wani abu dan dakatar da ita zata
iya kashe ko da mutum daya ne ba zan so hakan ba,zamanta a haka shine mafi alkairi har mu isa" jinjina
kai Almazeen yayi yana kara maida idonsa kan Azima.
197
HAUSACINEMA.COM
Basu isa yola ba sai yamma lilis, dan haka Aziza tace ba zai yu su afka jeji ba su bari su sake yin asubanci
gobe, dan haka suka kama hotel inda zasu kwana.
A gida kuwa karfe biyu Umma tayi oya-oya aka dauki amarya sultana aka kaita danƙareren gidanta da
Khalil dinta ya gina aka ajiyeta, Umma ce tayi mata komai tamkar Mom tana nan, Umma ce ta wakilci
mom a komai aka sallami baki da wasu daga cikin yan uwa.
Sadda aka ajiye sultana a gidanta za a watse a barta tasha kuka, duk hankalinta da adduarta Allah yasa
Aziza ta dawo.
Kamar yadda suka ce da washe gari asubanci sukayi, sallar asuba kawai suka yi suka yanki cikin jeji inda
zai sadasu da ƙauyen yankin kwana, Aziza ke nuna musu hanya, Nawaz ya kalleta yace
"Zamu iya isa a yau?" tace
"Hamma Nawaz yadda wannan mota ke gudu kamar a iska inaji nan da yamma zamu isa"
"Kai har yamma?" Nawaz ya tambaya a gajiye dan tsakani da Allah ya gaji, yadda ya zare ido ya ba wa
Aziza dariya dan haka tayi murmushi, suna tafiya Nawaz ya cewa Mazeen ya musu video recording ɗin
hanyar, Mazeen ya ciro waya ya hau musu video ɗin.
Yau tinda Hajja ta farka gabanta ke faduwa, ga shi jiya tayi mafarkin Azima da Aziza sun dawo, duk da
mafarkin ba sabon abu bane a wajanta.
Da yamma ligis wajan irinsu shidda haka Aziza ta shigo yankinta wani murna da annashuwa takeji,
yayinda hawaye ya b'alle mata, hakika yanayin al'karyan ya tafi da zuciyar su Nawaz, gari kore shar dashi
abun sha'awa ma sha Allah, ga korayen shuke-shuke da 'ya'yan itatuwa, yankin kwana sun ga abunda
basu taba gani ba, dan tun farkon shigowar su Nawaz a idon Salti ɗan gidan jauro nan yaje ya baza a gari
ya ga wasu sabbin masifa ya shigo musu gari, wasu bayyanannun aljanu,nan yara da manya aka hau bin
motar har gaban kofar gidan Baffa, nan aka hau cewa a kofar gidan Magaji masifan ta tsaya, mota na
tsayuwa da gudu Aziza ta fito, su ma su mom fitowa sukayi,yayinda Mazeen ya fito da Azima Banju, dasu
mom suka rufawa Aziza baya, mutane an cika ana kallon su mom, ko sallama Aziza bata iya yi ba tana
shiga ta tsaya turuss tana kallon mahaifiyarta wacce ta rame sosai ta karayin wani fari fal da ita, Hajja na
duƙe ta dibi ruwa a kwarya zata zagaya kewaye, su Mom ne suka shigo suma, cikin wani irin kuka da
shauki irinta 'ya wanda takeji a kan mahaifiyarta murya na rawa mai fizgar kuka Aziza ta ce
198
HAUSACINEMA.COM
"Hajja!" kwass!! Hajja ta saki kwarya ta juyo da sauri, haba duk daren daɗewa muryar Azizanta ba zai
goge a kunnuwanta ba, kallon Aziza Hajja ke yi jikinta na rawa tama kasa magana, da kyar Hajja ta ce
"Dan Allah Aziza yau karki b'ace ki barni, na yarda zan dinga zama da gizon naki dun Allah karki tafi" da
gudu Aziza ta shige cikin hajja ta riƙeta gam-gam suna wani irin kuka mai ban tausayi, harta su Mom
suma hawaye sukeyi, Malam Yunusa ya kalli Mom ya ce
"Hajiya Kamila(mom)Allah ya saka miki da mafificin alkairi, Nawaz da Al'mazeen Allah ya muku albarka"
suka amsa da Amin.
Ɗago Aziza daga jikinta Hajja tayi tana shafa fuskarta, Aziza cikin dashashshiyar muryarta tace
"Hajja nine na dawo, mun dawo" Hajja na shirin magana sai ga Baffa wujigan a muraran, yana can garkin
shanakunsa Salti yaje ya samesa yace ai ya ga bataliyan aljanu sun nufi gidansa yanzu haka aljanun suna
gidansa, shiyasa Baffa yazo a hargitse, Baffa na shigowa da sauri Aziza ta zo ta ce
"Baffa ni ce Azizanka! Baffa na dawo, kace kar na dawo sai da Azima, Baffa gata nan ga Azima nan" duk
irin kunya irinta fulani nan Baffa ya rungume Aziza yasa kuka, an jima ana koke-koke, Sarki Chubaɗo
dasu mai unguwa ori dasu Garkuwan yankin kwana, kai duk jama'ar yankin kwana an taro agidan Baffa,
sai bayan an gama kuka tukunna aka basu abun zama, Sarki Chubaɗo yace
"Kafin a zauna ya kamata mu fara sallar magriba, hakan kuwa akayi, Aziza ta basu ruwa sukayi Alwala
suka nufi masallaci.
A cikin gida ma Hajja ce ta ba wa Mom da Maman Beenah ruwan alwala, taki yarda ta daga kai ta kallesu
sabida kunya irinta fulani, Maman Beenah kuwa ba bakinciki kauyen ya mata kyau ya burgeta.
Bayan sun idar da sallar, Hajja na zaune kusa da yaranta nan suka hau gaisawa dasu mom,mom ta kalli
Hajja tayi murmushi ta ce
"Kyawu! Kyawun hali! Kunya! Natsuwa! Ashe duk ba a banza Aziza ta dauko ba, ta biyo Mahaifiyarta ne,
dadtako halin girma! Jarumta a fuska da kuma jiki ta biyo halin mahaifinta ne! Ina tayaku murna da
samun 'ya kamar Aziza" Al'mazeen da suke shigowa cikin gidan yace
"Kai mom,Aziman fa?"
"Har da itama mana"
"To kishi kakeyi dan an yabi Aziza?" cewar Nawaz yana hararan Mazeen, murmushi su Arɗo sukayi
sannan aka zauna aka hau gabatarwa da juna kai, mom ce tayi musu bayanin komai har izuwa auren da
199
HAUSACINEMA.COM
su Azima da Aziza suke da shi a yanzu, sannan ta gabatar da Nawaz a matsayin mijin Aziza ta gabatar da
Al-mazeen a matsayin mijin Azima, ta ɗan bada tahirin kansu a gajarce, dago ido baffa yayi ya kalli
Al'mazeen ya Kalli Nawaz kawai sai ya fashe da kuka, Baffa Mandi ya hau bubbuga kafadun Baffa yana
fadin
"Alhamdulillah! Hakika Allah baya bacci,kuma yana tare da masu hakuri da masu jahadi da sadaukarwa,
hakika kayi jahadi wa yankuna da dama, kayi sadaukarwa wa yankinka da komai naka, sannan kazo ka
kara bi da hakuri da juriya, taya Allah zai barka a haka Magaji? yanzu dubi ka ga mijin da Allah ya bai wa
Azima da Aziza, da munata tunani da kokonta wa zai auri Azima da Aziza dan ya kawo mana karshen
Banju, sai ga shi Allah ya turo mana mutane daga wasu duniya daban"
Sarki Chubaɗo ya ce
"Tabbas kuwa Magaji,kai ba mutum bane kamar kowa bane, hakika muna yiwa Allah godiya daku
sirakananmu, mun gode da wannan jahadi Allah ya baku lada" aka amsa da amin, nan Sarki Chubado da
mai unguwa ori suka bada umarni a shiryawa manyan baƙi kuma sirakanan Magaji Bawa Shugaban
garkuwan kwana abinci mai rai da lafiya, nan aka kawo wa su Mom hadaddiyar kindirmo yasha damu,
Inna wuro ta ce
"Wata kila ba zaku iya cin abincin mu ba" Mom tace
"Ai idan muka sha wannan furan wlh alhamdulillah sai kuma gobe" Al'mazeen ya ce
"Ana ta magana amma banji anyi maganar matata ba?" Baffa ne ya sunkuyar da kai Hajja kuwa rufe
fuska tayi, Arɗo ne yayi murmushi ya ce
"Ohh Allah Kaɗo babu kunya, yanzu kai a gabanmu kake maganar matarka?"
Almazeen ya sosa keya ya ce
"To ai kaka gani nayi to bari dai nayi shuru" aka sa dariya, Baffa yace
"Kayi hakuri ɗan nan, sakin matarka ba tare da kayan aiki ba babban hatsari ne ga mutanen yankin nan
gabadaya, ka jira har zuwa gobe idan na daure shi tukunna, ai yanzu ba matarka bace katon aljani ne
mugu" shuru Almazeen yayi yana kallon Azima wacce ta koma gunki, a hankali Aziza ta miƙe zata shiga
bukkarsu, jiri ne ya kwasheta nan ta fadi, kafin kowa yayi kanta Nawaz ya fara dagota, Hajja kuwa ganin
su Mom sun rufu a kan Aziza yasa ita taji kunya ta koma gefe tana leken fuskar Aziza, Baffa ne ya kama
hannunta ya ce
"Ya salam! Aziza an huda jikinki ko?" gya ɗa kai Aziza tayi tana jan numfashi, Baffa yace
"Dole sai an nemo furen huriri"
200
HAUSACINEMA.COM
"Me hakan yake nufi Baffa?"cewar Almazeen
"Ai kasan ita ba asalin mutum bace,maciji kuma baya son tab'o"
"Amma an harbi Azima bai bata illa har haka ba?"
"E sabida ita Aziza Banju ya rigada da ya maidata macijiya shine dalili, ga shi yanzu dare yayi ina zan
samu furen huriri?" tashi Baffa ya yi ya fita zaije jejin kwana ko Allah zai sa ya samu, yana fitowa da Inno
Fandi ya hadu ta mika masa furen huriri tace
"Ina matukar farin ciki da Allah ya dawo da Azima da Aziza lafiya, sai kuma shirin kashe Banju a gobe
ko?" Baffa ya sosa kai yace
"Humm Fandi, abun kunya nake jin kunya" Inno Fandi ta gano abunda yake nufi dan haka ta hau masa
dariya, dan kunyar kuwa na kusantar Azima da Al'mazeen zaiyi ne,tunda dole sai Almazeen ya kusanci
Azima kafin Banju ya fita a jikinta a kashesa.
Da sauri Baffa ya koma ciki, Ardo yace
"Magaji ina da kaje?"
"Da wai zanje jejin kwana ne nemo furen huriri to sai Fandi ta kawo mini" jin sunan Inno Fandi yasa Aziza
fara murmushi.
Jiƙa mata furen huririn akayi,tana sha ta ware.
Su mom sun saki jiki da mutanen yankin kwana sai hira sukeyi kamar an jima da sanin juna.
Sai da dare ya tsaga Ardo yace su mom suje su kwanta su huta, su mom gidan Arɗo aka kaisu aka gyara
musu wajan kwanciya, su Nawaz kuwa gidan Sarki Chubaɗo aka kaisu.
A ranar Aziza da Hajja basuyi bacci ba kwana zaune sukayi suna kuka suna hira, Azima na kafe a gefe, sai
da akayi asuba tukunna Aziza ta fara jin bacci Baffa kuma ya ce mata ta fito zai daure Banju sai ta sakesa,
Aziza ta miƙe tana hamma dan bacci takeji.
Kayan yaki Baffa ya tanada, sai wajan takwas jama'ar yankin kwana suka hallara, Baffa ya kalli Aziza ya
mata ido alaman ta saki Azima, gya ɗa kai Aziza tayi tasa hannun ta dafe goshin Azima wani haske na
shiga goshin Azima, wani ajiyar zuciya Azima ta sauke, nan ta dawo hayyacinta, idanunsu ne ya sarƙe da
na Baffa
201
HAUSACINEMA.COM
"MAGAJI BAWA!!?"
"na'am BANJU! maraba da dawowa Yankin kwana!"
"Wlh Baffana bani bace! Wlh ban yi yunkurin kasheka ba!" gya ɗa kai Baffa ya yi yana shafa kan Azima ya
ce
"Na sani Azima" riƙe Baffa tayi gam tana kan ci gaba kuka, nan al'umman yankin kwana suka hau
hamdala ana taya juna murna, wa inda sukayi wauta da farko ta hanyar dukan Aziza suka hau ba wa
Baffa hakuri yace shi kam ya wuce a wajansa, nan aka zauna ana ci gaba da jajinta lamarin, lokaci zuwa
lokaci Azima tana ɗaga ido ta kalli Almazeen wanda yake lullubi idonsa a lumshe bai san hayaniyar da
ake yi ba.
Maga isar da sako ne ya shigo da sallama yace Sarakunan Yankuna da Muƙarrabansu sun fara isowa da
wani lokaci za a fara fafatawa?" Baffa ya ce
"A shirye nake, amma a bar fafatawar sai anyi sallar la'asar da yamma kenan, a ƙara shiryawa mutanen
yankuna wajan zama mai kyau da abun motsa baki dan kar su gajiya, sannan a dama musu nono mai
kyau a tabbatar an basu isasshe ba ƙasasshe ba" Maga Isar da saƙo ya amsa da to, sannan Baffa yace
"Mu tafin ku dan a kara shiri" dukkansu suka fice aka bar Nawaz da Azima da Aziza, Azima idonta na kan
Almazeen wanda lokaci daya taji zuciyarta ta harba da shi, a yanzu yana cikin wannan halin ne sabida ita,
wanikuka Azima ta kara sakawa tana rufe fuskarta da sauri Aziza tasa hannu ta riƙo hannunta tana fadin
"Haba Azima miye haka? Godiya zakiyi wa Allah dasu Mom da Hamma Mazeen" cikin kuka har tana
sheshsheƙa ta dago idonta wanda yanzu ya koma daidai amma dik da haka basu da baƙin ido ta kalli
Aziza tana girgiza kai ta daga hannuwanta hawaye na zuba ta ce
"Aziza! Ni! Wai ni da kaina na ke son kashe mahaifin da ya haifeni! Wai ni da kaina na rayuwa bana
bautar wanda ya halicceni! Wai ni da kaina mutane suka shiga masifa da tashin hankali! wai ni da kaina
na maida yar uwata ta biyuna macijiya! Wai ni da kaina....!" kuka yaci karfinta da sauri Aziza ta
rungumeta tana bubbuga bayanta itama tana kuka
"Taya zan manta da wannan abun a rayuwata! Kenan mu haka kaddararmu take!" ɗago fuskarta Aziza
tayi tace
"Karki yi sab'o, ki godewa Allah, sannan duk abunda kika lissafa ai bake kikayi ba Banju ne ya yi, dan haka
ki bar fadin haka Sis" cikin kukan tausayi da Azima ta kasa tsayarwa tace
202
HAUSACINEMA.COM
"Amma da jikin wa!? Da fuskar wa?"
"Koma da miye ne komai zan zama tahiri, ki ta nanata kalman Innalillahi wa inna ilaihirrajiun! Yafi
wannan sambatun da kikeyi dan bana so,kina ji na ko?" Azima ta gya ɗa kai hawaye na kan sauka tana
kallon Almazeen wanda Nawaz ke riƙe da hannunsa yana ji kamar yasa kuka dan tausayinsa, zuwa can da
suka gama kukan Nawaz ya kalli Aziza ya ce
"Tashi mu tafi watakila yanzu kam ana can filin yaki, zo muje karo na farko a rayiwata naga yadda ake
faɗa tsakanin mutum da aljan" tashi Aziza tayi ta kalli Azima tace
"Ki kula da kanki da kuma Hamma Mazeen uhum?" Azima ta gya ɗa kai, Nawaz da Aziza suka fita, suna
fita Azima ta miƙe a hankali ta karasa jikin gadon ta kwanta a kusa da Almazeen har yanzu jikinsa da zafi
sosai, tana kwantawa ta kama hannunsa tana kallon kyakkyawar fuskarsa ta ɗora hannunsa a fuskarta ta
lumshe ido.
Hakika su Mom sun sha mamakin ganin mutane him a wannan alkarya, mutanen yankuna sun zo daga
yankuna daban-daban, jama'a an cika ana kallo, Aziza na zaune kusa da mom, Nawaz yana gefen hannun
hagunta, ya ce
"Mom wlh naso ace sultana tana nan da ta ga abunda take kalla a zahiri a tv" mom tayi murmushi.
A hankali Baffa ya fito yana riƙe da zureren takwabinsa wanda ya kashe Banju da shi a karon farko amma
wannan karon bai yi amfani da zaren sakar dana ba, dan ko ya koma jejin lore ba ba shi za ayi ba,amma
duk da haka yau sai ya kashe Banju da yardan Allah.
Kunce Banju Baffa ya yi, Banju yana ganin takwabin hannun Baffaya ce
"Magaji! ka ajiye takwabin nan ba da shi zamu gwabza ba" murmushi Baffa ya yi ya kalli Nawaz ya miƙa
masa takwabin, zuwa Nawaz ya yi ya karba yana riƙewa sai da yaji damtsen hannunsa ya girgiza, kara
sarawa