Showing 45001 words to 48000 words out of 94205 words
da zan muku, ruwa zaku sha? Ko abubuwan da kuke sha a robobi zaku sha?" cikin kuka
da majina da zufa suka ce ruwa, Azima tasa hannu ta janyo ruwa ta zuba a kofi uku ta ce
"Duk wanda baya son mutuwa ya sha wannan ruwan!" jikinsu na rawa suka dauka suka kafa baki suka
kwankwaɗe suna kan bata hakuri, kamar da minti biyu tsakani Hajiya ta hau tari tana rike wuya, da sauri
Zuby ta tashi tana fadin Hajiya meya sameki,nan ita ma ta hau riƙe wuya tana tari, Baby ma haka, tari
sosai suke yi jini na fita baki da hanci, Azima ta miƙe ta ce
"BANA MANTUWA! BANA YAFIYA! NA RIGA DA NA ZUBA DAFI TA YATSAR HANNUNA!" tana gama fadi ta
shiga ta dauki kayanta na fulani da Lantana ta wanke mata ta saka ta fice ta bar gidan.
Kwanan Aziza biyu a asibiti jikin nata alhamdulillah duk da da ace taso zata iya warkar da kanta amma
bata so ta sakawa su Mom da Sultana shakku a ransu su fara zarginta, sannan yanzu idan tace zata gudu
bata san duniyar da Azima take ba kuma tana ji a jikinta duk inda Azima take bata shuka alkairi, abu biyu
ne ya haɗe mata waje guda ya jagula mata lissafi, bata san taya zata fara neman Azima ba tunda basu
al'karya daya, sannan bata san wani hali iyayenta suke ciki ba,duk da tana da yaƙini a kan Baffa zai kula
da Hajja sosai shima zai kula da kansa, tana zaune tana tunani, wani dabara ne ya faɗo mata, wannan
dabara kuwa shine ta fara yawon bin garurruka! duk garin da suka haɗe da Azima idan ta lumshe ido
zata iya hangota ta cikin tauraronsu, da wannan tunani ta samu karfin guiwa,lumshe ido tayi ta shafi
tafin hannunta amma bata ga Azima ba, a fili ta ce
"Hakan na nufin bamu gari daya kenan, wannan hajiyar (Mom kenan) ta kira sunan wannan yankin da
kaduna ko? Ina gani gwara na tambayi wannan yarinyar tata sunayen yankuna sabida naje na dudduba
Azima, amma kuma kafin na tafi dole ina bukatar kudi, hakan yana nufin dole na yi musu aiki dan na tara
kudin neman Azima? Idan kuwa haka ne Banju ya cuci rayuwarmu,ga shi wahalar a kaina da Baffa yake
karewa" ta karasa maganar da sakin kukan tausayi, tana sakin kukan su Mom da Sultana suna shigowa.
99
HAUSACINEMA.COM
Ganin tana kuka yasa suka karaso wajanta da sauri suna tambayarta ko akwai inda yake mata ciwo ne?
ta girgiza musu kai alaman a'a, Mom ta ce
"Yarinya? Kiyi hakuri kodayaushe kina cikin kuka, ina yan uwanki suke? A wani ruga kuke a garin yola
idan yaso gobe sai a maidaki" jin haka yasa Aziza kara sakin sabon kuka,inaa ai ba zata so ta koma ba
tare da burin Baffa na su dawo tare da Azima ba, mafita daya ne shine kawai ta yi karya,cikin kuka ta ce
"Yan fashi ne suka fada rugarmu suka kashe mana kowa, nima da kyar na sha,dan Allah Hajiya ki taimaka
mini na dinga yi miki aiki kina biyana,yanzu idan na barku ban san inda zan hadu da mutane nagari
kamar ku ba dan Allah Hajiya!" Aziza ta fada tana kuka sosai,jikin Mom ne ya yi sanyi sosai, Sultana ma
kwalla ya cika a idonta ta kalli Mom ta ce
"Mom mu dauketa kawai,tunda dama kinga Haule ta yi aure,ita wannan ma zata jima " Mom ta ce
"To shikenan kira mana wani Dr ya zo ya rubuta mana sallama,dan munyi waya da Nawaz yace sai gobe
ko jibi zai dawo,kuma yace idan har jikin nata da sauki mu koma gida, to gwanda gidan dai zaman asibiti
ba dadi garesa ba"
"To Mom" Sultana ta fice bata jima ba suka dawo da wani likita ya rubuta musu sallama suka yi gida,
dakin masu aiki dake kasa wajan cikin parlour bayan step dakin mai aikinsu na da Haule wacce tayi
aure,bama iyakar Haule ba duk masu aikinsu nan ne dakin da suke zama,babban daki ne dasu babban
gado da wardrope da toilet da komai da komai, Sultana ce ta nuna mata yadda zata yi amfani da
komai,bayan ta nuna mata Aziza ta kalleta ta ce
"Na gode Anty Sultana" Sultana ta yi murmushi ta ce
"Ba komai mai kyau, amma meyasa kike son rufe fuskarki? Har yanzu baki saba damu bane?"
Cikin in-ina Aziza ta ce
"Inada matsalar ido ne, tun ina yarinya bana son haske, sannan bana iya kallon mutane da idona shiyasa
mahaifiyata ta bani wannan mayafin ina lullubi da shi, gashi na kuma na fiddo da shi dan ya rufe min
daya idon da zan dinga ganin hanya"
"Ayya Subhanallah! Idan Brother ya dawo zan gaya masa sai ya duba miki idon, watakila idan aka dace
sai ya miki magani"
Da sauri Aziza ta ce
100
HAUSACINEMA.COM
"A'a Anty Sultana karki gaya masa halittatace a haka aka haifeni"
"To shikenan,bari na bar ki ki huta sai na shigo anjima,idan kika warke sosai akwai abunda zan dinga
koya miki,ina sonki da ƙawa! kinga bana da ƙawa bana shiga hidimar mutane amma ke kin shiga raina"
murmushi kawai Aziza ta yi dan ita kadai tasan yaƙin da yake gabanta, tashi Sultana ta yi tana fadin
"Bari naje na kawo miki wasu kayana ki saka yanzu kiyi wanka duk da nasan kayan zasu miki yawa, amma
ki canza na jikinkin nan" Aziza ta amsa da to na gode sosai, Sultana tana fita Aziza tayi shuru tana saƙa da
warwara, zuwa can ta mike zata shiga bayi har ta manta da ciwon kafarta sai ji ta yi ta takesa, zafi taji ta
saki kara sannan ta koma ta zauna tana fadin
"Ba zan iya jurewa ba" hannu tasa ta shafe wajan nan kafarta ya dawo dai-dai sannan ta shiga ta yi
wanka kamar yadda Sultana ta nuna mata amma bata wanke kanta ba,tana fitowa Sultana na shigowa ta
kalleta ta ce
"Ba ki wanke kanki ba? To ki bari karki wanke,idan kikaji sauki sosai sai muje a wanke miki, wannan
gashin naki ai sai wajan masu salon, yanzu ga wa innan kayan ki fara lallabawa da shi Mom ta ce zata
siyo miki wasu" godiya sosai Aziza tayi,ta dauki wani dogon abaya ta saka ya mata kyau duk da ya mata
yawa tasa ta dau hijabi ta tada sallah,ta jima tana addua Allah ya bata mafita a kan wannan babban
lamari nasu, kafin sultana ta shigo ta kirata ta fito taci abinci.
KUNTAU.
wani hamshakin gate Azima ta tsaya tana kallon gate din, ganin tsaruwarsa da haduwarsa zuciyarta ne
ya raya mata wannan gida taji gidan ya kwanta mata a rai,kuma dole uwar naki sai ta zauna a wannan
gida ko ana ha maza ha mata, da wannan tunani ta yi gate din ta hau kwankwasawa.
101
HAUSACINEMA.COM
Da sauri Sultana ta fito tana kwalawa Aziza kira, fitowa Aziza ta yi ta ce
"Gani Anty Sultana"
"Yawwa Aziza dan Allah zo ki tayani kwashe tray zan kai wa Yaya abinci ashe ya dawo"
"Oh har ya dawo?"
"Nima wlh ban sani ba sai da ya kirani a waya"
"Ayye" cewar Aziza ta duƙa tana daukar tray din da Sultana ta gama jera su plates, sannan itama ta dau
ɗaya tayi gaba Aziza ta rakata a baya.
Da sallama suka shiga Sultana ce a gaba sai Aziza dake binta a baya kanta a duƙe cikin hijabi gabanta na
faduwa, yana kwance a dogon kujera yana sanye da jallabiyya, amsa sallamar tasu ya yi yana tashi
zaune, da sauri Sultana ta ajiye tray din hannunta ta zauna kusa da shi tana masa sannu da zuwa,kanta
ya shafa cikin kulawa yana amsawa, duƙawa kasa Aziza ta yi bakinta na rawa ta ce
"Ina wuni HAMMA NAWAZ ya hanya?" rassrassras! gaban Nawaz ya faɗi ya ƙura mata ido amma ta
gefen ido yana kallon yadda take rirriƙe yatsun hannunta jikinta na rawa daga nesa yake karantar
yanayinta duk da ta boye fuskarta cikin hijabi sai saitin ƙaramin bakinta da yake iya hangowa wanda shi
ma ke b'ari,
"HAMMA NAWAZ!" yake ta nanatawa a ransa, Aziza kuwa jin bai amsa mata gaisuwarta ba alhali ya
amsa na kanwarsayasa ta tashi a hankali jiki a sanyaye zata fita, watakila baya amsa gaisuwar masu aiki,
har ta kai bakin kofa sai taji Sultana na faɗin Aziza ina kuma zakije?"
"Amm dama Anty Sultana dama akwai kayan da ban....kwa.She...ba...ina...so..ne...naje....na kwashe" ta
karasa maganar da in-ina tana fita da sauri, cikin fuskar tausayi Sultana ta juyo ta kalli Yayanta ta ce
"Bro,wlh Aziza bata ji dadi ba, ta gaisheka baka amsa ba fa,kuma kamar ma naga tsoronka takeji"
"Za ki yi serving ɗina ne ko zaki cika min ciki da magana?" ya faɗa ba tare da ya kalleta ba, kasancewar
tasan halinsa yasa ta zuba masa abincin ta ajiye masa komai sannan ta fice itama,tana fita ya dauki
spoon zai kai abincin bakinsa sai ya tsinci kansa cikin rashin jin dadin amsa gaisuwarta da bai yi ba,
HAMMA NAWAZ! ya faɗa a fili ya saki murmushi jin yadda ta kira cike da harshen fullaci kuma sai sunan
ya yi daɗi a bakinta, da kyar ya lallaba ya ci abinci dan kuwa yaji dadin abincin sosai yaci yasha zobon da
102
HAUSACINEMA.COM
suka haɗa ya yi hamdala, nan ya zauna suna waya da amininsa yana gaya masa ranar thursday In sha
Allahu yana hanya zai bi jirgi amma sai ya ƙara komawa ta abuja, Allah ya kawo shi lafiya ya yi masa,yana
kan waya har aka kira sallar magriba dan haka yace masa za shi masallaci suka yi sallama akan cewa sai
sunyi waya anjima, alwala Nawaz ya yi ya tafi masallaci bai dawo ba sai da ya haɗa da isha'i, ko da ya
shigo gida babban parlourn gidansu ya wuce da sallama ya shiga a lokacin Aziza na riƙe da kaskon
turaren wuta ita kadai ce ma a parlourn, jin sallamarsa yasa jikinta ya dauki rawa wanda bata san dalilin
hakan ba, cikin rawar murya ta amsa sallamar ta shi ta ajiye kaskon hannunta tana shirin shigewa daki da
gudu taji muryarsa kamar daga sama
"Ya kike? ya jikin naki? Yanzu babu inda yake miki ciwo ko?" ya faɗa lokaci daya,cak Aziza taja ta tsaya,a
iya saninta Sultana da Mom suna sama,to kenan da ita yake yi? take tambayar kanta, bata amsa ba bata
juyo ba sai da taji ya sake fadin
"AZIZA baki ji ina miki magana ne?" sai a sannan ta juyo murya na rawa ta ce
"Alhamdulillah na warke" tana gama fadi ta shige daki, shuru ya ɗan yi yana nazartan yarinyar daga baya
kuma ya yi tsaki ya hau sama,dakin Mom ya je ya kwanta a gadonta suna hira, Mom ta ce
"Bana ma kenan a kasar waje zaku sake yin Azumi ga Azumi ya ƙarato, meyasa ba zaka sa amininka ya
dawo nigeria kuyi azumi a gida ba? Bana dai ace kunyi sallah a kasarku tare damu"
"Mom kema kin san ba zai dawo ba ko da na faɗa masa, azumi kuma In sha Allahu mai zuwa idan rai ya
kaimu ai muna nan a gida In sha Allah" Mom ta sauke ajiyar zuciya ta ce
"Ai ya kamata,ni na ƙagu ku dawo dan ku nemo matar aure ku aura,barin ma Son yana da bukatar mata
wacce zata kula da shi"
"Ai ya samu Mom"
Mom ta ce
"A'a gwara dai fa ya samo mai tarbiyya da natsuwa da hankali" Nawaz ya tabe baki ya ce
"Humm wanda yake fadin zai aura ni kwata-kwata bata min ba,bamu shiri da ita ko kadan amma shi yace
zai aureta,kuma abun takaicin fa Mom shima ba sonta yakeyi ba"
"To ina ruwanka? kai fa matsalarka Nawaz zafin zuciya" Mom ta fada tana kallonsa
"Mom ai ba zan can ina ruwana bane ko zafin zuciya,magana ce ta gaskiya,kuma ai abunda ya shafesa ya
shafeni"
"To kawai ka tayasa da addua shine babban soyayyar da zaka ci gaba da nuna masa"
103
HAUSACINEMA.COM
"In sha Allah Mom" daga haka suka ci gaba da hirarsu,bai baro dakin Mom ba kuwa sai sha biyu na dare
yana fitowa ya shiga dakin Sultana bata nan,tana can dakin Aziza tana koya mata karatu,cikin ikon Allah
Aziza ke ganewa, da bai ganta a dakin ba ya yi tunanin ko tana toilet ne dan haka ya wuce part dinsa ya
kwanta, sai sha biyu da rabi Sultana ta miƙe tana fadin
"To Aziza bari mu dakata da karatun haka sai Allah ya kaimu gobe kuma, yanzu akwai wani horror series
film din da nake kalla, 12 ake farawa a gama 1:30 ga shi yanzu har sha biyu da rabi sai dai na kalli
karashi,ko zaki zo muje ki kalla ne?" Aziza ta ce
"Me hakan ke nufi? shi horror din" sai da Sultana tayi dariya kafin ta ce
"Ina nufin fina-finan dodanni, kamar irinsu abun tsoro haka da film din macizai!"rassssss! gaban Aziza ya
buga ta yi sauri dago fuskarta ta kalli Sultana ta tsakiyar gashinta da ya rufe mata fuska,Sultana ta
kwashe da dariya ta ce
"Matsoraciya kawai,daga faɗa miki har kin firgita, wlh kuma fa Yaya ya hanani kalla har cewa yake min
ranar da na fara ganinsu a zahiri zan sani, yanzun ma inada tabbacin ya tafi part dinsa,kinga sai da safe"
tana fadi ta fice ta bar Aziza da zare ido tana tunanin ranar da Sultana zata ganta a macijiya mai zai faru?
Saurin kau da tunanin ta yi tana fadin "taya ma hakan zata faru?" ajiye tunanin tayi a gefe ta shiga ta
ɗauro alwala ta tada sallah,ta jima tana addua tana kuka tana neman taimakon mahaliccinta.
Kwana a tashi ba wuya a wajan Allah, Azima duk hankalinta ta karkata shi wajan sakawa su Maman
Hanan da Maman Beenah ido ganin manaƙisan da suke kullawa wanda bai ji ba bai gani ba, ta sha jin
haushin kanta a kan ƙutse da take yiwa wanda bai san da ita ba kamar yadda itama bata san da shi ba,
ga shi duk sadda ta yi yunkurin barin gidan sai taji kamar an ɗaure mata kafafu,wannan gida ya zame
mata karfen kafa.
104
HAUSACINEMA.COM
Ana gobe Nawaz sai tafi abuja jibi kuma zai wuce america ya yi wani mugun mafarkin da ya gigita
duniyarsa, Aziza ce ya gani a jejin da yafi na kullum muni tana kuka tana miƙa masa hannu ya taimaketa,
kar ya tafi ya taimaka mata,ƙiri-kiri ya ganta a macijiya.
Mai gadi ne ya leƙo jin ana kwankwasa kofa ya ga bafulatana tana tsaye kanta a duke,
"Baiwar Allah lafiya kuwa?" cewar Mai gadi,kuka Azima ta saka tana fadin ya taimaka ya yi mata magana
da masu gidan,mai gadi ya ce
"Baiwar Allah zan gaya miki gaskiya,me wannan gidan baya ma kasar gabadaya! Ya jima baya
nan,iyayensa ne a gidan,idan kuma wani neman taimako kikeyi to wallahi ba zaki samu komai a wajansu
ba,dan basu kyauta" Azima ta ce
"Ina da bukatar yi musu aiki ne,don Allah kayi mini magana dasu, ni ba kudinsu nake so ba"
Ganin yadda ta dage yasa Mai gadi fadin "to ɗan shigo daga ta ciki sai nayi miki magana dasu" Azima
tana sa kafa a gidan gabanta ya bada dammmm!! Da karfi sai da ta danne saitin zuciyarta,mamakin
faduwar gaban nata take yi, a kan benci mai gadi ya nuna mata ta zauna shi kuwa ya nufi babban
parlourn gidan da sallama, wata mata ce zaune a hakimce a kujera ta ɗora daya a kan ɗaya tana danna
waya,sallamar mai gadi ya sakata ɗagowa tana kallonsa da kyar ta amsa,
"Allah ya taimakeki ranki shi daɗe"
"Lafiya kuwa Ɗan'Bala?"
"Wlh Hajjaju wata 'yar fullo ce a waje take ta faman kuka a taimaka mata tana neman aiki, ina ga irin wa
inda 'yan fashi suke kai musu farmaki rugarsu ne, su kashe musu kowa su kwashe shanukansu, wlh
Hajjaju abun tausayi" shuru Hajjaju ta yi kafin ta kalli Dan'Balata ce
"Je ka shigo da ita" Ɗan'Bala ya amsa da to sannan ya fice da sauri ya zo ya samu Azima dake zaune ya ce
105
HAUSACINEMA.COM
"Zo mu shiga Hajjaju na kira" ba tare da Azima tayi magana ba ta tashi ta bi bayansa, suka shiga
parlourn, sosai Hajjaju ta karewa Azima kallo sannan ta kwala kiran wata mai aikinsu
"Hadiza! Hadiza! Hadiza!" wacce aka kira da sunan Hadiza ta amsa da na'am da fito da sauri ta duƙa a
gaban Hajjaju, Hajjaju ta ce
"Hadiza je ki yiwa Maman Hanan magana ki ce mata da sauko kasa yanzu" Hadiza ta amsa da to,sannan
ta hau da sauri, a tare Hadiza suka sauko da wata dakekkiyar mata wacce ita ma da ka ganta zaka san ta
yarda da kanta, tana tafiya a gaba Hadiza na binta a baya,tana saukowa ta ce
"Lafiya kuwa Maman Beenah?"
"E lafiya lau mai aiki ce dama za a dauka shine nace a kiraki tukunna"
"E ya kamata ai, idan yaso sai ta dinga gyara su dakuna tana sharewa da gogewa dan aiki ya masu Hadiza
yawa"
"To shikenan sai mu kirasa anjima mu gaya masa