Showing 129001 words to 132000 words out of 135555 words

Chapter 44 - AKIDATA book 1 HAUSA NOVEL

17 Jan 2026

677

kai Yusuf Asibiti, aka bar Widad da mutan gida tana ta faman yi musu kuka.

Gwaggo da Hindu ne suka iya zaman rarra????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? shin Widad.

Hari tace wai ke Wudas daga miji na zazzaSi seki zauna kita mana kuka, memakon ki masa Addu'a "

Ko kallon Hari ba tayi ba, ta mi?e ta tafi Wakinsu tayi kwanciyarta tana cigaba da kuka.

Nurat suka dinga communicatinga da cousin Winta akan yadda za'ayi belin Anwar.
Yanzu ma tana kwance akan gadonta hannunta Wauke da waya, tace" Brother ya ake ciki ne? Yakamata a gaggauta fitar da Anwar bashi da laifin komai fa"

"Nurat, kince bakyason asan muna ?o?arin belinsa, dan haka nake taka tsantsan, sedai abunda na gano shine tsare Anwar da akayi da manufa akayi shi, idan muka matsa tabbas za'a gano ke kikasa ayi belinamsa, tunda an san ala?ar dake tsakanin mu"

Cikin karaya Nurat tace "yanzu Brother babu abunda zaka iyayimin, Anwar be cancanci ya zauna a gurin nan ba"

Yace? "Nurat, lawyan mahaifiyarsa ma yana ta ?o?ari, amma har yanzu sun hana belinshi bansan meye abunyi ba, amma meyasa kika damu ya fita bayan kin san munin Ala?ar dake tsakanin mahaifinki da Daula?"

"Brother, idan akazo batun gaskiya da adalci ba'a kawo maganar ala?a, an cutar da Anwar fiye da yadda kake zato, shikaWai ne akan lamarin rashin lafiyar Alhaji Nasir, amma kalli abunda ya biyo baya, kodai an masa hakane dan a tozarta shi, ko kuma wanda ya sace shine yake son wanke kansa ta hanyar sawa a kama Anwar "

Barrister yace "Amma abun da mamaki ta yaya za'a iya sace mutum Attajiri kamar wannan a gadon Asibiti, kuma babu wani ?wa?waran bayani, abun da mamaki fa"

Nurat tace "Brother, dan Allah idan kana da dama ina son kazo in ganka, ina son mu tattauna wani zance da kai dan Allah"

Barrister yace? "Fara gayamin mana"

"A'a Brother, nidai so nake ina ganka, akwai magana ne a bakina"

"shikenan karki damu, Insha Allah idan ma samu lokaci zanzo insha Allah"

"Yawwa brother nagode sosai"

Ta kashe wayarta ta ajiye, shiru tayi abubuwa da dama suna damun zuciyarta, har yanzu bata ji alamar labarin inda su Yusuf suke ba, har yanzu bata sake jin wani magana game dasu ba, ta shiga tuna hirar da suka yi da Amal akan ala?ar Widad da Yusuf, ji tayi tana gumi dukda sanyin AC dake Wakin nata, amma ta shiga haWa gumi, mi?ewa tayi ta tafi toilet da niyyar ta watsa ruwa ta rage damuwa.

Har bayan magariba babu labarin dawowar su Yusuf, nan fa Widad ta sake gigicewa, ta shiga sintir a gidan nan tana?? "Allah ka duba Yoseef ka bashi lafiya, Allah ka bashi lafiya ba danni ba"

Gaba Waya tausayin ta ya hana Gwaggo nutsuwa, se aikin rarrashin Widad take, ita kuwa Hari harta ?ule saboda ganin abun na Widad take kama harda shagwaSa dan taga ana lallaSata, kawai dan mutum yana zazzaSi ta cikawa mutane gida da ihu.

Dukda Hanne itama tana cikin damuwar rashin lafiyar Yusuf, amma ji take kamar ta make Widad, gaba Waya ta hana mutane sukuni, se wani kuka take se kace wadda akace ya mutu.

Gwaggo ta zauna tasa Widad a gaba taci Abinci, amma ta gagara ci, Gwaggo tace "Amarya kiyi ha?uri, kici Abinci kinji, ki cigaba dayi masa Addu'a"

Cikin kuka Widad tace "Mama idan wani abu ya samu Yoseef sanadina ne, ba danni ba ba dan yasanni ba da duk baze shiga wannan halin ba"

Gwaggo tace "A'a kiyi ha?uri, Allah ne ya Wora masa, kuma ze yaye masa"

Har dare basu dawo ba, ba Saleh ba dalilinsa, hankalin Widad ya sake tashi, yanzu take sake ganin Amfanin Yusuf a tare da ita, dare yayi tace bazata iya zama a Wakin ita kaWai ba, Gwaggo tace taje Wakinta ta kwana, amma Widad fafur ta?i, ?arshe Hindu ce tabi Widad Wakinsu ta tayata kwana.




Har yanzu hankalin Umman Yusuf ya?i kwanciya, rashin Yusuf a tare da ita ba ?aramin abu bane a gurinta, sam rayuwa kawai take ba dan tana jin daWin rayuwar ba, Yusuf shine Wanta Waya tilo, yau a sanadin aikinsa yayi nesa da ita, bata san inda yake ba, gashi a hukumance babu wanda yace mata komai, se Suleiman da yake sintirin zuwa ganinta yana kwantar mata da hankali.

Wataran a Wakin Yusuf Win take kwana, taita kuka gwanin ban tausayi, tana matu?ar Wan nata rabuwarta da shi ji take kamar ta rasa komai na rayuwarta.



Bacci kam Widad ba tayi shi ba, Hindu tun tana rarrashin ta harta gaji tayi bacci, Widad kam kwana tayi tana Addu'a, Allah ya bawa Yusuf lafiya.

Se washegari sannan Ila da suka tafi kai Yusuf Asibiti tare yazo gidan, Widad na ganin shi a gigice tace "Ina Yoseef Win? Yana ina?"

Ila yace "ki kwantar da hankalinki, kwantar dashi akai, can cikin garin Bauchi muka kai shi, ya Wan samu sau?i Amma yaji jiki fa, kafin muje har Suma ya dinga yi a mota, amma ya farfaWo, baza'a sallameshi yau ba"

Hanne dake gefe tace? "Alhamdilillah"
Gaba Waya suka juya suna kallonta, banda Widad da tace "dan Allah dagaske kake ya tashi?"

Ila yace? "kwarankwatsa dagaske nake, dan yace in gaidaki, Saleh na baro a gurinsa"

Se a lokacin Widad ta Wanji hankalin ta ya Wan kwanta, harta samu tayi wanka, megari ma yayi ta mata Nasiha akan wannan kukan data dingayi.

Ramla kam a kusan buge ta dawo gidan nan, Hajiya Halima bata ga dawowarta ba, Amal ce taga wucewarta kamar tana tangaWi, binta tayi da sauri Wakinta, ta tarar tayi cilli da jakarta da takalmanta ta zube akan carfet tana bacci, Amal tace

"Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, Ramla me zan gani haka, meya same ki?"

Ramla kasa magana tayi se Waga hannu da take, cikin maye tace "ke.. Keee.. Nace ina ruwank.... Ki dani neeeee.. Ki fita nace"

"Ramla, shaye2 kika fara ne?"

Shiru Ramla tayi mata, ta cigaba da baccinta.

Gaba Waya hantar cikin Amal ya kaWa, tabbas Ramla shaye2 take, dan maye take yi, ta tuna yadda take bacci ba ?a??autawa, da tayi kamar taje ta gayawa mahaifiyarsu, se kuma ta tuna dama a ?ule take da Fahad da mahaifinsa, muddin ta gayamata za'ayi Satacciya ne.


Kwanan Yusuf uku a Asibiti, gaba Waya Widad ta rame, idanunta duk sun kumbura, jama'ar ?auyen duk sun san rashin lafiyar Yusuf, dan shike jansu Sallar Asuba da magariba zuwa isha'iyanzu, kuma ga karatu da yake koya musu suna jin daWinsa.

Widad ta zuba ido, taga ta ina Za'a dawo mata da Yusuf, dan Ila ya gaya musu ranar za'a sallameshi.

Gwaggo tasa akayi Abinci, aka dama Fura saboda Yusuf.

Ila ya shigo gidan da Sallama yace "ku kintsa, mun dawo ma?ota sun baibaye mota zasu shigo da shi"

Da ?yar Gwaggo ta janye Widad zuwa Wakinta, saboda maza zasu shigo, dukda damuwar da Widad ke ciki be hana Widad kallon ?akin Gwaggo ba, yasha jeren samiru da fanteku, ga gadonta na ?arfe me rumfa da mudubi, ginin tsurar ?asane Wakin amma yayiwa Widad kyau nesa ba kusa ba, ga ?warya da'akayi wa itama nata jeren, ?waryar ta sha zane mekyau, ga wasu a cikin ragaya, Widad bata taSa ganin irinsu ba"

Idan ba gizo kunnuwanta suka yi mata ba, to tabbas a cikin muryar mazan da suka yi Sallama hadda Yusuf.
Zumbur ta mi?e tsaye, Gwaggo tace "aikuwa ga muryar Wana nan, Alhamdilillah lafiya ta samu"

Kasa jurewa Widad tayi, kawai se gani Gwaggo tayi Widad tayi waje, kai tsaye ta nufi Wakinsu, ga mutane maza a ciki, wasu na ?o?arin fitowa, haka ta kutsa ta shiga, ta hango Yusuf yana zaune yana murmushi, sedai yayi rama sosai, yayi haske.

Da gudu ta ?arasa ta rungume shi, ta kasa magana kawai ta fashe da kuka.

?aya bayan Waya suka zame suka bar Wakin, yau suka ga taSara, ba kunya bakomai ba kara tazo ta rungume Yusuf a gabansu.

Suna fita Yusuf ya ha&a hannayensa ya rungumeta shima yace "Queen kin rame, duk kinyi wani iri"

Maimakon ta bashi amsa se sake kwanciya da tayi a jikinsa tace? "Ya jiki ka warke?"

" Na warke amma ina ganin yadda kika rame naji zata dawo"

Hanne ce tayi sallama da kayan Abinci a hannunta, sedai me taga Yusuf da Widad rungume da juna, take taji jikinta ya hau rawa, bata taSa ganin hakan a zahiri ba, sannan ga wani kishi daya taso mata, take ta saki kwanon dake hannunta.



(Gobe insha Allah, zan kammala book 1,Ashirin ga wata insha Allah zan fara book 2&3,? tuni an fara biyan kuWin, kuma zaku iya hanzarta biya ta wannan hanyar dake ?asa "



Normal group duka littafi biyun? ? 300
Idan kuma Waya zaki siya? ? 200

VIP ? 500

Inkuma sena gama zaki sai complete document ? 700

Account Number
Aisha Adam
0009450228
Ja'iz Bank

Ko katin MTN banda VTU please
A turo evidence of payment ta 07063065680


Duk Wanda ya biya yayi min magana ta what's app number Wina inyi adding Winsa a group Win Nagode


Domin gyara sharhi ko shawara
Ayshercool

? _*A?IDATA*_
? ? ? ?

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA _
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*A?IDA TA *

I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum

Ha??in Mallaka ?& : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ?unsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani Sangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

NOT EDITED? (BANYI EDITING BA)

ELEGANT ONLINE WRITER'S

? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ?? PART1
? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? Page 44_45

Yusuf ne yayi saurin Wagowa ya kalli Hanne, Yusuf yace "Subhanallah, garin yaya kika Sarar da Abinci?"

Widad kam ko motsawa ba tayi ba balle ta tashi daga jikin Yusuf.
? Cikin rawar jiki Hanne tace? "TuntuSe nayi shine ya zube, bari in samo in kwashe"
Ta juya ta fita da sauri, tana fita tsakar gida Gwaggo ta kalleta tace "ke meye haka, ba dai Abincin da nace ki kaiwa mara lafiyan kika zubar ba?"

Cikin inda inda tace "Amm.. Mm... TuntuSe nayi shine ya zube"

A fusace Gwaggo tace "kekam kamar mara hankali wani lokacin, kije ki kai Abinci kawai seki zubar dan shirme"

Hanne ba tace komai ba ta tafi ta Wau tsintsiya da abun kwashe shara ta tafi gyara inda ta Sata musu, cike da zullumin me zata je ta sake tararwa.

Gwaggo tace "Hindu tashi ki duba sauran kunu a Wakina ki kai musu ba'a bar mara lafiya da Yunwa ba"

Sukam Ma?ota da suka rako Yusuf ne suka dinga jinjina rashin ta ido irin na Widad, a gabansu ba kunya taje ta rungume mijinta.

Wani da'ake kira da Lado me Jakai yace "to ai kunsan su ba namu ne na nan ba, jama'ar birni ne baku ga matar tasa bama kamar balarabiya, su sun saba irin wannan bakomai ne ba"

?ayan da'ake cewa Liti yace "Aradu amma ai kunya wani abuce, tunda nasan duk abu Hausawa ne"

Lado yace "ku kuga haka, su a gurinsu ba wani abun bane ba"

Liti yace "Sumi sumi dashi haka, Amma ta rungume shi ya wani basar abunsa, memakon ma ya Wanyi mata tsawa ya hanata"

Wani me shekaru a cikin su yace "Kai waye ya gaya maka suna hantarar matansu, lallaSasu suke yi, ni wallahi birgeni ma suka yi"

Kwashewa sukayi da Dariya gaba Wayansu, harda ?ya?yacewa.

Hindu tayi Sallama, da kofin kunu tace "gashi inji Gwaggo, tace dan Allah kuyi ha?uri Hanne ta zubar da Abincin"

Yusuf yace "bakomai Hindatu hakanma mungode"

Hindu tace? "Amarya yau za'a ci Abinci, tunda me gidan ya dawo"

Yusuf yace "Ai naga alama bata cin Abinci ta rame sosai"

Hindu tace? "bata ci, Gwaggo taita fama da ita sedai tayi ta kuka, ko bacci bata iyayi"

Widad ta yatsine baki tace "Akanme zan?i bacci, in kasa cin Abinci toni ?iba ma nayi, ci nake in ?oshi"

Hindu tayi dariya tace "bari a kirawo Gwaggo a tambaye ta"

Sukayi dariya, Hindu tayi waje, Yusuf ya kalli Widad yace "bani kunun insha dan inajin Yunwa"

Widad ta mi?e ta Wakko kofin kunu, tazo ta zauna tana bawa Yusuf, Saleh ne yayi Sallama ya shigo Wakinsu.

Kallon Widad yayi yai murmushi yace "Allah me iko, Allah ba yadda be iyaba, wai Gimbiyar Daula ce ke bawa direbanta Abinci a baki, abun da mamaki"

Banza tayi masa ta cigaba da bawa Yusuf kunu, Yusuf yace "Saleh ?araso ka zauna mana"

Saleh yace "to bari in ?araso, ina fatan hankalinki ya kwanta ban gudu dashi ba, gashi na dawo miki da shi, kuma Alhamdilillah jikinsa yayi kyau"

Shiru ta kuma yi bata ce komai ba, Yusuf yace "Ana magana fa"

Widad tace "me zance?"

Saleh yace "base kince komai ba kam, Malaria me ?arfi da typhoid ne suka kama Yusuf, sannan ulcer na damunsa, ga rashin sabo da wasu abubuwa da yake yi, wanda be saba ba, dan haka shine damuwa gajiya da pressure ga kuma zazzaSi gaba Waya suka dameshi, amma Alhamdilillah mun samu an ceto miki shi, yasamu sau?i Alhamdilillah, na samo Net guda Waya, yace min ba guri Waya muke kwana ba, dan haka ga guda biyu nan ke Waya shi Waya, likita yace 'ya dena zama da yunwa, ya dena barin sauro yana cizonsa, sannan a kula ya shanye magungunansa"

Widad tace "Aishi zaka gayawa bani ba, tunda ze iya kula da kansa ko"

Mamkine ya kama Saleh, ya tuna yadda ta dinga kuka ranar da zasu tafi da Yusuf, amma yanzu tana faWar wata magana daban, shi kansa Yusuf beji daWin hakan ba, amma ya basar.

Saleh yace "koma dai menene, Zan zauna zuwa jibi in Allah ya kaimu zan koma, nayi muku siyayya wajen gobe in Allah ya kaimu za'a kawo muku"

Yusuf yace "Mungode sosai da Wawainiyar da kake mana, Allah ya saka da alkhairi, Allah ya biya ka"

Saleh yace? "Ameen"

Ita kuwa madigar, mi?ewa tayi tai waje abunta, ba tare da ta sake tanka musu ba.

Amal na kwance akan gadonta tayi shiru sosai take tunani, tayi zurfi sosai a tunani, Mummy ta shigo Waki Amal ta tarar a kwance tayi shiru tana ta tunani"

Mummy tace "ke meye haka? Tunanin me kike yi? "

Amal ta Wan tura baki tace "lafiya ?alau Mummy"

"Amma kika zauna kika yi shiru haka? Kina ?arama dake kike tunani haka"

"Mummy ina Wan zancen zuci ne kawai"

"to idan waccan uwar baccin ta tashi ki gaya mata zan fita, ni na rasa gane kan wannan baccin banzan dat take yi sekace wata kasa"

Ita dai Amal bata gayawa Mummy abunda Ramlan keyi ba.

Bayan fitar Mummy kwanciya Amal ta sake yi tana cigaba da tunani, kuma ba tunanin kowa take ba face Yusuf, tun tana dannewa yanzu abu yavfara gagara, bata iya Soyewa sam, Bata iya cin Abinci ba tayi zaton ?aunar Yusuf haka tayi mat wannan mugun kamun ba, gaba Waya yanzu haushin samarin ta take ji, gani take duk cikinsu Yusuf yafi su komai dukda Kasancewarsa talaka, amma ya haWu gashi nutsatse babu Hayaniya a tare da shi, ji tagi inama a sako Yusuf a ri?e Widad, dama itake hana ta rawar gaban hantsi, dan ta rasa wace irin Ala?ace ke tsakanin su, Widad bata da yadda kamar me, bata yadda kowa ya raSe ta ba, amma ta yadda da Yusuf ya shiga jikinta sosai da sosai, Yusuf yasan abubuwan dasu da suke zaune da ita basu sani ba.

"Ke Amal! Tun Wazu nake miki magana amma se kace wata kurma, kinmin shiru"

Firgigit Amal ta kalli Ramlah, tayi ajiyar zuciya tace "Meye nayi min ihu kuma?"

"na dole inyi miki ihu ba, tun Wazu nake kanki ina magana amma kinyi shiru"

Amal ta mi?e zaune ta kalli Ramlah tace?? "ban san kin shigo abane, dana san kin shigo ai zanyi responding"

"Wai nikam wane irin tunani haka kike yi?"

"Ramlah tunanin komai ma inayi, Abubuwa da yawa sun dameni, Amma Ramlah jiya fa maye kike kika dawo"

"Maye kuma?"

"Eh mana, wallahi jiya a buge kika dawo gidan nan, Mummy kuma a ?ule take dake, fitar da kikayi da Fahad"

Ramlah ta Wan Sata rai tace "ba wani maye da nake, na gaji ne kawai, sannan me Fahad Win kuma yayi?"

Amal tace "Eh to, kin san sunyi faWa da Wan uwanta akan belin Yaya Anwar, shiyasa"

"to kuma shine seya shafi Fahad, laifin meyayi? Kuma shima bakiga yadda yake ?o?ari akan lamarin ba, amma kin san halin babansu da kafiya"

Amal tace "wani tabacci kike da shi na yana ?o?arin nan, nifa kallon Fahad Win nan kawai nake, bakin ma?aryata ne dashi"

Ramlah tace "zaki fara ko? Karki kusakura kici masa mutunci"

Amal tace? "ke niba wannan ba, nifa naji tana cewa za'ayi uwar watsi idan ba'a fito mata da Yaya Anwar ba, karta yi wani abu daza'a zo ana da nasani daga baya"

Ramlah tace "kuma fa hakane, kin san bata iya fushi ba, bari inje Wakinta in sameta"

Amal tace "to ai ta fita"

"ta tafi ina?"

"Nima ban sani ba, ni dai tacemin zata fita"

Ramlah tace "Shikenan, bari inje kitchen in samu Wan abunda zanci, da yamma zanje gurin wani birthday na 'yar gidan IG na ?asa, na tura a Wakkomin wata sabuwar motar megidan nan daga kamfani, da ita zanje, kin san gurine na manyan yara fa"

Amal tace "Mhmm yakamata kam"

"waini meke damunki ne Amal, bakya walwala fa"

"Ramlah wace walwala zanyi? Yaya Anwar a rufe, hankalin Mummy ya?i kwanciya, ga uwa uba wallahi Ramlah Ji nake kamar inyi me saboda rashin Yusuf, na shiga damuwa wallahi ko bacci na kwanta yanzu mafarkinsa nake yi, na rasa inda zan saka raina, tun ina iya dannewa yanzu na kasa "

Wani uban dogon tsaki Ramlah taja tace " Aikin banza, shine zaki kashe kanki saboda wannan jakin"

"Karki sake kiransa da Jaki, Inda wanda za'a kira Jaki to tabbas Fahad ne, dan kunnuwansa ma irin na jakaine ga ?aryar tsiya".

Haka abun nasa ya koma faWa, ?arshe sukayi baran Baran.

Widad ta fita

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login