Showing 66001 words to 69000 words out of 135555 words

Chapter 23 - AKIDATA book 1 HAUSA NOVEL

17 Jan 2026

664

ka baro mutan gidan?"

"Lafiya ?alau Alhamdilillah, ina Yusuf kuwa?"
Isa ya taSa baki yace "Yana nan yanzun nan ya shiga cikin gida, gimbiyar masu gida tana kiransa"
"Allah sarki, ina fatan yana aikin sa babu matsala?"
"Eh to yana yi, se shishshigi da za?ewa, yaga ya samu gurin zama a gurin masu gidan, shine yake ta Wula?anta mu gamu gashi amma se yaga dama ze kula mu"

"Hmm ni kaina wannan ba?in halin nasa yana ?ular dani, dama haka yake se kunyi a hankali wasu lokutan bashi da kirki sam wallahi".

Yusuf seda ya Wan tsorata, ganin Widad ta rame daga jiya zuwa yau, idanunta a kumbure da alama kuka tayi sosai, gaba Waya se yaji tausayin ta ya kama shi.

"Gurin Bulama zaka kaini yanzun nan"

Jinjina mata kai yayi, ta mi?a masa jakarta ya karSa sannan suka fito.

Tunda suka fito Abbas ya ?ura musu ido, se kace mata da miji, tabbas Yusuf ya samu gindin zama yadda yakamata a gidan nan.

Yusuf na ganin Abbas tun daga nesa ya fara murmushi, suna isowa inda su Abbas suke kafin Yusuf yayi magana, Widad ta ?urawa Abbas ido, shikansa Abbas seda yasha jinin jikin sa.

"Waye wannan?" Widad ta tambayi Isa megadi"

Cikin inda inda Isa yace "Amm... Am. Dama abokina ne, kuma shine wanda ya kawo Yusuf aiki a gidan nan, ina tunanin ma Wan uwansa ne"

"Kar in ?ara ganin sa a gidan nan, ko a harabar area nan na sake ganinsa zan Wau matakin da ya dace"

Binta sukayi da kallo, inda sabo Yusuf ya saba da wannan halin nata, dan haja yayiwa Abbas Alama da zasu yi waya.

Abbas ya mi?e cikin mamaki ya bar gidan.

Yusuf dama beyi zaton zata gaya masa dalilin ta na korar Abbas ba, amma abun ya bashi mamaki, seya barshi a matsayin kawai duk cikin hakinta ne na rashin yarda da mutane.

Koda suka iso gidan Bulama, kafin su shiga megadi ya sanar dasu cewar Bulama da shi da iyalansa basa nan sun fita.

Haka Yusuf ya juya akalar motar suka koma gida.

Abbas ba ?aramin mamaki yayi ba, yaga dai farkon zuwansa gidan daya kawo Yusuf tare suka je, amma yau ta nuna bata sanshi ba wai kar ya ?ara, zuwa gidan.

Kai tsaye Abbas ya Wakko wayarsa ya kira layin Saleh.

"Hello Saleh kana ina ne?"

"ina gidan gona bakin aiki, meyafaru?"

"ina son ganinka ne"

"ka bari zanzo in same ka a gidanka, karka zo nan babu security"

"shikenan sekazo"

Yusuf Alla Alla yake ya kai Widad gida ya tafi gurin Abbas.

Seda suka je gida yay parking, Widad ta kalle shi tace "Karka bar gidan nan se bayan sallar isha'i"

"Saboda me?" ya tambaye ta

Bata bashi Amsa ba ta fice daga motar ta barshi a gurin, ba ?aramin haushi yaji ba, yasan dai duk abu ba wani gurin ze kuma kaita ba, Amma tace baze tafi ba, da niyyarsa yayi tafiyar sa amma se ya fasa, haka ya cigaba da zama har se lokacin da tace ya tafi.

Saleh ne zaune shida Abbas a wani Wan madaidaicin falo, Saleh yace
"Neman me kake min ne haka?"

Abbas yace "dole in neme ka ai, Yusuf se alheri yake samu a wannan aikin da yake, ta sakarmasa kuWi kawai take sakarmasa, seda nayi dana sanin rashin yin aikin nan da kaina"

Saleh yai murmushi yace "tabbas Widad akwai kyauta ta ban mamaki, Sedai kasan aikin da yake a rayuwar sa a hatsari take ko?"

"Nasani amma babban abunda ya Wauremin kai shine yau naje gidan gurin sa, Amma tana ganina tace kar in ?ara zuwa ko area gidan"

"zata aikata saboda bata da yadda sam, dan haka bata son ba?uwar fuska, gani take kowa ma cutar da ita zeyi, yanzu ya ake ciki game da binciken da yake yi, naga alamar yaron yasan aikin sa, duk yadda kaso ka daki cikin sa ba ze gaya maka komai ba, na jarraba shi rannan da suka zo tare, Amma naga yana da wayo "

Abbas yace " Hmmm, aiki kam yasan kan aikin sa sosai, dan ina tabbatar maka da yana aikin yadda ya kamata yana tattara abubuwa masu mahimmanci sedai har yanzu ban san meye sakamakon binciken nasa ba"

Saleh ya numfasa yace "yanzu abunda nake so da kai shine, ka kawomin rahoton duk binciken da yayi, ka kawomin file Win zan mi?a shi ga wannan mutanen dan su sakarmin Wan uwana dan ina zargin su suka yi poisoning Winsa yake kwance ba lafiya"

Abbas yace "yana na'aikaci ina ma'aikaci tayaya kake tunanin ze yadda ya bani kundin binciken sa?"

"wannan ya rage naka kuma Abbas, ni na gama magana kuma ka saka ido ka cigaba da bibiyar sa dan jin yanayin kusancinsa da ita"

"Shikenan zanyi iya abunda zan iya, Insha Allah zan kawo maka abunda ka bu?ata.

Ba ?aramin haushi Yusuf yaji ba da Widad ta hana shi tafiya da wuri, dan haka se bayan isha'i sannan ya tafi gida, bayan yaje gida yaci Abinci yana shirin kwanciya message ya shigo wayarsa

"HAR YANZU MUNA SANE DA KAI, KUMA ZAMU CIGABA DA BIBIYAR KA HAR SEKA BAMU ABUNDA MUKE SO A HANNUN WIDAD"

Tsaki Yusuf yayai ya Wanyi shiru yana tunanin wai wani abubne wannan haka da'ake son karSa a gurin Widad, da har ake masa barazana haka?
Ganin bashi da amsa yasa yai kwanciyarsa.

************************************
"Fahad kasan meyasa na kiraka muyi magana a daidai wannan lokacin?"

Fahad ya girgiza kai yace "a'a Daddy"

Bulama yace "Yawwa, na yanke wani hukunci ne kafin ka dawo, shine nake so ka baani aron hankalin ka da kunnuwan ka da kyau ka saurareni"

"To Daddy ina jinka"

"Kasan Widad ai ko? 'yar gidan Alhaji Nasir daula"?

"Eh Daddy nasani"

"Kasan ala?ar dake tsakanina da mahaifinta ko?"

"Nasani Daddy" Fahad ya bashi amsa

"Masha Allah, Kasancewar ka yaro me biyayya shiyasa na yanke wani hukunci wanda nasan ba zaka bijiremin ba Insha Allah"

"Ina jinka Daddy".

"Kamar yadda kasani, yarinyar nan ta gamu da larurar ?wa?walwa, ta Wau wata A?IDA da wata irin rayuwa ta nayi, ta zaSi rayuwar kaWaici wanda hakan ke barazana ga lafiyar ?wa?walrwata, shine muka yabke hukuncin yi mata Aure nida mahaifinta, koda Allah zesa a dace a samo kan hankalin ta"

Fahad yace "to ai Daddy ni banga meye nawa a ciki ba"

"Fahad kai muka yanke shawarar zaka auri Widad"

A razane Fahad ya kalli Mahaifinsa yace "Kamar ya ni Daddy, kawai se in auri mahaukaciya kaifa kace bata da hankali ta yaya zan Aure ta?"

"ta yadda na gaya maka mana, aiba hauka take tuburan ba se lokaci lokaci yake tashi, dan haka umarni nake baka ba shawara ba, idan bamu haWu an temaki yarinyar nan ba waze aure ta da wannan larurar?"

"Amma Daddy a rasa wanda za'a bawa seni? Ina da wadda nake so meyasa za'amin haka? Ta yaya za'a yanke min hukuncin yarinyar da zan aura ba tare da izinina ba"

Cikin tsawa Bulama yace "rufemin baki, na gaya maka wannan umarnina ne, kuma dole kabi gobe in Allah ya kaimu zakaje ku gaisa da ita, kuma wallahi naji wani abu daga gareka wanda be gamshe ni ba, kasan halina sakarai kawai"

A hasale Fahad ya tashi ya bar falon mahaifinsa, Wakin mahaifiyarsa ya tafi yana kumbura fuska.

"lafiya ka shigomin Waki ba ko sallama kana ta haWe rai kamar tsohon ra?umi?"

"Mumsy kina gidan nan, kina raye za'ayi min Auren dole? Kamarni ta yaya za'a auramin mahaukaciya?"

Ajiyar zuciya tayi tace "Fahad this is out of my control, I did my best to destroy this matter but is beyond my control, ba yadda banyi da mahaifinka ba amma fafur ya?i, ya zanyi sedai kayi ha?uri"

"Au Hakama zaki ce? Wallahi se yarinyar nan tayi dana sanin Aure na, sena mata wula?ancin daba'a taSa yi mata ba se naci mutuncin ta, zata gane kuskurenta"

"Kai Fahad ka shiga hankalin ka, 'yar gidan Daula ce fa, ita zaka ciwa mutuncin? Amma kasan me ci mata mutunci ke nufi ko?"

"ko' yar gidan bushashace ba Daula ba ba ruwana wallahi"

"shikenan kaje kayi abunda ka ga dama kaida ubanka ba me Wagamin hankali wallahi"

Fuuuu Fahad ya fice ya bar Wakin yana tsaki

Da safe Yusuf yanata shiri, dan yau gurin aiki yake son zuwa dole yana son ganin YallaSai Suleiman, Amma message ya shigo wayar sa.

"ka tabattar ?arfe takwas tayi maka a gidanmu, zakamin aiki yau"

Yana ganin message Win yasan daga Widad ne, haushi ne ya kama shi gaba Waya bashi da lokacin kansa sena wannan fitsararriyar yarinyar.

Haka ya shirya a gaggauce ya tafi gidansu Widad, mutan gidan ko tashi daga bacci basu yi ba, tsabar takura irin ta Widad da son nuna isarra yasa take masa wannan ikon.

Wani Wan ?aramin lambu dake gidan Yusuf ya tafi yai zaman sa, yana kallon shuke shuke da tsuntsayen dake gurin.

Jin tsayuwar mutum yayi a bayan sa dan haka da sauri ya juyo.
Amal ce tsaye a bakin lambun tana ?are masa kallo "barka da Safiya Yusuf"

"Yawwa barka" ya faWa a ta?aice

"Yusuf wai ya naga kana wani baya baya dani? Dan Allah kayi ha?uri da abunda ya faru, wallahi ina matu?ar kishin ka ne"

"Amal dan Allah kiyi ha?uri, ni bana son abunda zesa ki jamin matsala, ki ?yaleni dan Allah"

"Idan kaga na ?yaleka to tabbas Wayan mu ruhinsa ya rabu da gangar jikinsa, ni matsala duk girmanta duk ?an?antar ta bana gudun ta, indai akan biyan bu?ata tane, kalleni Yusuf me na rasa? Wace tawaye Allah yayimin da ban kai ka kalleni ka karSi soyayya ta ba, kana ganin irin mazan da suke sintiri a gidan nan da sunan suna sona, Amma na ajiye class Wina na ajesu a gefe nace kai nake so, me zesa kace baka sona"

"Saboda bana Soyayya, bata gabana babu ita a tsarina, dan Allah ki ?yaleni"

"?arya kake Yusuf kana Soyayya, koma baka yi zaka fara a kaina bazan taSa ?yaleka ba, zan cigaba da bibiyar ka sena hanaka jin daWi muddin baka amince da soyayya ta ba "

"Masoyiyar gaskiya ba zata taSa faWar haka ba, ke ba abun yadda bace dan haka bazan taSa yadda da wannan shirmen ba"

"Yusuf ko nawa kake so zan mallaka maka, in har zaka yadda ka karSi soyayya ta"

"Shi son gaskiya tsada ne dashi, kuWi komai yawan su basa siyansa, dan haka Allah be baki arzi?in da zaki siyi soyayya a gurin Yusuf ba"

Yana gama maganar ya juya ya fice daga lambun yana mamakin wannan naci irin na Amal.

************************************
Ramla ce kwance hannunta ri?e da waya tana magana a hankali cikin iyayi

"Abun ?auna ta, yau kwananka huWu da dawowa Nigeria, yakamata ace kazo na ganka fa, Allah badan inajin nauyi ba da tuni ni zanzo inda kake in ganka"

Daga can Sangaren Fahad yace "Am Sorry beb, ina cikin damuwa ne gidan naku ne gaba Waya bana son zuwa, Ramla wai Daddy ze haWani Aure da wata mahaukaciya a gidan ku, Ramlah kamarni za'ayiwa Auren dole? Auren ma da mahaukaciya, kuma Daddy se masifa yake wai se nazo mun gaisa da ita"

"Fahad nasan maganar nan tun kafin ka dawo, ban gaya maka ba saboda bana son Sacin ranka, Amma ina cikin damuwa Fahad you know I love you" tai maganar cikin damuwa

"easy baby, ki kwantar da hankalinki, idan nazo se nayiwa yarinyar nan rashin mutunci, ni bazan aure ta ba dan ba sonta nake ba, bazan taSa yadda da Auren nan ba, naga Daddy ya fara fushi, in anjima zan shigo gidan naku in ganta, Amma ni ke zanzo gani Beb"

Murmushi tayi tace "Ohh my God, amma naji daWi Fahad seka zo".

Ta kashe wayar tare da yin wani tsallen murna.

************************************

Se ?arfe sha Waya na safe tayi mi?a, ta farka daga nannauyan baccin da take, ta sakko daga kan gadonta magen ta yana biye da ita.
Corridor Win Wakin ta tabi wanda ze sada ta da barandar benen, mi?a ta sake yi tana ambaton sunan Allah tare da sha?ar sassanyar isakar dake kaWawa, haka nan take jin wai irin nishaWi da bata san dalilin jinsa ba, tsyawa tayi tana kallon komai dake harabar gidan.

Yusuf ji yayi kamar ana kallon sa dan haka ya Waga kansa sama, ai kuwa karaf idanunsa suka sauka a cikin nata, alama tayi masa da hannu ya zo, dan haka ya mi?e ya tafi.

Dukda yana jin haushin abunda tayi masa akan kayan daya bata, amma yau yaga fuskarta ba yabo ba fallasa haka nan yaji hakan yayi masa daWi.
A Wakinta ya sameta, tana tsaye a gaban madubi ta janyo drower mudubin tana ?o?arin Wakko wani abu.

Idan kunnuwan ta ba ?arya suke gaya mata ba tabbas Yusuf cewa yayi "Good morning daughter" kamar yadda Daddyn ta yakan faWa, shiru tayi ta cigaba da duba abunda take nema tsawon wasu da?i?u, sannan ta Wago ta kalle shi tace "Roux ta?i cin komai tun jiya, na rasa meke damunta na bata Madara ta?i sha, ka siyo mata ko cabin ne, in gani in zata ci ban san me yake damunta ba" (wato magenta)

Haushi ne ya kama Yusuf, saboda tsabar wula?anci mage ze fita siyowa Abinci.
Bece komai ba ya juya ya fita yana ?o?arin Soye jin haushin sa.

Yana tafiya ya tuna da Message Win da'aka turomasa da daddare dan haka ya samu guri ya kira Oga Suleiman.

Bayan sun gaisa Yusuf yace "YallaSai na so in shigo yau in nuna maka report Wina amma abu ya gagara, Wannan rigimammiyar ta kasa ta tsare ban samu na shigo ba"

Suleiman yace "Aikam dan har na fara ?orafin, yanzu me ake ciki?"

"YallaSai akwai abubuwa na ban mamaki a binciken nan, zan turomaka report Win ta Email Winka ka duba, YallaSai case Win akwai sa hannun mutanen dan ban zata ba, sannan karo na biyu ana min barazana wanda ya ?ara tabattar da tabbas ana bibiyar yarinyar nan ana son karSar wani abu a hannunta wanda ni kaina ban san menene ba"

"Masha Allah, har kayi aiki haka Yusuf? Ka turo zan duba in Allah ya yadda inda yuwuwa zan mi?a report Win naka gaba, nasan zaka iya dama bazan can zaka daga kan aikin ba"

"YallaSai da karSar aikin za kayi?"

"karka damu da wannan, ka turomin zan duba dan daga sama ana tambaya ta ina muka tsaya a binciken?"

Yusuf yace "Amma YallaSai wai wa yasa ayi wannan aikin ne? Waye yace ayi binciken?"

"Yusuf nima ban saniba, daga sama aka bada order ayi wannan aikin"

"YallaSai ya kamata kasan gawa zaka bada aikin, dan abun akwai sar?a?iya"

"Karka damu Yusuf, komai ze tafi daidai insha Allah, kamar yadda kace ana maka barazana, duk lokacin da ka bu?aci temako kayi magana, sannan ka kasance cikin shiri ka dinga yawo da makaminka"
"Ina lura sosai YallaSai, Allah yayi mana jagora gaba Waya"

"Ameen Yusuf Allah ya tsare"

Yusuf seda ya tsaya ya turawa Suleiman aikin sannan ya tafi.

Koda Yusuf ya dawo daga aiken yiwa mage siyayya, ya tarar da uwar Wakinsa ta fito daga wanka, pink Win rigar wanka ce a jikin ta, ta naWe gashin kanta da towel shima pink.

Zare towel Win dake kanta tayi, gashin ta ya zuba a kan kafaWunta, Satar kallon ta Yusuf yake, tabbas Allah yayi mata halitta mekyau, tana da kyau sosai ga dogon gashi, Yarinya ce sedai izza da gadara, tana kallon Ya dawo amma ta?i kula shi.

Wani ?aramin plate ta Wakko ta mi?awa Yusuf tace "ka sa mata cabin Win anan, ga madara ka haWa mata dashi"

Yusuf yai shiru yana sauraren ikon Allah, yanaji yana gani aka sashi haWawa mage Abinci.

Still dai magen bataci ba se kwanciya da take.

Cike da damuwa Widad ta kalli Yusuf tace "ta?i cin wannan ma, inaga bata da lafiya idan akwai wani private veterinary se mu kaita" ta faWa cike da damuwa tana sake shafa magen, hakan ya ?ara fito da tsantsar yarintar ta.

"waye ze buWewa wani private veterinary? Babu wani private veterinary dana sani nidai, yunwa take ji kawai bata ?oshi ne"

"kamarya? Ina bata Abinci sosai fa"

"Ai kema ba Abinci kike ciba balle magen, kullum abu Waya ai dole ta gaji ta dena ci"

Cikin damuwa tace "to me zan dinga bata?"

"Abinci me nauyi na hausawa, amma kullum daga popcorn se madara ai dole ta mutu"
Da sauri ta kalli Yusuf tana girgiza kai tace
"A'a ni bana so ta mutu ina sonta fa"

Gaba Waya yau Yusuf cike yake da mamakin yadda take masa magana cikin nutsuwa ba izza, yasan kuma saboda magen ne, dan ya lura tana tausayin dabbobi fiye da yadda take tausayin Wan Adam, tana matu?ar ?aunar dabbobi Yusuf a ransa yace "ta wani fannin rayuwar turai ba tayi ba"

"to muke rasa 'yan uwanmu mutane ma balle dabba, idan ta mutu seki Wakko wata"

"Ni nafison wannan gaskiya, tun ire iren magunan Ammi ne, idan ta mutu zan shiga damuwa"

Shiru yayi yana kallon Widad data sunkuyar da kanta tana shafa jikin magen, magen tayi lamo a jikinta, gashin kanta har rufe mata fuska yake, Yusuf yana mamakin wannan dogon gashin na kan Widad dan har yanzu yana tantama idan nata ne.

A hankali ya matso daf da ita ya shafa jikin magen dake hannun ta yace "Allah ya bata lafiya, don't worry Madam zata warke Insha Allah"

Widad ta jinjina kai, tare da jin ?aruwar bugun zuciyar ta kasancewar yadda suke daf da juna, ta Wago idonta ta kalle shi tace "da ina so mu fita zanje Saloon, Amma zan zauna inga yadda jikin nata ze kasance ko zuwa yamma ne semu tafi"

Yusuf ya Wan ?ura mata ido sannan a hankali yace "As you wish your majesty" ji tayi tsigar jikin ta tashi, wanda ta rasa dalilin jin hakan, haWe rai tayi tace
"karka sake ka fita kaje ko'ina idan ba nina baka izini ba, ka zauna zuwa la'asar insha Allah zamu fita"
Murmushi yayi mata tare da Wan du?awa cikin girmamawa yace "Considered it done Gimbiyar Daddy"

Ya yun?ura ze mi?e Amal ta shigo hannun ta Wauke da waya, turus tayi tana binsu da kallo, yayin da taji wani abu tundaga ?afarta zuwa ?irjinta ya to kare mata wuya.

Da ?yar ta mi?awa Widad waya tace "gashi Daddy zeyi magana dake"
Widad bata kalle ta ba, bata bata amsa ba ta kalli Yusuf tace "bani wayata akan mirror"
Amal bata kuma cewa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login