Showing 87001 words to 90000 words out of 135555 words

Chapter 30 - AKIDATA book 1 HAUSA NOVEL

17 Jan 2026

665

Allah, babu yadda za' ayi akasa gano inda Widad take, a matsayinka na babban mutum a ?asar nan, Insha Allah zasu kuSuta"

Daula yace "ai ba wai kuSutar tasu ba, yadda zasu tsira da rayuwar su bayan sun kuSutan shi nake tunani"

Saleh yace "karka damu da wannan YallaSai, yanzu Addu'ar mu suke bu?ata insha insha Allah zasu kuSuta"

Bulama ne da matarsa suka shigo Wakin shida Anwar da su Ramadan, Bulama yace "sannu ya jikin naka?"

"Alhamdilillah"

"Ubangiji Allah ya ?ara afuwa"

"Ameen" na suka shiga yi masa sannu, Anwar ya ?arasa kusa dashi yace "Sannu Daddy Allah ya baka lafiya"

Kasa Amsawa yayi sema share ?walla da yayi yace "Anwar an sacemin Widad, an sace autar daula, ga yaron dabe ji ba be gani ba shima ta ritsa dashi"

Cikin damuwa Anwar yace "ka kwantar da hankalinka Daddy, Insha Allah zasu kuSuta, za'a gansu, babansu Fahad yace min an kai report"

Alhaji Nasir yace "Allah yasa su kuSuta gaba Waya yasa karsu cutarmin da su"

Alhaji Bulama yace "ka jika da wani zance, muji da 'yarmu da' aka sace kana wani kar'a cutar dasu"

Alhaji Daula yace "haba Bulama, ai gara su ri?e Widad su saki Yusuf, yana zamansa a dalilina da 'yata ya shiga hatsari, in gaya maka gaskiya tsakanin Widad da Yusuf ba wanda bana so, Allah ya samin ?aunar yaron a zuciya ta, bazan so ya rasa ransa ba shima, Allah ya bayyana min su duka ba wanda bana so"

Kuka sosai Alhaji Nasir yake kamar ?aramin yaro, Anwar ne ya rungume shi a jikinsa, yana faWin "yi ha?uri Daddy, duk zasu kuSuta cikin ?oshin lafiya, kar lafiyar ka ta taSu, kaima muna bu?atarka"

Hajiya Sarah tace "dole Baban Widad yayi kuka kuma gaskiya ya faWa, yaron nan shima abun tausayi ne, beji ba be gani ba tsautsayi ya ritsa dashi abun da tausayi"

Alhaji Bulama yace "dama ku mata wani lokacin ba hankali kuka cika ba, dama Allah yayi haka zata faru dashi, amma mudai mu samu 'yarmu ta kuSuta"

Hajiya Sarah tace "shi Yusuf Win ba uwace ta haife shi ba? Ya zataji idan ta samu labarin Satan Wanta?"

Ramadan ne yai saurin cewa "Mummy kiyi ha?uri kiyi shiru, duk zasu bayyana insha Allah, Allah sarki Yusuf Win nan yana da kirki wallahi ga ha?uri da yawan murmushi"

Likita ne ya shigo ze duba Alhaji Nasir, dan haka duk aka basu umarnin su fita daga Wakin domin a duba shi.

Anwar ya maida su Alhaji Nasir gida, ya shiga part Win Fahad, sedai ya tarar da shi da mace suna shan shisha, Anwar ya girgiza kai dan ya saba ganin Anwar a wannan halin, mussman da suna ?asar waje, Anwar yace "Fahad baka san meya faru da Widad bane da direbanta, ina ta kiranka baka Waga ba?"

Fahad ya fesar da haya?i yace "Nasani mana"

"Amma ko Daddyn namu ai yakamata kaje ka duba"

Fahad ya kalle shi yace "Daddynku ku suwa? Baza'a dubo shi Win ba, ni burina duk inda ta shiga a nemo min mata ta, dan nasan wannan tsinannen direban ne ya gudu da ita, kuma sena nuna masa iyakarsa"

Karuwar dake tare da Fahad tace "Baby wai maganar wa kuke yi ne?"

Fahad yace "ba ruwan ki uwar shishshigi, jeki shirya inzo in maida ke gida"

Anwar yace "Fahad se yanzu na sake tabattar da Widad a kan gaskiya take na ?in yadda da mutane, yanzu Fahad kasan nida kai iyayenmu basu da ?arfin kaimu ?asashen waje, amma ya Wauke mu kamar yaransa, ya kaimu ?asar waje mukayi karatu, dukkaninmu ba wanda be mallakawa motar hawa ba da gidan kansa, muba komai ba silarsa muka zama wani abu, kalli yadda muke fantamawa a cikin rigar arzikinsa, albarkacin sunansa duk inda muka shiga a faWin ?asar nan muna da Alfarma, yau shine Iftila'i ze faWa masa amma ka nuna halin ko in kula, Anya Fahad kana gayawa kanka gaskiya kuwa "

Fahad yace " A'a sedai idan yanzu zaka fara gayamin gaskiyar "

Yai maganar tareda mi?ewa ya shige bedroom Winsa, jiki a saSule Anwar ya baro gidan Bulama ya koma Asibiti, ya bawa Alhaji Nasir Abinci ya canza masa kaya, sedai yaita mamakin rashin ganin mahaifiyarsa taje Asibitin gurin mijinta.

Gida ya koma yana tunanin butulci irin na Fahad, a falo ya tarar da Hajiya Halima tana cin Abinci suna kallon zee world, sedai kamar Amal ce a cikin damuwa.

Anwar yayi sallama suka amsa gaba Waya, Anwar yace "Mummy meyasa ba kije Asibiti ba?"

"bana jin daWine, bana son inje inga abunda ze sake Wagamin hankali"

"Amma Mummy ai jikin nasa da sau?i, kuma yakamata ace ko su Ramla sunje duba shi"

A fusace tace "Ubansu ne da lallai se sunje duba shi, fita ka bani guri dalla"

BuWe baki yayi yana kallon mahaifiyarsa yana ?o?arin tabattar da anya daga bakinta wannan maganar ke fitowa?



Duhu ya fara yi, sauro ya shiga ambaliya a gurin nan, Yusuf ya zauna se akin yi mata fifita yake da wani gutsararren kwali, A hankali Yusuf yace "Kidena musu taurin kai kinji, sannan idan an baki Abincin ki karSa kici, baze yuwu ki zauna da yunwa ba"

"ba zanci ba" ta bashi amsa

"kin fi son su cigaba da azabtar dake?"

Shiru tayi masa ba tace komai ba, can ya kuma cewa

"dan Allah ki basu abunda suke nema, dan su ?yale ki ko a yanzu kin galabaita"

"wallahi ko zasu kasheni bazan basu ba, shiyasa nace tun farko su sake ka ni su barni anan"

"tayaya zasu sakeni in tafi, alhalin kina gurinsu sedai kome ze faru ya faru muna tare"

Ajiyar zuciya ta shiga saukewa, tana jin yadda sauro ke shagali akanta, abunda bata saba ba, bata son yin kuka dan yanzu Yusuf ze Waga hankalinsa

Cikinsu babu wanda ya rintsa, har gari ya waye, taimama sukayi sukayi sallar Asuba.

Fuskar Widad duk ta kumbura saboda sanyi da cizon sauro, kuma har a lokacin jikinta babu ?wari.

Yusuf yana zaune, yayin da Widad ke kwance akan tabarmar, buWe ?ofar Wakin akayi suka sake shigowa su huWu.

Suka kalli inda Widad ke kwance, Wayan ya buga mata tsawa yace

"tashi ko in taka ?afarki in karya banza"

Gyara kwanciya tayi ta juya musu baya, alamar bata da niyyar tashin, yau Yusuf ya ?ara tabbatar da azababben taurin kai da Widad ke dashi.

Da sauri Yusuf yazo inda take ya Waga ta zaune yace "ya haka ne, so kike yauma su dake ki"

Wani banzan kallo tayiwa shugabn nasu ta Waunke kai tana hura hanci.

?ayan yace "shegiya se kyau kamar ita tayi kanta, amma zuciyar ta kamar dutse shegiya me kama da sadakar yalla"

Babban su yace "zamuyi maganinta kafin tabar gurin nan, da ganin idonta yunwa take ji, amma saboda taurin kai ta?i cin Abinci, ku Wakko Abinci ku bata idan taga dama taci"

Shinkafa da wake ce irin garau garau Win nan takan 'yan talla, tayi sanyi ?alau ga ba mai sosai, suka dire mata a gabanta, yun?urawa tayi zata sake fatali da Abincin Yusuf ya ri?e ta yace "dan Allah ki daure kici, kinga tun shekaranjiya rabonki da Abinci"

Ta kalli idon Yusuf tace "bazan ci ba"

?ayan yace "kai dalla ka ?yaleta mana, kar taci ubanwa tayiwa, Oga ka fara aiki kawai"

Rarrashin duniya Widad tayi mursisi ta?i cin Abinci.

Babban cikinsu ya Wakko wayarsa zeyi kira.



"Nurat ki kaiwa Daddynki tea Win nan da ba?insa, kafin yazo ya ishemu da faWa"

Nurat ta mi?e ta Wauki kayan tea ta nufi part Win mahaifinta.

Alhaji Munir ya shafa ?aton cikinsa yace "nifa bakina ya?i rufuwa ma, nasan dole abun nan yazo hannunmu a yau base gobe ba, nace a tura masa sa?o, kodai ya bayar ko mu cigaba da tsare ta"

Alhaji Musa yace "ba kai kaWai ba ni kaina ina cikin murna, sun kwana a hannu, Daula yana gadon Asibiti yana ta sharSar hawaye, mutum se taurin kan tsiya kamar arnen dutse"

Suka kwashe da dariya, Alhaji Haruna yace "dalla ?yaleshi, gefe guda baze samu Halartar taron shekara na kasuwanci ba, da haka zamu sanar da cewa an samu gagarumar Asara kasuwancin da muke yi, zamu bada fake Account statement, zamu kwashi rabonmu kafin wancan yazo hannunmu, ai daula ya gama yawo wai shi me gaskiya"

Suka sake kwashewa da dariya, wayar Alhaji Haruna ce ta fara ringing, ya Waga ya sa musu a hands free, Alhaji Haruna y??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ace "Ya me ake ciki ne?"

"YallaSai tunda nake aikin nan, ko a maza ban taSa ganin mutum me ba?in taurin kai kamar yarinyar nan ba, kwana biyu kenan ta?i cin Abinci, ruwa kawai take sha, gashi kamar bata da lafiya kullum tana kwance ko magana seta ga dama take yi"

Alhaji Munir yayi tsaki yace "dalla ku rabu da ita, ku karSo mana abunda muke bu?ata, sannan ku turawa ubanta sa?o shima koya bamu ko kuma ku kashe ta"

Daga wayar akace "An gama Oga, yadda kukace"

Nurat da taje kai musu shayi jikinta ya shiga Sari, dan tsaf taji hirar da mahaifinta suke yi, cikin sanWa taje ta ajiye farantin kayan shayin, ta ruga da gudu Wakinta ta saka hijjabi ta Wau wayarta ta fice daga gidan.



Babban cikin mutanen wanda suke cewa me Adda ne ya Wakko wata kujera ya zauna a gaban Widad ya kalle ta cikin tsawa yace

"ke kalleni nan, ina takaddun nan suke? Ki gayamin cikin ruwan sanyi ko kuma in kasheki in koma in kashe wancan da?i?in uban naki"

Sunkuyar da ka tayi tai shiru, Yusuf yace "Yana miki magana ki gaya masa, su ?yaleki ki huta"

Kallon Yusuf tayi da jajayen idonta sannan tace "takaddun da suke nema, akwai masu shi nayiwa Daddy Al?awarin mi?asu ga masu shi, kuma na bawa masu shi suna can suna yawon su a gari, me suke so kuma ince musu"

"?arya kike, duk binciken da'akayi sun tabattar da suna wajen ki dan haka ki gayamana inda suke"

A harzu?e tace "bazan faWa ba, nace bazan faWa ba kayi abunda zaka yi!"

Kan bindiga Waya yasa ya buga mata a baki, take jini ya shiga zuba daga bakinta Yusuf ya gigice ze tashi, suka Wora masa bindiga aka "kana motsawa zamu fasa kanka da harsashi"

Widad ta tattaro dukkan yawun bakinta, me Wauke da jini ta tofawa shugabannin nasu tace "wallahi ko me zaki sedai kayi, bazan bayar ba ka koma ka gayawa Azsaluman da suka saku aiki cewar bazan bayar ba, kuma matsorata ne tunda suka gaza fitowa gaba da gaba su karSi abunda suke so, kuma ko sun kasheni na kafa musu tarkon da ko bayan raina se Asirinsu ya tonu, saboda na sansu kuma na tattara duk wata hujja da yakamata a kansu san......

Bata ?arasa ba ta kuma jin wani marin a fuskarta, a duk lokacin da suka daki Widad Yusuf ji yake kamar ?irjinsa ya tsage dan ba?in ciki, sedai ba yadda ya iya muddin yayi wani yun?uri dabe gamshesu ba zasu mata illa, dan ba imani ne dasu ba, ga Widad bakinta ya?i mutuwa.



Nurat bata tsaya ko ina ba se gidan su Widad, a waje ta tarar da Anwar ya fito da mota ze fita, Anwar ne ya ganta dan sam bata lura dashi ba yace "Nurat"

?aga kai tai ta kalle shi sannan tace "Yaya Anwar ashe ka dawo, babu Labari"

Anwar yace "Na dawo, ina zaki haka naga kamar bakya hayyacinki"

Nurat tace "gurin Widad nazo"

Anwar yace "baki san na sace ta ba ita da direbanta?"

Hannu ta Wora a ka, ta dur?usa a gurin ta fashe da kuka, Anwar ya fito daga motar yace "Nurat lafiya kuwa?"

Nurat tace "lafiya ?alau, dan Allah kasan wani Wan uwanta wanda suke yawo tare?"

Anwar yace "Ai Widad bata da Wan uwa"

Nurat tacs "Nasani, wannan zaka ga tare suke yawo, ban san sunashi ba ya cemin Wan uwanta me shi, wani dogo kamar bafulatani, me yawan murmushi"

Anwar yace "ko Yusuf kike nufi?"

Nurat tace "ban san sunansa ba"

Anwar yace "indai Yusuf ne tare suke yawo kam, kuma tare aka sace su"

Zare ido waje tayi tace "tare aka sace su, na shiga uku ni Nurat, meyasa aka sace su?"

Anwar yace "shine abunda bamu sani ba, amma 'yan sanda na nan na bincike yanzu haka zanje Asibiti gurin daddynta ne, daga nan mu koma station"

Nurat tace "zan iya binka in duba shi?"

Anwar yace "meze hana? Muje"

Suka shiga motar suka tafi.



Me Adda ya jinjinawa wannan ba?i taurin kai na Widad, yasa bakin bindiga ya daki kanta dashi ta kurma wani uban ihu tace "wallahi ba zan faWa ba, sedai kayi min duk abunda zakamin"

Ya kuma Waga bakin bindiga ze da keta, Yusuf ya mi?e ya ri?e shi gam yace 'Anya akwai imaniba zuciyar ka, kalli yadda take kururuwa amma ba zaka ?yaleta ba"

Me adda yasa hannu ya hankaWa Yusuf amma Yusuf ko gezau beba, ya kalli Yusuf ya kuma ?o?arin hankaWeshi amma Yusuf ko gezau balle ya kai ?asa dukda ya kwana biyu ba Abinci amma hakan besa ya faWi ba.

HaWuwa sukayi su huWu suka kama dukan Yusuf, da manyan sanduna, suka masa jina jina sannan suka Waureshi, tun suna dukansa Widad na ihu harta suma a gurin.



Koda Anwar yaje a Asibiti seya tarar da mahaifiyarsa da su Ramlah a gurin, tayi masa ?aryar wai da'aka gayamata abunda ya faru suma tayi seda aka kaita Asibiti shiyasa bata zoba, shi kuma Daddy ya yarda da abunda ta faWa.

Anwar tun yana mamakin abubuwan da suke faruwa harya dena.

Nurat ta ?arasa gaban Gadon Alhaji Nasir tace "Sannu Daddy ya jiki".

Ta faWa tana shesheshe?ar kuka.

Alhaji Nasir yace "da sau?i Nurat, ashe kin samu labarin Satan ?awar ki?"

Ta jinjina masa kai alamar eh, yace "to ki cigaba da Addu'a Allah ya bayyana ta, sannan ki koma gida kar babanki yayi miki faWa kinzo nan"

Ya kalli Anwar yace "Wan beauty mayar min da ita gida kaji"

Yai maganar cikin ?arfin hali cike da zolayar Anwar.
Anwar yayi murmushi, tare da wayancewa ya goge ?wallar dake idonsa, kallo Waya zaka yiwa Alhaji Nasir kasan yana matu?ar jin jiki.

Tunawa yayi da abunda Widad ta gaya masa daren da abun ze faru, take yaji wasu hawayen na bin idonsa, duniya Kenan Abun tsoro.

Saleh ya kasa zama, ya kasa tsaye abun duniya ya dames hi, tabbas Alhaji Nasir mutumin kirki ne ya masa alkhairi daban daban a rayuwar sa, ga Yusuf dabe ji ba be gani ba shima an ritsa dashi, anya hakki ze barshi kuwa, wannan tunanin ne ya cika masa zuciya ko Abinci ya kasa ci.


Widad ta buWe ido a hankali ta kalli inda Yusuf ke kwance, duk jikinsa jini, se sauke ajiyar zuciya yake, gashi an Waure shi tamau da sar?a.

Ko tashi bata iyayi saboda dukan da take sha, jikin ta ko ina rauni ne, ta janyo jikinta a hankali tazo inda Yusuf ke kwance kawai ta faWa kansa tana kuka.

"Yoseef dan Allah ka tashi, dan Allah kayi magana idan kana jina"

A hankali can ?asan ma?oshinsa ido a lumshe yace "Insha Allah zamu kuSuta, ki dena kuka, ina mana Addu'a nasan Daddynki ma yana yi, Ummana ma tana yi mana"

Haka ta cigaba da ?o?ari ko zata iya kwance Yusuf, amma abu yaci tira.

"Ranka ya daWe yarinyar nan fa baza tayi magana ba, mun daka mun daka amma kamar jinjirar jaka saboda taurin kai, mun mata jina jina amma ta?i faWa se rashin kunya take yi, gashi kwana huWun nan Ruwa kawai suke sha, ita muna bata Abinci amma ta?i ci duk ta galabaita "

Alhaji Haruna yace " A tauna tsakuwa, dan aya taji tsoro kuyi mata azaba wadda zataji a jikinta"

Me adda yace "An gama ranka ya daWe"

Ya buWe ?ofar Wakin dasu Widad ke ciki, tana zaune a gaban Yusuf ta zuba masa ido idonta yayi jawur saboda yunwa da wahala, gashin kanta duk ?asa da abun ciyay, saboda birgimar da take a gurin, ya sauka a kafaWarta ya baje kamar mara hankali.

Suka ?araso suka kwance Yusuf, da shima yake a mugun galabaice, suna kwance shi Widad ta kama ?asan rigarsa tana goge masa jinin jikinsa, me Adda ya fizgota ya zaunar da ita tana fuskantar sa yace "ke dan uwarki wannan shine karo na ?arshe da zan tambayeki, dan mun gaji da wannan sintirn a wannan sur?umin dajin, ina takaddun nan suke?"

Cikin tsawa tace "ban sani ba! Kuma karka sake zagin uwata dan uwa bata fi uwa ba"

Yadda gashin kanta ba?i kamar na Larabawa ya baje, gaba Waya seta burgeshi dan?o gashin kanta yayi ya mi?ar da ita tsaye, tsanani zafi yasa ta fasa ihu, Yusuf ya yun?ura ze mi?e suka sake buga masa sanda a ?afa ya faWi ?asa.

Ya kai bakinsa na Widad da niyyar ya haWe bakinsu, tayi masa gware da kanta, dukda yaji zafi hakan besa ya cikata ba, ya kuma dan?ar gashin kanta ze haWe bakinsu, ta tattaro ?arfinta ta daki mararsa da ?afarta, a gigice yayi jifa da ita, ya Wakko ?aramar pistol ya harbe ta a hannu, tare sukayi ?ara da Yusuf ta zube a gurin jini na zuba a dantsenta.

Me adda mi?ewa tsaye ma kasawa yayi saboda bala'in azabar da yake ji, 'yan uwansa suka Wauke shi, suka sake kulle su Widad.

Yusuf ya ?arasa kan Widad ya Wagota, a gigice yake magana "Widad sannu, kina ganina?"

Ta jinjina masa kai dukda idonta na ?o?arin lumshewa, jikinta se rawa yaje gumi na tsatstsafo mata ta ko' ina.

Yusuf ya Wau Wan siririn mayafint da tazo dashi ya Waure mata damtsen, ya rungomata jikinsa yana jijjigata yace

"Dan Allah karki tafi ki barni, zamu bar gurin nan insha Allah, zan maida ke gurin Daddy, dan Allah Widad karki tafi ki bar Yusuf"

Sosai hawaye ke zuba daga idon Yusuf, magana takeson tayi amma ta kasa, se rawa da bakinta yake yi kawai, ta Waga hannu da nufin ta kaishi fuskar Yusuf amma abu ya gagara hannun ya sauka tun tana ganin Yusuf dishi dishi harta dena ganinsa wuyanta ya langaSe.

Rungume ta yayi a jikinsa yana ambaton Allah, yana shesheshe?ar kuma, yayin da mayafin da ya Waure mata hannu dashi ya ji?e sharkaf da jini.



In an karanta ayi share please, masu neman recent pages dan Allah ku dinga dubawa a watpad, @ Ayshercool7724.


Domin gyara, sharhi ko shawara
Ayshercool
07063065680

?? ? ? ? ? ? ? ?? ? _*A?IDATA*_
? ? ? ?

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login