Showing 105001 words to 108000 words out of 135555 words

Chapter 36 - AKIDATA book 1 HAUSA NOVEL

17 Jan 2026

663

shahararsa ne? Dole zasuji ai"

Wayar hannun Alhaji Musace ta fara ringing, ya fito da ita ya Waga .

"ban samu halartar zaman da kuke a daren yauba, hakanma duk yana cikin shirina ne, yakamata ku maida hankali gurin gane cewar wani yana muku zagon ?asa, akwai na jikinku wanda yasan siriinku shine yake ta dagula muku lissafi, ku maida hankali gurin gano waye, sannan kusam duk yadda zakuyi ku kama wanda sukayi garkuwa da 'yar gidan Daula ku kashe su, in bahaka ba akwai gagarumar matsala, sannan ko a mace ko a raye ku tabattar an kama yaran nan an kashesu"? yana gama maganar ya kashe wayarsa.

Nan fa suka sake shiga wani ruWanin, tabbas inba wanda yake cikinsu ba babu ta yadda za' ayi Su Widad su iya tsira daga inda aka Soyesu.

Alhaji Haruna yace "to kun daiji abunda Alhaji Bukar yace, yanzu abunda za'ayi shine, kusa a binciko mana wanda aka bawa bincike hukumar jam'ian tsaro, ayi karSo mana sakamakon binciken, hakan ze ?ara haska mana wani abun"

Alhaji Munir yace "wannan kuma aikin Saleh ne, shi'aka Worawa wannan ragamar"

Alhaji Musa yace "Na kira shi sam labarsa bata shiga, inaga zan tura Wan aike a kiramin shi da safe"

Haka suka gama tattaunawa suka tashi ba tare da cimma wata ?wa?warar matsaya ba.

Da safe Hajiya Halima nata safa da marwa, layin Ramlah sam baya shiga, ?arfe goma na safe sega Ramlah ta dawo, Hajiya Halima tace? "daga ina kike?"

Kafin tayi magana Fahad ya shigo, Yace? 'Mummy barka da safiya, mun miki laifi ko? Wallahi bayan mun dawo daga cinema ne naga kwana biyu ba taje gidanmu ba, kawai muka zarce can, daga nan kuma mumsy tace seta kwana tunda bata zumunci "

Hajiya Halima tace " Aida ta kira ta gayamin, hankalina ya tashi ince kaddai kuma an sace mana ku"

Ramlah tace "haba Mummy wani irin sacewa kuma, ai an san wanda ake sata, ina tare da Fahad waye yavisa ya saceni"

Sukayi dariya gaba Waya, Fahad ya kashe mata ido, sukayi Sallama ya tafi.

Ramlah na zuwa Wakinta ta jefar da jakarta ta kife akan gado ta cigaba da bacci, saboda har yanzu ?wayar da ta sha bata saketa ba, kuma ga rashin sabo dama, dan bata taSa shan kayan maye ba.

Yusuf bayan ya dawo daga sallar Asuba, har ya kwanta ya tashi, ya duba shimfiWar Widad yaga bata nan, zumbur ya mi?e zaune a gigice yana waige waige, mi?ewa yayi ya fito tsakar gidan bakowa, saboda yanayin garin da sanyi kuma gari be gama waye ba, le?e le?e ya shiga yi yana nemanta, can ya hangota daga wani Wan lungu tana tsaye tana le?a wata taga se murmushi take, hannunta ri?e da brush da toothpaste, kan nan ko Wan kwali babu, gashinta ko taza babu ta naWeshi da ribbon ya kwanta a bayanta.

A hankali ya ?arasa inda take cike da son sanin me takewa wannan murmushi haka?

Jin mutum tayi a tsaye a bayanta, ta juyo a Wan razane, Yusuf ta gani a tsaye a daf da ita.

"meye haka?"

Yusuf yace "gani nayi kina tsaye kina murmushi, shiyasa nace bari inga abunda ya saki nishaWi haka? Sannan gari akwai sanyi fa, kalli kanki babu Wan kwali kar mura ta kamaki, sannan kayan jikinki? maza na shiga na fita a gidan nan, kar gari yayi haske suzo su sameki a haka, su kansu matan gidan zasu ga hakan wani iri saboda ya saSawa Al'adunsu"

"Wai kai meyasa ka fiye shishshigi da takura ne?"

"ba shishshigi da takura bane, kinga yanzu kina da Aure fa"

"kaga wannan Auren fa dashi da babu duk Waya, karka ?ara sawa ranka wani Aure mukayi"

Yusuf ya Wanyi murmushi, cike da basar da zancen? yace?? "kin tsorata nifa, harna kwanta na duba ban ganki ba, shiru shiru kuma naga baki shigo Waki ba"

"hmm kayi zaton zan gudune? In gudu inje ina? Ko kana zaton zan gudu da wannan Auren naka a kaina? Idan kaga na gudu ko na bar ?auyen nan to tabbas ka sakeni ne"

Yusuf yace "idan kuma ban sake kin bafa?"

Juyowa tayi ta saka idonta a nasa tace "me kace?"

Girgiza mata kai yayi alamar bakomai, ta harareshi tace? "ban guri in wuce"

Seda ta tafi ya Le?a me take kallo, Wakin zomaye ne, an kunna musu aci balbal an rataye ta, se guje guje suke suna ha?a ?asa, da wasanninsu shine abunda yasa ta nishaWi ta tsaya take kallonsu.

Yusuf ya koma ya kwanta bacci ya Wauke shi, ita kuwa Widad data gama brush Win komawa tayi ta cigaba da kallon zomaye, seda ta gaji sannan ta koma Waki.

Yusuf yayi juyi ya buWe idonsa a hankali, ya sauke su akan Wid????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? ad, ta gyara shimfiWarta sa kanta, ta sauke Akwatunanta tana ta gyara kayan ciki, ta ware masu datti ta tattare Akwatunan ta canza musu guri, duk Yusuf yana kallonta, Widas sam bata son ?azanta, tana da matu?ar son tsafta a rayuwarta.

Yusuf ya tashi ya kwashe kayan shimfiWarasa ya ninke, bata kula shi ba sabgoginta kawai take, Yusuf yayi mamakin danganar da Widad tayi, dukda har yanzu bata saba da abubuwa da yawa ba.

"wai babu inda za'a samu inji wanki ne? Ina son a wanke min wannan kayan ne"

Yusuf yace "Ai baki da wani injin wankin daya wuceni, in kin haWa se in Wiba inje in wanko su"

Widad tace "kaine zaka wankemin kayan?"

Yusuf yace? "eh mana, ko kinga alamar injin wanki a garin nan, tunda muka zo kin taSa ganin wuta?"

"to gasu nan na haWa, kaje kace a bani ruwan wanka"

Yusuf ya girgiza kai yace "to"

Ya mi?e ya Wau bokiti ya fita, Widad ta buWe Akwatinta ta Wakko towel ta Waura, ta saka hijjabi ta biyo bayansa yadda ana haWa ruwan se ta shiga tayi wanka.

Mutan gidan sunata hada Hadar yadda za'a haWa karin kumallo, ga dukkan alamu yau mutuniyar Widas ce da girki, wato Harira.

Yusuf ya dur?usa ya gaishesu, cikin jin nauyi kafin yayi magana Gwaggo tace? "Yusufa na ganka da bokiti, ruwan wankan za'a zuba mata?"

Yusuf yace? "eh Mama"

Tace? "kawo in zuba maka anan, ya jikin nata kuwa"

Yusuf yace "jiki Alhamdilillah"

Tace? "Madalla, nikam ya sunan nata ne? Bamu san sunanta ba"

Yusuf yayi murmushi yace "Sunanta Widad"

Hari dake gaban murhu ta juyo da sauri tace?

"Bala'i, wannan wane irin sunane? Hudas ko wudas sekace kayan citta da masoro wane irin sunane wannan"

Tsakin Widad ne yasa Yusuf juyawa, yadda ta tamke fuskane ya tabattar maaa sa taji abunda Hari tace, Yusuf kamar yayi dariya Amma ya basar kar suyi faWa a gaban mutane.

Gwaggo tace "kaga 'yar halak, ana zancenta se gata, sedai ni wannan sunan nata na Larabawa bazan iya faWa ba, Amarya ya jikin naki?"

Widad a ranta tace "wai Amarya TaSWijan"

Yusuf yace "Ana miki ya jiki?"

"Naji sau?i"

Galala Hari ta bita da kallo tace "Ashe bahaushiya ce, wallahi ganinta nake kamar bata jin hausa, yo aini harna fara tunanin ko kurma ce, ashe tana magana sannu Amarya wudas, ashe kina magana Allah sarki, ya jiki?"

Sake yamutsa fuska Widad tayi, 'ita dai wannan matar bata gajiya da magana, kodai bata san yadda ha?oranta suke bane take buWesu tana surutu haka, bar wani kore kore ne a jikinsu, ga maganar tsiya da take dashi"

Widad bata kulata ba, aka haWa mata ruwanta, Yusuf ya kaimata inda take wanka.

Aka haWa Yusuf da yaro ya rakashi rafin da matasan garin suke haWuwa suyi wanki.

Amlace ta shiga Wakin Ramlah, ta dinga bubbuga mata filo, da ?yar Ramlah ta tashi a fusace tace? "Meye haka Amal?"

Amal tace? "Anya lafiyar ki kuwa? ?arfe biyi fa, amma har yanzu bacci kike, yakamata ki tashi haka ai"

Mi?ewa tayi zaune tana mi?a tare da duba agogo, dagaske biyu na rana, haka ta mi?e ta tafi banWaki tayi wanka sannan ta Wanji ?arfin jikinta.

Koda Saleh ya dawo kano, be biya ko'ima ba Asibiti ya fara zuwa duba jikin Alhaji Nasir, amma yanayin jikin nasa se godiyar Allah, Nurses suka gaya masa Anwar yaje masallaci.

Saleh ya zauna a kusa da Alhaji Nasir, wanda idanunsa ke lumshe yake numfashi da temakon Na'urar dakw bashi iskar Oxygen, ya ri?o hannunsa da suka yi sanyi ?alau, cike da tausayawa ya kai bakinsa daidai kunnensa? yace
"Allah ya baka lafiya YallaSai, 'ya' yanka sun kuSuta daga hannun miyagun nan, yanzu haka suna wasu ?auye na basu mafaka, saboda tseratar da Rayuwarsu, Yusuf yayi ?o?ari matu?a ya kula da Amanarka, yana kula da gimbiyarka sosai, Amma munyi maka wani laifi da ban san ya zaka Wauki abunba, Na wuce gaba Yusuf ya Auri 'yarka, dan kasan bata yadda da kowa seshi, kuma baze yuwu ya cigaba da kula da ita ba, tunda ba muharramarsa bace"

Dukda Alhaji Nasir ba iya magana zeba, da alama yana jin abunda Saleh yake faWa, ?ara ri?e hannun Saleh yayi gam sannan yayi masa murmushi.

Saleh yace "Amma karka kuskura ka gayawa kowa, kayi shiru da bakinka"

Anwar ne ya shigo bakinsa Wauke da Sallama, yana ganin Saleh yayi murmushi yace "Saleh sannu da zuwa, naje Sallane"

Saleh yace? "bakomai Anwar, ya me jiki?"

Shiru Anwar yayi, ?walla na taruwa a idonsa yace?

"Saleh na rasa wane irin abokai Allah ya bawa bawan Allah nan, sam hankalinsu baya kansa, amma lokacin da yake da lafiya sune kan gaba gurin nuna masa ?auna, Amma dubi yanzu, look at how he's suffering alone, ba wanda ya bani mamaki kamar mahaifiyata"

Anwar ya ?arasa maganar, jijiyoyin kansa na tashi idonsa yayi ja, Alhaji Nasir ne yayiwa Anwar Alamar yaje da hannunsa.

Anwar? ya ?arasa gaban gadon Alhaji Nasir ya zauna.

Alhaji Nasir ya kamo hannun Anwar, sannan ya mi?a hannunsa Waya yana shafa kan Anwar tareda yi masa murmushi a hankali yace? "Nagode, Nagode"

Kawai Anwar ya rungume Daula ya fashe da kuka, shima Daula hawayene suka fara bin gefen idonsa, da ba ?aramin mamaki ya shiga ba, ganin yadda gaba Waya mutanensa da suke tare dashi suka watse suka barshi, ciki harda matarsa da take morarsa.

Yusuf yaje ya tarar da matasa da magidanta a gurin wankin nan, wasu na wanki wasu na wanka a ruwan, in an koro dabbobi suma suzo su sha ruwan, amma a haka yaga wasu na Wiba na tafiya dashi abun ya bashi mamaki, dama a gurin salla megari ya gabatar dashi, dan haka wasu daga cikinsu sun sanshi.
Duk rashin son mutane irin na Yusuf ya Wan sake dasu, suka dinga hira suma bashi labari akan yanayin garin nasu.
Abun ya dinga bawa Yusuf mamaki, suna rayuwa cike da son juna mutanen ?auyen, sedai abun mamaki Wan majaillisar dake wakiltar yankin kakannisa 'yan garinne, amma abun mamaki sukace lokacin da yake campaign har falafalan wuta aka samu su, ya gina musu borehole guda Waya can wajen gidan kakaninsa shima se anyi tafiya me nisan gaske borehole Win yake, yace idan suka zaSe shi yaci ze janyo musu wutar lantarki, tundaga wannan campaign da yazo tsawon shekara uku basu sake ganinsa ba, ko gidan kakannin nasa baya zuwa ziyara gaba Waya ya koma Abuja.
Haka Yusuf suka cigaba da hira shikuma yana wankinsa, seda ya gama suka bushe ya ninko kayan tsaf, sannan suka taho sa wani ma?ocin gidan megari zuwa gida.

Yana zuwa gida ya tarar da Widad a ?ofar Wakinsu a zaune, zaman dirshen a ?asa fuskarta tayi jawur saboda kuka, Yusuf ya razana ko ciwonta ne ya tashi.
Gwaggo na ganinsa tace "yawwa Yusufa, wallahi muna tsakar gida muna aiki muka jiyo ihunta, ta fito da gudu mukaje kanta, juyin duniya ta?i magana tayi zamanta a nan gurin, munce ta bar ranar ta shiga ko Wakina ta zauna ta?i.

Yusuf ya ?arasa inda take ya ajiye bokitin hannunsa me Wauke da ninkakkun kayansu? yace "lafiya kuwa? Meyasameki haka?"

Cikin harshen turanci tace masa, "wasu ?warine suka yi ta cizona, sekuma naga spider manya guda biyu a Wakin, dana fito nan ma ?warin suka cigaba da cizona"

Girgiza kai yayi yace "shikenan tunda na dawo tashi mu shiga Waki, kalli a yadda kike kin zauna a tsakar gida kowa yana kallonki a haka, kuma kinga kin tayarwa da mutanen gidan hankali"

"wallahi bazan shiga ba se an cire wannan spider ni bana sonshi, bana son ganinsa it's irritating me, looks at my body"

Se yanzu ya lura da yadda kafofin gashinta suka buWe, jikinta yayi wani irin burWin_ burWin, fuskarta ma tayi ja saboda cizon sauro.

Hari tace "Allah dai yasa ba wani abun mukayi mata ba, dan naga alamar makirace, tun Wazu muke fama ta?i magana, Amma tana ganin mijinta ta fara magana hadda karairaya"

Widad ta Waga kai ta ?urawa Hari ido, yayin da gwaggo taji haushin abunda Harin tayi.

Yusuf kam ba ?aramin dariya Hari ke bashi ba idan ta kunna Widad, yasan Widad tana mata kawaici ne kafin ta Wan sake.

Yace "ba wani abun kukayi mata ba, wai wani abune ya cijeta amma, bakomai yanzu zan shiga in duba"

Yusuf ya shiga ya duba bega gizo2 ba, sedai cinnaku dake yawo a Wakin, da alama su suka cijeta.
Yasa tsintsiya ya shashsharesu tsaf, sannan yace ta dawo Wakin.

Yusuf "Yace meye ya cijekin?"

Guri ta zauna ta janye rigar jikinta, ta nuna masa cinyarta, fara tas fiye da fuskarta, sedai tayi ja saboda cizon cinnaka, banda wanda ya gasa mata a hannu.

Yusuf yace? "Sannu bari in tambayi gwaggo inda zaitun ta bani ki shafa"
ZumSura baki tayi tace? "ni banyi wanka ba"

Haka ya karSo ruwa tayi wanka, sannan ta dawo Wakin, ya bata guri ta sa kaya, ya Wakko zaitun ta zauna ya shafa mata a na hannun, ya fara shafa mata a ?afarta ne a hankali, haka kurum taji jikinta wani iri, kawai seji yayi ta doke hannunsa tace
"meye haka?"

"Me kuma nayi miki?"

"ban sani ba" ta bashi amsa tare da mi?ewa, Wan sunkuyar da kai yayi yana murmushi.

Daga Asibitin gurin Alhaji Musa Saleh ya wuce, yaje ya sames hi a office Winsa.
Saleh yace? "Ranka ya daWe kwana biyu bani da lafiya, ko ?ofar Waki bana iya fitowa, shiyasa kwana biyu bana zuwa"

Alhaji Haruna yace "Akwai damuwa fa, ko Kasan me Adda ya cemin yarinyar nan sun gudu"

A razane Saleh yace "wace irin maganar banzace wannan? Kamarya sun gudu?"

"Nima dai abunda na gani kenan, gaba Waya sun mayar mana da aiki baya, yanzu Bukar yace ko a raye ko'a mace anemosu a kashesu kar Asirinmu ya tonu, sannan kaje ka bincika mana wa'aka bawa aikin binciken nan a cikin jam'ian tsaro?"

Saleh yace "Amma fa wani hanzari ba gudu ba, ina kyautata zaton me Adda yana sane ya sake su, wata?ila tace zata bashi kuWine koma ta ninka masa abunda kuka bashi, shine ya sake su, in bahaka ba ta yaya zasu iya tserewa? Kokuma a cikinku ne wani ya zagaya ya haWa baki dashi, idan an karSo abun a gaya masa shikaWai ba"

Shiru Alhaji Haruna yayi yace "Biri yayi kama da mutum, kuma fa Saleh kayi magana, tabbas dan nasan zata iya, kuma babu Abunda me Adda baze iya akan kuWi ba"

Jinjina mara adadi ga Wumbin masoya littafin A?IDATA, niba abunda zance muku se godiya Allah ya bar ?auna, ga dogon page nan, nima inga dogon sharhi, ga link Win telegram nan a ?asa

https://t.me/joinchat/SYIfEaoQo_JlNDM0

Share, share and share please =?O? =?O? =?O?
Domin gyara sharhi, ko shawara
Ayshercool
07063065680

? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ?? _*A?IDATA*_
? ? ? ?

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA _
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*A?IDA TA *

I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum

Ha??in Mallaka ?& : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ?unsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani Sangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

NOT EDITED

ELEGANT ONLINE WRITER'S

? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ?? PART1
? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? Page 34_35



Saleh ya cigaba da ziga Alhaji Haruna, akan lallai yayi bincike, dan zata iya yuwuwa abokan har?allaesa ne wani yasa a karSo masa abun hannun Widad, shiyasa me Adda yace masa sun gudu.

Alhaji Haruna yace "Nagode sosai Saleh, Insha Allah zanyi tunani akai"

Saleh yace "bakomai yallaSai, bari in Wanje gida in huta, kasan bana jin daWin jikin nan nawa"

Alhaji Haruna yace? "shikenan Allah ya sawwake"

Saleh ya tashi ya tafi

Sakina ce fuskarta Wauke sa damuwa ta shiga ofishin Suleiman, Suleiman yace "Sakina lafiya kuwa?"

Sakina tace "YallaSai akwai damuwa, yau sati biyu sa sace Yusuf amma har yanzu babu wani kyakkyawan rahoto, da yake nuna ana bincike akan lamarin nan, anya anyi adalci kuwa duba da yadda Yusuf yake bada gudunmuwa akan harkar tsaro, amma ace shi wannan iftila'in ya faWa masa amma babu wani yun?uri da'ake gurin ceto shi, idan ya rasa ransa fa? "? ta ?arasa maganar kamar zata yi kuka.

Suleiman yace "look Sakina, kiyi wani tunani kodan Albarkacin 'yar babban attajirin da' aka sace su tare, yaci ace an maida hankali akan nemansu, amma har yanzu shiru, shikansa Daulan yana gadon Asibiti a kwance, na kai ?orafi akan abari muma mu gudanar da namu binciken, amma daga sama aka bani umarnin cewar ba'a samu ba, ana gudanar da bincike akan al'amarin, babu wani abu da zamu iya banda muyi musu Addu'a "

Sakina tace " shikenan YallaSai, ubangiji Allah ya kuSutar dasu lafiya, bari in koma kan aikina"

"Shikenan Sakina, Allah ya taimaka"

Sakina na tafiya, telephone Win gaban Suleiman ta fara ringing, ya sa hannu ya Waga, jin muryar wanda ya kira shin yasa shi mi?ewa tsaye cikin girmamawa yana amsa wayar.

"A cikin ma'aikatanka wa'aka saka akan binciken masu bibiyar Alhaji Nasir Daula?"

Suleiman yace? "YallaSai Yusuf ne, wanda aka ?arawa matsayi kwanan nan"

"A gaggauta kammala binciken nan,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login