Showing 63001 words to 66000 words out of 135555 words

Chapter 22 - AKIDATA book 1 HAUSA NOVEL

17 Jan 2026

671

yuwu ba"

"kiyi ha?uri Hajiya, nima ba da san raina ba, sedai ita Madam bata jiran izinin kowa kafin ta yanke hukunci, dan haka wannan maganar a tsakanin ku ya kamata ku tattauna ta"

Har Hajiya Halima ta buWe baki zata yi magana se kuma tayi shiru, waiwaya wa yayi yaga Shigowar Widad ce tasa ta yin shiru, bata kula su ba tayi part Winta, shima Yusuf ya silale ya bar falon.

*******************************

"Maman Yara ina cikin farinciki ?ana ze dawo, yakamata ayi dukkanin wasu shirye shirye da suka dace domin tarbarsa, yasuhe rabon sa da ?asar nan? Sannan ya dawo ya tarar da kyakkyawan Albishir"

HaWe rai Hajiya Sarah tayi tace? "nikuma takaici ne fal raina wallahi"

"Saboda me takaici fal ranki, kamar ba Wanki me ze dawo ba?"

"Eh Wana ne, amma abunda kake shirin yi kaima kasan be kamata ba, ta yaya yarona lafiyayye zaka haWa shi Aure da mahaukaciyar da bata san girman kowa ba, ga bata da tarbiyya"

Alhaji Bulama yace? "Easy Madam, Sarah shifa Wa na kowane, bekamata ki cigaba da aibata Widad ba, itama kamsr 'ya take a gurin mu duba da yadda mahaifinta yayi mana halacci a rayuwa, muna ?o?arin yin abunda zesa ta dawo hayyacin ta ne, kuma kinga mu munsan larurarta, Fahad ze iya ha?uri ya zauna da ita, saSanin a bawa wani a waje Auren ta"

"to kai kaWai ne yakamata kayi tamakon? Ina sauran mutanen gari? Nidai gaskiya aka haWa Auren Wana da wannan tantiriyar mara mutuncin an cucemu, kai kanka da kake matsayin uba a gurin ta cin zarafin ka take, inaga Wanka kuma?"

"Sarah, bazan zaSawa yarona abunda ze cutar da shi ba, Aure yana gyara mutum, wuyarta su zauna a guri Waya ze iya canza ta"

"A'a canza halin wannan yarinyar banga ta inda ze yuwu ba Sam, kawai ka canza shawara da tunani"

Tai maganar tare da mi?ewa ta bar masa Wakin

************************************

YallaSai Suleiman na dawowa, Abbas ya mi?e ya tafi Office Winsa, ya shiga ya gaida Sulaiman cikin girmamawa irin ta masu Wamara, se da yayi masa izini sannan ya zauna, suka sake gaisawa.

Abbas yace "YallaSai, lokaci fa na ?urewa, game da aikin nan daka bawa Yusuf, bana tunanin abunda aka sashi yake yi, Wazu yazo gurin nan, na Wanyi masa tambayoyi akan aikin, Amma Amsoshin daya bani sam basu gamsheni ba, da alama dukiyar dake gidan da alherin da suke masa yasa ya bar aikin da 'aka sashi "

" Amma a iya sanina Yusuf mutum ne me haza?a, nasan shi da ?wazo da himma akan aiki, ba shida kwaWayi sam"

"YallaSai mutum na iya canzawa a kowane lokaci, Yusuf abokina ne, amma ba yadda zanyi, bana son inci amanar aiki ko' a samu matsala akan harkar aikin mu kimar mu ta zube a idon duniya, Amma ya kamata kayi wani abu yallaSai"

Suleiman ya Wanyi shiru sannan yace? "idan kuwa hakane, to tabbas Yusuf ya bani mama, sedai zan kira shi muyi magana, zan bibiye shi idan har na gano maganar da kake gayamin gaskiya ne, zan Wau mataki na musamman akansa"

Abbas yace "YallaSai idan har ka kira shi kuyi magana ai zaka Sata komai, zeyi duk me yuwuwa ya kare kansa koda kuwa ?arya ze maka danka yarda da shi, tunda shima jami'in tsaro ne yasan duk hanyar da zebi ya kare kansa"

Suleman yace? "Abbas base ka nunamin aikina ba, Nagode da wannan bayani naka zan bincika, ka ciji jami'i nagari tunda har kishin aikin ka be hanaka Soye laifin Abokin ka ba"

Abbas ya mi?e ya sarawa Suleiman sannan ya fice.

Koda ya bar Office Win Suleiman Office Winsa ya koma yana tunani, tunani yake akanme zeyi wanda zesa gaba Waya aikin da Yusuf yayi ya lalace kowa ma ya huta?

************************************

Gaba Waya Nurat ta rasa abunda yake mata daWi, ta shiga damuwa rashin samun wayar mutumin da ko? sunansa bata sani ba, dama Widad ta dena Waga wayarta gaba Waya, tun ranar da tazo birthday Win ta, abun nan ya faru, ta fara shawarar ko gidan su Widad zata je don ta tambaye ta wannan wanda suka zo taren.
Sedai kuma tayi wani tunani, aiki ne me matu?ar sau?i a gurin Widad ta sa aka mata a Waure, bata da tabbacin Abokinta ya gayawa Widad abunda ya faru kokuma A'a, gaba Waya ta rasa abunda yake mata daWi, komai ya dena mata daWi se tunanin wannan bawan Allah, me matu?ar kirki, a farko tayi zaton shima mugu ne lokacin da ya ritsata har yayi mata barazana, amma yanzu ta gane ba haka abun yake ba, ranar da yazo gidan yanayin yadda ya mu'analance ta da kyakkyawar ma'amala.

************************************.

Fahad ne da Anwar tsaye a tashar jirgin Sama, Anwar yace "Fahad ina taya ka murnar kammala karatun ka, Allah ubangiji ya kaika gida lafiya, sena taho nima in next couple of weeks Insha Allah"

Fahad yayi murmushi yace? "to baban Soyayya, kaima ina taya ka murna, tsiran namu befi sati biyu, ina maka fatan Nasara Wan uwana seka taho".

Suka rungume juna suna murmushi, sannan Fahad yaja trolley Winsa yayi gaba.

"Amal kin san wani abu kuwa? Munyi waya da Yaya Anwar yace min Fahad yau ze dawo Nigeria, baki ji daWin da nake ji ba, dan Allah me ya kamata inyi wanda zan sake kama zuciyar sa, yaji in ba niba se rijiya"

Wani banzan kallo Amal tayi wa Ramlah tace? "Ban sani ba, kije kiyi abunda kika ga ya dace"

Cike da mamaki Ramlah tace? "lafiyar ki kuwa? Me yayi zafi daga neman shawara zaki hayayya?omin?"

"dole kice haka mana, da yake matsalarki itace damuwa kawai, ni ina lokacin da nake cikin tawa damuwar ziga Mummy kikeyi, kuka haWemin kai kuka dinga hantara ta, har dena kulani kukayi saboda kawai nace ina son Yusuf, Ashe ke kaWai kika san So, ni ban sanshi ba ko? Can ta mulmule miki gara tun wuri kema ki cire shi daga ranki, dan in kin manta bari in tuna miki, 'yar masu gida akace ze aura kuma kinsan baki isa kice kina da matsala da hakan ba, danke ba mutum bace a kanta, kuma kinsan baki isa kiyi takara da ita ba, akan haka ba' a?i a baki red card daga gidan nan ba, you better go back to your senses "

Tana gama faWin haka ta mi?e ta fice daga Wakin, wani zazzafan gumi ne ya shiga karyowa Ramla, dan gaba Waya ta manta ds batun ance za'a haWa Auren Widad da Fahad.
Gaba Waya kanta ys kulle dan bata san wama yakamata ta tunkara ba, Mummy ba abunda zata iyayi, shiru tayi tana tunanin meye mafita? "

************************************

Widad ta dudduba Aiken da Yusuf ya kawo mata, ya siyo komai kamar yadda tace, harda receipt ya kawo mata, tana duddubawa taci karo da wata leda, Wakko ledar tayi ta buWe me zata gani, wasu tsala tsalan Abaya ne kala biyar, kowacce da kalar ta sunsha stones se ?yalli sukeyi, ta Wauka Waya bayan Waya tana jujjuya su.
'me wannan gayen yake nufi?' ta tambayi kanta

'harni ze saiwa kaya ya bani? Meya maida ni ko nayi masa kalar saka wannan kayan?'

Tattare kayan tayi ta fito falo a fusace, da watsasu akan kujera, part Win su Amal ta nufa tana huci, babu ko sallama ta banka Wakin su Amal, gaba Waya seda suka razana, mussman Amal dan a tsorace take tun ranar da Widad ta gansu tare da Yusuf.

Ta kalli Amal tace? "Kije bakin gate, ki kiramin wancan sakaran direban yanzun nan" tana gama maganar ta juya ta fice

Ramalh na ganin a yadda Widad ta shigo tayi magana, tasan akwai matsala dan haka ta mi?e ta fita dan ganin me ze faru,
Jikin Amal na rawa ta mi?e tayi waje kiran Yusuf.

Koda sa?on Kiran Widad ya riski Yusuf yasan a rina, yasan ze fuskanci wula?anci, Amma ya dake ya shiga cikin gidan.

A falo ya tarar da ita a tsaye, tana wani irin huci, haWi da sauke numfashi, Tabbas Widad Yarinya ce ?arama Amma Allah yayi mata kwarjini na musamman.

Yaje daf da ita ya tsaya ya sunkuyar da kai ba tare da yace komai ba.

"Kalleni nan"

A hankali ya Waga idonsa yasa a nata, dukda bugawar da ?irjin Widad yayi be hanata cewa
"Nayi maka kama da matsiyaciya ko me neman temako?"

Kallon ta yayi bece komai ba
Cikin tsawa tace? "magana nake maka"

"temako ana yinsa ga kowa, duba da rayuwar gaba Waya taimakon juna mukeyi, dan haka ba fuska ake gane...

" Shut up!!! "
Tai maganar tare da Waga masa hannu

"waye kai? Me kake da shi? Me kake ta?ama dashi wanda har yasa kake ganin kana da abunda zaka Wauka ka bani? Me kake da shi? Ni zaka bawa wannan banzayen Abubuwan na maka kama da wadda zata saka wannan tarkacen, shara? Ka taSa ganin na saka irin wannan kayan? Ko na ce maka ina da bu?atar su? "

Te ?ebo kayan dake kan kujera ta watsa masa a fuskar sa tace " don't you ever try to make this mistake again, ka nemi mabu?ata ka basu? Widad tafi ?arfin saka wannan tsumman"

Idon Yusuf jawur ya Wago ya kafe ta da ido, ko ?yaftawa baya yi, dukda hucin da take hakan be hana ta tsayawa tana kallon sa ba itama.

Ba zato ba tsammani suka ga Daddy ya ?araso cikin falon, ya dur?usa ya tsince rigunan, yazo gaban Yusuf ya kamo hannun Yusuf yasa nasa yace
"Yusuf wannan kyautar ni kayi wa, ba Widad ba, lokacin da zanyi tafiya ka kawo alheri ka bani kace in ?ara a guzuri, kuma ka nemi da kar in gayawa kowa, yanzu ma ka Wakko kyauta ka bawa 'yata Wiya tilo da nafiso, Tunda Allah yayi min Arziki babu wanda ya taSa Waukar alherin naira biyar ya bani, saboda kowa gani yake ni me wadata ne bana bu?ata, sedai ma kullum a nema a gurina, idan kuwa kaga anmin kyauta to wani abu ake nema a gurina, Mutum na farko da yayi min kyauta har sau biyu kuma saboda Allah, nagode sosai Yusuf, nasan kana ha?uri Amma ka ?ara zaka ga ribar sa, Widad ta gode da wannan kyautar"

Tabbas ba dan Alhaji Nasir ba, ko duniya yake samu a gidan nan baze sake zuwa ba, da babu abunda ze hana ya mi?a file Win aikin a Wora wani dan ya gaji.

Yusuf bece komai ba, ya jinjinawa Alhaji Nasir kai ya fice, zuciyar sa na ?una dan gaba Waya jijiyoyin kansa sun mi?e saboda Sacin rai.

Alhaji Nasir yayi wa Widad wani irin kallo, ya wuce part Winsa da kayan a hannun sa.
Se a lokacin ta sha jinin jikin ta, bin bayan Daddy tayi da sauri zuwa part Winsa.

Ramla tace? "Allah ya ?ara, maganin me shishshigi kenan, da haka da haka wataran zata sallameshi kowa ya huta"

Amal tace? "kema kiji da abunda ke damunki mana, aikin banza kawai"

A Waki Widad ta riski Mahaifinta, tace "Daddy are you angry?"

Shiru yayi mata yana ?o?arin ninke rigunan.

"Daddy am talking to you, why will you be angry? Am I wrong?"

Shiru ya kuma yi bece mata komai ba.

"Daddy magana fa nake maka"

"Me kike so ince miki Widad? Yaron nan yana matu?ar ?o?ari da ha?urin zama dake, Amma kalli yadda kike treating Winsa, yana miki biyayya yadda ya kamata amma bakya gani, can you remember when last someone offer you a gift, for the sake of God? Meye laifin sa dan ya baki wannan kayan, irin wannan rigunan Amminki take sakawa, sunfi mutunci akan wanda ke kike sakawa, bana son takuramiki saboda yanayin halin da kike ciki, Amma ba kya tausayin kanki, meye aibu da wanda yake ?asan ka ya baka kyauta, dukda muzguna masa da kike da wula?anci amma ya miki alheri, meyasa zaki Wula?anta shi, Widad ko baki yadda da abunda na gaya miki kwanaki ba? "

Shiri tayi tana nazarin maganganun Mahaifinta.

"baki ga yadda ya fita ransa a Sace ba? Baki kyauta ba sam"

"to yanzu ni me kake so inyi?"

"ki karSi wannan kayan kiyi amfani da su"

"Over my death body, gaskiya Daddy bazan iya saka wannan kayan ba"

Daddy ya jinjina kai yace? "As you wish, zanje ganin likita gobe in Allah ya kaimu, sannan ba?onki yana nan zuwa da weekends Win nan"

"Waye ba?ona kuma?"

"Fahad, mijin da zaki aura!!!"

Widad ji tayi tamkar Daddy ya watsa mata wuta me matu?ar zafi.

(MASHA ALLAH NA KAMMALA JARRABAWA ALHAMDILILLAH, INA GODIYA DA ADDU'OINKU NAJI DA?I NAGODE SOSAI NA GAMA JARRABAWA YAU ALHAMDILILLAH)

Domin gyara sharhi ko shawara feel free to contact me
Ayshercool
07063065680

? ? ? ? ? ? ? ? ? ?? _*A?IDATA*_

? ? ??
PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*A?IDA TA *

I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum

Ha??in Mallaka ?& : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ?unsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani Sangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends





ELEGANT ONLINE WRITER'S

? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? PART1
? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? Page 16_17


(Ayimin afuwa jiya nayi mistake Win pages)

Ko kallon inda Daddy yake bata kuma yiba ta fice ta bar masa Wakin.

Komawa Wakinta tayi, tana jin yadda zuciyarta ke wani irin bugu kamar zata fasa ?irjinta ta fito 'kenan har yanzu Daddy be janye maganar nan ba? Daddy why?'
Tayi maganar da ?arfi, tana sauke numfashi a hankali ta zube a ?asan carfet, gaba Waya kanta ya kulle ta rasa abunyi, tabbas wannan karon Daddy dagaske yake, idan kuwa ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????har Daddy ya dage a wannan ?udurin nasa to tabbas zata bijre, koma hakan yayi sanadiyyar ya rasa ta gaba Waya, kuma seta shata babban layi tsakanin ta da Bulama.

Ramla tunani take me zata yi wanda zesa a janye maganar Widad da Fahad, ya za'ayi mutumin data daWe tana tararirayar soyayyar sa lokaci Waya a wargaza mata komai, sam hakan bame yuwuwa bane, dole tasan abunyi dan yiwa wannan tufkar hanci.

************************************

Kallo Waya zakayi wa iyalan kasan suna cikin farin ciki, gaba Waya sun hallara a katafaren falon gabansu sha?e da nau'ikan Abinci kala kala, kowanne fuskarsa Wauke da farinciki.

Ramadan yace "Wallahi broz Fahad gaba Waya kaima ka zama kamar Bature, kaga yadda skin Winka tayi fresh kamar wani jariri"

Alhaji Bulama yace "Wannan ?aton ne fatarsa kamar jariri, kai dai Ramadan ka fiye shiririta"

Hajiya Sarah tace "Haba Daddy, ka kalli yadda ya wani murje yayi ?alau dashi"

Iman tace "Nikam banga abunda ya canza ba sedai yayi haske ya ?aro iyayi, ko hausarma bata fita sosai se kace Widad"

?an Sata fuska Hajiya Sarah tayi jin an ambaci Widad.

Alhaji Bulama yace "se suje can su cigaba da gwarancinsu"

Sam Fahad be fahimci abunda mahaifinsa yake nufi ba, haka suka ci gaba da ciye ciyensu suna hira cike da ?aunar juna.

Yusuf kuwa tunda ya baro falon nan ransa a Sace kai tsaye gida ya wuce, zuciyar sa nata faman tafasa, tabbas ?arshen wula?anci yau Widad tayi masa, banda dalilin aikin sa da kuma mutuncin mahaifinta da baze sake komawa gidan ba.

Nurat bata da aiki se tunanin Yusuf, ko bacci ta kwanta mafarkinsa take, gaba Waya zuciyar ta ta kasa samun nutsuwa, ta kira lambar Yusuf harta gaji, ta koma kiran ta Widad, amma itama bata tafiya, abun duniya duk ya ishe ta.

Tana zaune tana wannan zaman tunanin mahaifinta ya shigo Wakin ta, da sauri ta mi?e daga kwanciyar da take.
Ya kalle ta yace "ke meya ke damun ki ne?"
Girgiza masa kai tayi tace "bakomai Daddy"
"to naga Maman ki bata nan, gobe in Allah ya kaimu zamuyi ba?i ki gaya mata, za'ayi mana girki bana son na masu aiki fa"

"To zan gaya mata insha Allah"

"shikenan sena dawo"
"Adawo lafiya Daddy"
"Allah yasa"

Gaba Waya Sacin rai ya hana Yusuf bacci, kamar shi dukda yasan ba wata uwace da shi ba amma Widad ta dinga gaya masa wannan ba?a?en maganganun gaskiya idan ya ?yaleta tabbas taci bulus.
Tunani ya shiga yi me ze mata wanda ze nuna mata mahimmancin Wan Adam.
Da ?yar bacci ya Wauke shi cike da Sacin rai.

Da gari ya waye so yayi yaje gurin aiki amma ya fasa, yayi zamansa a gida se bayan azahar sannan yaje gidan.

Nura da Isa se wani kallon banza suke masa, Yusuf bashi da lokacin su dan haka bebi ta kansu ba.

Be daWe da zuwa ba Alhaji Nasir ya fito, yana ganinsa kamar babu abunda ya faru Yusuf ya mi?e ya nufi inda yake.
Cike da girmamawa kamar kullum suka gaisa, Alhaji Nasir yace "Yusuf kaga yau ma tafiya ta kamani, kar a gaji dani dai ga Amanar tilon 'yata nan, Fahad zezo gurin ta a satin nan Insha Allah, dan Allah a samin ido akan ta, sannan ka cigaba da ha?uri"

Yusuf yace "Insha Allah, Allah ya kaika lafiya ya dawo da kai lafiya"

"Ameen Yusuf"

Ya shiga mota, Nura yaja suka fita.

Larai me aiki ce ta fito ta samu Yusuf tace "kaje inji 'yar masu gida"

Yusuf yace "Ina zuwa"

Yai zaman sa kamar bashi akace ana kira ba, Isa yace "da alama Yusuf ka raina Yarinyar nan, badan kaine ba akwai wanda ya isa yayi mata haka ta ?yaleshi, turowa fa tayi tana kiran ka, amma ka basar kana shagalinka"

Ko gezau Yusuf beyi ba, balle Ya nuna yasan me Isa yake faWa.

Isa yace "da kai fa nake magana"

Still be tanka masa ba, Isa yace "eh da alama kaima ta koya maka ba?in halin, kadai bi a hankali tunda kaima Wan uwa talaka ne, inka Wau wannan rayuwar ba inda zata kaika"

Yusuf be kula shi ba ya mi?e ya bar gurin.

Yusuf na tafiya sega Abbas yazo, Isa na ganin shi ya washe baki yace "Sani dama kana nan? Kwata kwata wayarka ta dena shiga"

"ina nan wallahi, na koma ?auye ne, ya kake ya aikin?"

"Alhamdilillah, ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login