Showing 51001 words to 54000 words out of 135555 words

Chapter 18 - AKIDATA book 1 HAUSA NOVEL

17 Jan 2026

661

aid box Winsa ya Wau magani ya sha, ya koma ya kwanta.

Kwanciyar sa ba daWewa Abbas ya kira shi, da ?yar Yusuf ya Waga wayar, Abbas yace? "Mutumina kana ina ne? Ina son ganin ka"

"Ina gida bana jin daWi ne"

"Subhanallah, meya sameka?"

"Zazzabi ne" Yusuf ya bashi amsa

"Shikenan gani nan zuwa"
Su kayi sallama

**************************

Hajiya Halima na zaune falon ta tana shan tea, Isa mai gadi yazo yana kwaWa sallama a ?ofar falon ta, A fusace tace "wai meye hakane? Lafiya kame do kamin wannan sallama kamar kana bina bashi?"

"Hajiya nine, Isa ne"
"to ya a kayi?"
"Hajiya gurin ki nazo"
Ta Wanyi tsaki sannan tace? "shigo"
Ya shiga falon ya dur?usa yace?
"Ina kwana?"
"Kai bana son doguwar gaisuwar nan meke tafe da kai?"

"to Hajiya kin san shi sha'ani na rayuwa kiwon mutum ake ba dabba ba koba haka ba?"

"kai nifa bana son wannan surutam banzae, ka faWamin kanka tsaye meke tafe da kai"

Isa ya gyara zama yace? "game da sabon direban nan ne Yusuf, gaskiya Hajiya akwai bu?atar kisa ido, jiya yadda na gansu Allah ya nuna min Annabi salallahu alaihi wassalam, kin san dai irin shigar da take yi, bayan kin fita ita dashi suka fita, basu dawo ba se ?arfe tara na dare, bayan sun dawo a gabana da idanun nan nawa" yai maganar yana gwalo idon nasa ya cigaba da cewa
"da idanu na naga suna rungume juna, Hajiya a saka ido, kina gani idan ba kiranmu akayi ba bamu da damar shigowa kiga yadda take hantarar mu, Amma shi ba yau ba gobe cikin sintiri yake har cikin Wakin kwanan ta, Allah kaWai yasan me suke yi, gaki da 'yan mata kema kyawawa bekamata yana gardi baligi ya dinga wucewa yana kalle miki su ba, shiyasa nace bari inzo in sanar dake abunda ake ciki "

Dire kofin hannun ta tayi, taja wata nannauyar Ajiyar zuciya tace " Hmm naji maganganun ka, kuma kazo da magana abun dubawa, tashi kaje zan san abunda zanyi "

Isa ya mi?e yana murna yace
"shikenan Hajiya na barki lafiya "

Shiru Hajiya Halima tayi tana zake nazartar kalaman Isa megadi, tabbas Widad bata yadda wani ya Wula?anta Yusuf ba, lokacin da ciwon ta ya tashi ta?i yadda da kowa se Yusuf, idan har dagaske wani abu na faruwa a tsakanin su to tabbas akwai yuwuwar ta gayawa Yusuf inda abunda suke nema yake.

**************************

Widad kwana tayi da zazzabi da ciwon kai, da ?yar ta samu tayi bacci.
Jikin ta sam babu ?wari ta mi?e domin haWawa magen ta abunda zeci.
Widad na matu?ar son dabbobi, tana tausayin su fiye da yadda take tausayin mutane, akwai sha?uwa me ?arfi tsakaninta da dabbobinta, mussman ma wannan magen nata pita, da kuma karen ta dake gidan gona, tana jin daWin kasancewa da su, dan ba ?aramin Webe mata kewa sukeyi ba.

Ta samu container ta zuba masa madara, ta samo wani ta zuba masa gugguru, ta koma gefe tana kallon magen, maimakon magen yaci seya koma jikin ta ya kwanta, dan ya saba idan lokacin cin Abinci yayi, ta zuba masa nasa yana ci itama tana cin nata

**********************************

Abbas ne yayi Sallama Wakin Yusuf, da ?yar Yusuf ya iya amsawa, ya mi?e zaune suka gaisa da Abbas.

"Sannu Yusuf, ko Asibiti za muje in sauke ka"

Yusuf ya girgiza kai yace? "A'a na sha magani kawai, ya kake ya aikin?"

"Alhamdilillah, jiya Oga Suleiman yake neman ka, shine kiran da nayi maka, kuma se kace baka jin daWi, yanzu yau ba zaka gidan su mutuniyar taka ba?"

Yusuf yace? "bazani ba gaskiya, sedai zuwa gobe in Allah ya kaimu idan naji sau?i"

Abbas yayi ?asa da murya yace?
"Ya kuWin nan waye ya turo dasu kuwa?"

"itace wai Albashi na ne na watanni uku da bata bani ba, nace mata yayi yawa ta rage ta?i"

"TaSWijan kaima Yusuf da wani abu, kamarya ta rage? Malam kawai kaci kuWi, meye labari kuma?"

Yusuf ya gaya masa Hotel da suka je, da yadda suka dawo tana kuka, Amma be gaya masa zancen wayar nan ba data bashi.
Nan suka cigaba da tattaunawa zuwa wani lokaci Abbas yace ze tafi, Naira dubu Wari Yusuf yayi masa transfer a cikin kuWin, Abbas yaita murna yana godiya suka yi sallama.

Amma ?asan zuciyar Abbas kamar ya fasa ihu
'dana san wannan alherin Yusuf zeje ya dinga samu da tun farko nina karSi aikin nan, ya samu dubu Wari biyar amma ya bani wata shegiyar dubu Wari, ga dan?areriyar waya ya samu, na tura shi dan ina gudun wula?anci amma yaje yana samo abun Arziki, dole in san yadda zanyi a cire shi daga kan aika ni maye ni"

'Amma hatsari da kasadar dake cikin aikin fa?' wata zuciyar ta tambaye shi, tsaki yayi yana ci gaba da surutai.

*******************************
Shafa jikin magen take a hankali tana lallaSashi yaci Abinci, wayarta ce ta fara ringing, muzurun nan ya kasa a guje yaje ya Wakko ta a bakin sa ya kawo mata, shafa kan muzurun tayi tace? "thank you Roux"
Ta amsa wayar tasa a kunnen ta
"Ranki ya daWe Bala fa babu lafiya, an Wauke shi rai a hannun Allah an kai shi Babban Asibitin cikin gari, dan besan waye a kansa ba"

Mi?ewa tayi tsaye tace? "what? How comes? Wace irin rashin lafiya ce wannan?"

"Nima ban sani ba gaskiya, Amma an fita da shi daga Asibitin cikin kurkukun gaba Waya"

Bata kashe wayar ba ta mi?e, da sauri ta shiga bedroom Winta ta canza kaya, dukda yanayi na rashin lafiya da take ciki, wayar ta ta koma ta Wakko ta fara daddanawa sannan tasa a kunnen ta.


Yusuf yana jin wayarsa tana ringing ya ?i Wagawa yasa ta a silent, ya ajiye wayar ya cigaba da kwanciyar sa.

Jifa tayi da wayar akan kujera ta fice harabar gidan, gurin su Nura ta nufa, tana zuwa suna gaishe ta amma bata kula suba tace?
"Ku kiramin driver yanzu"
Jiki na rawa suja shiga kiran Yusuf babu ?a??autawa, Amma be Waga ba.

Ta kalli Nura tace "Wakko mota da sauri, zaka fita dani"

Cike da washe baki yaje ya Wakko mota, ta shiga Nura yaja motar suka fita, gaba Waya ji take kamar tayi Amai, dukda a bayan motar ta zauna amma warin hammatar Nura ya cika motar, se tsaki take yi badan ya zama urgent ta fita ba babu yadda za'ayi ta yadda wannan ?azamin ya jata a mota, suna tafe tana masa tsawa gami da hantararsa, Amma Yusuf ze gane kurensa na ?in zuwa da yayi yau sannan ya?i Waga waya.

Prison tasa ya kaita, suna zuwa ta fita ta shiga, kai tsaye ofishin Hisham ta wuce.
Yana ganin ta yai murmushi ya sallami kowa daga office Win sannan yace? "barka da zuwa lady boss, Ashe kin dawo Nigeria?"

"Ya aka yi Bala ya kamu da rashin lafiya da har ta kai shi ga kwanciya, seda aka fita da shi daga gidan nan?"

"Ranki ya daWe gaskiya dama yana Wanyin rashin lafiyar a tsai tsaye, Kawai se Wan uwansa ya kawo masa ziyara, bayan ya tafi jikin sa ya rikice"

"yanzu kana nufin kace min ?an uwansa ne ya kawo masa abunda yaci, jikin sa ya rikice kenan? Saboda sakaci da rashin sanin aikin ku?"

"A'a ranki ya daWe kin san?...

"Yimin shiru malam, saura sati Waya tal a koma kotu, kawai se inji wannan banzar maganar mara tushe, shikenan amma kasani idan har rashin lafiyar Bala haWin baki ne, duk wanda yake da hannu a ciki shima abunda ya samu bala ze sameshi. "

Ta mi?e a fusace ta fito, Hashim ya biyo ta da sauri amma ta shiga mota da niyyar ta ta wuce gurin lawyern Daddy, amma ba zata iya jure wannan tsamin da Nura yake ba, dan haka tace ya nsida ita gida, tana mamakin ?o?ari irin na Daddy da yake iya sha?e wannan warin hammatar, Yusuf kullum tsaf dashi cikin ?amshi, amma wannan ?azamin kamar baya jin yadda yake wari, seda ta bari sun koma gida, sannan tayi wa Nura ta tas akan ?azanta da warin da yake yi a gaban sauran ma'aikatam.

Gaba Waya ranta a Sace, ga jikin ta ba ?wari gashi a ?ule take da Yusuf, tana shiga babban falo ta tarar da Hajiya Halima, bata kula ta ba tasa kai zata wuce
"Widad ina son Magana dake"

Widad ta tsaya ta juyo ta kalleta ba tare da tace komai ba.

"Widad bekamata ace kina fita lokacin da kike so ki dawo lokacin da kike so ba a matsayin ki na mace, sannan ki dinga dawowa sanda kika ga dama ba, Alhalin nida nake zaune tare dake ban san idan kike zuwa ba, Sannan wannan yaron da yake sintiri gurin ki har ?uryar Wakin ki, Sam be dace ba"

"kinga dakata Malama, zamanki nake a cikin gidan nan? Koke kika ajiyeni? In kun tashi taku yawon gayamin kuke? Kisawa ranki gidan nan tamkar bariki yake, kowa yayi abunda yaga dama muddin be ?etare abunda masu gidan suke so ba, karki ?ara shiga sabgata, kuma kowa zan kawo cikin gidan nan gidanmu ne, kowa ze je har cikin Wakina babu ruwanki, kome nake aikatawa karki ?ara shiga, dan ke ba uwa ta bace baki haifeni ba, baki da ikon ki samun ido, kema abar a sawa ido ce, kisa ido akan 'ya' yanki kawai, ba ruwan ki dani....

"Widad!!!" Ramlah ta kira sunan Widad da ?arfi

"Ramla don't ever try to shout at me, a gidan mu kike ba gidan ku ba, dan haka ki iya bakin ki, tun kan in fusata"

Tana gama maganar ta juya ta tafi part Win ta.

"Tir?ashi Mummy dan Allah ki bani dama ko sau Waya, inci mutuncin yarinyar nan in koya mata hankali ko zanji sanyi a zuciyata"

Mummy ta girgiza kai tace? "Kina yin haka Ramla kin Sata komai, rabu da ita lokaci ne, yana nan zuwa da zata girbi abunda ta shuka"

**********************************

Se wajen la'asar sannan Yusuf ya Wanji sau?i ya tashi, ya shirya yaje Asibiti, aka duba shi aka bashi magunguna.
ya dawo gida ya wuce Wakinsa, wayarsa ya Wakko ya duba, yaga missed calls rututu, ko ba'a? gaya masa ba yasan Widad ce take neman sa, bebi ta kansu ba ya ajiye wayar ya cigaba da harkokinsa.

Dayaji ya Wanji ?warin jikin sa, seya shirya tsaf ya tafi hotel Win da suka je da Widad, Manager yaje nema amma be sameshi ba, ya cewa ma'aikatan su bashi lambar wayar sa, da farko suka ?i, seda ya nuna musu id card Win sa sannan suka bashi, seda ya zagaya lungu da sa?o na Hotel Win, yana sake monitoring mutanen dake shiga da fice a hotel Win sannan ya koma gida.

Washegari da safe dukda ya tashi jikin sa babu daWi, Amma haka ya shirya ya tafi gidan su Widad.

Tunda yaje Isa yake masa wani irin kallon banza, yanata habaice habaice
Shi dai Yusuf be kula shi ba, Nura yace

"Wallahi Yusuf yau kana ruwa, bama kusa da kada ba, cikin bakin kada, jiya ta fusata sosai, dan zata fita seni na kaita saboda baka zo ba"

Murtalah ya kwashe da dariya yace? "bayan kun dawo kuma tai maka tatas a gabanmu ba, saboda ?azanta kai Nura jiya kaga tijara a tsakar rana, ai idan nine kai ko maganar ba zan Wakko yau ba" yai maganar yana dariya

Nura ya haWe rai yace
"Bana son rashin mutunci da Iskanci"

Ganin suna nema suyi faWa yasa Yusuf yin gaba abunsa ya barsu a gurin, tafiya kawai yake yi amma jikin sa babu daWi.

Yana shiga falon ya tarar da Ramadan Wan gidan Alhaji Bulama da Amal suna hira.

Yusuf yace? "barkanku da Safiya"

Bata amsa masa ba se Ramadan ne yace? "Yawwa barka dai, bodyguard Win gimbiya" Yusuf ya Wanyi murmushi ya nufi hanyar Widad.

Bayansa Amal tabi da kallo, taji wasu hawaye na ?o?arin zubo mata, ta tsani kusancin Widad da Yusuf gani take komai ze iya faruwa, wani sashin na zuciyar ta ma yana gaya mata akwai wata al?ar a tsakaninsu saboda kusancinsu yayi yawa.

Ramadan ya kalleta yace "lafiya kuwa my?"

Girgiza masa kai kawai tayi tace? "lafiya ?alau"

Yusuf ya shiga ya tsaya a bakin ?ofar bedroom Win ta sannan yayi sallama kamar yadda ya saba.

Yayi Sallama kusan uku amma bata amsa ba, haka ya cigaba da tsayuwa a gurin, seda aka kwashi wani lokaci sannan ta fito, kallon sa tayi daga sama zuwa ?asa sannan tace?
"Sannu ishashshe kaga damar zuwa kenan?"
Shiru Yayi ya sunkuyar da kai, Wakin ta shige yabi bayanta da sallama

"Meya hanaka zuwa jiya? Kuma ka?i Waga waya?"

"Bani da lafiya ne shiyasa"

"?arya kake" ta faWi kai tsaye ba tare da duba ratar shekarun da Yusuf Win ya bata ba, shiru ya sake yi bece komai ba, ta tako tazo daf dashi tace?
"for the second time meya hanaka zuwa jiya?"

"bani da lafiya ne" ya sake bata amsa

"wai me yasa baka kunyar yin ?arya ne, meyasa? Ban gaya maka bana son ?arya ba?" tai maganar tana ?o?arin sa idon ta a cikin nasa

Babu zato ya janyota gaba Waya tana facing Winsa, ya kafe ta da idon sa, nata cikin nashi ya ?ura mata ido

Ayi sharing please =?O?=?O?=?O?

Ayshercool
07063065680
? ? ? ? ? ? ? ? ? ??
? ? ? ? ? ? ? ? ? ? _*A?IDATA*_

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*A?IDA TA *

I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in


? ? ??

? ? ? ? ? ? ? ? ? ?





? ?? PART1
? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? Page 13



ELEGANT ONLINE WRITER'S





Ba ?aramin firgita tayi ba da abunda Yusuf Win yayi, sedai ri?on da yayi mata tana iya jin huci me zafin da jikin sa ke fitarwa, masifa take son yi amma gaba Waya Yusuf yayi mata wani irin kwarjini ta kasa cewa komai se binsa da tayi da manyan idanunta.

Cike da jarumta Yusuf yace "Meyasa koda yaushe idan nayi abu seki ?arya tani? A koda yaushe ina ?o?arin gaya miki iya gaskiya ta amma seki ce ?arya nake, kin san yadda mutum keji kuwa idan aka ?arya tashi, it's really hurts, duk abunda nake yi ba inayi ne dan in samu kusanci dake ba, nasan A?IDARKI nasan abunda bakya so, ina ?o?arin kiyaye dokokin da kika kafamin ne, dokokin dana sawa hannu amma koda yaushe burinki kici zarafina"

"Malam cikani ko"? ta faWa tana masa wani irin kallo

Cikata yayi ya koma gefe ya tsaya.

Seda tayi ajiyar zuciya sannan tace

"hmm tunda nake babu wanda ya taSa Yimin abunda kayi min a yanzu, ina Waga maka ?afa ne saboda wasu dalilai biyu zuwa uku, dalilai biyu bakomai ne a gurina ba, dan ba zasu hanani yanke hukuncin dana ga dama akan ka ba, dalili Waya ne me ?arfin da yazo da ?addarar da ni ban isa in canza shi ba koda hakan bemin ba, ba yadda zanyi da kai dukda har yanzu ina doubting akan wannan dalilin, Anyway zamu fita yanzu zamu je gidan gona"

"A wace motar?" ya tambayeta a ta?aice

"kowacce ta bashi amsa"

Har ya juya ze fita yaji tace?
"meya sameka a fuskarka?"

Ya juyo ya kalleta

"kar kayi min ?arya" ta faWa kafin ya bata amsa

"Duka ne" ya bata amsa

"Kamar ya ya duka? Suwaye suka dakeka?"

"Nima ban sansu ba"

?an tsayawa tayi ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????tana nazarinsa, yayin da ya Wauke kai ya?i kallonta

"Shikenan, muje"

Suka fito falo, yana gaba tana bayan sa, Amal ta bisu da wata uwar harara.

Ramadan yace?

"Allah ya temaki 'yar masu gida, Gimbiyar gida a biki a zauna lafiya, a Sata miki mutum yai kwanan ba?inciki,' yar gaban goshi sha lelen masu arziki, tun Wazu nake zaman jiranki anan, Megida ne ya aiko ni, yace yana son ganinki"

Ta yamutsa fuska tace? "Ina da abunyi, da? haka ba zani ba"

Ramadan yace "haka zanje in gaya masa"

"Eh haka za kaje ka gaya masa, bazan zo ba, bazan ?ara zuwa inda yake ba"

"shikenan, kunfi kusa keda shi"

Ta juya suka fice ita da Yusuf.

Amal tace? "Ramadan, dan Allah yanzu baka jin haushin irin abunda takewa mahaifinku?"

Ramadan yace? "to me zance Amal? Ni meye nawa a ciki? Da mahaifina da mahaifinta tashi nayi na gansu tare, kuma haka muka tashi muka ga an sangartata se abunda take so sukeyi, sun Wauki son duniya sun Wora mata, ba'a kwaSarta komai tayi dai dai ne, meyasa zanji haushi, tunda ba yau ta fara ba, kuma idan tayi baya jin haushi, a gabana a gaban sa idan bata ga dama ba? Bulama take cemasa kanta tsaye, an riga an barta ta tashi akan wannan A?IDAR"

"gaskiya ni abun yana damuna, mu kanmu a cikin gidan nan bamu tsira daga wula?ancin ta ba, bamu ba har mahaifiyar mu fa"

"kin san wani abu? Ni yanzu babbar damuwa ta itace, Daddy yace? Fahad zasu aurawa ita, Fahad kuma mutum me faWa baya son raini ni ban san ta yaya za'ayi wannan zaman auren ba"

Amal tace? "ai duk wanda ya kwashi wannan ya kwashi masifa, gata mahaukaciya ga ba tarbiyya, gaskiya ina tausayin Fahad"

***********************************

Yusuf yayi parking Win motar a gidan gona, Widad na fitowa kamar kullum haka ma'aikatan suka yo caa suna gaishe ta, Waga musu hannu tayi ta kalli Wani daga cikin ma'aikatan, wanda ya tsare Yusuf da tambayoyi wancan karon tace?
"Ya aiki ya kuma dabbobi na?"

"lafiya ?alau ranki ya daWe, ko za'a Wakko dokin ne?"

"A'a sedai ina so kayi min rakiya in zaga su"

"to shikenan ranki ya daWe" haka suka shiga suna zagawa, sosai Widad take jin nishaWi idan tana kallon dabbobi, gaba Waya mantawa take da damuwar da take ciki, suna cikin tafiya tace

"Sale naji wata magana, ban sani ba ko kai ka jita, takanas nace bari inzo domin mu tattauna ta"

Saleh yace? "Allah yasa ba wani abun akace nayi ba ranki ya daWe?"

"idan ka yadda da kanka ba kayi lefi ba meye na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login