Showing 48001 words to 51000 words out of 135555 words

Chapter 17 - AKIDATA book 1 HAUSA NOVEL

17 Jan 2026

651

ranki gidan nan tamkar bariki yake, kowa yayi abunda yaga dama muddin be ?etare abunda masu gidan suke so ba, karki ?ara shiga sabgata, kuma kowa zan kawo cikin gidan nan gidanmu ne, kowa ze je har cikin Wakina babu ruwanki, kome nake aikatawa karki ?ara shiga, dan ke ba uwa ta bace baki haifeni ba, baki da ikon ki samun ido, kema abar a sawa ido ce, kisa ido akan 'ya' yanki kawai, ba ruwan ki dani....

"Widad!!!" Ramlah ta kira sunan Widad da ?arfi

"Ramla don't ever try to shout at me, a gidan mu kike ba gidan ku ba, dan haka ki iya bakin ki, tun kan in fusata"

Tana gama maganar ta juya ta tafi part Win ta.

"Tir?ashi Mummy dan Allah ki bani dama ko sau Waya, inci mutuncin yarinyar nan in koya mata hankali ko zanji sanyi a zuciyata"

Mummy ta girgiza kai tace? "Kina yin haka Ramla kin Sata komai, rabu da ita lokaci ne, yana nan zuwa da zata girbi abunda ta shuka"

**********************************

Se wajen la'asar sannan Yusuf ya Wanji sau?i ya tashi, ya shirya yaje Asibiti, aka duba shi aka bashi magunguna.
ya dawo gida ya wuce Wakinsa, wayarsa ya Wakko ya duba, yaga missed calls rututu, ko ba'a? gaya masa ba yasan Widad ce take neman sa, bebi ta kansu ba ya ajiye wayar ya cigaba da harkokinsa.

Dayaji ya Wanji ?warin jikin sa, seya shirya tsaf ya tafi hotel Win da suka je da Widad, Manager yaje nema amma be sameshi ba, ya cewa ma'aikatan su bashi lambar wayar sa, da farko suka ?i, seda ya nuna musu id card Win sa sannan suka bashi, seda ya zagaya lungu da sa?o na Hotel Win, yana sake monitoring mutanen dake shiga da fice a hotel Win sannan ya koma gida.

Washegari da safe dukda ya tashi jikin sa babu daWi, Amma haka ya shirya ya tafi gidan su Widad.

Tunda yaje Isa yake masa wani irin kallon banza, yanata habaice habaice
Shi dai Yusuf be kula shi ba, Nura yace

"Wallahi Yusuf yau kana ruwa, bama kusa da kada ba, cikin bakin kada, jiya ta fusata sosai, dan zata fita seni na kaita saboda baka zo ba"

Murtalah ya kwashe da dariya yace? "bayan kun dawo kuma tai maka tatas a gabanmu ba, saboda ?azanta kai Nura jiya kaga tijara a tsakar rana, ai idan nine kai ko maganar ba zan Wakko yau ba" yai maganar yana dariya

Nura ya haWe rai yace
"Bana son rashin mutunci da Iskanci"

Ganin suna nema suyi faWa yasa Yusuf yin gaba abunsa ya barsu a gurin, tafiya kawai yake yi amma jikin sa babu daWi.

Yana shiga falon ya tarar da Ramadan Wan gidan Alhaji Bulama da Amal suna hira.

Yusuf yace? "barkanku da Safiya"

Bata amsa masa ba se Ramadan ne yace? "Yawwa barka dai, bodyguard Win gimbiya" Yusuf ya Wanyi murmushi ya nufi hanyar Widad.

Bayansa Amal tabi da kallo, taji wasu hawaye na ?o?arin zubo mata, ta tsani kusancin Widad da Yusuf gani take komai ze iya faruwa, wani sashin na zuciyar ta ma yana gaya mata akwai wata al?ar a tsakaninsu saboda kusancinsu yayi yawa.

Ramadan ya kalleta yace "lafiya kuwa my?"

Girgiza masa kai kawai tayi tace? "lafiya ?alau"

Yusuf ya shiga ya tsaya a bakin ?ofar bedroom Win ta sannan yayi sallama kamar yadda ya saba.

Yayi Sallama kusan uku amma bata amsa ba, haka ya cigaba da tsayuwa a gurin, seda aka kwashi wani lokaci sannan ta fito, kallon sa tayi daga sama zuwa ?asa sannan tace?
"Sannu ishashshe kaga damar zuwa kenan?"
Shiru Yayi ya sunkuyar da kai, Wakin ta shige yabi bayanta da sallama

"Meya hanaka zuwa jiya? Kuma ka?i Waga waya?"

"Bani da lafiya ne shiyasa"

"?arya kake" ta faWi kai tsaye ba tare da duba ratar shekarun da Yusuf Win ya bata ba, shiru ya sake yi bece komai ba, ta tako tazo daf dashi tace?
"for the second time meya hanaka zuwa jiya?"

"bani da lafiya ne" ya sake bata amsa

"wai me yasa baka kunyar yin ?arya ne, meyasa? Ban gaya maka bana son ?arya ba?" tai maganar tana ?o?arin sa idon ta a cikin nasa

Babu zato ya janyota gaba Waya tana facing Winsa, ya kafe ta da idon sa, nata cikin nashi ya ?ura mata ido

Ayi sharing please =?O?=?O?=?O?

Ayshercool
0706306568_*A?IDA TA*_


PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A



*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*A?IDA TA *

I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum




https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in








ELEGANT ONLINE WRITER'S






PART1
Page 12






?an sandan ya zare ido zeyi magana, Yusuf yayi saurin girgiza masa kai, ya juya ya kalli Widad yaga hankalinta baya kansu.

A hankali ya zura hannu a aljihun sa ya Wakko ID card ya nunawa Wan sandan, washe baki Wan sandan yayi yana niyyar sarawa Yusuf, amma Yusuf ya girgiza masa kai yace

"Dan Allah YallaSai ku duba lamarin nan, ni bani da laifi a abunda ya faru, kuma na bashi ha?uri ya?i ha?ura"

Mutumin ya ?araso inda su Yusuf suke yace? "kaga Ku tafi da shi ajiyata ne, ku kulle shi har se nazo station Win"

?an sandan Ya kalli Yusuf zeyi magana, sega wasu 'yan sandan sunzo, motar da' yan sandan suka zo ze tabattar maka da manyan wanda mutumin ya kirane, nan na farkon suka shiga sarawa wanda Widad ta kira.

Widad tace? "ina so a duba Accident Win nan, idan direba nane yake da laifi, zan biya shi kuWin motar sa uku, idan kuma shi yayi laifin ze dur?usa ya bamu ha?uri, saboda cin zarafi da Sata mana lokaci da yayi, in kuma ya?i a tafi da shi, ajiyata ne a kulle shi se nazo"

Nan fa kallo ya koma sama, nan 'yan sanda suka shiga dube duben su, aka tabattar da mutumin nan shine ya karya doka, nan fa mutanen gurin suka Wau sowa.

Widad taje gaban sa tace " if you are somebody you won't say it yourself, don't ever say you are Somebody when you are nobody, yanzu ka dur?usa ka bawa direba na ha?uri akan cin zarafin da kayi masa"

"Wallahi baki isa ba keWin banza, in bawa wannan wula?antaccen ha?uri, kin san koni waye?"

?aya daga 'yan sandan daya kira ne yaja shi gefe yace? "kai wallahi wannan' yar masu ?asa ce, idan taso zatasa a Satar da kai gaba Waya wallahi, kayi abunda tace kota sa a Waureka"

"wannan ?aramar yarinyar 'yar cikina?"

"to karkayi cigaba da taurin kai, wannan' yan sandan data kira muma iyayen gidanmu ne"

Mutumin ya dawo a ?ule ya kalli Yusuf yace? "Yi ha?uri"

"Akan gwiwowinka zaka dur?usa ka bashi ha?uri" cewar Widad

Cikin tsawa wani Wan sanda yace "ba zakayi bane? Semun tafi da kai?"

A hankali yaja da baya ze dur?usa, Yusuf yayi saurin ri?e shi tare da girgiza kai ya kalli Widad yace? "please Madam ina nema masa Alfarma, kiyi ha?uri dan Allah, ni zan dur?usa in baki ha?urin a madadinsa"

Dama Widad tasan Yusuf baze taSa yadda hakan ta faru ba, tayi ne dan nunawa Mutumin shi Win bakomai bane.

"Shikenan tunda ya ha?ura, gobe in Allah kaimu, yaje station Winka ya karSi kuWin motar sa, na ninka maka masa sau uku, Amma ya kiyaye gaba"

Ta juya ta tafi motar su, Izzar Widad da yadda ta tafi da al'amuran cikin isa da izza, da bajinta suka birge mutane, aka dinga sowa, anawa mutumin nan dariya.
Dare yayi musu a gurin nan saboda wannan incident Win, Yusuf yaja motar cikin nutsuwa suka tafi.

Amma still lokaci lokaci tana goge Hawaye a fuskarta, suka ci gaba da tafiya Yusuf na godewa Allah da Widad bata ga bindigar nan ba, tabbas yasan da Asirinsa ya tonu daya gama kaWewa, ?arshen ta seta kulle shi me fitar dashi se Allah.

suna zuwa gida Yusuf yayi horn Isa ya buWe musu gate, Yusuf ya shiga da motar yayi parking, har ya gama abunda zeyi ze buWe motar ya fita, Widad tana zaune ko gezau ba tayi ba, bata da niyyar fita daga motar.
fita yayi ya zagaya ya buWe mata ?ofar, yace? "Munzo fa" Waga kai tayi ta kalle shi, a hankali ta zuro ?afafunta da take jin kamar ba'a jikinta suke ba waje ta yun?uro ta fito, sedai tana fitowa ta tafi luuu zata faWi, cikin zafin nama Yusuf zama shamaki da faruwar hakan, ta hanyar? ri?eta ta faWa a jikinsa.
?irjinsa ya dinga bugawa da ?arfi, saboda jin hakan wani irin abu daban, Isa me gadi ne ya zaro ido ganin abunda yake faruwa, Yusuf kamar me raWa? yace? "Are you ok?"
Jinjina masa kai tayi ta sake ?o?arin mi?ewa, amma still jiri ke kuma Wibarta, tafiya take tana tangaWi kamar wadda tasha wani abu, Yusuf yabi bayanta ya mata rakiya har cikin babban falo, hannunsa ri?e da ?aramar jakarta da kuma wayar ta.

A babban falon ta zauna tana ri?e kai, hawaye nata zarya a fuskar ta, ?o?arin cire takalmin ?afarta take, amma abu ya gagara, se kokawa take da takalmin.
Yusuf ya taka inda take? ya dur?usa ya kwance igiyar takalmin nata me tsinin tsiya ya cire mata.

Ta gyara kwanciyar ta sosai ta mi?e ?afafunta akan doguwar kujerar tare da lumshe idonta, don bawa hawayen idon nata damar gangarowa.

Yusuf a ransa yace 'Ikon Allah, wannan wane irin kuka ne?'

"ko za'a kira likita ne?"

"Ni lafiya ta ?alau" ta bashi amsa idonta a rufe.

"Jikinki yana rawafa, kamar zazzaSi ze kamaki fa"

"to ina ruwan ka? Jikin ka ne ko nawa? Ni kaimin kayana Waki ka tafi ka ban guri"

?an girgiza kai Yusuf yayi yaje ya ajiye mata kayan ta ya fito, tana nan inda ya barta, yasa kai ya fice.

Yana fitowa ?ofar da zata sa dashi da harabar gidan yaji an ri?o rigarsa, waigawa yayi yaga waye wannan.
Amal ce tsaye tana huci,
"Amal lafiya kuwa?"
"dole kace lafiya mana? Yusuf daga ina kake kai da Widad?, saboda tsabar abu harda cire mata takalmi, Yusuf wai kai wani irin mutum ne dan Allah? Me kake aikatawa ne haka Yusuf? me yasa lallai seka yi abunda zaka birgeta, bayan kullum baka da kima a idon ta? Sau nawa nake gaya maka kusanci da ita tamkar kusanci da mutuwarka ne? "

Yusuf yace " look Amal niba wani abu nake nema a gurin Widad ba, kuma ba neman kusanci nake da ita ba, kawai ina tausayinta ne, kuma ina jin daWin yadda mahaifinta ke mutuntani"

"kace tausayi Yusuf? Yusuf daga tausayi so yake shiga, ban taSa ganin mutumin daya samu damar da ka samu a gurin ta ba, Yusuf a gidan nan ba kowa keda ikon zuwa inda take ba in bada izinin ta ba, kai kuwa kana iya zuwa gurin ta duk lokacin da kake so a matsayin ka na direbanta, Yusuf ina kishin ka, Yusuf sonka nake wallahi bazan zuba ido abubuwa su cigaba da gudana tsakanin ka da Widad a haka ba"

"Amal, Soyayya tsakanina dake ba zata yuwu ba, Mahaifiyarki bata ?aunar talaka, kuma ni talaka ne inani ina iya Soyayya dake Amal?Hausawa suka ce ?warya tabi ?warya, idan tabi akushi zata fashe"

"dakata Yusuf" Amal ta katse shi, hawaye tuni ya fara sintiri a idon ta, tace? "bazaka iya Soyayya dani ba, amma zaka iya da Widad ko?"

"Amal ni ba Soyayya nake da Widad ba, inani ina son mace kamar ta, ita a kanta bata yarda da wata soyayya ba, Amal nayi Soyayya a baya, abun da na fuskanta a soyayya bazan ?ara yadda in sake fuskantar sa ba, ke kanki da kin san wayeni bazaki soni ba, ba zaki so kasancewa da mutum kamar ni ba, kiyi hakuri "

"ba abunda ya shafeni, what I know is that ba zan zuba ido ka faWa soyayya da mahaukaciya mara tarbiyya ba, kuma bari in gaya maka ba zaka taSa kuSucemin ba kasa wannan a ranka"

Tana gama faWar haka ta juya da sauri ciki tana kuka, jikin Yusuf yayi sanyi a haka ya ja jiki ya fito.

Masallaci ya wuce yai sallolinsa, sannan ya zauna yana karatun Al'qur'ani mai girma, ya daWe yana addu'a sannan ya mi?e ya nufi titi dan samun abun hawa zuwa gida.

Abunka da unguwar masu kuWi, tuni unguwar tayi tsit se sanyi bishiyoyi dake kaWawa, yana ta tafiya a ?asa yana tunanin abubuwa da dama, ya baro layin su Widad sosai inda security suke, ba tsammani se gani yayi ansha gaban
sa da mota, tsayawa yayi cak yaga ikon Allah.

Wasu ?arti ne suka fito daga motar suka zagaye shi, Wayan yace? "kaine direban 'yar gidan Alhaji Nasir?"
Ba tare da tsoro ko shakka ba Yusuf yace? "Eh nine"

"Good labari ya ishemu cewar akwai kusanci tsakanin ka da ita, duk inda zata tare kuke zuwa, an samu mu Wakkota kwanaki amma ka hana, bari in gaya maka wani abu, zamu ?yaleka ne saboda zakayi mana amfani, zamu ci gaba da bibiyar ka saboda akwai wani abu da muke so ka karSo mana a gurin ta" cewar Waya daga cikin ?artin

Yusuf yace "Babu wani kusanci tsakanin mu, aiki nake mata tana biyana, ko meye kuje ku tambaye ta ta baku mana"

?aya daga cikin sune ya sakarwa Yusuf wani mummunan naushi, da seda jini ya fito daga bakin sa, a zuciye Yusuf ya Wago yana kallonsu, babban yace

"Wallahi idan baka kawo mana abun nan ba se mun kasheka, akwai wasu mahimman abubuwa da muke so ka karSo mana a gurinta idan ka?i semun maka yankan rago"

"Bayan yankan ragon se kuma me?" Yusuf ya faWa babu alamar tsoro

Wani naushin suka ?ara masa a gefen ido,
Maimakon Yusuf ya tsorata, ko ya nuna jin zafin naushin, se yayi murmushi yace

"idan kunmin yankan rago, ku kuma ku zauna a naWe duniya daku?, babu wani mahaluki daya isa yasa Yusuf yin wani abu dan son zuciya da zalunci, kuje ku gayawa wanda ya aiko ku cewar karya kuskura yayi gangancin cin iyakar gonar da ba tasa ba, idan kuma ya?i zanwa shukokin feshi in ?one nawa da nashi, kowa ya rasa, wannan sa?on Yusuf ne ga uban gidanku ko wayeshi"

Wani naushin suka yi niyyar kai masa amma ya ri?e hannun Wayan.

"Waye kai? Waye ya gaya maka wanine ya turomu?" cewar Waya daga cikin su

"yadda kuka binciko kuka gano nine direban Widad, haka yakamata ku bincika kusan wayeni, nasani aikoku akayi ku koma ku ?ara tabbatarwa wanda ya aikoku nina Wauke Widad lokacin da yasa a sace ta, ni aikina tu?ata a mota dan haka ya kiyayi yun?urin cutar dani"

Hausawa sukace 'sarkin yawa yafi sarkin ?arfi, sun daki Yusuf sosai, yaso yayi amfani da bindigar sa, amma yin hakan ze rusa masa da yawa daga shirinsa, dan haka ya fasa Waukar bindigar, suka daddake shi, wani yana iya ramawa wani kuma baya iyawa.

"zamu cigaba da bibiyarka, harse ka bamu abunda muke nema, zaka gane baka da wayo, Uban taurin kai, Ubangidanmu yafi ?arfinka"

haka suka barshi a gurin suka tafi.

Da ?yar Yusuf yaja jikin sa ya hau Napep ya tafi, hancinsa yana ta zubar da jini, jiri ne yake ta Wibarsa saboda jinin da yake zubarwa da yawa, da ?yar yaje gida, Allah ya temake shi Umma tayi bacci.

ya cire kayan jikinsa yana goge jinin fuskarsa, Aljihun wandonsa ya taSa yaji wayar da Widad ta bashi Wazu.

Hannu yasa ya Wakko ta yana jujjuya ta? "Ka Soye ta kamar yadda zaka Soye ranka, wannan wayar tamkar rayuwar ka ce"

Maganar Widad ta dawo masa, kunna wayar yayi, Amma akwai password akai shiru yayi yana nazarin kamar yaya wayar nan tamkar rayuwar sa take? Ajiye wayar yayi ya shiga yayi wanka ya fito, nan ya shiga aikin nasa na tunani dan abubuwa da dama sun faru da suke bu?atar nazari.

"Me Widad taje yi Hotel? Me ta gani ya sata kuka? Waye ya turo mutanen nan? Ko waye akwai sa hannun wani a gidan su Widad? Amma dagaske Tausayin Widad zesa ya fara sonta? Me yasa tasa a dur?usa a bashi ha?uri yau? Tabbas zata iya yuwuwa akwai Ala?a tsakanin wani a gidansu Widad da mahaifin Nurat"

Ji yayi kansa kamar ze fashe, dan haka ya rintse idon sa yana addu'a da fatan bacci ya Wauke shi koze Wan samu nutsuwa, Amal ta faWo masa a rai itama, wai ita bilha??i son shi take.
Wani tunani ya shigayi watanni shida da suka gabata, da yanzu yana nan da Auren sa, katsam a dalilin irin tasa ?addarar aka fasa wannan Aure, bayan cin zarafi da wula?anci daya fuskanta daga iyayen matar daze Aura, bacci dai se Sarawo ne ya Wauke shi.

*******************************

Da safe Yusuf ya tashi da matsanancin zazzabi, kansa har sarawa yake sosai saboda dukan da yasha jiya, juyi kawai yake akan gadon gaba Waya jikin sa ciwo yake masa, ganin har kusan ?arfe tara be fito ba yasa Umma le?awa Wakin sa, ta tarar da shi kwance a kan gadon sa, ?arasawa tayi ta taSa jikin sa tace? "Yusuf lafiya kuwa? Naga har ?arfe tara baka fito ba?"

"Bana jin daWi ne Umma"
"dan baka jin daWi seka zo ka kwanta kana juyi, ka tashi ka watsa ruwa, ka karya seka sha magani"
"to Umma"
Yusuf ya mi?e ya shiga yai wanka, kayan breakfast Win ta kawo masa Waki, ta kalle shi tace?
"Yusuf kamar kumburi nake gani a gefen idonka da bakin ka"

Yusuf yace? "Mun faWi akan babur ne jiya da daddare"

"Amma ka kasa gayamin? Meye amfanin hakan, haba Yusuf"
Yusuf yace? "Yi ha?uri Umma, bana son Waga miki hankali ne"

"Amma ina fatan ba wani mummunan ciwo daka ji?" tai maganar cike da damuwa

"Eh banji ciwo me yawa ba"

Da kanta ta zauna tana bashi Abinci a baki, ta Wakko masa first

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login