Showing 90001 words to 93000 words out of 135555 words

Chapter 31 - AKIDATA book 1 HAUSA NOVEL

17 Jan 2026

649

JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*A?IDA TA *

I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum

Ha??in Mallaka ?& : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ?unsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani Sangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

(GAMAYYAR MARUBUTA NA ELEGANT ONLINE WRITER'S, INA GODIYA DA KARRAMANI DA'AKAYI DA CERTIFICATE NIDA ?UNGIYATA TA PERFECT WRITERS ASSOCIATION, INA GODIYA DA WANNAN KARAMCI UBANGIJI ALLAH YA ?ARA HA?A KAN MARUBUTAN MU AMEEN, INAWA KOWA DA KOWA FATAN ALKHAIRI, TARE DA FATAN KOWA YAJE GIDA LAIFIN)




ELEGANT ONLINE WRITER'S

? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ?? PART1
? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? Page 26_27


Gaba Waya Widad ko motsi ba tayi, Yusuf ya rungumeta sosai a jikinsa kamar wani ze ?wace masa ita, zuciyar ta na bugawa amma numfashinta baya fita sosai, ga cikinta se ?ara yake saboda yunwa.



Anwar ya kai Nurat gida, suka yi Sallama, ta shige gida jikin ta na rawa ta tafi Wakin mahaifiyar ta.

"ke ina kika fita kikaje ban sani ba?"

"Mummy akwai matsala fa"

Cike da rashin fahimta mahaifiyar ta tace "matsalar me?"

"Widad ta Sata an sace ta"

Dafe ?irji tayi tace "innalillahi wa inna ialaihi raji'un, waye ya gaya miki?"

"Mummy can naje fa, Daddynta yana Asibiti ma naje na duba shi ma"

Zaro ido tayi tace? "ubanwa yace kije? Sekin jawa kanki faWa a gurin mahaifinki ko? Tashi maza kije ki cire hijjabin nan ki huta"

Nurat ta kalli mahaifiyar ta tace? "Mummy, Daddy ne fa yasa aka sace Widad"

"inji ubanwa? Rufen baki shashasha, in kika sake maganar nan yaji kema zeyi maganin ki"

"Mummy a matsayinki na uwa, ya zakiji idan ni aka sace, yakamata ki cire tsoro a ranki ki gayawa babana gaskiya, ranar da hakki ya tashi bashi kaWai ze kama ba harmu"
Ta ?are maganar tare da ficewa daga Wakin gaba Waya


Kwata kwata duk bidirin da'ake Fahad beje yaga jikin Alhaji Nasir ba shima kuma Alhaji Nasir be tambaya ba, yana fama da kansa.

Mussaman Abbas daga inda yake aiki ya kira Umman Yusuf ya sanar da ita Satan Wanta, dama ta kira wayar Yusuf harta gaji bata shiga.
Aikuwa ta kiWime sosai ta tashi hankalin ta, ta shirya ta tafi gurin aikin Yusuf.

Ma'aikatan su kansu a kiWime suke tun bayan da suka samu labarin Satan Yusuf, Suleman yayi duk yadda zeyi a basu damar bincike akam al'amarin amma daga sama aka hanasu, akace an riga an dan?a case Win a hannun wasu jam'ian tsaron.

Sosai Umman Yusuf tasa Abbas a gaba tana zabga kuka
"dan Allah ranka ya daWe ina Wana yake? Ku kuka sashi aikin nan ina kuka turamin shi shi kaWai nake kallo inji daWi, Yusuf ne kaWai dani, dan Allah ku temaka ku nemomin Yusuf Wina"

Cikin ?warin gwiwa Sulaiman yace "ki kwantar da hankalinki Umma, Insha Allah indai Yusuf ne zamuyi duk me yuwuwa muga mun kuSutar dashi, an baza jami'an tsaro kuma ins me tabbatar miki ba abunda zasuyi masa dan bashi suke hari ba, yarinyar da yakewa aiki suke hari, dan ba suce abasu komai ba, yanzu haka mahaifin yarinyar yana kwance a asibiti, kuma bashi da magana seta Yusuf"

Suleiman ya dinga kwantar mata da hankali, amma abunka da Wa d uwa ta saurari kalaman Suleiman ne kawai, amma bata ga alamar ana neman Wan nata ba.

Umman Yusuf bacci ya ga gareta, balle cin Abinci banda kuka da Addu'a babu abunda take yi wa Wan nata, dan yanzu a duniya idan ta rasa Yusuf ba.


Jikin Alhaji Nasir ?ara rikicewa yake saboda damuwa, Anwar yace wa Mahaifiyarsa "Mummy ya kamata ayi wani abu akan rashin lafiyar daddy, inze yuwu ayi visa a fita da shi, kullum jikinsa ?ara rikicewa yake babu sau?i"

Hajiya Halima tace? "ko bangon duniya za'a kai shi idan Allah yayi niyyar karSar rayuwarsa ba yadda muka iya, anan Winma naga likitocin suna iya ?o?arin su, meye kuma se an kwashi jiki an tafi ?asar waje dan Sarnar kuWi"

"Mummy Sarnar kuWi kuma? Koma Sarnar kuWin ne naga nasane ai, meye amfaninsu in baza'a nema masa lafiya ba"

"kaga Anwar ka kiyaye ni, kafini sanin abunda ya dace ne? Fita ka ban guri kafin in Sata maka rai, sakarai kawai"

Fitowa yayi gwiwa a saSule yana tunanin wannan halina Mummynsa.

Gidan Bulama ya tafi, yaje ya tarar yana shirin fita, suka gaisa da Anwar, Anwar yace "Daddy gurinka nazo"

Bulama yace "gashi ina shirin fita ne, Amma meya faru?"

Anwar yace? "Daddy dama cewa nayi meze hana a fita da Daddynmu waje a duba shi yadda ya kamata a can, naga kullum ciwon nasa gaba yake ba sau?i"

Alhaji Bulama yace? "Anwar kazo da magana me kyau, amma ka sani ko an fitar da Daula waje in har baze cire damuwa dake ransa ba, babu yadda za'ayi magunguna suyi masa aiki, haka likitoci suke ta faWa"

"Amma da dai an jarraba, amma jikinsa yana bani tsoro"

Alhaji Bulama yayi shiru sannan yace "shikenan Anwar, zamu yi maganar da mahaifiyarka, zanga abunda ya dace ayi"

Anwar yayi masa godiya sannan ya tafi.


Alhaji Haruna ne zaune akan kujera, fuskar nan tasa babu alamar imani ya kalli wani matashi dake zaune yace

"doctor Sufyan, mun yaba da ?o?arin da kuke yi a Asibitinka akan Shahararren Attajirin da'ake ji dashi a faWin ?asar nan wato Alhaji Nasir Daula"

Doctor Sufyan yayi murmushi yace? "Nagode ranka ya daWe"

Alhaji Musa yace? "Kasan meyasa muka kiraka?"

Sufyan ya girgiza kai alamar aa'

Alhaji Haruna ya gyara zama yace "Abunda muke so da kai shine, bama son Daula ya tashi"

Zare ido Sufyan yayi yace "kamar yaya?"

Alhaji Musa yace "Nutsu ka kwantar da hankalinka, ba muna nufin ka kasheshi ba, A'a bama so ya tashi ya warke ta hanyar dena bashi magungunan da ya dace, kayi duk abunda zakayi masa wanda ze ?ara kwantar dashi, idan kayi haka akwai lada me tsoka da zamu baka"

Saleh dake gurin gaba Waya ya rikice yace "Amma YallaSai ba muyi haka daku ba, idan kuma ya rasa ransa fa?"

Alhaji Haruna yace "Saleh ka rufewa mutane baki, karka Satamin rai"

Ya maida hankalinsa kan doctor Sufyan yace? "Yaya zakayi ko bazaka yi ba?"

Doctor Sufyan yace "Nifa na Wau Al?awarin bazan cutar da lafiyar kowa ba kafin in fara aiki, kuma Alhaji Nasir ya yadda dani, na daWe ina duba shi lokaci Waya kuma se in....

" Kai dakata "? Alhaji Musa ya dakawa Sufyan tsawa yace " karka kawo mana maganar banza malam, idan baka yi ba zamu nemi wani, kwata kwata aikin wata uku muke so kayi mana, za mu baka Naira miliyan goma, idan yayi maka kaWan zamu ?ara maka"

Zare ido Sufyan yayi yace "miliyan Goma"

"?warai kuwa, miliyan goma idan kuma ka?i zamu saka wani amma ka tabattar da kaima ba zamu ?yaleka ba"

Cikin hanzari Sufyan yace "zanyi ma, na amince zanyi insha Allah karka damu Alhaji"

Shiru Saleh yayi yana tunani, wato akan kuWi mutanen yanzu duk alkhairinka sesu manta, idan baze manta ba? dangin Sufyan WaiWaiku ne Daula be kai aikin Hajji ba, Amma ya amince ze karSi kuWi ya cutar da Alhaji Nasir "

Da Sufyan ze tafi dubu Wari biyar suka bashi wai ya zuba mai a mota.

Saleh yayi shiru abun duniya duk ya dameshi.
Su Alhaji Musa kuwa cigaba da ?ulle ?ullen sharrinsu suka yi.

Wayar Alhaji Haruna ce ta fara ringing, suka tsagaita da dariyar da suke Ya Waga wayar yace

"Yaya me Adda, ya ake ciki ta faWa maka kuwa?"

"Ina fa ta faWa se wahalar damu take, ga taurin kai da tsiwar tsiya, sannan ta bada sa?o a baku"

Alhaji Musa a gigice? yace? "Kamar ya ta bada sa?o abamu ta sanmu ne?"

Me adda yace "ina nasan mata, cewa tayi mu cewa wanda suka sa a sace ta, ta tattaar duk wata hujja akan su, ko bayan an kashe ta asirinku ze tonu"

Wani gumine ya shiga tsatsafowa Alhaji Haruna yace? "?arya take bata sanmu ba, a gidan uban wa ta sanmu balle ta tattara wata hujja a kanmu, yanzu kana ina ne?"

"ina cikin gari mana, naje Asibiti ne wani yarfi yarinyar nan ta min na kasa ko mi?ewa tsaye, na Wauka ma na tashi daga aiki"

Alhaji Musa yace? "wani sakarci ne zesa ku baro su acan, maza ka koma ku gana mata Azaba iya Azaba seta faWi inda takaddun suke, idan ta faWi inda suke ku kashe su kawai"

Saleh yace "What akan me za'a kashe ta?"

Alhaji Musa be saurari Saleh ba ya cigaba da wayar sa.

Me Adda yace "gaskiya Oga kisan Yarinya kamar wannan ba kamar kashe sauran mutane bane, tsaf wannan cinnakun zasuyi ram damu"

Alhji Haruna yace? "ba wanda ze kama ku, zancen nan da muke maka gaba Waya mun siye jami'an tsaro ba wani bincike da'ake akan Satan nata, dan haka ka gaggauta zuwa jibi idan bata faWa ba ka tirsasa ta, ta gaya maka wasu hujjoji take dasu sannan ka kashe mana su"

Me Adda yace? "angama Oga"

Alhaji Haruna ya sharce gumi yace? "bala'i, Musa anya ba dagaske yarinyar nan ta gano mu ba, karfa muje dagaske take"

"Rabu da ita ?arya take, da dagaske ta sanmu da tuni ta Wau mataki akanmu, amma kasan bamu gayawa Munir da Bukar hukuncin da muka yanke ba?"

Alhaji Haruna yace? "Suma idan mun gaya musu hukuncin da za susa ayi mata kenan a kashe ta kawai, karta ja mana masifa"

Alhaji Musa ya kalli Saleh yace? "wai kai meye naka na saka baki dan munce? a kashe ta, kabi a sannu fa wallahi kar kasa musa a haWa da kai, kabi umarnin mu kawai"

Saleh yayi murmushi yace "Tausayin Daula ne ya kamani wallahi, karka damu bazan baku kunya ba insha Allah dani za'a kammala komai nima in samu rabona"

"daka temaki kanka" cewar Alhaji Haruna, yayin da cikkunansu suka Wuri ruwa.



Yusuf yana nan zaune rungume da Widad, har duhu yayi gari ya waye, sam be bacci ba gani yake da yayi bacci Widad zata mutu, dan bugun zuciyar ta da yake ji shike tabattar masa tana da rai, dan wani lokacin har motsawa take.

A hankali Yusuf ya kwantar da ita, yayi taimama yayi sallar Asuba, shima gaba Waya jikinsa a sake yake babu ?wari saboda azabar wahala, ga yunwa ga duka ga cizon sauro ga azabar sanyi dake gurin, amma gaba Waya yafi tausayawa Widad, lokaci lokaci yakan kwance hannun nata, ya goge jinin ya sake Waure mata, ga wani irin zazzafan zazzabi da ko sauka bayayi a jikinta.

A hankali Widad ta buWe ido, sedai dishi dishi take gani bata gane komai, tana yi tana lumshe ido haka take kallon Yusuf.
Yusuf ya girgiza ta yace "Alhamdilillah, you are alive"
Bata iya amsa masa ba, sedai idonta ya sake rufewa

Yana rungume da ita, yayi shiru yana ta ambaton Allah, babu zato ba tsammani yaji ana ta sukuwa a saman roofing Win Wakin, Yusuf ya Waga kai yana son gane meke faruwa haka? Cigaba da sukuwa akayi a gurin anata ?o?arin Sare kwanon, can kuma se'aka dena, yaji anata ?o?arin buWe ?ofar da suke ciki, waze gani Saleh ne ya shigo cikin Wakin.

A gigice Yusuf yace? "kaine? Da kai aka haWa baki kenan aka mana haka?"

Saleh yace? "baka da lokacin wannan tambayoyin, zuwa nayi na tseratar da ku, ka adana tambayoyinka, idan kun tsira seka yi su"

Hankalinsa ya kai kan hannun Widad dake sume yama zubar da jini, da sauri ya ?araso yace? "meya sameta haka? Harbinta sukayi?"

Yusuf bece masa komai ba, sedai kallon tuhuma da yake ta binsa dashi.

Saleh yace "zaka iya tafiya kuwa?"

Yusuf ya jinjina masa kai alamar eh, "to taso maza"

Yusuf ya yun?ura ya mi?e, amma ?afafunsa se rawa suke saboda dukan daya sha, ga uwa uba yunwar da yake ji.
Amma cikin jarumta, da sadaukarwa ya mi?e ya goya Widad a bayansa.

Suka fito daga gidan, Saleh ya maida gidan ya rufe, sannan ya Sare saman roofing yayi hanya, sannan yayi musu jagora hannunsa Wauke da compass dake nuna masa direction suka nausa cikin daji.

Yusuf ji yake kamar ze kifa, amma haka ya cigaba da tafiya, Saleh ya kalle shi yace "ko zaka sauketa in ta yaka?"

Yusuf ya girgiza kai yace "A'a karka damu"

Tafiya sukayi bata wasa ba, ?afar Yusuf ko takalmi babu, ya dinga taka abubuwa danma ta cikin ciyayi suke kutsawa, haka suka dinga tafiyar cikin sauri, suna bi takan ciyayi dan kaucewa barin sawunsu yadda za'a gane hanyar da suka bi, daji ne har daji me sar?a?iyar tsiya, da manyan bishiyu.

Sunyi tafiya me nisan gaske sannan suka fito titi, sam Yusuf be san a ina suke bama, Saleh ya nunawa Yusuf mota yace? "ya shiga"

Yusuf yayi turus ya kalli Saleh, a wahalce yace "wannan taimakon ma da kayi mana mungode, amma bazan hauba, Insha Allah zamu bar gurin nan".

"Yusuf, wallahi suka kamaku kashe ku zasuyi, da inada niyyar cutar daku da bazan ceceku ba"

Da ?yar Yusuf ya yadda, ya hau motar, da alama Saleh ya gama shirya komai.

Shima Saleh haka yayi doguwar tafiya dasu a motar, tafiya kamar za'a bar duniya dazuka kawai suke ratsawa, tituna bakowa se su kaWai, Shiru ne ya wanzu tsakaninsu har suka fara fita gari.

Wani Wan madaidaicin Asibiti suka tarar a hanya, Saleh yayi parking Yasa Yusuf ya Wakko Widad suka shiga Asibitin.

KuWi Saleh ya ajiyewa likitan, dan haka ba wani dogon bincike suka karSi Widad, Amma Yusuf ya?i zuwa ko'ina, a gabansa aka cirewa Widad bullet, akace se an tafi neman jini za'a ?ara mata.

Yusuf yace a Wibi nashi, Saleh yace "baze yuwu a Webi naka ba, kaima a galabaice kake akwai bu?atar a duba ka"

Yusuf ya dage sedai a gwada jininsa in zeyi a Wiba a sa mata.

Aka duba aka ga Yusuf ze iya bawa Widad jini, saboda rukunin jininsa ake cewa universal donor wato O-, sedai an samu jinin Yusuf da malaria, likitan yace?

"baze yuwu asa mata jinin ba"

Shikuma Yusuf yace be yadda da kowa ba, jininsa za'a saka.

Saleh yace? "kaga doctor, koma menene a jinin nasa saka mata, can ta?arke musu dan zamanmu anan akwai hatsari"

Aka bawa Yusuf Abinci, amma ya kasa ci se Wan kaWan saboda hankalinsa na kan Widad, ana Wibar Jinin Yusuf jiri ya Webe shi ya yanke jiki ya faWi, haka aka Wauke shi aka bashi gado.

Akayi treating Win raunkan jikin Yusuf, aka masa allaurai dan samun relief.

Aka sakawa Widad jinin Yusuf, tare da sauran Allurai, Yusuf na farfaWowa ya fara tambayar ina Widad.

Likitan yace "wai dan Allah meye ala?arsa da wannan yarinyar haka?"

Saleh yace "?anwarsa ce shiyasa ya damu da ita, 'yan fashi ne suka harbeta akan hanyar su ta tafiya, ita kaWai yake da ita shiyasa"

Yusuf ya koma inda Widad take yasa ta a gaba, ya ?ura mata ido ko ?yaftawa bayayi, tunda aka cire bullet Win nan har yanzu bata farka ba.

A hankali ta buWe idonta, ta yun?ura zata mi?e Yusuf ya ri?eta yace "bi a hankali fa jikinki babu ?wari"

Ta kalli Yusuf tace? "A ina muke nan?"

"I think we are save now insha Allah, yanzu zamu koma gida" ya bata amsa

Saleh ya shigo Wakin yace? "waye yace maka zaku koma gida ne"?

Widad ta kalli Saleh ta ?ura masa ido, kamar taga ba?uwar halitta.

Yusuf yace "meyasa ba zamu koma gida ba yanzu?"

"saboda idan kuka koma, da kai da ita da mahafinta duk sesun kasheku"

Yusuf yace? "meyasa?"

"Zan gaya maka komai, Amma daga nan mafaka zan baku, inda zaku Suya ba zasu san inda kuke ba na gama shirya komai daga nan tafiya kawai zamuyi"

Saleh ya mi?owa Yusuf wata babbar jarkar youghurt yace "gashi nan kuci nasan ba wani Abincin kirki a cikinu, sannan ka canza riga ita kuma a sama ta hijjabi"

Yusuf ya karSi youghurt Win ya buWe ya mi?a mata, amma ta Wauke kai, Yusuf ya girgiza youghurt Win ya Waga kai ya sha, sannan ya sake mi?a mata.

Se a lokacin ta karSa, ta dinga sha saboda azabar yunwar da take ji, sedai tana gama sha ta dinga amai saboda kwanakin da tayi babu Abinci a cikinta.

Saleh yace? "Yusuf yakamata mu bar gurin nan da gaggawa in kaiku inda zaku fake, zamanmu anan hatsari ne na gaske"

Yusuf yace? "Amma jikinta har yanzu bata da lafiya, ya za'ayi mu tafi a haka?"

Saleh yace "zamu karSi magungunan da zaku cigaba da Amfani da shi, amma dole mu bar gurin nan"

Haka likitan ya tattara magungunan Yusuf dana Widad ya basu, suka hau mota Saleh ya cigaba da nausawa dasu seda suka sake shafe wata tafiyar, Widad kam magungunan data sha basu saketa ba dan haka duka tafiyar nan bacci take, seda sukazo wata mararraba sannan Saleh yayi parking, wata tsohuwar motace akori kura ('yar ?ur?ura) gaba Waya ta sha jiki ta fatattake, hatta fentin jikinta ya koWe duk ta mole, anyi parking Wintabakin hanya.

Wani mutum ne ya fito daga a kori kurar, suka gaisa da Saleh, Saleh ya bashi mukullin motar da suka je da ita, suka kwance lambar motar dake jiki da wata.

Saleh Ya kalli Yusuf yace "Yusuf ku fito wannan motar zamu hau mu ?arasa"

Yusuf yace "nifa Saleh ban gane wannan abubuwan ba, kodai kaima kana da wani ?udurin ne akanmu"

"Yusuf wallahi ba wani abu da nake shiryawa don in cutar daku, sedai ?o?arin ceton rayuwar ku"

Yusuf ya fito hannun sa Wauke da Widad suka shiga 'yar ?ur?uran nan, Saleh yaja motar.
(Yau Widad ce a cikin irin wannan motar=?D?)

Tashin hankali ba' a samasa rana, duk wannan uwar tafiyar da suka sha Nafila ce akan wadda suke yi yanzu, wata irin ruSaSSiyar hanya suka bi, banda ?ura babu abunda yake tashi wata irin lalatacciyar hanyace, duk kwazazzabai da turSaya ga uban ramuka, wani ramin in suka shiga da ?yar suke fita ga ?ur?uran nan se wani irin ?ugi injinta yake yi, gashi sun matsu a motar, duk yayin da suka shiga rami haka suke bige kafaWu da ?arfen motar.

Wannan kwaraf kwaraf Win ne yasa Widad ta farka, a hankali ta kalli Yusuf tace

"A ina muke?"

Yusuf yace "Sannu ya jikin naki?"

Bata bashi amsa ba ta kuma cewa? "A ina muke ne?"

"Mun kuSuta ne, Saleh ze bamu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login