Showing 24001 words to 27000 words out of 135555 words

Chapter 9 - AKIDATA book 1 HAUSA NOVEL

17 Jan 2026

679

duba gurin.

ba zato ba tsammani ya shammaci Nur ya fizgota ya shiga cikin duhuwar flowers? da ita, yasa hannu ya sha?eta, ya kalle ta a hasale kamar wani mahaukacin zaki yace

"Ko ki gayamin gaskiya ko kuma zan fita dake daga gurin nan, zan ri?e ki a matsayin garkuwa harse Naga Widad, idan kuwa rayuwar Widad ta salwanta taki ma ta salwanta, ki gayamin ina take?"
Yai maganar cikin Waga murya tare da sha?e Nurat.

"Dan Allah, please don't kill me I will tell you, please secure my life"

"Your life will be secured if you tell me the truth" ya faWa yana zare mata ido

Cikin kokawa da numfashi tace "Ok zan gaya maka, Dad ne yasa aka busa mata wani abu, yanzu tana harabar gurin nan a Soye, wasu zasu zo su Wauke ta, idan baka hanzarta ba komai ze iya faruwa"

"Meyasa Mahaifinki yake ?o?arin sace ta?"

Cikin kuka tace "I sure to the Almighty ban sani ba, trust me"

Tasa Nurat yayi a gaba ta nuna masa ?ar?ashin bishiyar da aka ajiye Widad, tana kwance helplessly a ?asa, unconscious kaman babu rai a jikin ta, ga jakar ta a gefen ta.

Ya waiga ba kowa a gurin, Yasa hannu ya sunkuce ta ya tafi da ita motar su da sauri, ya buWe bayan motar ya kwantar da ita, yaja motar da gudun tsiya ya bar gurin.

Da gudu Nurat ta koma cikin gidan su tana haki, da yake hall Win party a cikin gidansu yake, Wakin ta ta tafi kai tsaye ta shige banWaki tana sauke numfashi, ta wanke fuskarta, ta buWe fridge ta sha ruwa me sanyin gaske, sannan Wakko wayarta ta kira layin mahaifinta.

Seda ta kusa tsinkewa sannan ya Waga yace
"Yaya i hope everything is going according to how it's planned?"

Cikin rawar baki tace "No Daddy something is going wrong"

Cikin sauri yace "meya faru?"

Cikin Rawar Murya Nurat tace "Daddy basu ?araso da wuri ba, nayi abunda kace Amma..
" Amma me? Ki gayamin menene? "
" Daddy ita da wani tazo, nayi abunda kace, but someone intimidate me, yace in ban faWi inda take ba ze kashe ni"
"Waye shi?" ya faWa a fusace
"Ban sani ba Daddy, Amma tare suka zo"
"Wace irin wawuya ce ke haka? Kinsan lokacin dana Wauka ina wannan shirin? Idan wasu suka rigani mallakar Abun nan mun kaWe"
"Daddy ba laifi na bane, laifin wanda ka turo su Wauke ta nefa"
"Shut up, kin Sata min shiri kina gayamin maganar banza"
"Am Sorry Dad is not my fault, but....
" Common Keep quiet "? ya faWa a Hasale, tare da katse wayar yana tsaki, tabbas ba dan wawancin nan 'yar cikin sa ce ta aikata masa ba da ba abunda ze hana yasa a Kashe ta.
A fili Yace
"dole in? toshe duk wata kafa da zesa su Alhaji Haruna su san nayi yun?urin sace Yarinyar nan ni kaWai, kuma dole in gano wane yaron ne suka je gurin tare"


Yusuf kam gudu yake bana wasa ba, ya dinga kauce wa dukkanin hanyoyin da zesa ya haWu da cunkoson ababen hawa, ko kuma jam'ian tsaro, be sassauta da gudu ba seda yaga ya shigo layin su Widad, a hankali ya ?ara sa tu?in yana zuwa ?ofar gate Win ya saki wani irin horn me gigitarwa, duk a ?o?arin sa na ganin ya kai Widad gida lafiya.

A gigice Isa ya buWe ?ofar dake jikin tangamemen Gate Win ya le?o ya fara masifa "haba Yusufa, wannan wani irin horn ne kaman me shirin sanar da tashin duniya"

Cikin harzu?a Yusuf yace? "Open the Gate"
Dukda Isa ba turanci yake ji ba amma ya gane Yusuf na magana ne akan ya buWe masa ?ofa, Cikin Sauri Isa ya buWe masa Gate Yusuf ya shiga da motar yayi parking, ya sakko da sauri daga cikin Motar ya buWe inda ya Kwantar da Widad, har yanzu bata hayyacin ta, Yasa hannu ya Wakko ta tareda Jakar ta ya nufi Cikin gidan da ita, Isa ya biyo bayan sa da Sauri yana ?asa da murya cike da gulma yake FaWin

"Yusufa meyasami Uwar Wakin naka kuma? Kodai Shaye2 tayi ne? Naganta kamar a buge"

Cikin tsawa Yusuf yace "Idan ka ?ara taku Waya daga inda kake zan Sata maka rai"
Gaba Waya Isa mamaki ya kama shi yadda Yusuf Win ke wani magana cikin Izza da isa.

Babu kowa a babban Falon dan haka Kai tsaye part Win ta ya nufa da ita, Ya kwantar da ita akan gadon ta.
Yasa hannu a aljihunsa, ya Wau wayarsa ya kira Abbas, bugu Waya ya Wauka yace
"Kai ya haka? Zaka kirani a wannan daren?"
"Kai akwai matsala fa"
"Matsalar meke nan?"
"Widad na kai gurin birthday akayi barazanar za'a kasheni idan ban bar gurin ba, ina komawa na neme ta na rasa, da ?yar na ganta, yanzu haka na dawo da ita gida Amma bata san inda kanta yake ba, I thinks they Use sedative substance on her, nayi niyyar in tsaya da ita a Asibiti Amma naga hakan hatsari ne babba"

Abbas ya numfasa yace? "Gaskiya kam zata farfaWo Insha Allah, gobe in Allah ya kaimu ka shigo Office kawai za muyi magana"

"Shikenan Allah ya kaimu" suka yi Sallama, ya maida Wayar Aljihunsa ya kalli Widad da take ta bacci bata san meke faruwa ba se sauke numfashi take, Yusuf ya Wauki bargon dake gefen ta ya rufe ta dashi saboda yanayin Sanyi, wayarta ce keta ringing a Jakarta ya buWe Jakar ya Wakko wayar ya kashe ta gaba Waya, Sannan ya kama hanyar fita.

Yusuf ya fito ya nufi hanyar fita, yaci karo da Ramlah a babban falo, share ta yayi ze wuce.

"Daga ina kuke a daren nan? Me kake a Wakin Widad a wannan lokacin?" muryar Matar gidan ce, dake tsaye a ?afar bene.

Yusuf ya juyo ya kalle ta sannan yace "Na kaita unguwa ne"
"Me kake a Wakin ta a wannan lokacin? Bata da lafiya ne, na kaita Wakin ta ne"
"Ka kaita Wakin ta kai a wa?" Ramla ta tambaye shi.

"Ni ba a kowa ba, ni a Wan uwan ta musulmi, kuma ma'aikacinta"

"Kai shashasha rufemin baki" Hajiya Halima ta katse shi cikin tsawa.

"Naga kanka yana rawa, to bari in tuna maka kai ba kowa bane face matsiyacin talaka, ka dena jin kanka kamar wani me iko dan kaga mai gidan nan yana wani baka girma na musamman kai Win ba kowa bane ba"

Amal da take jiyo hayaniya ta fito daga Wakin ta, tana zuwa ta tarar da mahaifiyar ta ta saka Yusuf a gaba tana zagin sa
"Haba Mummy, me Yusuf yayi miki kike masa wannan cin mutunci haka?"
Ramla tace? "An zage shi Win, meye ala?ar ki dashi? ?an uban waye shi da ze dinga wani jin kansa, dan yaga ya samu gindin zama, saboda tsabar cin fuska akan wannan banzan waccan mara mutuncin ta dizgani"

Yusuf ya Wan murmusa yace
"Nasani niba kowa bane, talaka ne ni gaba da baya, dan haka ku kwantar da hankalin ku,kuma ni bana sawa kaina ni wani ne" yana gama faWin haka ya juya ya fice.

Amal tace "Mummy koma menene laifin Widad ne, ni banga abunda Yusuf yayi ba"

Hajiya Halima cikin tsawa tace "dalla rufemin baki banza, naga za?ewar ki kema tana yawa akan yaron nan, ki shiga hankalin ki tunda wuri, ni sam yaron nan be minba, ya fiye kalar munafukai"

Ramla tai caraf tace? "wallahi kuwa Mummy, ni kaina ban yadda dashi ba, Ina jiran sakamakon binciken da kika sa ayi a kansa ne"

Amal tace? "Mummy koma menene Yusuf bare ne aiki ne ya kawo shi gidan nan, bekamata a saka shi a wannan sabgar ba"

"Amal kenan ke har yanzu yarinya ce, baki san inda rayuwa tasa gaba ba, kashedina dake shine, tun wuri ki fita daga sabgar yaron nan, dan muddin na gano wani abu saSanin abunda nayi zato a tattare dashi ba abunda ze hana insa ayi masa abunda ya dace da shi"

"Amma mum....

"Ke rufemin baki, shashasha kawai"
Mummy tayi maganar tare da juyawa zuwa Sangaren ta, Ramla ma tabi bayan ta suka bar Amal a falon tsaye.

Yusuf na fitowa, Nura ya biyo shi yace
"A'a kaga Wan gatan 'yar masu gida, gaskiya Yusuf ka ciri tuta, naga' yar masu gida tana yi da kai, ?iri ?iri ta koreni kuka tafi unguwa, naga duk inda zaka tare kuke tafiya"

Kafin Yusuf ya bashi amsa, Isa mai gadi ma ya nufosu yana cewa
"Nikam Malam Yusuf baka gayamin meyasami Uwar Wakin ka ba, nifa abun ya bani mamaki, iya sanina dai bata shaye2, sedai taSun hankali amma meyafaru da ita haka?"

Kallon su yayi Waya bayan Waya yana karantar tsantsar munafunci da son jin gulma a fuskokin su, sharesu yayi bece musu komai ba yai gaba abunsa ya fice ya bar gidan.

Yusuf na fita, Nura yace
"Ji shi se kace Wan uban wani, muna masa magana amma yayi mana banza, da Alhaji ne uban sa bansan wula?ancin da ze ba"

Isa yace? "Bar mara mutunci, ji yadda muna masa magana ya share mu, Anya Nura mutumin nan ba Asiri yayi wa me gidan nan ba?"

"Ni zance maka Asiri yayi masa hadda 'yar sa ma, kana gani Wazu ta hana Ramla binsu saboda shi, da muka dawo daga filin jirgi se cewa tayi ni in sauka in hau motar haya in tafi gida, shi kuma ya kaita unguwa"

Isa ya jinjina kai yace? "Kana gani duk jin kai da izzar ta, duk A?idar ta ta rashin yadda da mutane Amma duk inda zata tare dashi suke tafiya, dudu yaushe yazo gidan nan? Ko wata Waya be cika ba ya samu wannan gindin zaman, mu kuwa shekara nawa muna aiki a gidan nan? Ba abunda yake haWamu da ita se cin mutunci da wula?anci "

Nura yace "to ai magana ce a buWe, Allah kaWai yasan abunda suke yi"

Isa yace "kuma fa hakane zancen ka Nura, taS aikuwa zamu ?ara saka ido sosai, zamuyi maganin wannan gani-ganin da yake mana"

Haka suka zauna suka cigaba da gulma, suna muzanta Yusuf da miyagun kalamai.

Yusuf kam kansa ya kulle Sosai, daya koma gida ma kasa bacci yayi, yana ta nazari akan abubuwa da dama yana son gano bakin zaren amma ya rasa ta ina ze fara, gaba Waya Al'amuran a cukurkuWe suke, me zesa Baban Nurat yun?urin sace Widad? Waye mahaifin Nurat? Dole Akwai dalilin da yasa Widad take da wannan A?IDA na ?yamar talaka da nesanta kanta da mutane, yanayin Abubuwan da take yi wasu lokutan yasa Yusuf ya fara gazgata cewar tana da taSin ?wa?walwa, tunani ya haWu ya cunkushe massarafar gangar jikinsa wato ?wa?walwarsa, ba shiri ya tsagaita tunanin ya kwanta da ?udurin dole yaje Office da safe, akwai bu?atar yaga Abbas.

A hankali ta motsa daga nannauyan Baccin da take, ji tayi kanta kamar an Wora mata wani nannauyan dutse, gaba Waya gaSoSinta sun mata nauyi, a hankali ta buWe idon ta ta ?arewa Wakin nata kallo, ta mayar da idanunta ta lumshe na wasu da?i?u sannan ta sake buWe su, a hankali taja jikin ta ta mi?e zaune, kallon jikin ta tayi tare da ?o?arin son tuna abunda ya faru, sosai take takura ?wa?walwarta don ta tuna mata abunda ya faru, Amma fafur ta kasa tuna komai, dafe kanta tayi wanda taji yana sara mata, ta mi?e jiri na kwasar ta ta tafi banWaki.

Da sassafe ko karyawa Yusuf beyi ba ya fito ze fita. Umma dake kitchen tana ?o?arin haWa Abinci ta le?o tace
"Yusuf me zan gani haka? Ba zaka tsaya ka karya bane?"
Yusuf yace? "Umma sauri nake ne, bana son in makara akwai aikin da nake son yi"
"Yusuf nifa gaskiya wannan aikin da kake a gidan masu kuWin nan ba sonsa nake ba, nasan halin masu kuWi da rashin mutunci da wula?anta talaka, nidai gaskiya su canza maka wannan aikin su baka wani, danni gaskiya bana son kaje inda za'a wula?anta min kai"
Kallon Umman sa yayi, ya Wanyi murmushi ya tako gaban ta ya ri?e hannayen ta yace
"Kyakkyawar Uwa, Uwa da babu irin ta, ina Alfahari dake Umma na, yadda kike kula dani Allah ya kulamin dake ko bayan raina, ki kwantar da hankalin ki, basa wula?anta ni, kuma yanayin aiki ne yazo a haka, dana Kamm zan koma Office, idan kuma kince ba kyason aikin se in ha?ura gaba Waya"

Badan ranta yaso ba tace? "Yusuf ba aikin ne bana so ba, ni wannan aikin da suka baka ne bana so, yaushe rabon da muci Abinci tare, in ka fita tun safe se dare, Amma shikenan dai, Allah yayi maka Albarka, Allah ya sadaka da Alkhairi a duk inda kake"

"Ameen Umma na, bari in sauri sena dawo"

"Allah ya kiyaye hanya"
Ya amsa da "Ameen" ya fice.

Kai tsaye headquarters su ta jam'ian tsaro na farin kaya ya tafi.
Kasancewar Yusuf mutumin kirki yasa tun daga gate masu gadi suke gaida shi, ya tsaya suka gama gaisawa sannan ya shige ciki.
Ofishin sa ya nufa kai tsaye, yana zuwa ya tarar da shi tsaf ana shiga a gyara masa dukda baya nan, Na'ura me ?wa?walwarsa ya Wakko ya kunna, ya Wan jira kaWan sannan ya fara daddanawa.
Gaba Waya ya nutsu sosai hankalinsa kacokan yana kan Computer, da gani kasan ?o?arin gano wani abu yake me mahimmanci.

Sallamar da'akayi a office Win ne yasa shi Wagowa, Sakina ce sanye da suit na aiki kamar yadda ta saba, fuskar ta Wauke da murmushi ta ?araso tana wani fari da ido, Sam Yusuf baya ?aunar mace mara kamun kai, shiyasa sam Sakina bata burgeshi.

Kujera taja ta zauna, ta kalle shi tace "wata sabon gani, aiki ya Soye mana kai gaba Waya haka, ba'a jin Wuriyar ka ko a waya, na kira ka harna gaji baka Wagawa"

Yusuf "Aikine ya Wanmin yawa shiyasa, Ya aikin?"

Cikin iyayi tace? "Alhamdilillah, Fatan dai kana lafiya?"

Cike da basarwa yace "Lafiya ?alau"
Ya cigaba da latsa computer sa.

"Kwana biyu da baka zuwa duk gurin nan ba daWi, nayi farincikin zuwan ka sosai"

Bece mata komai ba ya Wakko wayarsa ya Wan daddana ya kanga a kunnen sa, ya Wanyi shiru na wasu da?i?u sannan yace
"Ya Abbas ka shigo ne?"

Ya sake yin shiru sannan yace?
"Ok nima na shigo yau akwai bu?atar in ganka, bari inzo office Win naka"

Yana gama wayar ya mi?e ya fice ya bar Sakina a gurin, ba tare da yace mata komai ba.

Wani ?ululun ba?in ciki ne ya tokarewa Sakina zuciya, tabi bayan sa da kallo tare da yin ?wafa.

Yana fita ya nufi Office Win Abbas, yaje ya tarar da shi yana karin kumallo, ya zauna suka gaisa, Abbas ya zubawa Yusuf shayi ya mi?a masa sannan yace "Mutumin ya? Yau ka samu chance Win Sullowa kenan? Meye labari ne?"

Yusuf yace? "labari kam akwai shi Abbas, nifa gaba Waya a rikice nake wallahi, gaba Waya na rasa bakin zaren"

"Take it easy man, bi komai a sannu, me ake ciki?"

Nan Yusuf ya warware masa irin abubuwan da suka faru har zuwa ga yun?urin sace Widad da'akayi jiya.

Shiru Abbas yayi yace? "Lallai lamarin akwai rikitarwa, Mahaifin Nurat ze shiga cikin suspects Winmu, yanzu abunda za'ayi ka bani Adress Win gidan, zamu je muyi bincike, semun fara gano waye ma mahaifin Nurat Win"

Shikenan zan turomaka Complete Adress Win ta Email Winka. Suka zauna suka cigaba da tattaunawa.
Wayar Yusuf ce ta fara ringing ya Wakko ya duba, lambar Isa megadi ce a akan allon wayar tasa, ya Waga ya kara a kunnen sa, suka gaisa Isa yace masa? "Ana neman ka"

"Shikenan gani nan zuwa"

Yusuf ya kalli Abbas yace? "Abbas bari in canza kaya, waccan rigimammiyar tana nemana yau nasan zan sha tijara, dan titsiyeni za tayi tace sena gayamata meyafaru"
Dariya Abbas yayi yace? "Ina jinjina maka Yusuf, yadda kake iya aiki da wannan Yarinyar mara al?ibla"
"to ya zanyi tunda kun takura kunce se nayi, dole in kwantar da kai inyi ha?uri da halin ta, Amma kasan wani abu Abbas?"

"A'a seka faWa"

"Ni yanzu gaba Waya tausayi take bani, gaba Waya rayuwar ta ba irin yadda kowa ke gudanar da rayuwar sa take yi ba, duk yadda zan kwatanta naka ba zaka gane ba, ina kyauta ta zaton akwai wani pain a zuciyar ta, da yake ?ara assasa condition Win da take ciki "

"Hmm Yusuf kenan ba wani pain, kawai iskanci ne na yaran masu kuWi, ta taka wanda take so tayi rashin mutunci saboda tana da masu gidan rana"

Yusuf yace? "Haba Abbas, su talakawan me suka yi take musu haka? Wai waya gaya maka talakawa kawai take wa haka? Hmm ni nasan abunda nake gani kawai, ba iya Wula?anta mutane ba, Akwai wani Soyayyen abu da yake damun ta, ina jin tausayinta sosai"

Abbas ya ?yal?yale da dariya yace? "Kai mutumina, ko dai ka koma ruwa ne?"

"Na koma ruwa kamar Yaya?"

"To naji kace kana tausayinta, na sani ko babbar magana zaka janyo mana"

Shiru Yusuf ya Wanyi jiki a sanyaye ya kalli Abbas yace
"Abbas ai na rufe wannan babin har Abada, sedai wani ikon na Allah, just recently ka manta abunda ya faru dani ne? Ina ni ina Widad, as i told you before i give up gaskiya babu yarinyar da zan ?ara cewa ina so, zanyi ha?uri da ?addara ta, in zauna Yadda Allah ya ajiye ni, ni yanzu bari in tafi kar in ?arawa kaina laifi, dukda yanzu ma nasan laifi na riga nayi shi, zan sha tijara a gurin Widad"? yai maganar tare da mi?ewa ya fice.

Abbas yayi shiru yabi bayan Yusuf da kallo, he's very gentle and innocent, abubuwa da yawa marasa daWi sun faru da Yusuf, gashi shi kullum zuciyar sa a wanke take, baya nufin cutar da kowa.
A fili Abbas yace? "Anya kuwa nayi adalci idan aka haWa kai dani, aka cutar da Yusuf, Kai Amma kuma Alherin da zan samu a wannan sabgar ya isa in ajiye wannan wahalallen aikin in more rayuwa ta"

Yusuf ya canza kaya ya tafi gidan su Widad, ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login