Showing 12001 words to 15000 words out of 135555 words

Chapter 5 - AKIDATA book 1 HAUSA NOVEL

17 Jan 2026

681

A BAYA NASAKA RAN KAMMALAWA DA MAKARANTA A AUGUST, KATSAM AKA ?AGA JARRABAWA AKA MAIDA ITA 20 GA WATAN SATUMBA, AMMA TUNDA NI NAYI MUKU AL?AWARIN CIGABA DA KAWO MUKU WANNAN LITTAFI A WANNAN WATA, NA SHIRYA TSAF DAN CIKA AL?AWARIN KU 'YAN AMANA, WATTANI HU?U KUNA SAURARE NA, INSHA ALLAH BAZAN BAKU KUNYA BA, KU SHIRYA DOMIN SALON NA DABAN NE, AKWAI TUFKA DA WARWARARA ME MATU?AR SAR?A?IYA A WANNAN LITTAFI DA KUKA DA?E KUNA JIRA.
KARA ?AYA ZAKUYI MIN, SHINE NUNAMIN JIN DA?IN KU TA HANYAR YIMIN COMMENT TARE DA SHARE, LITTAFIN NAN KYAUTA NE DOMIN JIN DA?IN KU MASOYA NA, AMMA A DALILIN RASHIN COMMENT ?INKU KOMAI NA IYA CANZAWA, GA MASU MANHAJAR WATPAD KU GARZAYA KU NEMENI
@AYSHERCOOL7724
KU NEMI LITTAFIN A FACEBOOK A
GROUP ?IN PERFECT WRITERS ASSOCIATION
?OFA TA A BU?E TAKE DOMIN GYARA SHARHI KOKUMA SHAWARA
AYSHERCOOL
07063065680

YADDA NA FARA LAFIYA ALLAH YASA IN KAMMALA LAFIYA

Ha??in Mallaka ?& : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ?unsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani Sangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode

BISMILLAHIRAHMANIRRAHIM

ELEGANT ONLINE WRITER'S





? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ?? *PART1*
? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ??
? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? _Page 4_









Babu alamar sassauci fuskar Widad, yanayin fuskarta ze tabattar maka da gaske har cikin zuciyar ta zata aikata abunda ta faWa, ta juya ta koma cikin gidan da hanzari.

Jinjina kai Isa ya dinga yi yana kuma sake shafa kumatunsa yadda yske masa raWaWi, tare da tausayawa wula?ancin da Yusuf ze fuskanta.

Ramla kam cikin sassarfa ta nufi Wakin mahaifiyar ta, tun daga waje take kiran "Mummy"

Hajiya Halima tace "Ramla wannan wane irin kira ne haka? Ke kam bakya girma"

Ramla ta ?arasa kusa da mahaifiyar ta ta zauna tace "wai nikam nace me akayiwa 'yar gwal ne? Naga kaman ciwon nata na ?o?arin tashi fa? Kuma ga dukkanin alamu yau ta kwaSe mata itada uban tane"

?an tsaki Mummy tayi tace
"sakani yake cikin sha' aninsa shida 'yar sa ne? Ai sedai inga suna lamauran su ta yaya zan san meya sameta?"

Ramla ta sake gyara zama "hmm kinsan dai halin ciwon ta, a corridor Win ?asa na haWu da ita, tana ta surutai, wai Daddy Aure zeyi mata, se safa da marwa take tana zufa"

Zaro ido Mummy tayi tace "Aure kuma? Wane irin Aure ana zaman lafiya? Waye ze Auri mahaukaciya mara tarbiyya kamar wannan Yarinyar? Shi mijin da haukan zeji ko kuma da rashin tarbiyya?"

Ramla tace "waya sani musu?, sedai ki jiyo mana kanun Labaran muma ki fesa mana, Amma ina tunanin wanda ze kwashi wannan Mahaukaciyar"

"To nidai a iya sanina bata yadda da mutane ma, to ta yaya ta samo wanda ze Aure ta?"

Ramlah tace "Ai samun miji ba wuya ze mata ba, ko dan wannan haWaWiyar Daular, dan haka ko'a turu take dan hauka, za'a iya samun me sonta yace ze aureta a haka"

Mummy tace "hakane, Amma ya zama dole musan waye ze Aureta, dole in gano"
Haka Suka ci gaba da tattauna wa akan lamarin.

Yusuf kam kashe wayoyin sa yayi ya shiga sabgoginsa, duk yadda Isa yaso kiran Yusuf a waya ya gaya masa Sa?on Widad abu ya gagara wayar sa ta?i shiga, ?arshe se ha?ura Isa yayi.

Widad kam baranda ta samu ta kwanta, akan tiles ga sanyin tiles na ratsa ta amma sam bata ji, tayi ruf da ciki tana jin yadda zuciyar ta take mata raWaWi, kamar ta tsaga ?irjinta ta fito, Babban Abunda ya ?ara bata mamaki shine yadda mahaifin nata be biyo sahunta ba balle ya rarrashe ta kaman yadda yake yi abaya, shima kamar yayi fushi da ita karon farko ya barta cikin damuwa, lallai wannan karon mahaifin nata dagaske yake.

Washegari Yusuf ba shida Niyyar zuwa gidan su Widad Sam, da ya tashi da safe ma shirin tafiya Office yayi abun sa, ya shirya ya fito Umman sa ta kalle shi tace
"Ya haka kuma? Yau ina zakane?"

Murmushi yayi yace "Yau Office zanje Umma"

"Kacemin kuma, an turaka aiki gidan Alhaji Nasir Daula, yanzu kuma kace min zaka gurin aiki ya haka?"

Yusuf yace "hakane Umma, an turani aiki gidan Alhaji Nasir Daula, Amma dole zan dinga le?awa Office, ina documenting findings Wina sannan indinga presenting sakamakon bincike na"

"shikenan a sauka lafiya, Allah ya tsare ya kiyaye hanya"

"Allah yasa Umma, dan Allah yau ki mana dambu kinji Umma na"

Umma tace "banyi Al?awari ba, ka bari ranar da kake nan se kayi"

No?e kafaWa Yusuf yayi yace "dan Allah Umma, ni gaskiya idan ba dambu kika yi yau ba bana cin Abincin"

"kar kaci Win, ai cikin ka ba nawa ba"

Haka yaita zolayar umman nasa sannan yai mata sallama ya tafi.

Da yaje Office Win ma Ayyuka sun Wanyi masa Yawa, ya du?ufa sosai yana ta shigar da ayyukan sa cikin system.

Sallamar da'akayi a office Win ne ya sashi Wagowa yaga me Sallamar, kamar yadda ya zata sakine ce ta shigo.

Kallo Waya yayi mata, ya Amsa sallamar ya maida kansa ya cigaba da danna system Win shi.
Yauma cikin ba?a?en suit Sakina take, amma skirt ga ?aramin hijjabi da ta saka, gaba Waya kayan sun bayyanar da surar jikin ta.
Kujera ta ja ta zauna tana facing Win sa.

"Yusuf sannu da Aiki"
Ba tare da ya kalle ta ba yace "lafiya kalau Alhamdilillah"

"kwana biyu baka shigowa Aiki, lafiya dai ko?"

?an Wagowa yayi yace "Eh an bani wani Assignment ne"

Cikin iyayi da lumshe ido tace "to Allah yaba da sa'a"

Ya amsa da "Ameen"

"Can i offer you something to eat?"

Ba tare da yace komai ba ya girgiza mata kai, Alamar A'a.

Mi?ewa tayi ta zagayo inda yake tace
"ko Akwai abunda zan taya ka ne?"

?agowa yayi ya kalleta a hankali yace "dan Allah ki fitar min daga Office inada Ayyuka da yawa kina takuramin fa"

A ShagwaSe tace "Yusuf meyasa kake son yi mun wula?anci ne?"

"ba wula?anci bane, gaskiya ce, Aikine ya kawo ni gurin nan ki barni inyi aikina mana"

"Amma Yusuf meyasa zaka maida Soyayya ?iyayya, tunda na nuna ina sonka kake wula?antani haba Yusuf"

"Sakina niba wula?antaki nake ba, yanzu lokacin aiki nane, dan Allah ki tashi ki tafi, bearable in shiga lokacin aiki ba"

"Yusuf" ta kira sunansa, Waga mata Hannu yayi ya dakatar da ita tare da faWin

"Sakina dan Allah ki barmin office, kalli shigar jikin ki, kuma kinzo kin sani gaba, dan Allah ki tafi"

Suna cikin Jayayyar ne Abbas ya shigo, Sakina ta mi?e ta bar office Win a fusace.

Abbas ya kalli Yusuf yace

"Anya Sakina bata fara kama zuciyar ka ba Yusuf?"

?an girgiza kai Yusuf yayi yace

"Abbas kenan anyi na farko, baza'ayi na biyu dani ba, bana son yi mata wula?anci ne amma ta?i ganewa, Soyayya kam sedai inga anayi, bazan sake ba, in Allah yayi zanyi Aure shikenan, Amma na gama Soyayya"

Abbas ya jinjina kai yace "shikenan Allah ya kyauta, na kiraka tun jiya bata shiga ya labarin mutuniyar ne?"

Shafa Aljihun sa Yusuf yayi, sannan ya jingina da jikin kujera yace

"Aini tun jiya dana dawo na kashe waya ta, bana son a dameni ne sam"

Abbas yace "kayi mata aikine jiya?"

"Eh munfi ta, na kaita wani gida, inaga gidan Wan uwan mahaifinta ne ko makamancin haka"

Abbas yace "babu dai wata matsala ko?"

"Babu wata matsala, ba tayi min dai wula?anci ba, Amma fa naga izza wadda ban taSa ganin makamanciyarta ba, dan cikin isa da gadara take wa kowa magana, bata shakkar kowa bata girmama kowa, kai ko Dariya banga tayi ba Jiyan nan, magana ma aiki ce a gurin ta"

Abbas yace "taS, aishi yasa nace bazan iya ba, saboda na samu labarin yarinyar, shikenan ka dai kula sosai akan abunda muke son ganowa"

Jinjina kai Yusuf yayi, tare da cewa "Insha Allah, komai ze tafi dai dai"

***********

?arfe goma na safe Yusuf ya bar gurin aikin, ya koma gida seda yayi wa Umman sa cefane, ya kai mata markaWe ya kama mata Ayyukan gida sannan ya sauya kaya, ya nufi gidan Alhaji Nasir.

Yau da yaje ya tarar da Isa mai gadi dashi da wani, Suka gaisa, Isa yayi farat yace
"Yusuf ga Nura shine direban megidan nan, lokacin da kazo yaje garin su ne, amma gashi ya dawo, shike kai Alhaji unguwa"

Yusuf ya mi?a wa Nura hannu suka gaisa.
Isa ya nisa yace "Yusuf kayi gangancin tafiya jiya, nan ta fito a birkice jiya kaman mara hankali tazo nan tana neman ka wai ka fita da ita, baka ga shigar jikin ta ba, daga tambayar ta a haka zaka fita da ita ta mareni, wallahi har yanzu ko ?uda bana so ya taSa fuskata dan ba ?aramin shiga marin nan yayi min ba"

Zaro ido Yusuf yayi yace "mari kuma?"

"Wallahi Yusuf mari na tayi"

Nura yace "aiba abun mamaki bane, dama wani lokacin haka take birkice wa, kun san abunka dame rangwamen ?wa?walwa, aini tunda naji zata dawo naji aikin gidan nan ya fita daga kaina, Allah ya temakeni aka samo mata nata direban"

Kallon su Yusuf yake dan be fuskanci inda zancen nasu ya dosa ba.

Isa yayi ?asa da muryar sa yacewa Yusuf
"wani lokacin birkicewa take kaman hauka hauka, shiyasa kaga bata son mutane suje inda take, tana da larurar ?wa?walwa shiyasa....

Yusuf ya katse shi ta hanyar cewa
"Shikenan shikenan, Allah ya bata lafiya be kamata a dinga yayatawa ba, Addu'a ya dace ayi mata, faWar bashi da Amfani sam"

Widad ce ta fito ?aton falon gidan, ta tarar da matar gidan da yaran ta Suna ta ciye ciye suna hira, tana fitowa suka yi tsit suka shiga taitayin su, suka dena hirar.

Ta dube su Waya bayan Waya, kamar me nazari, sannan ta yatsuna fuska tace

"Amal jeki kira min wancan matsiyacin talakan direban, yau in fara gwada masa wacece ni"

Sam Amal ba taji daWin kalaman da Widad tayi amfani da su akan Yusuf ba, Amma babu yadda ta iya ta mi?e ta tafi kiran sa.

Tunda Amal ta fito ta hangi Yusuf yana hira da su Nura, yayi kyau sosai komai nasa gwanin sha'awa, kamar ba direba ba.

Amal Ta ?araso inda suke bata kula su Isa dake ?o?arin gaishe ta ba, ta dubi Yusuf tace

"barka da rana Yusuf"

Fuskarsa ba yabo ba fallasa yace
"Yawwa barka, ina uwa Wakina?"

Bata jin daWin yadda koda yaushe yake ta?aita magana da ita, Amma ta basar tace

"itace tace in kira ka ma"

Yusuf ya mi?e yace "shikenan muje"

Yabi bayan Amal, tsananin kwarjinin Yusuf ne yasa Amal sam ta kasa kuma ce masa komai, se ?amshin turare yake fitarwa me daWin ?amshi kaman ba direba ba.

A falon suka tarar da hakimar ta harWe da alewa me tsinke a bakin ta, tana danna waya tareda kaWa ?afafuwan ta.
Kamar kullum yanzu ma kanta babu Wan kwali, ta baje gashin ta, Amma yau anyi sa'a skirt ne dogo a jikin ta da wata 'yar ?aramar riga shara shara.
Tunda Yusuf ya shigo Wakin ?amshin turaren sa ya daki hancin ta taji ya saukar mata da wata muguwar kasala, a duk lokacin da Yusuf zezo gidan nan taji wannan ?amshin turaren a jikin sa se kasala ta saukar mata.

Kallo Waya Yusuf yayi mata yaji ?irjin sa ya buga da ?arfi, da sauri ya Wauke idon sa daga kanta, Sam fuskar ta babu alamar afuwa.

Ya kalli matar gidan yace
"barka da yamma Hajiya"

"Yawwa barka sannu ya aikin?"

"Alhamdilillah"
Ya juya ga Widad yace "sannu da hutawa ranki ya daWe"

Dama be zaci zata amsa ba, dan haka be kuma cewa komai ba se sunkuyar da kansa ?asa da yayi.

Ya shafe mintuna Arba'in a dur?ushe a gaban ta ba tare da tace komai ba, shi kuma ko kansa be Waga ba.

Amal ji take tamkar ita ce a dur?ushe a gurin, gaba Waya taji kaman ta cewa Yusuf ya tashi yayi tafiyar sa.

Ba zato ba tsammani ya tsinkayi maganar ta

"Waye ya baka iznin tafiya jiya?"

"ba kowa Ranki ya daWe"

Seda ta kuma jan wasu mintunan sannan tace
"meyasa ka tafi?"

Ba tare da ya Wago kansa ba yace

"na zata na gama aikina na jiyane shiyasa, Amma hakan ba zata sake faruwa ba Insha Allah, kiyi ha?u....

Cikin tsawa tace
"Shut up, what the hell are you trying to say? Do you sign my conditions based on Assumption? Don't you read what is in that paper? Why are you trying to applogise? Talaka baze canza hali ba, baku da Al?awari baku san ?a'idar Aiki ba, se an jima ku buWe baki kuna zagin shugabanni da masu kuWi, waye kai da zaka karyamin doka? Me kake ta?ama dashi da zaka nemi ka raina min hankali? ?an uban waye kai? Ko ban gaya maka lokacin aiki nawane ba? Har da zaka fara da rainamin hankali"

Tunda Widad ta fara zazzaga rashin mutuncin ta Yusuf be Waga kai ba, dukda yadda zuciyar sa ke harbawa jijiyoyin kansa suka mi?e saboda Sacin rai, Amma ya dake.

Amal kaman ta Wora hannu akai tayi ihu, ji take tamkar ita Widad ke ciwa mutunci, ita kuwa matar gidan da Ramlah ko a jikin su dan babu wanda Widad ta bari a rashin mutunci.

"kasan tsanani ba?in cikin da na shiga zama na a gidan nan bayan an Sata min rai, daka nan ka fita dani da ban shiga damuwar dana shiga ba, tun jiya nake fama da damuwa saboda sakacinka, nayi kwanan ba?in ciki da Sacin rai, this is my last warning to you, idan makamancin haka ya kuma faruwa, sena nuna maka wace ce Widad"

Risinawa ya kuma yi da kai

"zan kiyaye ba zana kuma ba insha Allah"

Jefo masa key tayi fuskar sa tare da faWin
"Car Number 8, to bulama's residence"

Yaji zafin yadda ta jefa masa key a fuska, da maganganu marasa daWi da tayi masa, amma yasa hannu ya Wauka, kaman wanda ?wai ya fashewa a ciki ya nufi hanyar fita.

Fakar idon Widad Amal tayi ta biyo bayan Yusuf, wajen ?ofar fita ta cin masa, yana ta sauri fuskarsa babu Annuri, Amal ta kira sunan sa, dan tsayawa yayi ya waigo yana kallon ta

"Dan Allah kayi ha?uri da abunda Widad tayi maka, haka halin ta yake muma duk ha?uri muke da ita, dan Allah kayi hakuri"

Ga mamakin ta se taga murmushi akan fuskarsa yace

"aini banji haushi ba, tabbas laifi nane da banbi komai a ?a'ida ba, bayan nasan hakan ya saSawa Yarjejeniyar dana sakawa hannu, kuma nasan yana daga A?IDAR uwa Wakina girmama Al?awari, ya kamata in nemi Afuwa ne ba jin haushi ba"

?an zare ido Amal tayi "yanzu duk abunda tayi maka kana nufin ba kaji haushin hakan ba?"

Jinjina mata kai yayi alamar eh tareda faWin,

"bari in hanzarta in fito da motar karta fito ta sameni anan ranta ya kuma Saci" yayi gaba abun sa yayin da shi kaWai yasan me yake ji a ransa.

Yaje ya fito da motar da ce masa, ya buWe ya shiga ya zauna ya kifa kansa akan sitiyari, tabbas badan duk cikin aikin sa yake wannan abun ba to da ko Gidan su Widad gold ake sarrafawa baze kuma aiki a gidan ba.

Jin ?amshin turaren ta yasa shi saurin Wagowa, ta buWe gaban motar ta zauna, tace "jeka falo inda na zauna ka Wakko min wayata"

Ikon Allah wayar ma bazata fito da ita ba seya Wakko mata? Bece komai ba ya fita daga motar ya koma cikin gidan, yana zuwa ya tarar falon ba kowa wayar tana kan center table, ya Wakko ya fito ya kawo mata.

Tasa hannu ta karSa ba tare da ta kalle shi ba tace "A ina kaga wayar"

"Akan center table"

Murmushin gefen baki tayi tace "let's go"

Kamar yadda tace gidan Bulama ya kai ta, ya samu guri yayi parking ya fito ya buWe mata ?ofa ta fito, ?afarta sanye da takalmi me tsini sosai shigar nan tata baka ce musulma ce ba, kayan sun kamata tsam a jikin ta a hankali ta furta "do not accept any gift from anyone"
GyaWa mata kai yayi yace "Insha Allah"
"Follow me"

Haka yabi bayan ta, cikin hanzari take tafiyar yau.

Yau kai tsaye bata nemi iso ba cikin gidan ta nufa, Yusuf na bin bayan ta.
A babban falon dake gidan suka ga wata budurwa da wannan matashin da suka tarar jiya, da wata babbar mace da alama itace matar gidan.

Maimakon Widad tayi Sallama se tace "Hi how are you doing guys?"

Matar tace "Widad dama kina garin nan amma ko ganin ki ba'ayi"

Budurwar tace "Wallahi Mum Ramadan yace tazo jiya amma ta?i shigowa" Yusuf dai bece komai ba saboda jan kunnen da tayi masa jiya.

Ramadan ya kalli Widad yace "you look so Cute in this outfit Dear"

Ba ta amsa musu maganganun su ba tace "Is Daddy Around?"

Yusuf ya kalli kayan dake jikin Widad, da kuma abunda Ramadan yace kawai ya girgiza kai

Ramadan yace "yeah yana nan"

?o?arin hawa bene Widad take yi, budurwar tace

"hey Baby who is this gentleman with you?"

Aiko tsaya ba tayi ba balle bada amsa, ta haye saman benen da sauri, Yusuf bashi da zaSin daya fi yabi bayan ta.

Wata ?atuwar ?ofa ta buWe, ta kutsa kai Yusuf yabi bayan ta, shima wani haWaWWen falo ne me girman gaske, sanyi Ac ke rasa ko ina na Wakin.

Alhaji Bulama ne ke zaune akan Waya daga cikin kujerun falon, yana shan tea tareda dannan system, Yusuf ne yayi sallama, Alhaji Bulama ya Wago ya kalle su.

Murmushi yayi ya amsa sallamar Yusuf, yana ?arewa Widad kallo, guri ta nema ta zauna tana fuskantar Bulama.

Bulama yace "Daughter wai shi wannan duk inda zaki se tare da shine? Ina direba ne kawai? Kodai Allah ya karSi Addu'armu kin fara sakin jiki da mutane?"

HaWe rai tayi tace "my policies remain constant, babu abunda ya canza, babu ruwan ka da dalilin da yasa duk inda zani yake bina"

Alhaji Bulama ya murmusa yace "shikenan Allah ya baki ha?uri"

Ya kalli Yusuf yace "Sannu Wan Samari, daughter Win tamu seka na ha?uri, muma lallaSata muke"

Da ido ta kalli Yusuf, dan haka Yusuf bece komai ba se Wan murmusawa da yayi.

Alhaji Bulama ya maida kallon sa ga Widad yace "ina jinki?"

"Meyasa ka turawa Daddy na ra'ayin ayimin Aure?"

?an girgiza kai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login