Showing 108001 words to 111000 words out of 135555 words

Chapter 37 - AKIDATA book 1 HAUSA NOVEL

17 Jan 2026

667

a mi?o bayanan binciken nan headquarter"

Suleiman yace "Ok Sir"

Yusuf ya kalli Widad da tayi kicin kicin da fuska yace "ga kayan nan na wankesu, sun bushe ma gaba Waya"

Tasa hannu ta ciro kayan daga bokiti, taga kayan a haWe dana Yusuf, kwashe nata tayi ta zube masa nasa a gurin, Yusuf yasa hannu ya kwashe ya zuba a jakarsa.

Ya kalleta yace "kinci Abinci kuwa?"

"ni banci wani Abinci ba, kaga fa abunda aka kawo"

Kwano ta mi?a masa, yasa hannu ya buWe dafaffiyar masarace a ciki da Sawonta da komai, Yusuf yace "to me yasa baki ciba?"

"ta ina zanci ? Kawai se in kama cin masara, ni ban taSa ganin anci masara ba, nidai kawai nasan Abinci akeyi da ita, amma ba'aci"

Yusuf yace "ikon Allah, wannan wace irin hausa ce? Waye ya gaya miki ba'a cin masara"

Ya zauna ya Sare masarar tsaf, ya Waurayeta, yace "nasan kece baki taSa ciba, amma ana cin masara dafaffiya ko gasashiya, ci kiji"

?auke kai tayi ta?i karSa, Yusuf kuwa yasa masara a gaba ya fara ci, zuba masa ido tayi tana kallon ikon Allah, yana nufin itama haka zata Wau masarar ta dinga wannan kokawar haka sekace wata saniya.

Plate ya Wakko ya shiga SanSarowa yana tara mata a plate yace "gashi na ciro miki Wauki kici"

Ba kunya tasa hannu ta fara tsinta tana kaiwa bakinta, dan bilha??i ita bata taSa ganin ana cin masara a haka ba, amma kuma tabbas da daWi, ya dinga cirowa yana tara mata tana tsinta tana ci, kamar wata 'yar yaye, cikin ikon Allah a haka kuma ta ?oshi.

Shiru tayi ta tuna lokacin da sukaje restaurant cin Abinci, Yusuf yake gayamata Naira Warin cin Abinci tana gagarar wasu, take ganin kamar ?arya yake, se gashi yanzu ta gani da idonta, da wanine ya bata labarin ana dafa masara aci a matsayin Abinci zata ce ?aryane dan bata taSa gani ba.

Can Yusuf yace "inda ?waron ya cijeki ya dena zafin?"

Ta gyaWa masa kai alamar eh, yace "hannun da'aka harbe ki fa?"

"yayi sau?i, ina iya motsa hannun sosai, sedai idan ma bige ne nake jin zafin"

Yusuf yace "masha Allah, Allah ya ?ara miki ingantacciyar lafiya"

Shiru tayi kamar ba taji ba, Yusuf yace "Addu'ar ma bakya so?"

Shiru tayi masa tana sake ?arewa roofing Win Wakin kallo, tana son gane dame akayi shi.

Yusuf yace "me kike kallone?"

Widad tace? "kai subhanallah, wallahi ka dameni da surutu haba, sekace waccan matar me ha?ora"

Yusuf yace "to shikenan na dena gimbiyata"

?agowa tayi ta masa wani irin kallo, ba shiri ya mi?e yayi waje ya bar mata Wakin yana murmushi.

Wasa2 Ramlah ta ganewa shaye2, bata salla se wajen ?arfe takwas na safe, da ta idar zata Wakko Coca-Cola tasha, seta kai ?arfe biyun rana tana bacci.

Yanzuma Amal ce ta shiga Wakin Ramlah, ta tarar da ita tana girgiza jarkar Coca-Cola.

Amal tace? "Ramlah, wai me yake damunki ne haka? Wane irin coc ne kike sha ba yau ba gobe ga shegen bacci kamae kin haWiyi kasa"

Ramlah ta kalleta tace "kina da matsala da hakanne?"

"ba wai batun ina da matsala da hakan bane, sedai cewa kina ganganci da rayuwar ki, baccin da kike ya wuce ?a'ida, kuma wannan coc da kike sha yayi yawa sosai, nifa na fara zargin wani abu kike sha a cikin coc Win nan"

"Ke Amal! Ki kiyayeni, dalla wuce ki barmin Waki, ina ruwanki dani idanma wani abun nake sha?"

Amal tace "shawara ce nake baki, amma

" wallahi Amal in baki barmin Waki ba sena miki rashin mutunci, Dalla ?ara gaba kije kiji da kanki"

Amal tace "shikenan Kije ki ?arata" ta fito daga Wakin.

Yanzu kusan kullum se Ramlah ta fita, ko tare da Fahad ko ita kaWai, kuma Hajiya Halima bata taSa yi mata magana akan hakan ba.

Anwar kam ya tattara yasa musu ido, ya maida hankali akan kula da Alhaji Nasir, kwata kwata ya dena shiga sabgarsu ma.

Abubuwa suka fara cakuWewa su Alhaji Musa, suka kuma hayar wasu 'yan ta' addan domin a nemo musu? su Me Adda, yayin da Alhaji Haruna ya keta tunani akan maganar da Saleh ya gaya masa game da tserewar Su Yusuf.

Meeting suke akai akai akan yadda zasu Sullowa al'amarin,
Alhaji Munir yace? "tabbas idan har yaran nan suka kuSuta suka dawo Asirinmu ze iya tonuwa"

Alhaji Musa yace "yakamata ku kwantar da hankalinku, babu yadda za'ayi Asirinmu ya tonu, yanzu naga Likitan nan yana aikin da muka sashi,? dan yanzu baya gane waye akansa sam"

Alhaji Haruna yace "hakane Daula ya zama abun tausayi, talakawan da yake fafutuka akansu, an hana kowa zuwa inda yake, manyan ?asar nan ma kowa yayi watsi da lamarinsa, yanzu haka nasa Jam'ian tsaro su hana kowa shiga inda yake, se Wan matar nan tasa, shi kuma wannan soko ne, ba abunda yake ganewa, shekaranjiya wasu ba?in turawa sunzo duba shi, amma an hana su ganinsa ance yana ?ar?ashin kulawar likita baza'a ganshi ba"

Alhaji Musa yace "Good hakanma yayi, a hana kowa zuwa inda yake muyi yadda muke so, Amma Nifa har yanzu ina mamaki akan guduwar yaran nan, kuma da suka kuSuta aida zasu dawo a gari a gansu, amma har yanzu babu wanda yaji Wuriyarsu"

Alhaji Munir yace? "ni kaina abunda yake Wauremin kai kenan, zuwa yanzu ai yaci ace anji labarin sun dawo, amma babu wanda yaji hakan"

Alhaji Musa yace "shiyasa nake tunanin akwai wata a ?asa ruwa baya tsami banza, akwai munafiki a cikin mu"

Alhaji Haruna yace "kamarya? Kana nufin a tsakaninmu munafikin yake kokuwa?"

Alhaji Munir yace "kunga ya isa haka, nima nayi zargin haka amma babu lallai da munafuki a tsakaninmu, sedai a wanda suke mana aiki tabbas, kokuma akwai wani a gefe daya ke farautar abunda muke nema"

Alhj Haruna yace? "ba abunda baze iya faruwa ba, Amma kar mu Wora komai akan zargi semun tabattar"

Kamar yadda Saleh ya bada umarni, aka ginawa Widad nata banWakin, akwai wata ?atuwar rijiya a gidan ruwan sam bashi da kyau, haka nan ake amfani dashi a gidan, ko kuma mutum yayi tafiyayyiya yaje rafi ya ?ebo.

Yusuf kuwa tafiya yake me nisa, yaje ya Webo ruwa a wannan borehole guda Waya tal ta garin, yazo gida ya tafasa idan ya huce seya zuba a randarsu suke amfani da shi a matsayin na sha.

Har yanzu Widad bata saba da kowa a gidan ba, ba ruwanta dasu sedai in sun haWu a tsakar gida suka mata sannu ta amsa, amma bata shiga sabgar Hari sam, saboda Hari ba?ar magana take gaya mata.

Yanzu ma tana tsugune tana brush da yamma, yaran Hari suka kewaye Widad suna kallonta, mussman dogon gashinta dake Waukar ido, gata ba ma'abociyar saka kallabi ba, abun haushi hadda 'yan matan gidan da suka tasa, se kallonta suke ita ta rasa se yaushe zasu saba da ganinta su dena mata wannan kallon haka?.

Widad tace "kai me kuke kallone, haba bana son kallon nan da kuke min, did i look like a beast?"

Hari tace "yo sunga abunda basu saba gani ba, kin fito tiSitiSi da wasu irin kaya ai dole su kalleki ni wallahi da ban zaci ma musulma ce ke kina jin hausa ba"

Widad tace "eh ba musulma bace ni, gunki nake bautawa yana Waki idan kina so ki ganshi"

Sam hari bata zaci Widad tana da baki hadda ba?ar magana ba.

Gwaggo tace "Amarya ?yaleta kiyi ha?uri"

Sannan ta kalli Hari tace "haba Hari, kin fiye magana wallahi duk ha?urin yarinyar nan kinsa ta fara tanka miki"

Hari tace "yo Yaya yara sunga abunda basu saba gani ba ba dole su kalla ba"

Yusuf yana ta tunanin wace sana'ar ze Wan fara, saboda ya saukewa mutan gidan Wawainiyar da'ake dasu, ga Widad bakomai take ciba duk ta rame, ya dawo daga sallar Azahar ya tarar an kawowa Widad gujjiya, tanaci hadda Sawon, Yusuf yace? "mekike ci ne?"

Ta Wan taSe baki tace "na manta sunanshi, amma inaga wake ne wannan maman ce ta bani"

Yusuf ya kwashe da dariya, ta haWe rai tana kallonsa, yace "haba Madam, wannan ne waken? Kuma da Sawo kike ci bari kiga"

Ya zauna yana Sarewa yana bata, ita tunda take bata san wata gujjiya ba, da taci a baki se taji kamar wake, ta zata ma wake ne yazo a haka.

Tun Yusuf yana mamakin bata san abubuwa da yawa ba, har ya dena mussman duba da yanayin rayuwarta, ita ba sakewa take da mutane ba, kuma mafi yawa a waje tayi rayuwarta, dan haka yake mata uzuri a wasu abubuwan.

Yusuf yace "Ina son in fara zuwa kasuwar garin nan, inga me zan fara siyarwa saboda mu ragewa mutanen gidan nan Wawainiyar da suke damu"

"dama akwai kasuwa a dajin nan?"

"daji kuma?"

"Eh mana" ta bashi amsa

Yusuf yace "eh akwai kasuwa amma se anyi tafiya me nisa sosai, nayi magana da megari ya haWani da yaronsa tare zamuje kasuwar gobe in Allah ya kaimu inga yanayin abubuwan"

Tace "Shikenan" tana ci gaba da cin gujjiyarta, seda ta gama ta kalle shi tace "Wanka"

Yusuf yace "to"? ya haWa mata ruwa sannan ya fita sallar la'asar

A gurin salla Yusuf yaga abun mamaki, akwai ?aramin gurin da suke jam'in salla, akwai ?arancin ilimi ga mutan ?auyen, liman ya makara wani yaja salla a raka'ar ?arshe liman yazo, raka'ar ?arshe kawai ya samu, itama an Wago daga ruku'u, da'aka idar Yusuf yana jira yaga liman ya tashi ya kawo wadda be samu ba amma yaga liman yayi ?yam yaja gefe yana laziminsa.

Yusuf ya dinga kallonsa ko ze tashi ya canza sallane, amma yaga aka jima liman ya shafa addu'a ya mi?e ya gaisa da mutane ya ?ara gaba.

Yusuf yayi shiru a ransa yace "wannan mutumin dabe san hukuncin salla ba, shine kuma yake jan salla? Tabbas akwai matsala babba, mutanen garin nan suna bu?atar ilimin Addini, ya barwa ransa cewa zeyi wa megari magana, yaga ta inda ze iya basu gudunmuwa.

Ya shiga cikin gida ya shiga Wakinsu da sallama, Widad ta fito daga wankan tana shafa mai, ba tare da ta kalle shi ba ta amsa ?asa ?asa, ta cigaba da abunda take.

Kusa da ita yaje ya zauna yana kallonta, duk cikin salon son yasa ta kula shi, dan idan har bashi yayi mata magana ba in zasu kwana idan ba wani abu take bu?ata ba, ba zata kula shi ba.

Tana jin yadda ya zauna daf da ita ya ?ureta da ido, kamar tasan maganar yake so tayi, ta?i magana.

Cike da fargaba dan yasan ze sha masifa, amma ya maze ya kai hannunsa gashin kanta yace

"wannan gashin yaushe rabonsa da a taje shi? Insha Allah idan na fara zuwa kasuwa? indai naga comb zan siyo, in taje shi da kaina"

Bige hannunsa tayi tace "wai kai meye haka? Me yasa kake son taSani ne? Na gaya maka bana son karka ?ara taSani na gaya maka, in ba haka ba duk abunda nayi maka kai ka siya, haba sekace baka da zuciya, ko baka gane magana"

Shiru yayi kawai yana kallonta yadda take ta masa masifa, shi yaga tana magana ma se yaji daWi a ransa, dan yaga ta rage yawan kukan da take yi.

Ga mamakinta murmushi yayi maimakon taga yaji haushi.

"kawo man in tayaki shafawa" yai maganar yana Waukar robar man, ?wacewa tayi tace
"bana so na gama"

Yusuf yace"Shikenan bari in baki guri kisa kaya"

"inma baka bani gurin ba baze hanani sa kayana ba"

Yayi murmushi ya mi?e cike da jin daWin yasa ta magana, bayansa tabi kallo yana fita ta ajiye abunda ke hannunta ta shiga goge hawayen da ita kaWai tasan dalilinsu.

Doctor Sufyan yana Office Winsa, yana jiran lokaci yayi ze shiga tiyata, wayarsa yaji ta fara ringin, ya tsaya ya Waga tareda yin sallama.

"Sufyan ne?"

"Eh nine"

"ina son ka kasa kunne ka saurareni dakyau, dukda nasan baka san dawa kake magana ba, hakan ya faru ne sakamakon sanin wanda kake maganar dashi a gurinka bashi da amfani, ina son ka saurareni da kyau kaji abunda zan gaya maka, kana jina ko?"

Sufyan yace "ina jinka"

"kamar yadda aka baka kwangilar sake kwantar da Daula, aka baka miliyoyin kuWi akan karya warke, kuma kayi dan tuni wani percentage ya shiga hannunka, to nima aiki nake son kayi min, niba kwantar da Daula nake so kayi ba, kawar da Daula nake son kayi!!!"

Mi?ewa doctor Sufyan yayi tsaye ya shiga waige waige karya je wani yaji abunda ake faWa masa a waya, cikin rawar murya yace "amm.. Ban gane me kake fada ba fa"

"?arya ka keyi ka gane, kuma kaji me nace tunda ka iya karSar kuWi kake bashi wrong treatment, to zaka iya karSar kuWi ka kasheshi, likita ne kai babu me zarginka, tunda kowa yasan condition Winsa yayi worse, bazance ga abunda zan bi yaka ba, sedai da kanka nakeso ka yanke abunda zan bi yaka "

Wani wahallalen gumine ya dinga ratsowa Sufyan, gumi yake ji har tsakanin cinyoyinsa, yace " Amma kisan Alhaji Daula hatsari ne, dole se anyi bincike akan gawar sa, don a tabattar da abunda ya kashe shi, idan aka ganoni fa, ina da iyali da ?ananan yara nasan kasheni za'ayi, Daula babban Attajiri ne"

"meye marabar abunda kake masa yanzu da wanda nace kayi masa, sanin kanka ne wrong treatment Winma ze iya kasheshi, baka da damar cewa ba zakayi ba, saboda na maka tarko ta ko'ina, ina da duk yadda akayi ka karSi kuWi kake bashi wrong treatment, duk wata hujja daza'a kamaka ina dashi, idan kuma naga dama zan saka Wauke Waya daga
'ya' yan naka ko kayi ko kuma ransa ya salwanta, zaSi ya rage naka, sannan idan kaga dama ka gayawa wani"

?it aka katse kiran, gaba Waya doctor Sufyan yaji kamar an zare masa laka, jikinsa se rawa yake ya duba wayarsa yaga anyi hiding Win lambar, dan ko unknown number be fito ba,? duk sanyin Ac dake office Win shi gumi yake, kamar wanda ya tu?a tuwon gidan biki a tsakae rana.

Yau da wuri Yusuf ya shirya, dan zebi Wan megari kasuwa, Wan megarin shima matashi ne be kai Yusuf ba, a bayan gidan megari nasa gidan yake, da matarsa da 'ya' yansa shida.

Har Yusuf ya gama shirinsa, aka kawo musu Abincin safe Widad bacci take, a hankali ya ?arasa gaban katifarta ya janye bargon jikinta, bacci take hankalinta kwance, se yarintarta ta sake fitowa ta ?ara kyau a idon Yusuf, yayi shiru yana kallonta.

A hankali ya Wan daki pillow Win da take kai, amma bata motsa ba, ya sake taSa pillow amma still bata motsa ba, hannu yasa ya Wan daddaki nata hannun, kamar me tashin ?aramin yaro, juyi tayi amma ta?i buWe ido.

"Widad" karo na farko a rayuwarta data ji ya kira sunanta, taji zuciyar ta ta buga da ?arfi, ta buWe ido ta kalle shi

Yace "ga breakfast an kawo karya huce, kuma inason zan fita ni"

"shine zaka wani dur?uso kaina haka? Kamar zaka shige cikina"

"ke komai nayi miki lefi ne? To sorry tashi karya huce kinji gimbiyar..

Kallonsa take taji meze ?arasa, maimakon ya ?arasa se yayi murmushi yace "tashi kije kiyi brush, muci Abinci "

Ta mi?e ta Wau brush tayi waje, Yusuf ya gyara mata shimfiWa, ya gyara Wakin.

Widad ta fita tsakar gida, gwaggo tace "Amarya ina kwana"

Widad tace "lafiya ?alau"

Gwaggo tace "Alhamdilillah ya ?arfin jiki?"

"Naji sau?i"

Gwaggo tace? "to madalla"

Hari ta ?urowa Widad ido tana so tayi magana, Widad tace?

"idan baki dena kallona ba, sena saka butar hannuna na? Sallo miki wannan ha?orin da yake le?owa idan kina magana"

Hari tace "ke hudas kike ko wudas, yau dai ban kulaki ba balle ace na shiga harkarki"

Widad ta Harareta ta wuce banWakinta.

Data fito ta manta da batun Yusuf dake jiranta, ta tsaya gurin da take le?en zomaye.

Seda tayi me isarta, sannan ta koma Waki.
seda taga Yusuf sannan ta tuna ashe ita yake jira suci Abinci, yace? "naga kin daWe?"

Kai tsaye tace "kallon zomaye nayi" , ta ajiye kayan brush Winta, tazo ta zauna ta buWe kwanon farko, dakakken ?uli ?uli ne a ciki, ta rufe ta buWe Wayan dafaffen dankalin hausa ne a ciki da Sawonsa da komai manya guda uku.

Ta kalli Yusuf tace "meye wannan?"

"Dankali" ya bata amsa

"kuma a haka? Ta yaya za'aci"

Yusuf yace "ga mahaWin nan ?uli?uli a wannan kwanon"

Widad tace "ta yaya za'aci wannan abun ba tea?"

Yusuf yace? "seki kora da ruwa" yai maganar tare da fara Sare dankalin.

ta zuba masa ido, ya Sare tsaf ya yayyanka shi a kwano, ya Webo ruwa ya ajiye mata yace? "bismillah"

Tsayawa tayi tana kallonsa kamar wata sokuwa, ya Wakko Waya ya dangwala da ?uli ?uli ya kai bakinta, Wauke kanta tayi tasa hannu ta karSa tasa a bakinta.

Ba zata ce babu daWi ba, sedai gurin haWiyewa ne da?yar take yi, dan kasa haWiyewa tayi seda ta haWa da ruwa.

Dan haka shima ba taci dayawa ba tace ita bazata iya cin wannan abun ba, sha?e mata wuya yake.

Yusuf ne yaci sauran, sannan yayi mata sallama ya tafi.

Sufyan abun duniya ya dameshi, ya rasa inda ze saka ransa, ba ?aramin hatsari bane kashe shahararren mutum kamar Daula, amma kowa se saka rayuwarsa yake a hatsari saboda suna ta?amar suna da kuWi, shiba abun ya kaisu gurin 'yan sanda ba, shi ze kwana a ciki.

Gaba Waya daren nan yakasa bacci, sedai juyi dafa da Asuba aka kuma sake kiransa, bashi da zaSin daya wuce ya amsa wayar.

"baka da isasheshen lokacin Satawa gurin aiwatar sa wannan aikin, kana da yau zuwa gobe in Allah ya kaimu ne kawai, idan baka yi ba ni zan aikata maka abunda nace"

Aka katse layin, Doctor Sufyan yayi jifa da wayar ya dafe kai, matarsa ta lura da yana cikin damuwa ta tambaye shi ko lafiya, yace mata babu komai.


Widad bata taSa shiga damuwa ba, tsawon lokacin data Wauka tana rayuwar kaWaici a rayuwarta se wannan karon, tunda Yusuf ya fita be dawo ba taji gaba Waya duniyar ta mata faWi, gashi ita bata saba da kowa ba se shi, seta ji ta wani iri kamar ita kaWaice

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login