Showing 111001 words to 114000 words out of 135555 words

Chapter 38 - AKIDATA book 1 HAUSA NOVEL

17 Jan 2026

658

a duniyar, koba komai ganin motsinsa yana rage mata damuwa.

Yau wuni guda tana Waki, ba wanda yake shigowa inda take, saboda bata da fuskar daza'ayi mata hakan, bayan tayi sallar la'asar yunwa ta isheta ta fito tsakar gida.

Gwaggo tace "Amarya lafiya dai ko?"

Widad tace "Naga har yanzu Yusuf be dawo ba kuma ni yunwa nakeji"

Gwaggo tace? "Allah sarki, yau Harice da girki bata aiko miki da Abinci ba kenan"

Widad tace? "kota aiko ba zanci ba, dan ?azama ce"

Hari dake salla a tsakar gida ko sallamewa ba tayi ba tace "jar'uba kekam anyi mara albarka, nice ?azamar?"

"Eh kece ?azama, kalli zanin jikinki kalli faratanki, hijjabin jikinki ma me datti ne, sekiyi abu ki bani inci, an gaya miki komai nake ci?"

Wato Widad sam ta dena ragawa Hari, gwaggo tayi murmushi tace "Yanzu to me zakici?

Widad tayi shiru ba tace komai ba, gwaggo tace? "Akwai Furar megari dana dama, bari in Webar miki"

Widad tace "Nagode"

Hari tace "Furar malam Win zaki Wiba ki bata? Lallai Yaya akwaiki da neman gindin zama"

Widad tace "Eh ita za'a ban, ba zanci Abincinki ba"

Gwaggo dai ba tace komai ba, ta Webowa Widad fura a kofin silba ta bata, ta samu guri ta zauna tana sha.

Furar tayi za?i zau da zumar da'aka zuba a ciki, tana cikin shan furar can seta mi?e tsaye, gwaggo tace? "kin ?oshi ne?"

Widad tace? "A'a Yusuf na ragewa"

Hari tace "Ohh ni jikar Hama, ji wata fitsara take cewa ta ragewa mijinta abu"

Wasu matane suka shigo su Uku, Waya 'yar babba biyu kuma 'yan mata da sallama suka shigo, Hari tace
"Ahh marabanku da dawowa, wai an sha suna"

?ayace ta kalli Widad tace? "Hari wace wannan?"

Hari tace? "wasu ba?ine mukayi"

?ayar tace? "kalleta kamar balarabiya"

Widad bata tanka musu ba ta koma Wakinta.

Sukam bajewa sukayi a tsakar gida, Wayar itama matar megari ce hansai, se 'yan matan Hindu da Hanne, suma' ya'yansa ne sunje wani ?auyene, inda 'yar megari take Aure ta haihu.

Se bayan la'asar Yusuf ya dawo gida, kallo Waya zakayi masa kasan a gajiye yake, ya gaisa da mutanen gidan ya shiga Wakinsu.

Ba sannu da zuwa bakomai Widad tace "Shine ka?i dawowa se yanzu?"

Yusuf yace yanzun ma tun Wazu na taho, akwai nisane sosai.

Ya ajiye kayan hannunsa, yaje yayi wanka, a Waki yayi salla saboda gajiya ya nemi guri ya kwanta yayi shiru.

Widad tace? "to ni dai gaskiya ka dinga dawowa da wuri, kawai seka tafi ka barni nikaWai, gaba Waya nagaji"

Yusuf ya kalleta yace "Aikin me kikayi kika gaji?"

"Aikin zama ba abunda nake, ba kowa a Wakin nan seni kaWai"

"Amma ai da mutane a gidan, seki fita kuyi hira"

"Ni gaskiya dana fita wannan me ha?oran take min rashin mutunci, nikuma ramawa nake"

Yusuf yace? "Kidinga ?yaleta, kinga babbace ba sa'arki bace ta girmeki"

"da alama ka manta Widad Nasir Daula ce ko?"

Yusuf yace "ya za'ayi na manta nina isa? Yau ba'a kawo komai bane yunwa nake ji"

Widad ta taSe baki tace "wannan ?azamarce tayi girki, ni kuma nace ba zamu ciba, shine Mama ta bani furar mijinta"

BuWe baki Yusuf yayi yace "ba dai ce mata kikayi ?azama a gabanta ba?"

"idan na gaya mata zata cinye nine?"

Yusuf ya dafe kai, ita Widad a rayuwar ta bata san kara ko alkunya ba sam.

Ta Wakko kofin furar nan tace? "gashi nasha na rage maka"

Yusuf????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 
yace "dagaske ragemin kikayi?"

"is there anything special, dan na rage maka?"

Yusuf yace a"a a ransa kuma yace "lallai kin damu dani"

Yusuf yace? "Naje kasuwa, naga abubuwa ana saye da siyarwa ba laifi, Wan megari ze aran kuWi, inga me zan fara siyarwa, ranar daba kasuwa kuma naje wani gurin inga me zanyi"

"to duk meye na wannan wahalar?, naga dai barin gurin nan zamuyi"

"A'a yakamata in koma ciyar dake da kaina, da duk bu?atunki be kamata mucigaba da Wora musu Wawainiya ba, nauyinki a kaina yake yanzu"

Kallonsa tayi tace "don't bother yourself, wannan fa ba Aure neba"

"meye inba Aure ba?"

Tace "Shiri mana"

Yace "Ba ruwan Allah da shiri, kuma koda shirin ne aini yakamata in kula da Gimbiya ta"

"karka ?ara cemin gimbiyarka"

Yusuf yayi murmushi yace "Lokacin da muna gida gimbiyar Daddy ce, yanzu kuma da muke nan ba wanda kika sani seni, dan haka gimbiyata ce"

Tsaki tayi ta mi?e daga inda take zaune, Yusuf yace? "Komai naki me kyau ne Widad"

Ko Kallonsa ba tayi ba tayi masa shiru, yace? "ga Al?awarin da nayi miki, na samo comb da ?yar a kasuwa, yaushe zamu gyara gashin namu?"

Ficewa tayi daga Wakin ta barshi, shi kuma ya dinga murmushi ganin takaici ya hana ta magana, Yusuf yace da haka da haka gimbiya"

Sufyan fa hankalinsa gaba Waya ya gama tashi, ya hanga yaga bashi da wata mafita data rage masa banda ya aikata abunda akace, ya haWa allurai a cikin syringe ya zauna ya zuba musu ido, gabansa nata dukan biyar biyar, kiransa akayi a waya, hannun narawa ya Wauka

"Ka shirya aiwatar da aikinne ko kuwa?"

Cikin jan numfashi Sufyan yace? "Eh na shirya"

"shikenan, ina jiran sakamako a yau, ka duba wayarka zakaga Alert Win kuWi"
Sufyan bece komai ba ya ajiye wayar yana yakice gumi.

Zuwa yanzu Widad ta fara dangana, ta Wan fara sabawa da halin data tsinci kanta a ciki, Cikin dare Widad tana bacci tayi juyi, hasken farin wata ya hasake Wakin, ta hangi Yusuf a zaune akan shimfiWarsa yayi tagumi,
Da alama tunani yake.

A ranta tace? 'Ashe shima yana damuwa, amma ya dinga basarwa yace nize hanani kuka'

"wai tunanin mekake?"

Firgigit ya dawo hayyacinsa, yace "idonki biyune?"

"A'a mafarki nake na maka magana"

Yusuf yace "hmm ba tunani nake bafa, cinnaka ne ya cijeni na kasa bacci"

"yaushe ka fara ?arya?"

"dagaske nake" yai maganar tare da mi?ewa ya fita waje, Alwala yaje ya Wauro yazo ya tada salla, Widad kam baccinta ta koma.

Yusuf yana cikin sallar ne yaji A gigice Widad tace? "Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, wayyo Allah Daddyna"

Ta mi?e da gudu tayi hanyar waje





(Up Up masoya littafin A?IDATA, Comments Winku na matukar ?ayatar dani, shike bani ?warin gwiwa nayin posting, Allah ya bar ?auna =?
? =?
? =?
?)

Share, share and share please =?O? =?O? =?O?
Domin gyara, sharhi ko shawara
Ayshercool
07063065680

? ? ? ?? _*A?IDATA*_
? ? ? ?

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA _
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*A?IDA TA *

I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum

Ha??in Mallaka ?& : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ?unsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani Sangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

NOT EDITED

ELEGANT ONLINE WRITER'S

? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ?? PART1
? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? Page 36_37

Ri?eta gam Yusuf yayi, yayin da ta cigaba da fizge fizge tana kuka, a hankali Yusuf ya zame ya zauna da ita a jikinsa, ya toshe mata baki, saboda dare ne nan da nan sautinta ze iya cika ko'ina.

Yusuf yace "Widad, ki nutsu mana darene yanzu karkisa hankalin mutane ya dawo kanmu, mafarki kikayi fa"

Girgiza masa kai ta shiga yi, cikin kuka tace "is not just a dream, wani abu na shirin faruwa da Daddyna, ka ?yaleni inje in ganshi, wani abu ze sameshi"

"yanzu idan kika tafi ina zaki? Daddy Addu'ar mu yake bu?ata, tun Wazu nan salla nake ina mana addu'a muda iyayen mu, Insha Allah babu wanda ze iya cutar dasu, kuma Saleh ya cemin ya gaya masa muna nan tare, kidena kuka"

Girgiza kai take tana kuka tace "Daddy na, shikaWai ya ragemin bani da kowa, bana son in rasa Daddyna, idan na rasa Daddy babu sauran me ?aunata sedai dukiyar daze bari, wayyo Allah Daddyna, ya Allah secure my Dad, Allah yasa in koma in tarad da kai a raye"

Gaban Yusuf ne ya faWi, ya tuna abunda Saleh ya gaya masa game da mahaifin Widad.

Kuka take sosai jikinta har rawa yake, ga wani irin gumi daya rufe ta, Wora hannunsa yayi a saman ?irjinta, se bugawa zuciyarta take da ?arfin gaske.

Yusuf ya shiga karanta mata dukkan Addu'ar da tazo bakinsa, a hankali zuciyarta ta rage bugawa da sauri da sauri, can kuma bacci ya Wauketa, ta shiga sauke Ajiyar zuciya.

Yusuf ya mi?e a hankali da ita, ya kaita kan katifarta ya rufe ta da bargo, ya koma ya sake alwala ya cigaba da sallar sa.

Alhaji Musane keta sintiri a cikin Wakinsa, se safa da marwa yake ya kai gwauro ya kai mari, ya rasa abunda yake masa daWi, sosai maganganun Saleh sunyi tasiri a zuciyarsa, sosai zargi ya Warsu a ransa cewar a cikinsu akwai wanda ya zame yake shirin cin amanarsu, kamar yadda ya zame a baya yaso ya haWa kai shida Alhaji Bukar.
A fili ya furta dole? "inyi wani abu akai"

Juyowa yayi yaga Nurat a tsaye a ?ofar Wakinsa da tray Wauke da kayan marmari a ciki, a fusace yace "dan uwarki laSe kika koma Yimin ko?"

Cikin dakewa tace "meyasa zan maka laSe kuma Daddy, tun Wazu nake sallama amma baka amsa ba"

"Kuma shine seki tsaya ki laSe?"

"Daddy bafa laSewa nayi ba"

"zoki ajiye kayan nan ki fita ki ban guri"

Nurat taje ta ajiye masa tray Win ta fita, gaba Waya Nurat ta lura mahaifinta a kamar a ruWe yake, akwai abunda yake damunsa, zata so sanin abunda yake damunsa, dan wata?ila yana da ala?a da har?allar da suke ?ullawa akan Alhaji Nasir da iyalansa.

Bayan sallar Asuba yau a masallaci, Yusuf ne ya tsaya ya Wanyi wa mutanen ?auyen Nasiha akan neman ilimin Addini, ta hanyar janyo musu ayoyi da hadisan manzon Allah salallahu alaihi wassalam, be fito yace musu basu da ilimi ba, amma a cikin bayanin da yake musu ya kawo musu misalin yadda mutum ze kawo raka'oin daya rasa idan yazo bin jam'i, nan suka dinga gano irin tafka tafka da kwaSar da suke yi.

Wani mutum yace "gaskiya Malam Yusufa munji daWin wannan bayanin naka, danni harga Allah na ?aru da abubuwa da dama, danni wallahi na zata idan mutum yayi alwala in yayi tusa indai ba tayi ?ara ba to bata karye ba"

Na kusa dashi yace "Nikuma wallahi na zata ko sujjada ka samu in ana salla shikenan ka samu salla, dan Allah yakamata ka cigaba da yi mana wannan bayanin idan anyi sallar Asuba ko kuma da daddare mudinga taruwa anan kana ?ara fahimtar damu abubuwa"

Megari yace? "hakane kam, Yusufa idan bamu takura maka ba, muna bu?atar hakan"

Yusuf yace "Ai babu batun takura ranka ya daWe, mafi alkairin mutane shine wanda yasan ilimi kuma ya sanar dashi"

Seda gari yayi haske tukuna suka watse, suna mamakin kurakuran da suke aikatawa a sha'anin addininsu.

Yana shiga gidan yayi karo da wata budurwa tana koro dabbobi daga turke zasu fita kiwo, tana ganin Yusuf tayi turus tana kallonsa, har Yusuf ze wuce tace masa "Ina kwana"

Yusuf yace? "Yawwa lafiya ?alau sannunki"

Yai gaba abunsa, ?ura masa ido tayi harya wuce ya shige Wakinsu, anan ta tabattar da cewa shine mijin wannan farar matar me gashi.

Da sauri ta koma Wakinsu, tana kiran "Hindu, Hindu"

Hindu dake sharar Waki tace? "lafiya kikemin wannan kiran?"

Hanne tace "kinga mijin wannan farar matar nan ta jiya kuwa?"

"me yayi?" hindu ta tambaya

"innalillahi, wallahi ban taSa ganin namiji me kyau kamarsa ba"

Hindu tace "har LamiWon rigarsu gwaggo?"

Hanne tace? "wallahi harshi, taS bakiga kyau ba masha Allah, ban taSa ganin namiji me kyansa ba"

Hindu tace "bakiga matarsa bama, fara me kyau"

Hanne tace "dalla wannan da gani bata da mutunci, kinga kallon da tayi mana jiya kamar taga kashi, da gani bata da mutunci"

Hindu tace? "ke Hanne karkice haka, aikinga bata sanmu ba"

Hanne tace? "ke dallacan Allah yasa in kuma ganinsa"

Yusuf ya shiga Waki ya tarar da Widad a zaune, ya kalleta yace? "ina kwana?"

Kallonsa tayi kawai ba tace komai ba, Yusuf yace "Munyi magana da Wan megari na bashi kuWi, zeje cikin gari ze siyo miki kayan tea da sauran abun bu?ata"

Ita dai ba tace komai ba, sema lumshe idanunta da tayi.

"wai meke damunki ne kuma?"

"Bakomai"

"zakiyi wanka ne? Ina son zan fita"

Tace? "kaje kawai, zanyi komai da kaina"

Yusuf yace "Aini tsoron fitarma nakeji, jiya da daddare ki tsoratani sosai, kar in fitane kema kice zaki tafi"

Shiru tayi masa ta ?ara rufe idonta, "Widad" ya kira sunanta, a Wan hasale tace? "meye ne?"

"Inaga bari in ha?ura da fitar nan, bari inje inyiwa abokin tafiyar tawa magana se in dawo"

"Nifa ban hanaka tafiya ba, ba inda zani jiyanma na tsorata ne mafarkin da nayi"

Yusuf yace? "dagaske idan na fita bazaki tafi ki barni ba"?

?agowa tayi tana kallon cikin ?wayar idonsa, ta jinjina masa kai alamar eh, yayi murmushi yace?

"to bari inje in wanke mana kwanuka, in wanke miki banWaki se in tafi, sena dawo, in a kawo abun karyawa kiyi breakfast Winki kawai, base kin ragemin ba"

Yai maganar tare da mi?ewa ya fice, ya kwashi kwanukan ya zuba ruwa, Hanne ce ta hango Yusuf da kwanuka, ta taho da sauri tace
"kawo in wanke maka"

Yusuf yace "A'a bakomai nagode, yanzu zan wanke in gama"

"dan Allah ka kawo, ai be kamata kayi wanke wanke da kanka ba, idan Baffa ya gani ma ze iyayi mana faWa"

Yusuf yace "kema 'yarsa ce ne?"

Hanne tace? "eh nima' yarsa ce nida Hindu, muje wani ?auyene suna, se jiya muka dawo"

Yusuf yace "Allah sarki, Allah yayiwa rayuwar ku Albarka"

Cike da jin daWi Hanne tace? "Ameen" ta karSi kwanukan, yace? "in kin gama, seki kai mata Wakin"

Hanne tace? "to" tana mamakin ace yana da mata amma shize wanke wanke, Yusuf ya janyo ruwa a rijiya ya wanke banWakinsu, yayi wanka ya fice.

Hanne ta gama wanke wanke, ta tafi ?ofar Wakinsu Widad, ta tsaya tana sallama, ?asa ?asa Hanne ta shiga Wakin ta cewa Widad "ga kwanuka inji mijinki"

"Ajiye anan"
Hanne ta ajiye, ta juya ta fita tana mamakin wannan irin nuna isa na Widad.



Anwar ya gayarawa Daula jikinsa, ya canza masa kaya ya bashi Abinci da sirinji, ta cikin robar dake hancin Daula, ya gyara Wakin ya tattara kayansa marasa kyau ya fita ze bayar akai gida su Nura su wanke.

Sufyan ne ya tinkari Wakin da Alhaji Nasir yake, gaban sa se faWuwa yake, ji yake kamar kowa kallonsa yake a baranda ya haWu da Anwar, suka gaisa da Anwar, doctor Sufyan yace? "ina zaka haka Anwar? Kasan bama san ana barinsa shi kaWai"

Anwar yace? "yanzu zan koma, kayan nan na fito dashi zan kaiwa direba ya kai gida a wanke"

Sufyan yace? "to masha Allah, ga wasu magunguna na rubuta, idan ka kai kayan wankin seka biya pharmacy ka siyo"

Suna nan tsaye aka fito da wani mutum ya mutu an turo shi a gado za'a fita dashi.

Anwar yace "doctor, dan Allah nasan lafiyar Alhaji ba a hannunka take ba tana hannun Allah, dan Allah ka ?ara ?o?ari, bawan Allah nan kullum jikinsa ?ara rikicewa yake"

Sufyan ya dafa kafaWar Anwar yace "karka damu Anwar, kamar yadda ka faWa sau?i na Allah ne, Amma muna fatan Allah ya bawa Daula lafiya"

Anwar yace "shikenan nagode, bari inje"

Anwar yayi gaba, Sufyan ya tsaya a gurin yayi shiru, sannan yayi gaba jikinsa gaba Waya babu ?wari, a haka ya taka har yaje ?ofar Wakin da Daula yake, yasa hannu ya murWa ?ofar ya shiga, sedai me yana shiga yaga wayam ba kowa akan gadon, ya ?arasa gaban gadon da sauri ya yaye bargon kai, ba Daula babu alamarsa, ya buWe banWaki ya duba nan ma kowa, ya duba bayan ?ofa zuwa ?ar?ashin gado, amma be ganshi ba ?arewa har fridge ya buWe amma bega alamar Daula ba.

Cire gilashin dake idonsa yayi yana zazzare ido, yana waige waige kamar ?arawo

Fitowa yayi da sauri daga Wakin, aikuwa yayi karo da Anwar, Anwar yace "doctor Sufyan ya dai? Naganka a haka? Na kawo maganin"

Doctor Sufyan yace "Amm... Mmm.. Nace ina Mara lafiyar ne?"

Anwar yace? "kamarya? Yana ciki mana"

Sufyan yace? "Baya nan na duba ko ina ban ganshi ba"

Anwar yace? "kamar yaya? Ya za'ayi in fita barshi, daga zuwa siyo magani kace baka gasnhi ba? Sekace wata eiga, mutumin da komai sena masa ta yaya ze iya fita?"

Sufyan yace?? "Nima abunda ya bani mamaki kenan, na duba ko'ina ban ganshi ba, har banWaki na duba baya nan"

Kallon tuhuma Anwar yayiwa Sufyan yace "Amma gaskiya ni ina tantama, babu wanda ya shiga Wakin bayan fita ta sekai"

Sufyan yace "Wallahi ban tarar dashi a Wakin nan ba kaji na rantse"

Anwar ya Waga waya ya kira 'yan sanda, ya kira ya sanar da Bulama abunda ake ciki.





Widad ta gaji da zaman Waki, ta fito tsakar gida ?ar?ashin bishiya ta zauna, yaron gurin hansai ne da baze wuce shekaru uku ba, yake ta kallon Widad yana le?a gashin kanta, murmushi Widad tayi tace "Naga kana son gashin nan, zo in baka ka taSa"

Tsayawa yaron yayi yana murmushi, a hankali ya ?araso inda Widad take, ta ri?e hannunsa ta Wora akan gashinta, nan yaron ya shiga wasa da gashin nata yana dariya.

Hansai data fito taga abunda yake faruwa, tunda suka dawo suka tarar dasu Widad, ko sannu bata taSa haWasu ba, ko murmurewa bata taSa ganin tayi ba, Hausawa sukace me Wa wawa se taji daWin yadda Widad take wasa da Wan nata.

Hindu data fito tsakar gidanma, tana ganin haka ta ?araso tace "kai Sani sakar mata gashi mana, ya takura miki ko?"

Widad tace? "A'a nibe takura min ba, naga yana son kamawa ne shiyasa nace yazo ya taSa"

Hindu tace "Abunka daba'a saba ganiba shiyasa yazo ya saki gaba"

Widad tayi murmushi har ha?oranta suka fito tace? "gashin ne ba'a saba gani ba, bayan duk kanku ba'a aske yake ba"

Hindu tace "to ai ganin gashi me yawan naki dai basu saba gani ba, kuma dan Allah ke 'yar ?asar nan ce?"

Hansai dake ?o?arin haWa wuta tace "wallahi nima abunda ke bani mamaki kenan, dan Allah' yar ?asar nan ce ke?"

Widad tace? "taS 'yar ?asar nan ceni mana, banyi kama da Hausawa bane"

Hindu tace "gaskiya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login