Showing 93001 words to 96000 words out of 135555 words

Chapter 32 - AKIDATA book 1 HAUSA NOVEL

17 Jan 2026

668

mafaka"

?an lumshe ido tayi sannan tace "Na gaji jikina ciwo yake, hannuna zafi kaina ze fashe, Wayyo Allah Daddy na"

Yusuf yace "kiyi ha?uri insha Allah komai ze daidaita, zakiji sau?i mun taho da magunguna"

Shiru tayi ta sake kwantar da jikinta a ?irjin Yusuf, hawaye na bin gefen idonta.

Tun Yusuf yana sa ran tafiyar ta ?are har yayi shiru ya zubawa sarautar Allah ido.

A hankali Yusuf ya fara ganin gidaje? tsilla tsilla a gurin, gine gine na tsurar ?asa haka Gidajen suke, wasuma ko katanga babu a haka suke, yayi mamakin wannan irin ?asurgumin ?auye haka da yadda mutane ke rayuwa a cikinsa, suka baro duk bakin hanya suka shigo wannan sur?u?in guri sukayi ginin Gidaje.

A hankali suna cigaba da tafiya, yaga ?auyene sosai me Wauke da gidaje da mutane a ciki, sedai sunyi hannun riga da duk wani abun more rayuwa da jin daWi, kama daga Makaranta, Asibiti, ko wani abu me kama da borehole tunda suka shiga ?auyen Yusuf be ganshi ba.

A ?ofar wani babban gidan ?asa, an shafawa ?ofar gidan farar ?asa, alama dai mamallakin gidan yana ri?e da wata sarauta ne a ?auyen.

Saleh yace "Yusuf ina zuwa"

Ya sauka daga motar ya shiga cikin gidan, Yusuf yana ta ?arewa gurin kallo yana tunanin anya Widad zata iya rayuwa a cikin gurin nan?

A hankali yaji tace? "Ka yadda da Saleh, kana da tabbacin shima ba cutar damu zeba?"

"Ko ban yadda dashi ba, Allah baze bashi damae cutar damu ba, nidai fatana inga kinji sau?i gaba Waya"

Ajiyar zuciya tayi, tai shiru ba tace komai ba can Saleh ya fito shida wani dattijon Mutum, kansa Wauke sa rawani.

Suka ?araso gaban akori kurar, dattijon yace "sannu dai Wan samari"

Yusuf yace yawwa Baba, barka da yamma

"Yawwa barka" mutumin ya kalli Saleh yace? "sune wannan?"

"Eh sune wanda na gaya maka, ina son su zauna a gidanka na wani lokaci, kafin komai ya lafa su koma"

"Amma kana ganin babu wata matsala Saleh, nifa bana son abunda zezo ya Wagawa Al'ummar garina hankali, kasan ku mutan binni se a hankali"

Saleh yace "Haba dai, wane irin matsala taimako zakayi, baka ga yadda suke a galabaice ba, babu wata matsala insha Allah"

"Shikenan, shigo dasu se a kaisu Wakin daka gyara musun"

Yanzu ma Widad ba zata iya tafiya ba, Yusuf ne ya Wauke ta zuwa cikin gidan.

Duk da rabi tana hayyacin ta rabi bata hayyacin ta, tana mamakin mutane ne ke rayuwa a wannan gidan, roofing gidan kansa na Azarane, ta dinga kallon roofing tana tunanin menene wannan?
Yayin da wasu Wakunan roofing danga ne.

Tunda suka shigo gidan, mutan gidan maza da mata suka fito suka yi cirko cirko kamar zakaru suna binsu Yusuf da kallo kamar sunga ba?in halitta.

Wani Wakine a can ?arshen gidan, Saleh yasa mukulli ya buWe ?ofar katakon dake Wakin ya shiga yacewa Yusuf "bismillah"

Ba lefi Wakin yana da girma amma ba sosai ba, yana da taga guda Waya wadda akayi ta da katako da kuma langa langa, Wakin ginin ?asa ne tsura, sedai anyiwa ?asan floor, aka shimfiWa buhu a ?asa sannan aka kawo tabarma duk aka shimfiWa.

Akwai matsaikaciyar katifa a shimfiWe a ?asa, da bargo guda biyu se fula guda Waya duk sababbi.

Gefe ga tulu, da wani ?aramin kwandon kwanuka da 'yan kwanuka a ciki, gefe ga sababbun bokitai guda biyu, da sabuwar buta.

Akan katifar Yusuf ya kwantar da Widad, da duk inda ya motsa ta ciwo yake mata.

Dattijon yace? "wannan bata da lafiya ne haka?"

Saleh yace "Eh bata da lafiya, a hannun masu garkuwa fa na karSo su, na maka bayanin komai, dan Allah Baba a kula dasu, duk abunda suke bu?ata ayi musu"

"Shikenan, indai nine baka da matsala, ko baka kawo kowa ya zauna a gidan nan ba, gidan nan na jama'a ne, Allah ya basu lafiya"

Ya juya ya fita, yana kora yaran da suka yi dandazo a ?ofar Wakin suna le?en su Widad.

Idon Yusuf ne ya sauka akan akwatunan Widad data shirya domin tafiyar da zasuyi, da traveling bag Winsa da suka bari a motar da'aka sace su.

Yusuf ya zare ido yace "Nifa Saleh ina bu?atar kamin bayanin abubuwa, ya akayi ka samu jakunkunan mu na tafiya? Ya akayi kasan idan muke kaje ka tseratar damu?"

Saleh yace? "Nasan zakayi mamaki, kuma dole ku tambaya, Amma yanzu ina sauri saboda zan koma kano kar su gane wani abu a ?asa su fara zargina, duk yadda aka shirya sace ku dani akayi shi, Tun bayan sace ku ni kuma na fara shirin yadda zaku tsira, amma ka sani koda wasa karka kuskura kayi gangancin barin ?auyen nan in bani na fita daku ba, dan wallahi suka ganku sekun kasheku"

Yusuf yace "wai tsaya, wai inane nan ma tukuna?"

"Nan wani ?auye ne a cikin garin Bauchi, Zan dinga zuwa ina duba ku, a waccan jakar na ajiye muku abubuwan da ba'a rasa ba da zaku bu?ata kafin ku saba da irin rayuwar da suke yi, ga kuma kayanku can dana kawo nan, nan gidan ?anin kakana ne dan haka insha Allah baku da wata matsala, idan ma dawo za kaji komai "

Saleh ya fita tsakar gida ya kalli wata dattijuwa yace "Gwaggo dan Allah Amana nan, a kula da ba?in nan dan manyane duk abunda suke bu?ata ayi musu"

Gwaggo tace? "Lallai kam, ba?in suna da girma a gurinka, tunda sanadinsu gashi kana le?o mu"

Wata mata a tsakar gidan tace "Eh aimu da yake cinyesu zamuyi shiyasa ba'a bamu amanar ba?in ba se ita"

Saleh yace "Aifa kedai halinki yana nan bazaki canza ba" yayi gaba abunsa, ya tafi gurin me gari suka sake tattaunawa sannan ya tafi.

Haka Saleh ya tafi ya bar su Yusuf a cikin wannan ?asurgumin ?auye.

A hankali Widad tayi juyi, ta ?arewa Wakin da take ciki kallo, wai anan zata zauna ita da suka zo sam bata zaci wai nan mutane ne ke rayuwa a cikin gurin ba se yanzu.

Yusuf yaje yayo Alwala, yazo ya tada salla sedai duk inda yayi se mutanen gidan su bishi da kallo.

Widad ta cire hijjabin jikinta, jikinta se faman ?ai?ayi yake mata, Yusuf ya idar da salla zeyi magana ta riga shi ta hanyar cewa "zanyi wanka"

?an zare ido yayi yace "to shikenan, bari inwa mutan gidan magana"

Ya fito tsakar gidan, yaga wadda Saleh ya kira da Gwaggo Wazu tana ta aiki a tsakar gida, yace mata? "dan Allah Mama ko zamu samu ruwan Wumi, mara lafiyar zata yi wanka, nikuma ko na sanyi ne na samu se inyi Amfani da shi"

Tayi murmushi tace? "bakomai, na zuba ruwan tuwon dare dama, bari in Wibar maka"

Yusuf yace? "to nagode"

Ya tafi Wakin su, ya Wakko sabon bokiti, aka zuba ruwa aka sirka Yusuf ya koma Wakin yace? "An haWa ruwan"

Ta tashi zaune ta fara kiciniyar cire rigar jikinta, sedai hannunta na hagu shine wanda aka harbeta, na dama kuma ya???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?na ciwo saboda duka da wahalar mota.

Yusuf ya juya mata baya da nufin ta kintsa ya kaita banWakin.

"Zoka tayani cire wannan rigar na kasa cirewa....

(Akwa ?ura fa=ض? =ض? =ض? =ض? =ض?)

Share, share and share please =?O?

Domin, gyara sharhi ko shawara
Ayshercool
07063065680

?? ? _*A?IDATA*_
? ? ? ?

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*A?IDA TA *

I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum

Ha??in Mallaka ?& : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ?unsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani Sangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

ELEGANT ONLINE WRITER'S

? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ?? PART1
? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? Page 28_29

Gaba Waya dirircewa Yusuf yayi, se yayi kamar beji me tace ba, ganin ya?i magana yasa itama tai shiru ta nemi guri ta kashingiWa.

Yusuf ya waigo yace? "Kin gama kintsawar ne?"

Kawai ya ganta a zaune.

"Ya haka kuma? Se ruwan ya huce?"

"Ban sani ba, ai kana jina ina magana kayi min shiru, nace kazo ka tayani in cire rigar nan, amma kayi kamar baka jiba"

Ikon Allah bata da lafiyar ma, an tsira da ?yar bakinta be mutu ba, gashi da ?yar take maganar.

Yusuf yace? "bari inyiwa mutanen gidan magana, se suzo su cire miki"

"Wallahi babu matar da zata taSani" tai maganar tana kuka

Seda Yusuf yayi shiru, sannan ya tako a hankali kan katifar da take, ya zagaya bayanta hannunsa rawa yake ya zuge zip Win doguwar rigar tata ?asa.

Farar fatarta ta bayyana cikin wata ba?ar vest, shiru yayi yana kallonta, ta janyo hijjabi ta mayar ta yun?ura zata mi?e tsaye amma jiri ya kwashe ta.

Yusuf yace? "ki dena gaggawa, a halin da kike ciki Win nan, idan kika faWi zaki ji ciwo fa"

Ya duba ya Wakko soson wankanta dake cikin Akwatinta, sedai babu sabulu haka ya ri?ota suka fito, Gwaggo na ganin haka ta taho da sauri da nufin ta taya Yusuf, Amma Widad ta ma?ale hannunta, ta manne a jikin Yusuf tabi gwaggo da ido, gwaggo ta tsaya sororo tana kallonsu.

Yusuf yace "Mama karki damu, kiyi ha?uri haka halinta yake bata da yadda ne"

Matar dake gaban murhu ta juyo ta kallesu tace "yau nake ganin ikon Allah, wannan gwandamemiyar matar ce take ?yuya se kace me shan Nono, taS amma lamari ya Saci, koda yake wannan kamar ma ba irin tamuce ta nan ?asar ba"

Widad tabi matar gaban murhun da kallo, ha?oranta yellow shar ga ha?orannata wasu sunyi goyon kura, gata ba?a sosai ga fuskarta duk tsagu, gashi se ?ara baje hanci take.

Gwaggo tace "Haba Hari, ina ruwanki da ita irinku ne ke sawa adinga cewa Hausawa basu da kirki, yanzu da taji abunda kike faWa ba"

Zatonsu duk Widad bata jin hausa, gwaggo ta kalli Yusuf tace "ga banWakin can seka kaita"

Suna zuwa ?ofar banWakin Widad tayi tiris ta?i gaba ta?i baya.
Yusuf yace "muje mana seki shiga kiyi wankan"

Girgiza masa kai tayi tace? "Ni wallahi tsoro nake ji bazan iya shiga ba" sam Widad gurin be mata kama da banWaki ba, kamar wani gidan horo haka taga gurin.

"meye abun tsoron, zan jiraki anan gurin kiyi ki fito"

Ri?e shi tayi tsam tana girgiza kai tace? "Ni na fasa wankan, bazan shiga nan ba"

Gwaggo tace? "Wan nan ya naga bata shiga ba, lafiya kuwa?"

Yusuf yace? "wai tsoro take ji ba zata iya shiga ba"

Gwaggo tace? "Allah sarki, ?asashenku babu irin wannan banWakin ko? Abun duk se ha?uri ai, akwai wani Waki da babu komai a ciki ta shiga tayi a ciki kawai"

Yusuf yace "mungode Mama"

"A'a bakomai"

Ta nuna musu Wakin, duk yadda Yusuf ya tsani ro?o, haka ya karya billensa ya tambayi sabulun wanka, sedai Sabulun da suke wanka da shi irin sabulun nan ne kore na wanki me ?arnin tsiya, Yusuf ya mi?awa Widad, tasa hannu ta karSi sabulun ta kalli Yusuf kawai yaga Hawaye a idonta.

Tausayinta ya kama shi, amma ya basar kamar bega hawayen idonta ba, haka ta shiga Wakin da siminti a ?asan Wakin, tayi wankan nan tsigar jikinta na tashi saboda yadda ruwan in ya zuba a ?asa yake taSata, ga tashin zuciya saboda ?arnin sabulun, ba shiri ta ajiye sabulun tayi wankan a haja, sedai taji daWin ruwan zafin sosai "

Ta fito tana kama bango, Yusuf ya ri?eta ya maida ita Waki, ya duba Akwatinta ya Wakko kaya ya bata, ta saka itama tayi salla.

Saleh beje gida ba se bayan sha biyu na dare, yayi tunanin ko yaje yayi magana da doctor Safwan amma wata zuciyar ta hana shi, saboda yadda Safwan ya dinga rawar jiki da yaji batun kuWi tsaf zeje ya gaya musu, yaje ya sameshi.
Gaba Waya tunaninsa ya koma kan yaze ?waci Alhaji Nasir a gurin wannan Azzaluman mutanen? Dan ba ?aramin shiri suke dashi ba.

Me Adda suka koma inda suka ajiye su Widad, da niyyar ayita ta ?are, suna zuwa suka buWe gidan, suka shiga suka saka mukulli suka buWe Wakin suka ga wayam ba kowa a ciki, a kiWime Wayan yace? "Me Adda bafa kowa a Wakin nan"

?arasawa yayi da sauri ya shiga Wakin shima amma ba kowa a ciki, nan da nan suka gigice suka shiga lalauben su Widad.

Me Adda yace "Mutanen da ko iya takawa basayi, ta yaya zasu gudu? Duk matakan tsaron dake gurin nan ina sukabi suka fita?"

Cam Waya daga cikinsu ya Waga kai ya kalli Roofing Wakin yace? "me Adda kalli ta nan suka fice" yai maganar yana nuna musu saman roofing Wakin

Me Adda a gigice yace "ya zama dole mu bazama neman su, amma ta yaya suka samu abu sukayi hanya har suka fita?"

?aya daga cikinsu yace "Allah ne ya san yadda suka gudu"

Me Adda yace? "bamu da lokacin Satawa, maza maza mubi sahun su yadda suke a galabaice ba lallai su iya tafiya me nisa ba"
Haka kuwa akayi suka rarraba kansu a cikin daji.

Saleh yaje duba Alhaji Nasir a Asibiti, ya tarar da Anwar a gurinsa, suka gaisa yayi masa ya me jiki, ya Wan dubi Anwar yace
"Amma meyasa baza'a fita da Alhaji waje a nema masa magani ba?"

Anwar yace? "Nayi duk me yuwuwa inga an fita da shi, amma Mummy da Alhaji Bulama sunce nan ma ana kula da shi"

Saleh yace "Abunda za'ayi yanzu shi ne, ka Wauke shi ka canza masa Asibiti ba tare da ka sanar dasu ba, ko ba'a fita dashi waje ba a camza masa Asibiti, sedai kawai suga ka canza maaa Asibiti"

Anwar yace? "Amma zasuji babu daWi idan nayi hakan, suna ganin nanma ana ?o?ari akansa amma inyi haka kamar ban kyauta ba"

"Anwar zamanku a Asibitin nan yaci ace jikinsa yana karSar treatment yadda yakamata, amma har yanzu babu wani cigaba, mu canza masa wani Asibitin kawai"

Anwar yace? "Kana ganin babu matsala idan muka yi hakan?"

"eh babu matsala, Amma karkace ni nace ka canza masa Asibiti"

Anwae yace? "shikenan, ka kawo shawara me kyau insha Allah gobe in Allah ya kaimu da Safe, sedai suzo su tarar na canza masa Asibiti ni kaina rashin samun sau?in nan nasa yana bani mamaki"

Doctor Sufyan ne yake ta zagaye acikin Office Winsa, yana tunanin me yakamata yayi akan batun su Alhaji Haruna, yana tuno irin halacci da kirkin Alhaji Daula, idan aka haWa kai dashi aka cutar dashi to tabbas mesa Adalci ba, Amma wani mataki Alhaji Musa zasu Wauka akansa idan har be abunda sukace ba?.

Fitowa yayi da sauri daga office Win nasa ya nufi Wakin da Alhaji Nasir yake, yana zuwa shiga suka haWu da Saleh, suka yi kallon kallo babu wanda ya cewa kowa komai suka wuce.

Ya shiga Wakin da Sallama, Anwar ya amsa masa, doctor Sufyan yace "Anwar yame jikin kuwa?"

"Jiki sedai muce Alhamdilillah, amma doctor na fara karaya da yanayin jikin sa, babu wani cigaba fa gashi nayiwa su Mummy magana a fita dashi amma sun?i amincewa, na rasa dalili"

Sufyan yace? "ka kwantar da hankalinka Anwar, treatments Win dai da muke masa anan, shi za suyi masa a can, komai ze tafi dai dai ze warke in Allah ya yarda"

Anwar yace "Shikenan Allah yasa"

Haka Widad ta kwanta akan katifar, Yusuf ya Wau bargo Waya ya koma bakin ?ofa ya shimfiWa ya kwanta, shiru Widad ta kasa bacci, tana tunanin wai itace zata kwana a gurin nan, ga sauro se kururuwa yake mata a kunne, ga zafi ga jikinta da yake ciwo, ga rashin lafiya tana fama.

?angaren Yusuf ma shiru Yayi yana sa?e sa?e, yana tunanin wani hali Ummansa take ciki, yasan duk inda take hankalin ta a tashe yake, dan tun tasowarsa be taSa nesa da ita ba, wani Sangare na zuciyar sa yana tunanin Alhaji Nasir yasan tabbas shima yana cikin damuwa, ko wani haki yake ciki Allah masani, ga zamansa da Widad a Waki Waya baze yuwu ba, tunda ba muharramarsa bace, gashi ba ta yadda da kowa se shi, ga wasu abubuwan se anyi mata saboda bata da lafiya, dole idan Saleh yazo yayi masa magana asama masa wani Wakin, dan gudun afkawa tarkon sheWan.

Yana nan kwancw sauro yana cizonsa, yana masa hada hada aka, ga cinnaka da yake ta gasa masa cizo a gurin nan, tunani yake Allah yasa kae cinnakan ya ciji Widad.

Katsam ya jiyo sheshshe?ar Widad tana kuka, da yayi kamar ya basar amma ya dinga jin kukan nata a zuciyar sa, tabbas yakamata a tausaya mata.

?akin ba?i?irin da duhu, ko tafin hannu ba'a iya gani saboda duhu, haka yaja jikinsa cikin lalube yaje gefen katifar ta yace "uwa Wakina kukan me kike?"

Maimakon tayi magana seta sake fashewa da kuka, Yusuf yace "Am sorry, i feel your pain kiyi ha?uri ki karSi hakan a matsayin ?addarar mu, yakamata ki gode Allah da yasa muka tsira daga hannun mutanen nan, kuma insha Allah zamu koma gida ki dena kuka, kiyi bacci zaki ji daWin jikin ki"

"I can't sleep, sauro ya dameni zafi nake ji, kuma ina tunanin Daddy na"

Tai maganar tana sake fashewa da kuka.

"kiyi hakuri, Insha Allah Daddy yana nan lafiya, komai ze wuce kamar be faru ba, ki dena kuka kinga baki da lafiya"

Ajiyar zuciya kawai tayi, ta lumshe idinta tana jin yadda zuciyarta ke raWaWi.

Da Asuba yayi Alwala yazo ya tada Salla, bacci take dan sam bata samu bacci ba da daddare, seda ya idar sannan ya tashe ta ya kaita tayi alwala tazo ta tada salla.

Da gari ya fara haske me gari da kansa yayi sallama a ?ofar Wakin su Yusuf, Yusuf ya fita ya dur?usa ya gaishe shi.

Ya amsa cikin mutuntawa yace "Ya me jikin kuwa?"

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login