Showing 42001 words to 45000 words out of 135555 words

Chapter 15 - AKIDATA book 1 HAUSA NOVEL

17 Jan 2026

607

a gidan nan ba"

Ramla tace "ina ze sani, muna nan ta mayar damu kamar bayi, cin kashi kala kala, ana Wula?anta mu muda mahaifiyar mu amma kana neman ta"

Anwar yace? "Amma Mummy....

A fusace tace "ke Amal katse min kiran nan, shashashan banza kawai"

Amal ta katse kiran.

Anwar ya turawa Amal message
"Amal Wan turomin lambar Widad"

Ta masa reply da? "TaSWijan wa kake tunanin ze samu lambar wannan? Duk yadda kake tunanin abun ya wuce haka, ba ruwan ta damu fa"

Jujjuya message Win ya dinga yi, babban abunda yake bashi takaici be wuce duk lokacin da ya kira Mummy, ya tambayi ina Widad seta balbaleshi da masifa, duk wanda ya tambaya ya bashi lambar ta kowa se yace bashi da ita, ya rasa meye dalilin hakan.

Yana wannan tunanin Fahad ya shigo Wakin da sallama, ya kalli Anwar yace? "Man what's wrong ne? Nayi sallama baka amsa ba"

?an guntun tsaki Anwar yayi yace? "Fahad, ni gaba Waya na kasa gane kan lamuran nan dake faruwa, duk lokacin da zamuyi waya da Mummy, idan har zan tambayi Widad se taita faWa, babban abunda yake bani mamaki shine, wai ace duk gidanmu babu me lambar Widad balle ya bani"
Fahad yace
"Widad Widad Widad, kai dai baka da zance se wannan Yarinyar, please don't kill yourself mana, Nifa yadda kake bani labarin ta sam bata Yimin ba, nifa tun tana ?arama yadda take wannan Share mutanen haushi take bani, kuma gashi da bakin ka ka gayamin tana da taSun hankali "

Anwar yace " shut up please, tunda ba zaka bani shawara ba ka ?yaleni, baka san yadda nake ji akan ta ba, kai kana soyayya amma kamar baka san meye son ba, Ni anya ma in baka Ramla zaka iya ri?e ta kuwa? "

Fahad yayi murmushi yace
"Anwar kenan, aini Soyayya ta da Ramla tana sona ina sonta, amma kai banda wahala babu abunda kake yi"

"Kai kaga wahala, ni bangan ta ba, Ni na ?agu kamar in janyo lokaci in koma gida, gashi seka rigani komawa Nigeria"

"Allah ya baka lafiya Anwar, dan ga dukkanin alamu ta shafa maka haukan"

Shiru Anwar yayi ya mi?e ya bar Wakin, dan Fahad ya fara ba?anta masa rai.

Widad tana ta shirin fita, wayarta ta fara ringing, hannu tasa ta Wau wayar tasa a kunnen ta, shiru ta Wanyi tace?
"Ok, thank you very much, send the address via my email" ta ajiye wayar tana ci gaba da shiryawa.

Maimakon ta fito seta tsaya ta saman bene tana duba lokaci, Yusuf ta hango ya fito da Mota yana ta gogewa dukda a wanke take, abun da ta fuskanta da Yusuf mutum ne meson tsafta sosai, baya son datti sam.

Message ne ya shigo wayar Yusuf ya Waga ya duba.

"Ba'a wannan motar zamu fita ba, ka fita waje ka jirani"

Mamaki ne ya kama Yusuf, tabbas Wannan message Win daga Widad ne, 'Amma yaushe ta samu lamba ta?' ya tambayi kansa, basarwa yayi ya mayar da motar, yana fita wajen gate yaga wata mota, ba dai me tsada bace dan kamar ma ta Wanji jiki.
Guri ya samu ya tsaya yana jiran fitowar ta.

Seda yayi kusan mintuna talatin kamar ance ya Waga kai ya kalli gate, ganin Widad ne yasa ?irjin Yusuf bugawa da ?arfi.

Wani arnen black leg jeans ne a jikin ta, da wata tied pitted blue body hook, tayi stocking ta saka beilt, Wan ?aramin ba?in veil ta Waure gashin kanta, dukda ?asan gashin nata ya fito.
Google glass ne a fuskar ta ba?i, ga takalmi me matu?ar tsini, se 'yar ?aramar jakarta, gaba Waya bazaka ce idan Widad ta buWe baki zata yi hausa ba, duk wani shape da surar jikin ta ya fito.

Tabbas da Yusuf nada damar Mayar da Widad ta canza kaya da tabbas zeyi, dan haka kurum yaji takaicin fitar Widad a haka.

?arasowa tayi ta mi?awa Yusuf key ba tare da tace komai ba, jiji a sanyaye ya karSa, ya buWe mata motar ta shiga ya rufe ya zaga mazaunin direba ya zauna, gaba Waya ?amshin turaren da take ya cika motar, ya kalle ta yace
"Ina zamu je?" shiru tayi na Wan wani lokaci sannan ta mi?a masa wayarta, yasa hannu ya karSa ya duba.
Adress Win inda ze kaita ne, ya Wago ya kalleta zeyi magana, amma yaga ta ?ara yi masa kwarjini, dan haka ya bata wayar ta ya kunna motar.

Yana cikin tu?i wayarsa ta fara ringing, Umman Yusuf ne a jikin screen Win wayar, ya Waga wayar yasa a hansfree ya ajiye ta yace
"Umman Yusuf"

"?an gidan Umman sa, yau zaka dawo da wuri ne, an kawomin wani kifi tun daga Yobe, nayi maka farfesu ka dawo da wuri karya huce, ko kuma in cinye abuna"

Duk da ransa a dagule yake wanda ya rasa dalilin hakan, Amma seda ya maze yace?
"Umman Yusuf, ai bazaki iya ci baki ajiye min ba, zan siyo gurasa yai akwai dinner me kyau"

Hirarsa yake yi da maman sa hankali kwance, se shagwaSa yake yi kamar yaro ?arami, Widad kuwa ?ura masa ido tayi ko ?iftawa ba tayi, dukda ta cikin Glas Win idonta take kallon sa amma yadda yake wayar da Mahaifiyar sa ba ?aramin birge ta yayi ba.

A ranta tace 'dama suma talakawa suna jin wannan shau?in da ?aunar na iyaye, inama Ammi na tana raye nima in kwanta a jikin ta in ji daWi'
Ba tayi aune ba taji hawayen da bata shirya zubowarsu ba. Cire glass Win fuskarta tayi tana goge hawayen idon ta, katse wayar Yusuf yayi ya kalleta yace
"lafiya dai?"
"Lafiya cigaba da tu?inka, ina so muje gurin nan kafin 5"
Ya jinjina kai ya ci gaba da tu?in, wani katafaren hotel ne, motocine suke shiga suna fita a ciki, kowa harkar gaban sa yake yi, sedai mafi akasari kallo Waya zakayi wa mafi yawa daga mutanen dake shiga suna fita, ka gano rashin tarbiyya da ta ido a tattare dasu, musamman matan duba da yanayin irin shigar dake jikin su.

Yusuf yayi parking yana kallon Widad, ta buWe motar ta tsaya tana ?arewa harabar hotel Win kallo.
Da sauri Yusuf ya fito daga motar yana kallon ta, ta dubeshi tace? "wait for me here"
ta sa kai da nufin shiga cikin hotel Win, da yawa mazan dake gurin nan hankalinsu ya dawo kanta, Widad ta haWu iya haWuwa, wani takaici ne ya kama Yusuf, ace 'yar musulmi ce da wannan shigar a wannan gurSataccen gurin.
Bin bayanta ya kuma yi da sauri, ta tsaya ta kalle shi tace?
"I said you should wait me inside the car, don't let anyone to see you here, don't tarnish your image because of me"
Ta sake juyawa, ba zato cikin zafin nama da zafin rai Yusuf ya ri?o Widad gaba Waya zuciyar su ta buga a tare, Yusuf ya kalli cikin idon ta yace
"Guri irin wannan be dace da mace me daraja kamar ki ba, Mahaifinki babban mutum ne be kamata aga 'yarsa a irin wannan gurin ba, ke mace ce kuma me daraja bekamata kowane gara ya dinga kallon surar jikin ki haka ba, think about it"
Nutsuwa Widad tayi seda ya gama tsaf sannan tace?
"Cikani tun kan in wanka maka mari a gurin nan, kai waye da zaka gayamin abunda ya dace dani? this is my life style not yours, dalla Cikani Malam kana Satamin lokaci ni"

A hankali Yusuf yace? "I am musulm, ina kishin yadda mutane ke ?are miki kallo a haka, kalli irin mutanen dake gurin nan, da yawan su karuwai ne fa da mutanen banza, shigarki bata da maraba da wanda matan gurin nan marasa daraja suka yi"

Cikin isa tace masa "koba maruwanci ba, Nima shi nazo yi, am prostitute karka ?ara shiga rayuwa ta, na gaya maks"

Ta juya ta shiga Hotel Win da sauri, wani ba?in ciki ne ya tokare zuciyar Yusuf, ya koma mota ya zauna yana tunani a ransa
'to wai kai Yusuf banda shisshigi ina ruwanka da ita ne?'
Wata zuciyar ta tambaye shi.

Yana nan zaune a mota kusan mintuna Arba'in, gajiya yayi da zaman motar ya fito ya zauna akan motar yana ?urawa hanyar da Widad tabi ido.
Ba tsammani ya hangota tana fitowa, sedai fuskarta Wauke da hawaye tana ta share hawayen da handkerchief, inda motar su take ta nufo idanunta jawur, wani ne ya biyo ta yana ?o?arin tsaida ita yayi mata Magana amma bata tsaya ba, tana zuwa ta buWe motar ta shige.
Yusuf ya zagaya ya shiga ya kunna motar, gaba Waya se yaji ya tsargu da yanayin daya ganta, gaba Waya hankalinsa ya tashi "Are you ok?"

"Do you have any conscience with me being ok or not?" ta tambaye shi a hasale

"Yes i have" ya bata amsa, tsaki tayi ta Wauke kanta tace?
"drive very fast please" gudu sosai Yusuf yake amma azalzalarsa take wai ya ?ara gudu, kuma still bata dena kukan ba, kuka take me fallasa da tsantsar Sacin rai da damuwa.
Guri Yusuf ya samu yayi parking ya juyo yana kallonta, ba tace komai ba tasa hannu a jakarta ta Wakko wayar ta, ta Wan daddana sannan ta saka a kunnen ta, tayi shiru na wasu 'yan mintuna sannan tace "Hello Daddy"

Yusuf baya jin me mahaifin Widad ke cewa, cikin kuka tace? "please Daddy I want Flight back to U. K, i regret coming back to Nigeria, please Daddy talk to Bulama ask him to set up my visa"

Shiru ta Wanyi sannan tace? "Daddy don't take it for granted please, i can't define what happens today, dan Allah kace ayimin visa in koma"

"Daddy why? Kayi shekaru ba tare da ni ba se yanzu zaka ce baka so inyi nesa da kai? Karo na biyu ina neman abu kana ?in Yimin, shikenan Daddy bayan ciwon ?wa?walwa am at risk of having cardiac attack" ta saki wayar ?asa ta cigaba da kuka.

Yusuf ya cika da mamakin meyasa Widad kuka haka? Akwai bu?atar yasan me taje yi Hotel.

"malam kayi sauri ka maida ni gida, ka tsaya kana kallo na"

"Bazan iya tu?in ba muddin zan cigaba da jin kukan ki" yai maganar fuskarsa Wauke da damuwa

A hankali ta Wago idanunta da suka yi jawur, ta saka ana Yusuf tana son gano gaskiyar abunda ya faWa

"to meye haWinka dani da kuka na ze dame ka, just drive ba ruwan ka da kukana, kayi abunda ke gabanka"

A hankali ya kunna motar, ya bata wuta ya cigaba da tu?i, sedai gaba Waya hankalin sa baya jikin sa, yana can yana tunani daban daban.

Ihun Widad ne ya dawo dashi hayyacin sa, sannan ya lura da abunda ke shirin faruwa, duk yadda yayi ?o?arin kaucewa motar, seda me motar ya daki tasu.

Dafe kai Yusuf yayi yace? "Subhanallah"

A fusace ta kalli Yusuf "Are you out of your sense, see how you ruin my life, kashe ni kake so kayi? Baka gani ne? Dama so kake ka kasheni, an haWa baki da kai zaka kashe ni ko? Dama na sani"

Kafin Yusuf ya bata amsa tuni me waccan motar ya fito yana zazzaga bala'i, an lotsa masa mota se an biya shi.

Yusuf ya buWe motar ya fita jiki ba ?wari, ya kalli mutumin ze kai shekaru Arba'in, Yusuf yace?
"Dan Allah kayi ha?uri, birki ne ya ?wacemin, kuma kaga traffic ta tsaida hannun ka amma baka tsaya ba, kuma ni na riga na taho da gudu, amma dai kayi ha?uri"

"Shut up my friend, ni zaka gayawa traffic ta tsaida hannu na? Titin naka ne kai kaWai da zaka dinga wannan gudun, banza shashasha kuma wallahi seka biya ni asarar da kayi min kokuma kaga abunda zan maka"

Tuni mutane suka fara taruwa, suka cika gurin ana ta bawa Mutumin nan ha?uri, dukda zagin da yakewa Yusuf amma ha?uri yake bashi, amma mutumin nan ya rintse ido yana zazzaga masifa yana cin zarafin Yusuf, hakimar kuwa ko fitowa ba tayi ba tana mota a zaune.

Yusuf yace "Amma naga idan laifi ne fa kaine kayi bani ba, Amma se baka ha?uri nake kana cigaba da cimin mutunci a gaban mutane, shikenan Yimin duk abunda zaka iya ka huce"

Yusuf dama gashi a cikin damuwa yake, ga shi ze zagin sa mutumin yake, aikuwa nan da nan temper Winsa ta hau zuciyar sa ta shiga tafasa, dan haka se yayi shiru ya dena cewa komai.

Mutumin ya cigaba da zazzaga masifa "Do you know who I am da zaka dingamin magana da gadara,? I will show you what am capable of doing, sena nuna maka ni waye, sena sa an sauke maka wannan rashin Wa'ar taka mara tarbiyya kawai"

"You are nobody More than stupid Malam, waye kai idan har kai wani ne bazaka tsaya kana Waga murya akan wannan banzan gwangwanin motar taka ba, kayi abunda zaka yi an bige motar taka, ina son inga kai waye, kuma me zaka iya?"

Gaba Waya suka juyo inda Widad ke magana da jajayen idanunta.

Mutumin ya kalli Widad yace
"Lallai ka Wakko karuwa a mota, dole ka Wagamin murya danka birgeta, zanyi maganin ku daga kai har ita"
Ya ciro wayarsa yana waya.

Yusuf a harzu?e zeyi magana Widad ta Waga masa hannu alamar yayi shiru.
Ta Wakko wayar ta tayi 'yan taSe taSe.

Mutane suka ja gefe suna son ganin ?arshen dramar, mintuna kaWan sega motar 'yan sanda, suka zo suna wuri wuri, mutumin ya nuna musu Yusuf yace? "gashi nan shine, ku kama shi shida wannan koWaWiyar Yarinya me kama da sadakar Yalla"

Tuni Waya daga Wan sandan yaje ya cakumo Yusuf, sedai me Wan sandan ya jiyo bindiga a jikin Yusuf!!!


SHARE PLEASE =?O?

__Masha Allah nagode da addu'oinku Daddy yana samun sau?i Alhamdilillah nagode sosai Allah yasaka da alkhairi __

Ayshercool
07063065680

_*A?IDA TA*_


PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A



*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*A?IDA TA *

I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum




https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in








ELEGANT ONLINE WRITER'S






PART1
Page 12






?an sandan ya zare ido zeyi magana, Yusuf yayi saurin girgiza masa kai, ya juya ya kalli Widad yaga hankalinta baya kansu.

A hankali ya zura hannu a aljihun sa ya Wakko ID card ya nunawa Wan sandan, washe baki Wan sandan yayi yana niyyar sarawa Yusuf, amma Yusuf ya girgiza masa kai yace

"Dan Allah YallaSai ku duba lamarin nan, ni bani da laifi a abunda ya faru, kuma na bashi ha?uri ya?i ha?ura"

Mutumin ya ?araso inda su Yusuf suke yace? "kaga Ku tafi da shi ajiyata ne, ku kulle shi har se nazo station Win"

?an sandan Ya kalli Yusuf zeyi magana, sega wasu 'yan sandan sunzo, motar da' yan sandan suka zo ze tabattar maka da manyan wanda mutumin ya kirane, nan na farkon suka shiga sarawa wanda Widad ta kira.

Widad tace? "ina so a duba Accident Win nan, idan direba nane yake da laifi, zan biya shi kuWin motar sa uku, idan kuma shi yayi laifin ze dur?usa ya bamu ha?uri, saboda cin zarafi da Sata mana lokaci da yayi, in kuma ya?i a tafi da shi, ajiyata ne a kulle shi se nazo"

Nan fa kallo ya koma sama, nan 'yan sanda suka shiga dube duben su, aka tabattar da mutumin nan shine ya karya doka, nan fa mutanen gurin suka Wau sowa.

Widad taje gaban sa tace " if you are somebody you won't say it yourself, don't ever say you are Somebody when you are nobody, yanzu ka dur?usa ka bawa direba na ha?uri akan cin zarafin da kayi masa"

"Wallahi baki isa ba keWin banza, in bawa wannan wula?antaccen ha?uri, kin san koni waye?"

?aya daga 'yan sandan daya kira ne yaja shi gefe yace? "kai wallahi wannan' yar masu ?asa ce, idan taso zatasa a Satar da kai gaba Waya wallahi, kayi abunda tace kota sa a Waureka"

"wannan ?aramar yarinyar 'yar cikina?"

"to karkayi cigaba da taurin kai, wannan' yan sandan data kira muma iyayen gidanmu ne"

Mutumin ya dawo a ?ule ya kalli Yusuf yace? "Yi ha?uri"

"Akan gwiwowinka zaka dur?usa ka bashi ha?uri" cewar Widad

Cikin tsawa wani Wan sanda yace "ba zakayi bane? Semun tafi da kai?"

A hankali yaja da baya ze dur?usa, Yusuf yayi saurin ri?e shi tare da girgiza kai ya kalli Widad yace? "please Madam ina nema masa Alfarma, kiyi ha?uri dan Allah, ni zan dur?usa in baki ha?urin a madadinsa"

Dama Widad tasan Yusuf baze taSa yadda hakan ta faru ba, tayi ne dan nunawa Mutumin shi Win bakomai bane.

"Shikenan tunda ya ha?ura, gobe in Allah kaimu, yaje station Winka ya karSi kuWin motar sa, na ninka maka masa sau uku, Amma ya kiyaye gaba"

Ta juya ta tafi motar su, Izzar Widad da yadda ta tafi da al'amuran cikin isa da izza, da bajinta suka birge mutane, aka dinga sowa, anawa mutumin nan dariya.
Dare yayi musu a gurin nan saboda wannan incident Win, Yusuf yaja motar cikin nutsuwa suka tafi.

Amma still lokaci lokaci tana goge Hawaye a fuskarta, suka ci gaba da tafiya Yusuf na godewa Allah da Widad bata ga bindigar nan ba, tabbas yasan da Asirinsa ya tonu daya gama kaWewa, ?arshen ta seta kulle shi me fitar dashi se Allah.

suna zuwa gida Yusuf yayi horn Isa ya buWe musu gate, Yusuf ya shiga da motar yayi parking, har ya gama abunda zeyi ze buWe motar ya fita, Widad tana zaune ko gezau ba tayi ba, bata da niyyar fita daga motar.
fita yayi ya zagaya ya buWe mata ?ofar, yace? "Munzo fa" Waga kai tayi ta kalle shi, a hankali ta zuro ?afafunta da take jin kamar ba'a jikinta suke ba waje ta yun?uro ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login