Showing 120001 words to 123000 words out of 135555 words

Chapter 41 - AKIDATA book 1 HAUSA NOVEL

17 Jan 2026

672

our family image"

Ramlah tace 'but your dad can bale him out, so you don't care about my feelings, Wan uwana yana rufe kaikuma abunda ya dameka daban ko? "

"Ai na miki bayani, ban san me kike so ayi ba kuma"

"ina son ka saka baki, Daddynka yayi magana a sake shi"

"Amma Ramlah kin san ba abune me sau?i yin hakan ba ko, yaynki an haWa baki dashi an sace Daula, me zesa Daddy yasa baki"

A fusace? Ramlah tace "shut up Fahad, ta yaya Anwar ze hakan, tare kukayi school room Winku Waya, you know what he can do and what he cannot do, dan haka ina jiran kaje kayi magana da mahaifinka a fito da shi, that's the only way you can prove to me that you loves me"

Tana gama maganar tayi waje ta bar motar, Wan taSe baki yayi ya kunna motarsa yayi tafiyarsa.


Yau da Yusuf ya dawo a Waki ya tarar da widad, kamar tana cikin damuwa ya kalle ta yace "Na dawo"

Jinjina masa kai kawai tayi, amma ta kasa magana, se ya zata tun abunda ya faru da safe ne yasa take jin haushinsa.

"Meke damun kine? Ko har yanzu fushin kike dani?"

A kasale tace "Bakomai fa"

Haka ya fita yaje yayi wanka ya dawo ya sameta a inda ya barta, yau dambun tsaki Hansai ta girka ta aiko musu, amma ta?i sakin jiki taci, ya kaWa ya raya amma tace lafiyarta ?alau, sedai ya lura buni buni seta tafi toilet ta dawo.

"Gimbiya ko cikin kine ya Saci?"

Girgiza masa kai tayi tare da kwanciya, haka taita yi har washegari gaba Waya kamar bata da sukuni, kuma ta?i gaya masa abunda yake damun ta, haka ya fita ya barta ya Wauka dai fushi kawai take, Da Azahar ya dawo sedai ya tarar da tun Abincin safe bata kuma cin komai ba.

Yaje gabanta ya dur?usa yana ?are mata kallo yace "dan Allah idan fushi kike dani kiyi ha?uri, kin sani a damuwa fa"

"Nifa ba fushi nake ba, ka ?yaleni kawai"

"baki da lafiya ne?"

"lafiya ta ?alau"

"but you look so much restless"

Shiru tayi bata ce uffan ba, ya mi?e yana duba kwanuka yaga abunda aka kawao, se yaga tana ta dube duben abun shimfiWar dake kan katifarta.

Yana zuwa ya Wagata cak daga kan katifar, meze gani jini ne a jikin ta, ya Sata mata jiki da katifar.

A gigice yace "Subhanallah, Widad meya same ki haka?"

Take ta fashe da kuka tace "Period yazo min tun jiya bani da pad"

Cike da damuwa yace "shikenan is ok, kwantar da hankalinki"

Yasa hannu ya naWe bedsheets Win, ya Wora ruwa yayi Wumi ya haWa mata ruwa, ya rakata banWaki, ya dawo ya haWa abun shimfiWar da kayan data cire ya zubasu a bokiti.

Tayi wankan ta fito ta dawo Wakin, har yanzu bata dena kuka ba, Yusuf yace "jeki zauna bari inje gurin Mama inga inda wani taimako da zata bamu"

"Idan na zauna Sata gurin zanyi"

Yusuf yace "bakomai zauna, idan ya Saci zan gyara"

Ya zaunar da ita ya fita da sauri.

Yana fita tsakar gida Hanne ta kalle shi tayi murmushi tace?? "kana bu?atar wani abune?"

Yusuf yace "gwaggo zaki kira min dan Allah"

Tace "to"

Ta tashi ta shiga Wakin gwaggo, gwaggo ta fito ta kalli Yusuf tace "lafiya dai malam Yusuf?"

Cike da kunya, Yusuf yayi mata bayani, Gwaggo tace "to mudai yaranmu da tsimmane suke amfani, ban sani ba ko zata iya amfani da shi"

Yusuf yace "bakomai Gwaggo, zata iya insha Allah"

Gwaggo ta shiga Waki ta Wakko sabon turmin Atamfa, da sabuwar reza, da ?yar Gwaggo ta iya shiga Wakin nasu saboda kunya.

Widad na zaune da towel se vest a jikinta, Gwaggo tace "Sannu Amarya ya jiki?"

Widad tace "lafiya ?alau"

Tasa reza ta yanka Sabuwar Atamfa ta gwadawa Widad yadda zata yi.

Widad tayi shiru ta?i cewa uffan, Yusuf yace "Mama nagode sosai da taimakonki, Allah ya saka da alkhairi"

Gwaggo tace "bakomai Malam Yusufa"

Gwaggo ta fita, tana fita Hari tace "Yaya wai Wudas Wince bata da lafiya?"

Gwaggo tace "Eh"

"meya same ta?"

Gwaggo bata amsa mata ba, Hanne tace "waini Gwaggo meye na yanka sabuwar Atamfarki, wallahi kin fiye za?ewa akan wannan fitsararriyar"

Gwaggo a fusace tace "wallahi kika kuma magana sena kwaWa miki mari, ina kallon ki duk abunda kike yi, Wa na kowa ne, meye dan na yanka Atamfa? Abum duniya fararre ?ararre"

Haushi Hanne taji, dan da wuya kaga Gwaggo tana faWa se an Sata mata rai sosai, Amma yau akan wannan koWaWWiyar tana ta mata masifa.

Yusuf ya kalli Widad yace "gimbiyata nasan baki saba amfani da irin wannan ba, amma kiyi ha?uri gidanmu babu mata nikaWai ne shiyasa nima ban san kan wannan abubuwan ba, da tuntuni nasa an nemo miki abunda zaki yi amfani dashi"

Da ?yar Yusuf ya lallaSata ta saka ?yallen nan, sam she's not comfortable with this thing, gaba Waya ta takure kanta, Yusuf yana kallonta ta kwanta ta zauna gaba Waya ta kasa zama.

Ya kwashi kayan data Sata yaje ya wanke su tsaf, taga ya dawo Waki yana goge hannu ta kalleshi tace "wai me kayi?"

"kayanki na wanke"

"Kayan jinin?"

"Eh mana, nasan idan na bar miki ba zaki iya wankewa ba"

Shiru tayi ta bishi da kallo, tuno abunda ya faru da safe tayi, yadda tay masa wula?anci amma har ya manta yana tarairayarta, yasa hannu a kayanta na jini ya wanke.

Ganin da yayi ta kasa zaune ta kasa tsaye yace? "Gimbiyata meya ke damunki yanzu?"

"?afafuna ne kamar ba nawa ba, babu daWi marata ma ciwo takemin"

Yazo ya zauna a kusa da ita, ya kamo ?afafunta ya Wora akan cinyarsa yana matsa mata a hankali, lumshe ido ta dinga yi.

Ta Wauke ?afafunta daga kan cinyarsa, ta Wora kanta sannan ta mi?a masa hannunta, tana masa nuni daya ja mata yatsun, haka Yusuf ya ri?e yatsun ta yana matsawa a hankali, babu daWewa kuwa bacci yayi gaba da ita.



Seda Nurat ta tinkaro komawa gida sannan gabanta ya shiga faWuwa, dan se yanzu ma ta tuna taSargazar da tayi.

Kanta tsaye tana ta Addu'a ta fara buga gate Win, me gadi yazo ya buWe mata bece mata uffan ba, ta shiga cikin gidan, sedai me a harabar gidan idonta ya sauka a cikin na mahaifinta yana zaune yana kallonta.



SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!

(Ina ma'abota karatun littafin A?IDATA, a fari nace zan bada littafin kyauta ba tare da ko sisi ba, amin Afuwa wani dalili zesa zan saida book2 and 3,dukda nima ba hakan naso ba, gaba Waya kyauta nayi niyya bada littafina, Amma dalilin me ?arfi zesa in saida ?arashen in na gama book1 ina fatan zaku fahimceni)





Domin gyara, sharhi ko shawara
Ayshercool
07063065680
? ? ? ? ? ? ? ? ? _*A?IDATA*_
? ? ? ?

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA _
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*A?IDA TA *

I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum

Ha??in Mallaka ?& : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ?unsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani Sangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

NOT EDITED

ELEGANT ONLINE WRITER'S

? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ?? PART1
? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? Page 40_41

Gaban Nurat ne ya shiga bugawa da sauri da sauri, ta shiga zazzare ido be kula ta ba bece mata komai ba, tazo ta tsaya tana kallon sa, taga harta wuce bece mata uffan ba.

Ta shiga Waki ta nemi guri ta zauna, tayi shiru tana tunanin yadda zata samu Anwar ya kuSuta, babu zato? taji an murWa ?ofar Wakin nata.

Mahaifinta ne ya shigo yana rarraba ido, gadan gadan yayo kanta yana faWin "gidan ubanwa kika je?"

Mi?ewa tayi a gigice ta shiga ja da baya tana faWin "babu inda naje Daddy"

"?arya kike munafuka, harni zan saka doka ki sa ?afa kiyi fatali da ita? Uwarki ta Waure miki gindin kiyi rashin mutunci ko? Ni da Daula waye ya haifeki?"

"Daddy niba gurinsa na je ba, Ai an Wauke shi daga Asibiti"

Sekuma yayi sak, "Ubanwa waye ya gaya miki?"

"wallahi Daddy a gari naji"

"to gidan ubanwa kikaje? Zaki gayamin ko sena yanka ki a gidan nan?"

Girgiza kai take, takasa magana ya cakumo wuyanta yana zazzare ido, kakari ta dinga yi tana kuka tace "Wallahi Daddy ba inda naje, kawai gajiya nayi da zaman gidan na fita, dan Allah kayi ha?uri"

"se naci ubanki yadda idan na sake saka doka ba zaki takamin ba"

Cikin kuka Nurat tace "Wayyo Allah Mummy, ki temakeni karya kasheni"

Maimakon ya saketa sake sha?eta yayi, yana kuma zaro mata ido kamar tsohon maye.

Kakarin Nurat ne yasa mahaifiyar ta, ta sallame salar da take, a guje ta rugo Wakin Nurat, ta tarar ya sha?e Nurat kamar ya kama sa'ansa ko kuma wani shahararren ?arawo.

"Kayi haukane, ka cikamin 'yata ita kaWai ce dani, kana gani duk yaranmu mutuwa suke, ita kaWai Allah ya barmin ka ?yalemin' yata"

Juyowa yayi a fusace ya mangare mahaifiyar Nurat yace "itama Win gara in aikata inda waWancn suka tafi, muddin zata dinga takemin doka, tasan a duniya bani da ma?iyi sama da Daula, danme zata dinga zuwa inda yake, akan me?"

Yai maganar tare da wurgi da Nurat, wadda tuni ta fara fita a hayyacinta, dan daya jefar da ita ko motsi ba tayi, se kokawa take da numfashi.

Da sauri Maman Nurat ta nufi kan Nurat, yayin da Alhaji Musa ya cigaba da banbami, ta Wago Nurat sedai bata numfashi.

Cikin kuka tace "wallahi idan ka kashe min 'ya se nayi shari'a da kai, Kai kanka kawai ka sani, bu?ata in ba ta kaba baka damu da kowa ba"

A fusace yace "Maza karki fasa yin shari'a dani, idan na kashe ta na kashe banza, duk son da nakewa mutum muddin ze bujiremin to zega ba dai dai ba tabbas"

Banza tayi masa, Taje ta buWe fridge ta Wakko ruwa me sanyi ta shiga shafawa Nurat, a hankali ta dinga sauke Numfashi, tana buWe ido ta fashe da kuka tace "Mummy anya Daddy ne ya haife ni? Kalli yadda yayi yun?urin kasheni me nayi masa haka?"

"kema da halinki Nurat, kin fiye taurin kai, na hana ki wannan abun da kike amma kin kasa ganewa, gashi ze kashe ki a banza"

Shiru Nurat tayi, tabbas tunda mahaifinta yake yun?urin kashe ta akan taje inda Daula yake, to tabbas wani mummunan abu yake aikatawa, kuma na abunda baze iya aikatawa akan kowa ba.
Lumshe idon ta tayi tana jin yadda ?irjinta yayi nauyi, wani irin ba?inciki ya mamaye zuciyarta.

Shikuwa Alhaji Musa yana komawa Waki ya shiga sintiri, kamar yadda ya zame masa jiki a 'yan kwanakin nan, ba shi da nutsuwa sam, musamman da' aka ce su Widad sun gudu daga inda aka sace su, gashi sunsa a nemo su a ko'ina suke amma abu ya gagara.

Gashi yanzu wata maganar rainin hankali da ta taso, wai an sace Daula akan gadon Asibiti, 'Anya ba wani rainin hankalim su Alhaji Haruna suke shiryawa ba?'

A hankali Widad ta buWe ido daga baccin da yayi awon gaba da ita, taga Yusuf ya jingina da jikin bango ya lumshe idanunsa, hannunsa Waya yana wasa da gashin kanta, a hankali tayi mi?a tare da hamma, da sauri ya buWe ido yana jera mata sannu.

Ba tace komai ba se jinjina masa kai da take.

Mi?ewa tayi zaune, se kuma yaga ta yamutsa fuska.

Kallon ta yayi da sauri yace "lafiya dai?"

?an tura baki tayi tace "am not confortable at all, ji nake kaman am stain"

Yusuf yace "kiyi ha?uri insha Allah, zan san yadda zanyi a samo miki wancan da kike amfani da shi"

Widad tace "baza a samu wanda nake amfani da shi ba, sedai a siyomin kowanne ne, bana son wannan abun da nake using dashi yanzu, is so much irritating"

Yusuf yace "Shikenan, Insha Allah zan san abunyi"

"Sannan kuma..." se kuma tayi shiru

"sannan kuma me?" Yusuf ya tambaya

"Nasan baza'a samu shaving cream ko powder ba, a siyomin shaver please"

Cike da son ya kunnata Yusuf yace "shaver kuma, me zakiyi da shaver?"

"Abunda kake yi da ita" ta bashi amsa cike da tsiwa

Yayi murmushi yace "Aini gemuna nake askewa da ita"

Ta kalle shi ta Wan tsuke baki tace "Nima nawa gemun zan aske"

Aikuwa Yusuf ya kwashe da dariya, sosai yadda tayi magana da abunda ta faWa Win ya bashi dariya, kallonsa take yi yadda dariyar tayi masa kyau.

"wallahi idan ka ?ware ba ruwana"

Tai maganar tana shirin Mi?ewa, ya kalleta yace "Ina zaki?"

"tsakar gida nake son fita"

"Amma kin manta halin da kike ciki ne?"

"To zama zan tayi ina kallonka, ni na gaji da kwanciyar ma, zan kula sosai"

Yusuf yace "Aini bana gajiya da kallon kyakkyawar fuskar nan taki, muyi zamanmu a Waki nima na iya hirar se in miki, kuma baki ci Abinci ba, ko kin manta?"

'?yale Abincin nan, ni idan ina period bana son Abinci sosai "

Yusuf yace " dama can haka kike, ina lura dake tarkace kawai kike ci ba Abinci ba, so nake ki ?ara ?iba ki daure kici ko kaWan ne mana"

"Ni gaskiya, ba irin wannan nake so ba"

"wanne kike so" ya faWa cike da kulawa.

?an tsura masa ido tayi, sannan tace
"Bari dai inci kaWan"

Ya Wakko kwanon dambun ya ajiye mata, tasa cokali ta fara ci, dambun tsaki ne amma yaji gyaWa da zogale yayi daWi Sosai.

Widad tace "tunda nazo ?auyen nan, ban taSa cin Abinci me daWin wannan ba"

Yusuf yayi murmushi yace? "harda bredin jiya?"

Widad tace "hmm dan dai kar kaji haushi ne, amma gaskiya bredin nan ya daWe a ajiye, se marmashewa yake ba daWi"

Yusuf yace "dagaske ba kya son inji haushi?"

?an kallonsa tayi tace "No i mean banyi niyyar magana ba lokacin shine kawai, ka Wakko spoon muci Abinci mana"

Yusuf ya girgiza kai yace "A'a kici kawai, idan kin rage se inci"

Widad tace "meyasa? Ai ze ishemu"

Yusuf yace "bana son in samiki yawuna a jiki, naga bakya son hakan"

?an tura baki tayi, cikin ?un?uni tace "na nawa kuma, ?arewa ma ai Yawun naka ka samun a bakina jiya"

Yusuf yace "ai bazan manta wannan moment Winba, nayi kissing Win gimbiyata the most memorable moment in my life"

Widad tace "tabbas kam, ka kafa tarihi, kayi abunda wani mahaluki be taSa gangancin gwadawa ba, kayi min abunda ban taSa zaton wani zemin in ?yaleshi ba, hmm ban san meyasa kake min abubuwa son ranka ba, ?yaleka kawai nake"

"Are you sure babu wanda ya taSa kissing Winki seni?"

Watsa dambu tayi a bakinta, ta ja wasu seconds sannan tace "Idan an taSayi kana tunanin zanji tsoron ka ne? Ban taSa shan yawun ?ato ba se a kanka, kuma bashi ka Wauka, tunda kasa na haWiye yawunka"

Murmushi Yusuf yayi yace "Yaushe ne ranar biyan bashin?"

Banza tayi masa ta?i ko kallon inda yake, can Yusuf yace "Amma meyasa kike zuwa Clubs da kuma Hotel?"

Jin tambayar tayi a bazata, take taji tana kokawa da dambun dake bakinta, gaba Waya Mood Winta ya canza a hankali tace

"ai tun a lokacin na gaya maka me nake zuwa yi, na gaya maka ni karuwa ce kamar yadda matan gurin suke"

HaWe rai Yusuf yayi yace "Kamar yadda bakya son ?arya, na tabbata kema bakya aikata ta se bisa kuskure, meyasa zaki gayamin haka? Ko kina son zuciya ta ta buga ne?".

"Tunda baka yarda ba shikenan, amma kasan dai bazan zauna ina rantse maka dan ka yarda dani bako?"

Ta ajiye spoon Win Abincin ta je ta sha ruwa, tayi waje abunta ta bar Yusuf a gurin a zaune.

Ro?on Allah ya shiga yi akan Allah yasa abunda Widad ta faWa ?aryane, dan ba ?aramin kishi yaji ba, kuma yasan halin ta ko meye zata yi ?o?arin gaya maka gaskiya, ko ta maka daWi ko akasin hakan'

Tana fitowa Gwaggo tace "Amarya kin ware kenan?"

Widad tace "eh Alhamdilillah"

"Masha Allah, haka nake son ji"

Hari tace "Wai meya same ki ne?"

Widad tace "Kaji Baba Harin nan, sekace kin damu dani, bayan ko gani kika yi zan mutu murna zaki yi, to ciwon yara nake bana tsofaffi ba dan haka base kinji ba"

Aikuwa a fusace Hari tace "karki ?ara cemin tsohuwa, ta ina nayi miki kama da tsohuwa? Da ?uruciyata dudu shekarun nawa ba zasu gaza Ashirin da shida ba, amma kike kiramin tsufa"

Ai gaba Waya wanda ke tsakar gidan ba wanda be dariya ba, Widad tace "A'a kin manta a zanin goyo kike ma ?arewar yarinta, harfa jikokine dake amma kice shekarar ki Ashirin da shida, shekarar ki biyar akamiki Aure kenan"

Hari tace "koma yane dai, niba tsohuwa bace ba ehee, dan jina nake garas kamar 'yar shekara goma sha shida"

Widad tayi dariya tace "dama zaki dinga gayune, za kiga yadda zaki koma yarinya sharaf, amma indai baki dena ?azanta ba, to tabbas wataran za' a kalle ki ace shekararki sittin da 'yan kai"

Hari tayi kicin kicin da Fuska, dan Widad ta fara kaita bango, idan ta cigaba da biye mata to tabbas za suyi ba daWi, dan haka tayiwa Widad banza.

Widad ta ?arasa inda Hindu ke tsinke zogale ta zauna tace "Hindatu, ya ki keyi? bari in tayaki"

Hindu Ta gwadawa Widad yadda ake tsintar zogale, ta zauna suna yi tare.

Can Widad tace "Hindu, wai kuma idan kuna period bakwa amfani da pad ne? Se tsimma"

Hindu tace "meye kuma firiyios?"

Widad tace "A'a ba kije makaranta bane? Me yasa Common things idan na faWa, seki ce baki sani ba?"

Hindu tace "bari Amarya wallahi muna son karatun nan, amma ba yadda muka iya ne, kinga inda muke zuwa makarantar furamarai can wani ?auye ne, kusan ?auyuka biyar duk ita muke zuwa, to guri ba kusa ba nisa kafin kaje duk anyi wani abu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login