Showing 36001 words to 39000 words out of 135555 words

Chapter 13 - AKIDATA book 1 HAUSA NOVEL

17 Jan 2026

657

? ? ? ? ? PART1
? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ?? Page 10

Shiru Yusuf yayi yana bin Amal da kallo, tare da nazarin maganganun ta.

"Waye ya kashe Mahaifiyar Widad? Me yasa aka kasheta!!? Meyasa ake bibiya da barazana ga dukkanin wanda yake da kusanci da ita!!!? Meye dalilin rushewar binciken wanda suka kashe mahaifiyar Widad? Meye Ala?ar kisan Mahaifiyar Widad da wanda Widad tasa aka Waure!!!? Meye ala?ar ciwon Widad da ?wayar dake cikin tea Win da'aka kawo mata?

Wannan sune jerin tambayoyin da suka shiga kaiwa suna komowa a cikin ?wa?walwar Yusuf.

Ta Wago ta kalli Yusuf tace? "let's keep this aside, Yusuf ka taSayin budurwa? Ko kana da budurwa a halin yanzu?"

Jin tambayar Yusuf yayi wani banbarakwai, ta tuna masa da abu mafi ciwo a rayuwar sa da baze manta ba har ya koma ga Allah, ya kalle ta ya Soye damuwar sa yayi murmushi yace? "Budurwa kuma? Wacece zata so talakan mutum kamata? Ni bani da wata budurwa ni kaWai ne, ai nayi ?arami inyi budurwa"
Murmushi tayi tace "ka fiye abun dariya, a haka kamar baka magana, Amma ka iya sa mutum dariya, yanzu babba da kai kace kayi ?arami da budurwa?"
"Eh mana ko dan kin gani ?ato? Yarone ni ?arami"
Ta sake yi masa wani murmushin tace? "hmm Shikenan, kodai Widad kake so?"
Zare ido yayi kamar idon ze faWo yace? "Ni, rufamin Asiri, inani ina 'ya' yan manya, ai iyakacin talaka daku yayi muku aiki ku biyashi"
"Amma meyasa kake nuna damuwar ka a kanta haka? Dukda tarin wula?anci da rashin mutunci da take maka a wasu lokutan?"
"Saboda batamin wula?anci se idan na saSawa umarnin ta, kuma mahaifinta yana matu?ar mutuntani, kuma kinga nine a ?ar?ashin
ta, dole inyi ha?uri da duk abunda zata yi min"
Amal ta numfasa tace? "hakane, Amma ina shiga matu?ar ba?in ciki a duk lokacin da naga tana cin zarafin ka, shiyasa nake ganin meze hana ka ajiye mata aikin ta, in samo maka wani aikin ka huta da wula?anci?"

Yusuf yayi Murmushi yace? "Inajin daWin wannan aikin a hakan, bana so kiyi wani abu da ze Sata ran mahaifiyar ki, Amma ina godiya da karamcinki a kowane lokaci, tunda kin gama, muje in sauke ki a gida nima in tafi, kafin Madam ta farga tare muka fita dake"? yai maganar cike da ?o?arin basar da maganganun Amal

Amal ta jinjina kai ta mi?e, suka bar gurin.

***************************

"Bayanai sun sameni cewar, Akwai yuwuwar Bala ya tona mana Asiri, yayi i?rarin cewa tunda aka kaishi prison babu wani ?o?ari da muke dan fitar dashi, munawa kabmu ?o?arine kawai, dan haka na yanke shawarar in kiraka muyi wata magana, fatan zaka buWe kunnenka ka saurereni"

"To YallaSai, ina saurarenka"

"Hashim, Abunda nake so da kai shine, So nake a zuba magani a Abincin daza'a bawa Bala, wanda ze sashi rashin lafiya, daga nan se a kaishi Asibitin doctor Mukhtar, a can nake so a ?arasamin shi, a kauda shi daga duniyar gaba Waya dan baze Sata mana shiri ba"

Hashim Yace "Amma YallaSai aikin nan fa yana da hatsari sosai, kasada ne me girma, idan aka gano da hannuna a ciki zan rasa aikina, kuma za'a kamani"

A hasle mutumin yace "Kowace irin kasada ce gara ayita matu?ar Sunana baze fito ba, bazan zuba ido suna na ya Saci a banza ba ba tare da na cimma burina ba, Amfanin Bala ya ?are dan haka a kauda shi bashi da sauran amfani a gareni, kana da damar yin hakan, kana da dama a hannunka dan haka kayi yadda nace, tun kafin raina ya Saci"

Hashim yace "Amma YallaSai......

"Sadakin aikinka naira million biyu ne, idan ba zaka iya ba zan saka a gefe in saka wani yayi min, Amma kasani kaima bazan barka a doron ?asa ba tunda kasan sirrina, tashi ka fita na gama magana da kai "

**********************

Widad ta koma normal kamar ba ita ba, dan haka Daddy ya fara shirin komawa saboda Ayyukan da yake dasu, sedai sun fafata da Widad sosai dan ya sake yi mata batun Aure, ita kuma ta ?ara tabbatar masa tana nan akan bakarta ba gudu ba ja da baya, hakan yasa suka Wan samu saSani, ya tafi ba tare da tayi masa rakiya ba.

Yusuf yaje ya tsananta bincike akan gano waye mahaifin Nurat, wadda suka je gurin birthday Winta shi da Widad, ya samu bayanin wasu abubuwan ne daga gurin Amal, wadda ta riga ta gama narkewa a ?aunar Yusuf.
Mahaifin Nurat babban Wan siyasa ne, sukan haWu da mahaifin Widad a gurin kasuwanci, amma bayanai sun nuna akwai tsohuwar Ala?a dake tsakaninsu wadda daga baya tayi rauni, 'yarsa da Widad sun haWu a gurin karatu ne a ?asar waje, ita kaWaice ?awar Widad a Nigeria, se
'ya'yan Alhaji Bulama, shima ba wata ala?ace ta kusa tsakanin su ba, dan bata yarda a raSeta, ba kowa ke iya jure halinta ba.

Tsangwama ta yau daban ta gobe daban, haka Hajiya Halima, Ramla da ma'aikatan gidan suke nunawa Yusuf, shi kuma ko a jikin sa, aikin da yaje yi shi kawai yake.

Isa mai gadi yayi yayi yasan daga ina Yusuf yake zuwa, Amma fafur Yusuf ya?i gayamasa, daga baya ma se ya janye jikin sa, bayan gaisawa babu abunda ke shiga tsakankanin su.

Wasa2 aka shiga wata na uku, Amma Widad bata biya Yusuf ha??insa ba, shi kuma koda wasa be taSa magana ba.
Yusuf yana zaune a harabar gidan yana danna wayar sa, daga sama yaji ance? "Ssss" Waga kai yayi ya hango Widad ta saman bene, tayi masa alama da hannun ta yaje.

Yusuf ya mi?e ya shiga, tana zaune a falo tana cin gugguru, tana ci tana bawa magenta, Su Hajiya Halima na falon ita da su Ramla gaba Waya.

Yana shigowa Amal ta kalle shi tana kashe masa ido, seda yakusa faWuwa dan gani yake gaba Waya sunga abunda Amal tayi, Widad dake kaWa ?afa tana kallon Abunda Amal tayi, bata tanka ba ta cigaba da watsa popcorn Winta.

Gefen kujerar da Widad ke zaune yaje ya zauna a ?asan carfet yace?
"Gani ranki ya daWe"
Ta kalle shi ta yamutse tace?
"Kai nifa bana son all such kind of names, Malam sunana Widad, ka dinga kirana da sunana"
Murmushi yayi mata tare da Wan girgiza kai yace? "Bazan iya ba, nafi jin daWin ince Madam, ko ranki ya daWe"

"to bana so, niba basarakiya bace, ka kira ni da sunana kawai"

"Aike kinfi basarakiya ma gimbiyar Daddynta"

Wani Wan guntun Murmushi tayi, wanda ita kaWai tasan ma'anar sa.

Wani uban tsaki Amal tayi wanda bata san ya fito ba, ta mi?e a fusace da nufin ta bar falon saboda haushi.

"Amal!" Widad ta kira sunan ta. cak ta tsaya ba tare da ta waigo ba.

"Me nayi miki ne?" Widad ta jefa mata tambayar

Fuska a cunkushe Amal tace? "bakomai"

Murmushi Widad tayi wanda ya ?ara fito da kyawunta, tana girgiza santala santalan ?afafuwanta, sannan tace

"Kin san Widad bata Soyayya, balle ince zan so abunda kike so, shi kansa Son ban yadda dashi ba balle inyi shi, koda zanyi so bazan so ma?as?ancin Mutum kamar direba na ba, balle inyi wani abu da zesa kiji haushi saboda shi, ki kwantar da hankalinki ba abunda zanyi da wannan abun, rainin hankalinsa da ?warin gwiwarsa gurin karyamin dokoki ne ke burgeni wasu lokutan, ban taSa ma'aikacin da yake rainamin hankali da son yimin katsaladan a cikin lamaurana yadda yakeso kamarsa ba, wani abu dana fuskanta shine, ze iya jure duk wani hali da A?IDATA, hmm ki huta beb ba wani abun damuwa a cikin abunda nake" ta ?arasa maganar tare da wani murmushi na rainin hankali.

Yusuf ya kalli Widad, yaji haushin maganganun ta, ya ?udurce wani abu a ransa.

Ta kalli Yusuf cike da kashedi tace? "Kaikuma tara ka kawai nake, ina sane da duk abunda kake yi, ina gargaWinka akan contract Win daka sawa hannu, Ni kaWai na Waukeka aiki, ni kaWai zakayiwa Aiki, idan har zakayi soyayya or what ever Rubbish you call it, kayishi bayan ka bar gidan nan, hope I made my self clear "

Yusuf ya jinjina kai, a fusace Mummy tace "Aikuwa se naci uban Amal akan yaron nan, ka kiyayi 'yata ba kai ba ita, banda tsiyar Wan talaka ina kai ina Amal, ?warya tabi ?warya mana, wallahi duk lokacin da ka kuma shiga sabgarta sena saSa maka"

"Cewa akayi ana sonsa bashi yace yana so ba, ko ba kya gani ne? Kina za?ewa gurin ci masa mutunci wasu lokutan, na lura Daddy yana matu?ar ji dashi saboda biyayyarsa, yana girmama shi sosai, ko dan haka at least dole a Wagamasa ?afa saboda yana matsayi me girma a gurin megida, dan haka a dinga Waga masa ?afa a dena son shiga hurumin dabe dace ba"

Ta kalli Yusuf tace? "Aiken ka zanyi, kaje Wakina, ka Wauki key a drower mudubi, ka buWe wardrobe Wina ta ?arshe, ka Wakko ATM Wina kazo"

Ba Hajiya Halima ba har Ramla da Yusuf seda suka kalle ta da sauri.
Ta basar ta maida hankali kan talabijin, kamar ba ita tayi magana ba, jiki a sanyaye Yusuf ya mi?e ya nufi Wakin ta, gaban sa se faWuwa yake, inda ta kwatanta masa yaje ya Wau key Win ya buWe wardrobe Win da tace.

Ramla ta kalli Widad tace? "Amma Widad kamar be kamata kitura ?ato kamar wannan Wakinki ba"

Widad bata kalle ta ba tace?
"gayamin abunda ya kamata Uwata"

Ramla taja bakin ta ta tsuke, dan tasan idan taja maganar se ranta ya Saci.

"Subhanallah" shine abunda Yusuf ya furta, dan bayan sutura dake cikin wardrobe Win Widad, hadda bandir bandir na kuWi na Nigeria dana ?asashen ?etare.
A gagguce ya Wau abunda ze Wauka ya fita ya kai mata, maimakon ta karSa se ce masa tayi "Kaje na baka hutu na sati Waya dan ba inda zanje a kwanan nan, ina so kaje da ATM card Win nan, ka cire kuWi, ka siyomin latest trending phone me kyau guda biyu"

Yusuf yace "Yanzu zan siyo in kawo miki?"

?ura masa ido tayi ba tace komai ba, kallon gargaWi take masa akan bata son rainin hankali, dan haja Yusuf ya girgiza kai ze fita, Widad tace "Ji mana" ya tsaya tare da waigowa ya kalle ta
"Yanzu idan na tambaye ka kasan inda rai yake, wace amsa zaka bani?"

?oye mamakin tambayar da tayi masa yayi yace "Allah Mahalicci shikaWai yasan wannan Amsar"

Ta jinjina kai tace "Good you can go"

Hajiya Halima a gigice tace?
"Widad baki da hankali ne? Ya zaki bawa ba?o wanda baki san daga inda yake ba ki Wau ATM wanda Account Win cike yake da kuWi, YallaSai ma yana zuba dukiyar sa a ciki, kodan baki san zafin dukiyar ba sama taka aka tara aka baki, yanzu idan ya gudu ya?i dawowa fa?"

"Kalma ta farko kin faWi abunda ya dace a kaina, kin faWa daidai ba kuskure, bani da hankali ni mahaukaciya ce kamar yadda kuka saba faWa, dukiya kuma ta ubana ce, idan na salwantar da ita ba abunda zece tunda nima akwai tawa a ciki, ki dena tada jijiyar wuya akan dukiyar daba taki ba, idan tunanin ki abunda zaki samu bayan me ita ya mutu, sena tabattar da na ?arar da komai kafin ya mutu koni na mutu, shine hanyar da zan ba?antawa masu harin dukiyar nan rai, and Mark you idan wani abu ya samu dukiya ta a yanzu to ba shakka kece, saboda babu wanda yasan da ATM Wina a hannun sa seke da iyalanki"

Widad ta mi?e ta barmusu falon suna kallon kallo.

***********************
"Mummy, me yasa Daddy yayi yun?urin sawa a sace Widad ne? Am so much Confused fa, tunda akayi abun nan ta bar gidan nan bata ?ara kirana a waya ba"

Mahaifiyar Nurat tayi ajiyar zuciya tace "Nurat nima ban sani ba gaskiya, ni banda yanzu da kika gayamin ma ban san abunda yake shiryawa ba, yanzu ina magana ze iya Waukar mummunan mataki a kaina, kin san halin sa"

"Amma Mummy abun ya Wauremin kai, kinji yadda ya dingamin masifa dan na bari an Wauke ta, kuma fa wani ne yayi barazanar ze saceni nima in har ban gaya masa inda take ba"

"Mhmm Nurat, kija bakinki kiyi shiru da wannan maganar, dan muddin kika bari wani yaji maganar nan mun kaWe a gurin mahaifinki"

"Insha Allah Mum ba wanda zan gayawa"

*************************
Tunda Yusuf ya tafi da ATM Win nan Hajiya Halima ke cikin zullumi, dan ba ?aramar dukiya ce dan?are a account Win nan ba, tunani take yadda zata gano inda Yusuf yake, tasa a ?wato mata ATM card Win nan.
Ramla ta aika ta kira mata Isa me gadi, ba tare da Sata lokaci ba ya biyo Ramla jikin sa na tsuma zuwa falon Matar gidan.

"Kai wani irin sokon gara ne haka? Har yanzu ace ka kasa gano inda wannan talakan banzan yake?"

"Wallahi ranki ya daWe ya dena zama a cikin mu ma, wani girman kai yake ji da shi, yanzu shi kaWai yake al'amuransa ko inda muke ya dena zuwa, iyakacinmu da shi gaisawa"
Dogon tsaki Hajiya Halima taja tace? "dallacan sakarai ni rufemin baki, tashi ka bar nan sakarai kawai, ni na tsaya bi ta kanka, zan nemi wanda zasu yi min aikin".
Isa ya tashi jiki a sanyaye ya bar falon,
Mummy ta kalli Ramla tace? "Ramla meye abunyi ne? Me ya kamata muyi?"

"wallahi Mummy kaina ya kulle, na rasa abunyi, yarinyar nan ta tabbata mahaukaciya, Mummy idan dukiyar nan ta salwanta ya zamuyi?"

Hajiya Halima tayi ajiyar zuciya tace? "bana tunanin yaron nan ze gudu da ATM Win nan, Widad tana da wayo ze iya yuwuwa tarko tayi masa, Amma tunda harta yadda dashi haka, dole mu janyo shi cikin mu"

"Hakane Mummy zeyi mana Amfani, idan har ya kasance a Sangaren mu, Ammafa kamar zeyi taurin kai gayen"

'idan ya?i yin yadda muke so, then we should exact power over him, you know what I mean "

Ramla ta jinjina kai tare da yin murmushi tace
"Am proud of you Momma "

*****************************

Kwance yake akan makeken gado a wani tangamemen Waki me Wauke da kayan alatu, ya mimmi?e ?afafuwan sa hannun sa ri?e da waya yana kallon hotuna. Gefen sa wani matashin ne zaune a gefen gado yana tattaSa System.

Hotunan Widad ne akan screen Win wayar kala kala yana kallo yana murmushi, kowanne se ya tsaya yayi zooming Winsa ya ?are mata kallo, yanayi yana shafa sajensa tare da tattausan murmushi, ga dukkan alamu yana jin daWin kallon hotunan nata. A hankali ya furta
"Can't wait to see you darling"
Matashin da ke gefen sa ne ya waigo ya kalle shi yace?
"Nifa ka isheni, se kace akanka aka fara Soyayya, kullum se kayi zancen yarinyar nan seka kalli hotunan ta, kuma ban taSa jin ko waya kayi da ita ba"
Shafa sumar kansa yayi tare da yin murmushi yace? "bazaka gane bane Fahad, yarinyar ce 'yar daru se hankali, dukda ?anwa tace amma halinta daban yake, ina tunanin yadda zata karSi soyayya ta idan na bayyana mata"

"saboda me kake wannan tunanin?"

"saboda tace shi kansa son bata yadda dashi ba"

?yal?yalewa da dariya Fahad yayi yace? "Wallahi Anwar kana ruwa, se kace ita kaWaice mace kaje ka nemi wata mana, dama da ganin ta zatayi izza, nifa rabona da ita tun tana yarinya ?arama sosai"

Anwar yace? "hmm tabbas da zaka ga Widad a yanzu ba zaka taSa cewa in ha?ura da ita ba, Ina matu?ar sonta, na ?agu in koma gida, wallahi yadda na ?agu in ganta be kai yadda nake son ganin su Amal da Ramla ba, gashi seka rigani komawa da sati biyu"

Fahad yace "lallai ka tsunduma da yawa, nima ina son in koma inga Ramla, dukda ni muna waya da chatting da ita"

"Aishi yasa nake ta Addu'a, Allah ya bani Widad a matsayin mata"

Fahad yace "Hmm Allah dai ya baka me sonka"

***********************
Gaba Waya hankalin Hajiya Halima ya?i kwanciya, gashi duk wanda ze kaiwa Alhaji Nasir ?arar Widad to lallai zasu Sata, ranar kwana na bakwai da tafiyar Yusuf, Hajiya Halima se sintiri take tsakanin part Winta da babban falo, Widad kam ko a jikin ta shagalin ta kawai take.

Yusuf ne yayi Sallama a falon, Hajiya Halima na zaune a falon tun safe ta kasa sukuni seda? Yusuf yazo.
Abunda ya Waurewa Yusuf kai be wuce yadda yau ta sakar masa fuska ta amsa masa gaisuwar cikin mutunci ba.

Zeyi magana kenan yaji ?amshin turaren Widad, wanda ya alamta masa ta fito falon, waiwayawa yayi ita Win ce kuwa cikin shigarta ta ?ananan kaya kamar yadda ta saba, bakin ta Wauke da chew gum tana taunawa tare da lumshe ido, a hankali tana taku me Waukar hankali ta tako ta ?arasa shigowa falon, ta samu guri ta zauna ba tare da tace komai ba.

Yusuf ya tako zuwa gaban kujerar da take zaune ya dur?usa a gabanta ze fara magana, katse shi tayi ta hanyar yi masa alama da hannun ta na ya zauna akan kujerar dake kusa da wadda take kai.

Seda ya Waga ido ya kalli Hajiya Halima sannan ya tashi ya zauna yace?
"Ranki ya daWe ga sa?on"

Ya mi?a mata ledar wayoyin da receipt Winsu da kuma ATM card Win. Tasa hannu ta karSa, ta buWe ta ciro wayoyin manya masu kyau, ta jujjuya su a hannunta sannan ta kalli Yusuf tace "can i have your phone?"

Kallon ta yayi, tare da yin sororo
"are you deaf?" ta tambaye shi tana tsare shi da ido.

Ciro wayarsa yayi daga aljihu ya mi?a mata, Android phone ce, dukda ba wata me tsada bace Amma hoton sane da Ummansa akan wallpaper Win wayar, seda tayi nazarin hoton na wasu seconds sannan ta buWe wayar Yusuf ta cire sim cards Winsa da memory ta haWa da sabuwar waya guda Waya, da tsohuwar wayarsa ta bashi sannan tace

"i want see you tomorrow by 9:am Insha Allah, you will get your salary alert today, you can leave"

"amma ranki ya daWe, wannan wayar ai tayi min girma, kuma..."

Ai ko kallon inda yake bata sake yiba ta mi?e ta nufi part Win ta.

Gaba Waya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login