Showing 9001 words to 12000 words out of 135555 words

Chapter 4 - AKIDATA book 1 HAUSA NOVEL

17 Jan 2026

683

hannun ta babu jaka se key Win mota.
Guri ta samu ta tsaya, yayin da Yusuf yai sauri ya ?arasa inda take tsaye, gaban sa na ta dukan uku2, yaje gabanta ya Wan risina yace "barka da safiya ranki ya daWe"

Bata amsa ba, ta mi?a masa mukullin mota, yasa hannu biyu ya karSa a hankali ta furta masa Lambar motar da zata hau, kowace mota dake parking space tana da lamba, dan haka be sha wuya gurin gano wadda take nufi ba, abun da ya Waure masa kai shine kaddai a haka da wannan shigar zata fita?.

Ya fito da motar, ya fito ya buWe mata ?ofar Bayan motar, wuce shi tayi taje ta buWe gaba ta shige ta zauna.
Ya zagayo ya buWe shima ya zauna yana ta Addu'a, gashi besan inda za suje ba, haka yai shahada ya kunna motar Isa ya buWe musu gate, taiwa Isa Alama da hannun ta yazo, a guje jiki na rawa Isa ya ?araso gefen window Win da take zaune ya risina

"kwatanta masa gidan Bulama" ta furta kaman wadda aka yi wa dole, Isa yace
"kina nufin Alhaji Bulama Abokin Alhaji?"
?auke kai tayi tana kallon wani gurin daban, se Yanzu Isa ya tuna bata maimaita magana, ya gyara tsayuwa yayi wa Yusuf kwatancen gidan.

A hankali Yusuf yaja motar suka bar gidan, tunda suka fara tafiya babu wanda yayi wa wani magana, Yusuf ya dinga bin kwatancen gidan da Isa yayi masa, har zuwa ?ofar wani katafaren gida da suka zo ?ofar gate Win Yusuf ya kalle ta yace
"Nan ne ranki ya daWe?"
Shiru tai masa ko motsawa ba tayi ba balle ta kalle shi, Wan taSe baki yayi, yai horn megadi ya buWe ?ofa ya le?o yana ganin motar ya ja da baya da sauri, ya koma ya buWe gate Win gidan, gidan yayi kyau ya tsaru matu?a sedai be kai gidan Alhaji Nasir ba.
Yusuf yaje parking space yayi parking, kafin ya sakko ya buWe mata ta buWe motar ta fita.
Fitowa yayi shima ko da wani abu dazata bu?ata ya fito ya tsaya a bayan ta, me gadi ya ?araso cikin girmamawa yana gaishe ta, bata amsa ba tace "Bulama yana nan ne?"

"Eh ranki ya daWe, Amma bana jin ya tashi"

"Ace masa gani na zo, ya tashi ko be tashi ba be dameni ba, bazan haura mintuna talatin a gidan nan ba"

Da sauri megadin yace "Angama ranki ya daWe" nufi cikin gidan.

Ba tare da ta kalli inda Yusuf yake ba tace "biyo ni" ba musu yabi bayan ta, Wata rumfa dake harabar gidan me Wauke da fararen kujeru ta nufa taje ta zauna akan kujera, bayan ta yusuf ya tsaya ba tare da ya zauna ba.

Me gadi ne ya fito tare da wani matashi, matashin na ganin ta ya fara murmushi ya ?ara so inda take zaune

Matashin yace "Manya maganin ?anana, Dama yaran talaka irin mu na ganin ku?"

?an taSe baki tayi tace "Gurin Alhaji Bulama nazo, yace yana son gani na, a ce masa gani nazo"

Matashin yayi murmushi yace "Yau kuma a Alhaji Bulama yake ba Daddyn ba, WIDAD kenan, to ki shiga ciki mana ku gaisa da su Hajiya da Iman mana"

Yusuf a ransa ya maimaita "Ikon Allah wani irin suna ne wannan? Widad?

Widad tace "banzo da niyyar ganin su ba a yanzu"

"Shikenan bari ayiwa Daddy magana"

Har ze wuce ya kalli Yusuf yace "am Sorry young man bamu gaisa ba"

Ya mi?awa Yusuf hannu, Yusuf yayi murmushi ya mi?o masa hannu da nufin suyi musabiha, Amma Widad ta kalli Yusuf ta haWe rai tace
"don't try it"
A hankali Yusuf ya janye hannun sa suka fasa gaisawar, saurayin ya girgiza kai yace "Hmm bari in kira Daddy"

Yusuf a ransa yace "wai ita wannan shikenan kowa se dai yabi abunda take so? Kowa ma wula?anci take masa?"

Sunan a harabar gurin, aka turo 'yar aiki da kayan drinks da fruit ta kawo musu, yadda aka ajiye kayan ko kallon su ba tayi ba.

Ba tare da ta kalli inda Yusuf yake ba tace "duk wanda yazo gurin nan ban yadda ka kula shi ba, ba ruwan ka da kowa"

Yusuf yace "angama ranki ya daWe"

Wani babban mutum ne ya fito sanye da jallabiya fara ?al, a?alla zeyi sa' an mahaifin widad.

Ya ?araso gurin fuskarsa Wauke da murmushi, yaja kujera ya zauna ya kalli widad yace
"daughter yau kuma cikin gidan nawa ne baza'a shiga ba?"

"Eh bazan shiga ba banyi niyya ba, yanzu ma Daddy ne yace kana nemana nazo" ta bashi amsa kai tsaye

Alhaji Bulama yace "yanzu daughter ace kina Nigeria amma ki kasa zuwa ki ganni mu gaisa, ko na miki laifi ne?"

?an girgiza kai tayi tace "nafison zamana ni kaWai ne"

Alhaji Bulama ya kalli Yusuf yace "daughter shi kuma wannan fa?"

"driver nane, ba ruwan ka da shi"

"Shikenan naji ba ruwana da shi, amma idan bodyguards kike bu?ata ai za'a iya samo miki, wannan ba abunda ze iyayi miki"

Ba kunya Widad Ta kalli tsabar idon mutumin nan a gadaran ce tace "bana bu?ata, bana son kowa ya raSeni"

Alhaji Bulama yace "A'a daughter sama miki masu tsaron ki yana da mahimmanci, musamman tunda kin san amfanin hakan a tare da ke"

"Bana bu?atar kowa a tare da ni, bana bu?atar saka rayuwar kowa a hatsari, ban yadda da kowa ba dan haka bana bu?atar su"

Alhaji Bulama ya jinjina kai yace
"Amma daughter kin san likita ya hana ki wannan Wabi'ar kaWaice kan naki, rayuwa ba zata taSa yuwuwa a ce kina gudun mutane ba, ya kamata ki samu kiyi aure zaki samu nutsuwa, da kuma farinciki zaki rage kaWaicin nan"

Karon farko da Yusuf yaga dariya a fuskar ta, ba ?aramin kyau tayi ba da tayi Dariya ta wani jinjina kai cike da rainin hankali tace

"Alhaji Bulama kenan, an gaya maka rayuwar kaWaicin da nakeyi tana damuna ne? Karnuka na da maguna suna Webe min kewa sosai fiye da yadda mutane zasu yi min, tunda nasan sun baza su cutar dani ba"

Ta mi?e tsaye tsam ta kalli Alhaji Bulama ta haWe rai kaman ba ita ta gama dariya ba tace

"Ka cire wa zuciyar ka cewar ni widad zanyi Aure, ban yadda in zauna a ?ar?ashin wani ba yana juyani yadda yake so ba, in anyi Aure ana neman Aljanna ne, ni kuma idan nayi Aure sedai Rahamar Allah ta shigar dani Aljannah, ba dan zanyi wa wanda nake tare da shi biyayya ba, na faWa bazan zauna ?ar?ashin wani ba, babu wani farinciki da'ake a tsinta a Aure, babu komai cikin rayuwar aure se takura da matsaloli, NO MARRIAGE IN MY POLICY!!! Rayuwa ta da nake nika Wai ta fiye min bazan gayyato wa kaina matsala ba bayan wadda nake ciki"

Ba Alhaji Bulama ba hatta Yusuf maganganun Widad sun Waure masa kai, ita kam wannan wace irin zuciya ce da ita haka?

Inda motar su take ta nufa, hakan yasa Yusuf bin ta da sauri ya riga ta ?ara sawa inda motar take ya buWe mata.

Suna tafe yana lura da ita, ranta a Sace yake sosai, haka yayi tu?i a hankali koda suka je gida part Win ta ta nufa ba tare da ta kula kowa ba.

Yusuf kam rasa abunyi yayi, ita ba tace ta sallame shi ba ko A'a, ga mukullin mota bata karSa ba.

Bayan ya kulle motar Isa ya nufoshi yana murmushi yana zuwa yace
"har kun dawo kenan?"

"Eh min dawo malam Isa"

"to yaya, fatan dai bata maka halin ba?"

Yusuf yayi murmushi yace "niba abunda tayi min, ni yanzu damuwa ta ban sani ba ko ta sallameni ba tace min komai ba, ina son tafiya gida ne"

Isa yace "kaje ina? ai zama zakayi setace ta sallame ka"

Harar Isa Yusuf yayi yace
"shikenan ni bani da Abunyi na kaita inda zan kaita meya rage banda in tafi tawa sabgar, mahaifiya ta Nason ganina dan haka bazan zauna ba"
Yana gama maganar ya nufi ?ofar shiga cikin gidan, yana jin Isa yana kiransa amma yai masa banza.

Yana shiga yayi karo da Amal ta taho da sauri zata fkta.

Tana ganin sa ta tsaya tana ajiyar zuciya, taji wani farinciki na ratsa zuciyar ta Yusuf yace "barka da rana"

"Yawwa barka ya kake ya aikin?"

"Alhamdilillah, ga key Win mota? nan bata karSa ba ta tafi, ina son zan tafi gida ne inga mahaifiya ta"

Ya mi?awa Amal, be jira me zata ce ba yai waje abun sa.
Jinjina kai Amal tayi tace "lallai wannan besan wacece Widad ba, da alama shima kansa yana Wan rawa"
Babban abunda ya bata haushi irin yadda be tsaya ko gaisawar kirki sunyi ba.

Koda Yusuf ya koma gida ya sha tambayoyi a gurin Ummansa, seda ya tabattar mata da babu wata matsala sannan hankalin ta ya kwanta.

Tunda ya shiga Wakinsa yake sa?awa yana warwarewa, abubuwa da yawa sun bashi mamaki yana da tarin tambayoyin da besan me bashi amsar su ba, Amma kusan akwai alamar tambaya akan dukkanin iyalan gidan akwai wani Soyayyen abu da kowa yake Soyewa a ransa.

"Amma me yasa Widad ta zaSi rayuwar kaWaici akan rayuwa da mutane? Me yasa tayi wa Aure mummunar fahimta haka? Me yasa kowa yake biyayya ga Umarnin ta abunda take so, ko da kuwa hakan na nufin Sacin ran mutane ne?"

Bashi da Amsar tambayoyin nan, Shi ze nemowa kansa amsoshin tambayoyin.

Widad tana kan gadon ta ta ?urawa sama ido, Hawaye na bin gefen idon ta, Mahaifin ta yayi Sallama a Wakinta, tana jinsa amma tayi masa shiru, ta mi?e zaune a hankali, ya ?araso gefen gadon ta ya zauna ya kalli idon ta yace

"daughter ya akayi ne? Meke faruwa? Abbanki ya gayamin ko gidansa baki shiga ba iyakarki harabar gidan, daughter me yasa?"

"Bana son hayaniya ne, shiyasa na tsaya kawai a harabar gidan" ta bashi Amsa

Alhaji Nasir yayi ajiyar zuciya yace

"Alhaji Bulama ya gayamin yadda kuka yi, Lovely bamu yanke shawarar batun yi miki aure ba sedan na gaji da ganin halin dake ciki, Widad zuciya ta na shiga ?unci da irin wannan rayuwar da kike yi, kin san larura dake damunki, likita ya hana ki kaWaicewa, idan kika cigaba a haka fa ze cigaba da taSa ?wa?walwar ki, dan Allah daughter ki amince da ro?ona, kiyi Aure ina son ganin farincikin ki, ko baki yadda da kowa ba, idan dai zaki buWe ido kiga 'ya' yanki da mijinki zakiji daWi sosai, dan Allah Widad bani da kowa yanzu seke, se kuma Aminina Bukar Bulama, naso Inkuma samun yara bayan ke, Allah be bani ba, zanji daWi idan naga 'ya' yanki, please Widad help your Dad, nasan bana tunanin akwai wanda kika tsayar kike so, Amma nida Bulama mun yanke shawarar zaSa miki mijin da zakiyi Alfahari da shi, wanda ze nuna miki so ya kula dake ko bayan raina, Widad a yau idan na faWi na mutu bayan Alhaji Bulama bana tunanin Akwai wanda ze kulamin da Rayuwar ki, sannan kinsan a haWarin da muke daga ni har ke, please Widad ki Amincewa batun Auren nan, am sure if you got true love you will never regret been married, Akwai Soyayya da tausayi a cikin rayuwa da wanda yake son ka, na tabattar da Aure ze wanke miki dukkanin wani pain da yake ranki"

Tunda ta ?ura masa ido ko ?yaftawa ba tayi, seda ta bari ya gama, ta mi?e tsaye ta fice ta bar masa Wakin ba tare da tace komai ba.

Alhaji Nasir ya jinjina kai, babu alamar Nasara, Amma ya yanke wa zuciyar sa ze cigaba da lallaSata yana bin kanta, dan babu wata mafita da ta rage masa se Amincewa da shawarar Alhaji Bulama.
A fili yace "Wannan karon ke zakiyi biyayya ga unarnina daughter, duk wannan abun inayi ne saboda ke"

Widad kam gaba Waya maganganun mahaifinta haushi suka bata, kaman korarriya haka ta sakko daga kan bene, ta samu corridor ta tsaya tana zancen zuci, "wai Aure, waya gaya musu akwai Aure a tsarin Rayuwar ta? TaSWijan inyi Aure in zauna a ?ar?ashin wani yana juya ni yadda yake so? Ko kuma a haWa kai da shi a cutar dani, kaman yanda yake Wabi'ar mutane ne cin amanar wanda ya yadda da su, idan har Akwai mutane masu amana da suka rage a doron ?asa to sunyi nisa da duniyar da ni Widad nake ciki, waima waye ake cewa za'a haWa da shi ne Aure? Idan kuma ya zamana yana Waya daga cikin mutanen da nake nema fa, hakan yana nufin in masa Alfarma ko in Waga masa ?afa?

A fili tace

"Baze yuwu ba wallahi, ba wani Aure da zanyi, what is their in marriage apart from pains!, hurting each other!, tensions!, regrets and restriction of rights,!! No Impossible i want free life, i can't live under someone's control, i better live alone and die alone than to got married to irresponsible man of now a day's, bazanyi Aure ba, idan har Soyayya da sha?uwa basa hana Wan Adam ya cutar da Wan uwan sa, to tabbas Love doesn't exist is just an imagination, love does not exist talk less of true love, So shike sa ayi Aure, kuma yadda ce ke kawo so ban yadda da kowa ba, Daddy Bulama kayi min katsalandan bisa ga kawo wannan shawarar da Waya take da ?arasa gurgunta rayuwa ta" hawaye ne ya wanke mata fuska sharkaf se ajiyar zuciya take yayin da take maganar.

Ramla da tazo wucewa ta tsaya taji surutan da Widad take yi, ta jinjina kai a ranta tace "to Aure kuma? Waye ze auri wannan Jarababbiyar? Kuma mahaukaciya? Anya Mummy ta san zancen nan kuwa?

Widad kam ji tayi zuciyar ta tana wani irin raWaWi, ta fito harabar gidan da sauri kanta ko Wan kwali babu, dan gaba Waya ji tayi kaman tana cikin wuta dole ta fita dan ta samu sassauci,
Tana fitowa harabar gidan ta nufi inda Isa yake tace

"ina direban nan yake, yazo ya fita dani ya bar arear nan dani"

Isa ya kalleta ya kalli kayan jikin ta, mini skirt ne a jikin ta se wata riga armless, gashin kanta a baje kaman ta zare, Isa ya Wan ?are mata kallo, a ransa yace "Masha Allah, Allah ya yi halitta anan" yace
"Ranki ya daWe a hakan za'a fita dake?"
Kallon da yake mata ne da tambayar da ya tsareta da shi, yasa ta ?ara fusata ba zato ba tsammani Isa yaji saukar lafiyayyen mari a fuskar sa.

Gigicewa yayi ya dafe kuncin sa yace "ranki ya daWe ya tafi tun Wazu, nace ya tsaya amma yace baze tsaya ba yana da uzuri"

?an?ance ido tayi ta dubi Isa, a hankali tayi ?asa sa muryar ta tace
"Wan uban waye shi da ze saka hannu akan dukkan sharuWai na, kuma yau da ya fara min aiki har ya fara saSamin doka?"

Shiru Isa yayi yana sake shafa kumatunsa dan bashi da amsar da ze bata

"Wallahi sena masa wula?ancin da babu wata halitta data taSa yi masa, sena sauke dukkan ba?in cikin da nake ciki akansa, waye ubansa? Yana ?as?antacce zeyi watsi da dokokin da shi yasa hannu da kansa, Matsiyatan banza marasa Al?awari, shiyasa wani talakan har ya mutu baze Arziki ba saboda rashin sanin mahimmancin Al?awari da Amana, ya shirya karSar hukuncin da ba'a taSa masa makamancin sa ba"

(Nikam nace masu kuWi ne kawai suka san Al?awari da Amana? Ko kuwa Al?awari da Amana ce tasa suka yi Arziki? Shikenan idan mutum yana aiki a ?ar?ashin wani me kuWi se ya zama kaman Bawa? Shi besan jin daWi ba se Bauta? Bashi da wani 'yanci na walwala da jin daWi kenan? Tabbas da ba talaka ?aryar me kuWi yaji daWin Rayuwar sa komai Arzi?in sa kuwa, Naga kowane Wan Adam dai ajizine babu wanda baya kuskure, ke Widad ba kya kuskure ne ko kuwa? A ce mutum ya zabi Rayuwa shi kaWai ?wal ba mutane? Kowa be iya komai ba ciki hada mahaifinki, Gaskiya kin zafafa A?idojin ki, wata sabuwa kuma Widad tace "Love doesn't exist, is just an imagination talk less of getting true love" masu karatu wannan kaWanne daga A?idojin Widad

TIR?ASHI!!!

Yaseen Akwai cakwakiya, Hassada, Munafunci, tsantsar Soyayya, Fuska biyu, kutsen ?addara me sauya rayuwar bawa ko be shirya mata ba, da sar?a?iyar gaske a cikin wannan littafin kar ku bari a baku labari dan ya haWu.

Insha Allah ze cigaba da zuwar muku 1 ga watan September

Domin sharhi, gyara, ?orafi ko makamancin haka ku tuntuSeni akan
Wannan lambar ta what's app kawai
07063065680

Masu bina private akan in tura musu ABDUL JALAL dan Allah kumin afuwa, Abubuwa sunmin Yawa na kammala part two a document na sake shima, idan baku samu ba ku duba manhajar watpad a account Wina
Ayshercool7724 insha Allah zaku samu dama sauran litattaafai na.

Masoya a cigaba da ha?uri dani, sakamakon harkar makaranta da wasu abubuwan da suka sani gaba Insha Allah wannan littafi ze fara zuwar muku 1 ga watan September, a what's App, da? telegram groups Wina, da kuma Facebook a shafin mu na perfect writers Association, ko kuma YouTube channel dinmu

Ina godiya da Adduoin ku.

_*A?IDA TA*_


*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*
( WE ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS =ت?)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A
'?


*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *

And now *A?IDA TA *

I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum

Special thanks to all members of my Association
Perfect writers Association may Allah subhanahu wata'ala bless our pens and grant us wisdom to write what will bring positive changes to our Community.

I won't forget you my fans =?
?=?
?=?
? you are always in my heart, my love to you is endless, especially those that shows me love support and follow me with prayers since my first Novel to date, i can't mentioned you all but am proud of you all =?
?

HAUSAWA SUKACE KYAN AL?AWARI CIKAWA, KAMAR YADDA YAKE KOYAR WAR ADDININ MU CIKA AL?AWARI ABU NE ME MATU?AR MAHIMMANCI, NAZO DOMIN CIKA MUKU AL?AWARI,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login