Showing 102001 words to 105000 words out of 135555 words

Chapter 35 - AKIDATA book 1 HAUSA NOVEL

17 Jan 2026

673

damuwa yake yace " Madalla, Allah yasaka miki da Alkhairi Nurat, abokan kasuwancinsa da yakamata suyi wannan ?o?arin babu wanda yayi tunanin yin hakan, kowa harkar gabansa kawai yake, kamar ba wanda ya damu da halin da yake ciki"

Nurat tace "Hakane dama Yaya Anwar, kasan wani ya gayawa mahaifina naje duba Baban Widad, yanzu ya hanani fita kwata2"

Anwar yace "haba dai? Waye ya gaya masa?"

"Nima ban sani ba, amma insha Allah karka damu, zamu cigaba da communicating ta waya, ya jikin nasa kuwa?"

Anwar yace "to Alhamdilillah za'ace, yau dai naga jikin nasa ya tashi, dan se NG tube aka samasa tanan na bashi Abinci yau"

Nurat tace "Allah yasaka maka da alheri Yaya Anwar"

Anwar yace "Nurat kome nayiwa Alhaji Nasir Daula ai kaina nayiwa, karki damu Allah yayi mana jagora"

Ta amsa da Ameen.
Sukayi sallama tace "Alhamdilillah, saura kuma kuSutar da Yusuf, Allah ka bani ikon kuSutar dashi"? tunani ta shigayi, ta yaya zata san inda su Yusuf suke balle ta kuSutar dasu?

Yusuf, da Saleh se megari da samarin 'ya' yansa suka shigo gidan, hannunsu Wauke da goro dabino da alawa, uwargidan megari wadda suke cewa gwaggo tace
"Malam ya dai na ganku da kayan Waurin Aure haka? Bikinwa akeyi?"

Megari yace "ba?in 'ya' yanmu aka Waurawa Aure yau, ga naku kayan ?aurin Auren nan ayi musu addu'a"

Harira wadda itace matarsa ta tsakiya tace "TaSWijan kwaWo, auda ba matarsa bace suke kwana Waki Waya? Aikin gama ya gama ai, me kuma za'a Waurawa Aure?"

Megari yace "ina ruwanki? Meye naki a ciki? Ke bakinki baya taSa faWar alkhairi"

Saleh yace "ke Hari ki iya bakinki akan mutanen nan, bana son rigima fa kin san halina, uwar gulma kawai"
Dama sun saba faWa basa jituwa da Saleh sam

Gwaggo tace "daka gayamana da wuri, aida mun Wanyi girki mun gayawa ma?wabta"

Saleh yace "gwaggona 'yar Aljanna, karki damu hakanma mungode, Allah yasaka miki da alkhairinsa"

Daga nan Yusuf da Saleh suka wuce Wakin Widad, tana sanye da hijjabi da alama salla ta idar, tana zaune a gefen katifa suka shigo Wakin, Yusuf ya ?araso gabanta ya ajiye mata goro da alawar Waurin Auren, ya mi?a mata sadakinta yace "uwaWakina ga Sadakinki nan, an Waura Auren"

Ta Waga kai ta Wan tsurawa Yusuf ido, sekuma ta sunkuyar da kai tana zubda hawaye, Yusuf yace? "me kuma ya faru?"
Girgiza masa kai tayi alamar bakomai, yace "ga sadakinki nan, ki karSa na kine"

"ka barsu a gurinka ni ba'abunda zanyi dashi"

"Ai ha??inki ne, mallakin kine"

"Nikuma nace ka ri?e" tai maganar a Wan hasale

"Ai hakan baze yuwu bane, amma ki dena kuka kinji, bana son yawan kukan da kike, nidai tunda na sanki kusan kullum cikin kuka kike, dan Allah kiyi hakuri ki sassautawa zuciyarki, wallahi ba ?aramin damuwa nake shiga ba idan naga kina kukan nan"

Saleh yace "dalla in bazata karSa ba, ka sai mata Wan Akuya da kuWin, idan na tafi ka zauna kayi ta rarrashin nata, kazo muje zanyi magana dakai, ina son in tafi kafin mutanen nan su farga"

Alhaji Musa ne a tsaye, hannunsa Wauke da waya yace "wai kaji abunda naji kuwa, wai an Waga taron kasuwanci na kamfanunnukan Daula saboda bashi da lafiya"

Wanda yake wayar dashi yace "Naji, ?arewa ma ni message aka turomin"

Alhaji Musa yace "to wani matsiyacin ne ya shirya hakan? Waye da wannan aikin, ya'akayi ma turawan nan suka san da bashi da lafiya?"

"Nima ban sani ba, nayi iya bincike na ban gane wanda ya gaya musu ba, amma dole muyi wani abu akai, idan wannan damar ta wuce mu, kuma bamu samu abun hannun 'yarsa ba to tabbas zamu tafka gagarumar asara"

Alhaji Musa yace "Shikenan, dole muyi meeting yau ?arfe biyu na dare, zan sanar dasu Alhaji Haruna"

Ya kashe wayar yana cigaba da masifa, wayar ta sace ta sake fara ringing, a fusace ya Waga yace "meye waye?"

"Me Adda ne"

"Yawwa me ake cikine me Adda? Ta faWa Win ko kuwa? Kaga idan bata faWa ba, kusa flier ku dinga cire mata yatsu Waya bayan Waya har seta faWa"

Me Adda yace "ka tsaya ka saurareni da kyau, yau kwana biyar kenan sun gudu da inda muka ajiye su, mun zaga ko'ina a dajin nam bamu samesu ba shine ma yanke shawarar in sanar da kai"

"what!!!"




(Mutanen Zamfara masu an yanke mana Network, da masu Anty cool daga farko, dan Allah idan kuna da manhajar Wattpad, idan kukayi searching Win littafin A?IDATA kokuma Ayshercool7724 zaku sameshi tun daga farko har inda na tsaya, kuna bani aiki yaseen =?D?=?D?=?D? duba ga yadda ake ta yaWa cewar what's app ze dena aiki dukda bani da tabbas, ga link Win group Wina na telegram nan meso se yayi joining
https://t.me/joinchat/SYIfEaoQo_JlNDM0 ina godiya da ?aunar ku masoya =?
?=?
?=?
?)

Domin gyara, sharhi ko shawara
Ayshercool
07063065680

? ? _*A?IDATA*_
? ? ? ?

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*A?IDA TA *

I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum

Ha??in Mallaka ?& : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ?unsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani Sangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

NOT EDITED

ELEGANT ONLINE WRITER'S

? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ?? PART1
? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? Page 32_33

Alhaji Musa yace "Me Adda, ina irin wannan wasan da kaine? Wace irin maganar banza kake faWa haka?"

Me Adda yace "ba maganar banza bace, roofing kwano suka buWe suka gudu"

"Roofing kwanon ne ba kuyi da kyauba kokuwa?"

"wallahi munyi komai yadda yakamata, ni babban abunda ya bani mamaki be wuce yadda ko iya mi?ewa tsaye ba sayi saboda wahala, amma suka iya tserewa, ni yanz....

Alhaji Musa ya katse shi ta hanyar cewa " kaga dalla rufemin baki, na yadda da ?arewarka? a wannan fannin shiyasa na baka aikin nan, amma ka kunyatani, shekara nawa kayi kana aikata irin wannan Aikin? Miyagun ayyuka mawa ka aikata kana Nasara, amma se yanzu wannan Wan ?aramin aikin ka bari har suka gudu saboda hauka, wallahi tun wuri ka nemo su na gaya maka"

Ya ajiye wayar tare da yin jifa da ita yana dafe kai, jinjina kai yayi yace "Akwai babbar matsala"

Ramlah ce kwance akan gadon Hotel, se bacci take yi kamar matacciya, ta lulluSe jikinta da blanket, Fahad na gefenta yana ta busa shisha.
Seda yasha me isarsa sannan ya duba agogon hannunsa, ya mi?e zaune dagashi se gajeren wando, yaye blanket Win da Ramlah ke ciki yayi ya Wagota zaune, ko sutura babu a jikinta, busa mata haya?i yayi a fuska, a hankali ta motsa ta fara tari, buWe idanunta tayi wanda sukayi mata matu?ar nauyi ta kalle shi.

Fahad yayi wani murmushi irin na 'yan bariki yace "baccin ya isa haka, yakamata mu koma gida, kafin yaynki ya fara masifa"

Mi?a tayi ta sake kwanciya a jikinsa tace "?arfe nawa ne?"

"?arfe takwas na safe" ya bata amsa, ba shiri ta watsakke tare da zaro ido tace

"takwas na safe, na shiga uku Fahad, wacw irin ?waya ka bani haka? Me zan cewa Mummy?"

Murmushi yayi yace "matsoraciya kawai, ashe iskancin naki na ?arya ne, karki damu baby zance mata a gidanmu kika kwana kawai"

Tayi ajiyar zuciya tace? "kuma kasan Mummy tana yarda da maganar ka sosai, har naji daWi wallahi I love you Fahad"

"Love you too baby"

"Fahad tunda Widad ta Sata zaka Aureni?"

Ya sake rungumeta yace? "idan ban Aureki ba wa zan aura? Itama na yadda da Aurenta ne dan in Aureta in Wula?anta ta, Allah ya temake ta wannan abu ya faru, amma a duniya in bake ba wace macece ta dace da Fahad?"

Murmushi tayi tama jin daWin kalamansa ma yaudara suna ratsa ta.

Saleh ya kamo hannun Yusuf suka fito waje, Saleh yace

" Samun mutum managarci me Amana kamarka abune me matu?ar wahala Yusuf, ka cika mutum nagari abun a jinjina masa, iyakar sadaukarwa kayi ta, ina fatan wannan Auren anyi shi kenan har gaban Abada, duk macen da ta auri namiji irinka yakamata ta gode Allah, nasan kayi ha?uri a baya dan haka ina fatan ka ?ara ha?uri, Widad yarinya ce me tsiwa da girman kai amma zakaji daWin zama da ita, saboda tana sa sau?in kai ga wanda ya gane kanta, dan wani lokacin gane kanta se a hankali, nasan zata baka wahala kafin ta saba da zaman garin nan, amma kayi ha?uri a hankali zata saba, babu wanda ta sani a yanzu daga Allah se kai, ka ri?e Amana Yusuf babu tabbacin ku koma gida Widad ta tarar da mahaifinta a raye! "

Wata irin mummunar faWuwar gaba Yusuf yaji, yace " Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, me kake Nufi? "

"tunda kuka Sata Daula yake gadon Asibiti, kullum zancensa 'ya' yana wani hali suke ciki? An Waga taron da suke burin ayi suyi amfani da sunan Daula su damfari biliyoyin kuWi, yanzu idan suka farga kun gudu akwai gagarumar matsala, maganar da nake maka matarsa ba ita take jinyarsa ba, tana can tana shagalinta, babban Wanta Anwar shike ta sintirin jinyarsa, sannan an bawa likitansa ma?udan kuWi sunce yayi duk me yuwuwa kar Daula ya warke, Nayi duk ?o?arin da zanyi a rabashi da Asibitin amma ba hali, muddin nayi wani babban yun?uri komai ze lalace "

Yusuf ya dafe kai ya shiga jera salati,
"Rananar da'aka Waukeku ni naje na janye Motar da kuke ciki daga titi na maida ita, aka cire lamabr motar, shiyasa na samu wayoyinku da kuma wannan Akwatunan naku, amma bazan baku wayoyin ba, dan nasan tabbas za'a iya tracking Win inda kuke, zan kawo maka ?aramar waya da sim wadda zamu dinga communicating da kai, mahaifiyarka na gaisheka tana ta samaka Albarka "

Yusuf kasa magana yayi se zuciyarsa daketa faman tafasa, suka nufi turakar megari Saleh yace? " Baffa zan koma yau, na bawa ila kuWi da kayan aiki, zezo yayi musu banWaki, wallahi nan da kwana uku idan beyi ba, yasan halina, na bashi isassun kuWi wallahi na dawo beyi ba koya cinye kuWin sena karya shi, kaja masa kunne"
Megari yace
"Subhanallah zeyima Insha Allah, Wakin nan da bakomai shi za'a gyara ba wani abu, ai kaine ka sashi zeyi insha Allah"
Saleh yayiwa Megari sallama, Yusuf ya Wanyiwa Saleh rakiya sannan ya koma.
Gaba Waya kamar an zarewa Yusuf laka jin maganganun da Saleh ya gaya masa, ji yake tamkar mahaifinsa ne a wannan haWarin, wani irin tausayin Widad ya kama shi.

Ya shiga gidan yana takawa da ?yar, gwaggo ce tace "Malam Yusufa Allah ya Sanya Alkhairi ya baku zaman lafiya, yasa anyi kenan kasan lamarin Aure se anyi ha?uri Allah ya baku zaman lafiya"

Yusuf ya ?a?aro murmushi yace "Ameen ya Allah nagode sosai"

Gwaggo tace? "sedai akwai Wan bikin Al'ada da mukeyi anan in akayi Aure, yakamata mu gayyaci mutane mu Wanyi mu tayaku murna"

Yusuf yace "Allah sarki Mama, base kin wahal da kanki ba, kinga ita Amaryar ma bata cikakkiyar lafiya kuma har yanzu a tsorace take, baki ga ko magana bata sonyi ba, Addu'ar ku da kulawar da kuke bamuma mungode sosai"

Gwaggo tace "shikenan Allah ya bata lafiya"

Yusuf yace "Ameen"

Jiki babu ?wari ya ?arasa Wakin nasu, kayan Waurin Auren suna nan a inda suke, da kuWin sadakin nata, tana zaune ta haWe kai da gwiwa se rusar uban kuka take.

Dole Widad tayi kuka, rayuwar ta cike take da ?addara daban daban, a hankali ya ?araso bakin katifar ya zauna, sam bataji zuwansa ba seji tayi ya taSa ta, a Wan razane ta Wago ta kalleshi, ganin Yusuf ne yasa ta maida kanta kan gwiwarta ta cigaba da kukanta.

Yusuf yasa hannu ya Wagota yana kallon yadda farar fatarta ta koma ja saboda kuka da wahala.
Girgiza mata kai yayi amma yakasa ce mata komai, dan bema san ta'ina ze fara ba, Widad ta cancanci tayi kuka.

A hankali tasa hannu ta ture nasa hannun ta kwanta, tare da Wora hannunta akan fuskarta tana ci gaba da kukan, A hankali take furta
"Ya Allah, aslihli sha'ani kullahu, wala takilni ila Nafsi, Warfatu ainun"

(wuya koda magani ba daWi, ashe Widad ta iya Addu'a haka =?D?)

Yusuf ya zauna ya zuba mata ido wai a hakama bata san halin da mahaifinta ke cikiba kenan, inaga inta sani.

Yarone yayi Sallama Wakinsu Yusuf, Yusuf ya amsa, yaron yace "Wai gashi inji gwaggo"

Yusuf ya karSi ?waryar da'aka rufeya da faifai, yace "Masha Allah, kace mata mungode"

Yaron yace to ya fita, Yusuf ya ajiye ?waryar yayi shiru yana kallon Widad da jikinta har rawa yake saboda tsabar kuka.

Yusuf yayi shiru, abubuwa suka cinkushe masa kai, nan da nan kansa ya fara sarawa, ya jingina da jikin bango ya rasa abunda yake masa daWi.

A hankali Widad ta buWe idonta, ta kalli inda Yusuf ke zaune yayi shiru, jijiyoyin kansa duk sun tashi, ga idonsa yayi ja kallo Waya zaka masa kasan a cikin damuwa yake.

Ta mi?e zaune a hankali, yai saurin juyowa yana kallonta, ta goge hawayenta tace
"me'aka kawo? Yunwa nakeji"

Yusuf yace "ban san me'aka kawo ba bari im duba"

Ya Wakko ?waryar ya duba, fura da Nono ne aka dama, tace "bani cokali a can gurin"

Ya duba ya Wakko mata, ya bata. Sosai take jin yunwa ta Wiba ta kai bakinta, ajiye cokalin tayi a gefe ta kafa kai ta dinga sha, tasha ya kai rabi sannan ta ajiye, ta koma gefe ta zauna tana lumshe ido.

Yusuf yace "kin ?oshi ne?" ta jinjina masa kai ba tare da ta buWe idonta ba, yasa hannu ya Wau wadda ta rage ya fara sha, an zuba zuma a cikin furar shiyasa tasha da yawa.

Gaba Waya Yusuf tausayi yake bata, beji ba be gani ba ?addara ta haWasj se wahala suke sha tare, duk abunda za'a kawo na Abinci indai zata iya ci, se taci ta rage sannan zeci, kuma seya tabattar ta ?oshi sannan ko yaya ta rage shima yaci.

Kallonsa take yadda ya du?a yana shan furar, wadda ba isarsa za tayi ba, ta lura shidai a rayuwarsa be Wau komai da zafi ba, irin mutanen nan ne da duk yadda rayuwa tazo zasu karSeta a haka.

Yusuf ji yayi kamar tana kallonsa, ya Wago kai ba tayi zato ba suka haWa ido, tao saurin Wauke nata idon.

Jiki a sanyaye yace "har yanzu dai kukan baki dena ba? Yakamata ace zuwa yanzu kin sawa zuciyarki ha?uri, kukan nan bashi da amfani, kina ?aramin damuwa akan wadda nake ciki ne"

"Ni nace ka damu dani ne? Don't try to comfort me when ever am crying, kaji da damuwarka kaima"

Yusuf yace "tun daga lokacin da kika fara kuka saboda damuwa zuwa yanzu, maganin me kuka yayi miki? Kuka baya maganin damuwa wasu lokutan sema dai ya ?ara maka ?uncin zuciya, ina tare da ke a guri Waya ta yaya zan zuba miki ido kiyi ta kuka, kina wahalar da kanki da yawa "

" kowa yaji da kansa malam ka dena damun kanka akaina"

Yusuf yace "Ai bazan iya bane, in dai kina kuka nikuma zuciyata rauni take"

Tsaki tayi tace "Se kai tayi ai"

Yusuf murmushi yayi bece komai ba.

Can tace "yanzu kaga death contract Win da nake gaya maka muddin zakayi aiki dani ko? Meyasa baka yi tunani akai ba kasa hannu, dukda na gaya maka haka? "

Yusuf yace "saboda shi bawa baya taSa tsallake ?addararsa, Allah ya ?addara se haka ta faru"

Shiru tayi ta shiga duniyar tunani, tana cikin tunanin ne bacci ya kwasheta daga nan inda take zaune, ta lan?washe wuyanta.

Yusuf ya mi?e yaje da nufin ya gyara mata kwanciya saboda wuyanta, ashe baccin nata ba nisa yayi ba, ta buWe idonta ta kalle shi, haWe rai tayi tace "meye haka?"

"yi ha?uri, gani nai kin lan?wasa wuyanki, kar yayi miki ciwo kuma bana son in tasheki"

"to ina ruwanka inma yayi min ciwon? Dalla cikani kuma karka ?ara taSani na gaya maka"

(Nikam nace Mamaki =?? jimin mara kunya, sekace yau aka fara)

Murmushi yayi yace "shikenan Allah ya huci zuciyarki"

Ta kwanta tareda juya masa baya, Yusuf ya ?ura mata ido tare da yin murmushi a ransa yace 'insha Allah sena maye gurbin wannan damuwar taki da farinciki'

Yusuf ji yake kamar bashi ba, wai shine ya Auri Widad, yasan badan ?addara ta Ubangiji ba, kamar shi a yadda yake ya Auri mace irin Widad kyakkyawa 'yar me kuWi haka, sedai wani iko na ubangiji.

Haka nan yake fatan Allah yasa su kasance tare har Abada, Allah yasa idan ta gano waye shi karta guje shi.

Misalin ?arfe biyu da rabi na dare, Nurat taji motsi a harabar gidansu, ta le?a ta taga ta hango mahaifinta ya fita shida direbansa, tunani ta shiga yi ina mahaifinta zeje a wannan daren haka? Tashi tayi ta tafi Wakinsa, ta murWa ?ofar a hankali ta shiga, ?ar?ashin gadonsa taje ta Wakko wayarta da ta ajiye ta kunna recording.

Tayi saving ta fito daga Wakin ta koma nata Wakin, anan taji wayar da yayi da batun kuSutar su Widad, da sauri ta mi?e tsaye tana Alhamdilillah, ta dinga kunna recording Win tana sake saurara, hankalinta ya koma son sanin me zasu tattauna a meeting Win da zasuyi a wannan tsakiyar dare kamar wasu matsafa.

Babban falon Hotel ne suke zaune, sunyi jugum jugum kamar masu jiran tsammani kallo Waya zaka musu kasan suna cikin damuwa.
Alhaji Haruna yace? "jama'a ayi magana, abubuwa da sun taho kamar abun arziki, amma yanzu komai taSarSarwa yake, ta yaya za'ace sun gudu se kace a film, ko wata tatsuniya.

Alhaji Munir yace "nima abun ya Wauremin kai, ga kuma wannan samu da rashi da muka gani, muna shirya abu amma wai an fasa taron, wannan shegun turawan ne suka ce a Waga, na rasa wani ba?in munafukin ne ya gaya musu ba, nifa kaina gaba Waya ya kulle"

Alhaji Musa yace? "babu yadda za'ayi ace su kasa jim rashin lafiyarsa ko kun manta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login