Showing 21001 words to 24000 words out of 93691 words

Chapter 8 - RASH ƁOYAYYEN MASHEƘI. COMPLETE HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

212

ta sauke na ta wanda suka cika da hawaye dan ita sam bata da juriya akan komai kuka yake yi

" Kinsan ni masaki ne koh?."

"Eh." ta furta tare da share hawayen ta, ya so yayi mata faɗa sosai a kan shiga mai rayuwa data yi amma yaji an ce bata da masaniyar wa zata aura kawai an ce an mata miji ne kawai.

"So nake muyi rayuwa kaman mata da miji a waje amma a cikin gidan nan kowa ya yi harkan gaban sa." maganan sai da ya dake ta amma ta daure ta ce

"Ko zan iya sanin dalili? Shin dole aka maka da ka aure ni ko yaya ne?." Sai yaji ta bashi tausayi amma ya dake ya ce

"No akwai dalili banda lafiya ne, ina akan wani tsarin maganine wanda nan da watanni uku zan ga ma sha shiyasa, sannan ni ban san za'amin aure ba sai a jiya kinga ko bazan iya bijirewa ba."

"Shikenan." yaji daɗin amince wa da ta yi babu wani tambayan sai yaji ta burgeshi

" Me sunan ki ?."

"Ramlat." sai kuka ya kwace mata ace wai mijinta ne besan sunan ta ba miƙewa ta yi take fuskanta tabayyana sosai kaman zata ce wani abu sai ta share ta nufi ɗakinta zata shiga kenan taji ya na ce wa

" Zo ki dauki abinci."

" Na ƙoshi." ta shige tare da rufo ƙofa, da ƙyar ya dafa ya sauka akan keken ya hau kujera tare da lumshe idanuwan sa, amma jin sautin kukan ta yake yi kaɗan-kaɗan, ji yayi baze iya jurewa dan ya tsani kukan mace, a hankali ya janyo basket din abincin tare da hawa keken yanufa ɗakin nata, babu key dan haka ya tura ya shiga tare da sallama. can kan bed ya hange ta ta nada kuka, sai yaji duk babu daɗi, a daddafe ya hau gadon kusa da ita hannu yasa ya gyara mata hijab din kanta sannan ya ce
" I'm sorry Ramlat, ki bar kukan ya isheni amsa kici kinji." daƙyar ta tsai da hawayen ta, amsa abincin ta yi ta'aje gefenta sannan ta ɗan matsa ganin yana gab da ita.

"Faɗamin me na miki?." ya tambaya yana mai kallon kyakkyawan fuskan ta mai kyau

"Ni shikenan haka zanyi rayuwa ace babu ruwan kowa da kowa, ai ba haka addini yace ba." take tafara jawo mai ayoyi akan aure ta na fassara mai, mutawar zaune yayi jin yadda ta ke ta kawo hukunce hukuncen sosai akan aure, sai da yaja dogon nunfashi sannan ya ce

" Shikenan zamu zama abokai kenan kafin nasamu cikakken lafiya koh?."

"Ni bance ina buƙatar ka ba amma tuna maka na yi, be ka mata naga kana ƙoƙarin hala na taimaka gurin faɗa wa ba, so nake mu taimaka ma juna gurin shiga aljanna. ba damuwa na amince muyi abota." murmushi ya yi, yau dai an samu macce da ta burgeshi a karo na farko, a ransa yana cewa 'ai wannan dole na zauna dake ko dan ilimin ki da sani nishaɗi.' kallon ta kawai yake yi dan ta burgeshi sosai yana kallon yadda ta ke cin yam ball din a cikin ƙaramin bakinta, sauka yayi yahau keken san sannan ya ce

" Na gode kin min halacci duk da ance miki ni masaki ne amma kin yadda kin aure ni, Insha Allah zan saka miki da mafificin alkairi, kishirya nan da 1h ƙanaina zasu shigo gaishe mu sannan za muje gaishe da iyayena anjiman." da ido ta bishi har ya fice, jita yi ta raina kanta sosai duk da shi masaki ne amma kyauwunsa ya toshe rashin ƙafarsa, fari ne fat kaman ka taɓa jini ya fito, haka ƙafafunsa kaman na jarirai. murmushin sa me tafiya da imanin mutum ta tuna.......

END
✍️✍️✍️ꜱᴀᴋɪɴᴀ ᴀʙᴅᴜʟʟᴀʜɪ

[6/13, 22:30] ᑭᖇᗴTTY ՏK ✍️✍️✍️: https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

💪 JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIAION (J.W.A)💪
Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi.✍️

If marriage is part of your plans this year, may Ar-Razzaq open beautiful doors for you & bless you with someone who leads You to Jannah

𝐑𝐀𝐒𝐇 Ɓ𝐎𝐘𝐀𝐘𝐘𝐄𝐍 𝐌𝐀𝐒𝐇𝐄Ƙ𝐈
ᑭᖇᗴTTY ՏK
ꜱᴀᴋɪɴᴀ ᴀʙᴅᴜʟʟᴀʜɪ

page 15

************ **************
Suna zaune a Parlour aka yi Knocking, permission aka basu suka shigo dukan su, sun sha kyau kaman za su wani bikin, dan yau akwai walima da yamma, jallabiyoyi baƙake suka sanya da vails, simple make-up aka mu su ma sha Allah, gaishe su suka yi, sai suka amsa sannan Aliyu ya shiga ɗaki ya barsu dan amsa call ɗin ya da shigo wayan sa, shuru ya ratsa parlourn na wani lokaci sai Baby ta ce
"Aunty Meera wai ke Police ce in ji Uncle?." Meerah murmushin ta yi ta na mai da Idonta gareta dan kallon t.v take yi

" Eh kuma ni sam bansan raini, in mutum ya shiga gabana harbe mutum kawai nake yi." tafaɗa ta na haɗe rai dan ganin irin kallon da Kandy, Beasty, Beauty da Karis ke mata yasa ta faɗa haka.

" Kwarai kuwa Madam ba ta da sauƙi ko kaɗan, kubita a hankali shine kawai." Aliyu ya faɗa bayan ya iso Parlourn, ko 5mnt ba su ƙaraba suka fice abinbsu, suna fita Aliyu ya yi dariya ya na ce wa

"Ai kin min dai-dai, dan halinsu sai haƙuri, Baby, Hasty da Husty sun fi sauƙin kai."

" Tsaf zan se ta su kuwa, dan ni ban ɗaukan raini.".

****** Knocking din ma cikin ladabi suka yi dan ba'a wani jami'in sosai, sun jima suna yi kafin Ramlat ta ji sai ta buɗe cikin sakin fuskan ta na musu iso, da ma sunji labarin ta an ce ƴar talakawa ce, dan haka ba dukkan sune suka gaishe ta ba.

A kallo ɗaya Ramlat ta ga ne Kandy sai ta basar dan ta haddace fuskan ta sosai, ita ma dan niƙaf ne da ta shaidata, can sai ga shi ya fito, shima gaishe shi suka yi sannan su ka fice dan ba sa son zama inuwa ɗaya da shi.

"Lafiyan su na ga sun fice kaman sun ga dodo."

"Ai haka su ke kallona kaman wani mugu."

" Uhmm faɗi gaskiya dai." sai da ya yi murmushi sanann ya ce

" Yanzu ni na miki kama da mugu?."

" A'a amma in ka haɗe rai sam ba ka kyen gani, Yaya Shuraim naji wa su sun ce, wasu kuma Babban yaya koh?."

"Eh dukka sunan ne, akwai ma su cemin Boss ma."

"Uhmmmm Boss kenan, okh ni ma Babban yaya zan ce yafi Shuraim daɗi." ji yayi kaman ita ce ta raɗa mai sunan dan yadda ta furta cikin ba ma ko wani kalma haƙƙinsa.

"Kefa matata ce ya ka mata ki zaɓi wani suna daban haka."

"Uhmmm toh ba ra na dinga ce ma Zawji, tin da dai Zawjin ne."

" Ni kuma zan faɗa miki amma ba yau ba." Daga nan suka sha hira kaman sun san juna har da ba ta labarin aikinsa na Business Online a haka har suka nufa part din Pazars a can suka tadda su Haidar, nasiha a ka musu sosai sannan Pazar Q yaji daɗin ganin su cikin farin ciki dan Ramlat ita ta turoshi duk da keken me tafiya ne da kansa.

** AFTER ELECTION DAY **
Gaba ɗaya Kaduna state kowa yana son jin saka makon zaɓen Governor wanda ya gudana jiya, T.v gaba ɗaya ƙirgan ƙuriƙu a ke ta yi. Bayan sa'a ɗa ya da farawa aka faɗi wanda ya ci wato Aliyu Haidar Ƙanƙara shine governor na Kaduna state ƙarƙashin jam'iyar NPP me alaman fatanya, ta ke murna ya cika wasu, wasu kuwa a nata ƙus-ƙus a gari. Bayan kwana biyu ya yi rantsu tare da fara aiki, an bashi gidan gomnati amma ya ce a nasu gidan ze zanan, harta Meerah ba ta sa ni ba sai a yau da aka nunnuna a duniya da shafukan sa da zumunta, mamaki ne ya cika ta amma haka tabasar har lokacin daya dawo, nan fa ta fara balbale shi da bala'i, haƙuri ya dinga ba ta amma dagyar ta haƙura.

*********** *************
sanye ya ke cikin baƙaƙen kaya kamar kullum yakulle fuskan sa da mask wanda ya kewaye face dinsa, miƙewa ya yi tsaye ya fara ta kunsa mai ɗaukan hankali sannan yakalli camera ta re da fara magana cikin kakkausar muryansa.

" Nasan kun jiini shuru kwana biyu, na ɓuya to ina nan kuma ina muku albishir da ce wa yau zan sheƙe muta ne uku, babu ɓata lokaci zan fara da wani ɗan Edo state, sai wani babban jami'in soja wanda ya ke aiki a Abuja sai kuma babban ɗan kasuwan nan me sunan Sunusi Yusuf manajan hatsi."

yana kai wa nan ya zatar da hukunsa ga muta ne uku, dattijai biyun da bindiga ya harbesu ɗaya kuwa sa bo da tsoro haɗiye zuciya ya yi. take Camera ta tsaya da record sai ya kalli na gefan cameran wanda shima irin kayansa ne jikinsa sannan ya ce "ku mai dasu in da ya dace, sai gobe da safe ƙarfe 10 ku saki video din." da ga ha ka ya juya ya fara wannan tafiyar na sa cikin ƙasaita da jan aji.


************** **************

Cikin sauri ta sanya riga da wando irin wanda ta sa ba sa wa sai dai na yau ta ɗaura after-drees Black a kai kuma ta yafa gyalan, a matuƙar ruɗa ni ta fita ta bi ta main parlour, sama-sama ta gaidasu sannan ta fice ta shiga motar ta direct gidan commission of police ta nufa, ko su ƴan parlourn jikinsu a sanyaye ya ke saboda video din da suka kalla yanzu, ba ga ɗaya gari ya ɗau maganan a ke yi. dan an zaci Rash ya dena kisan ne ashe hutu ya je, yau daya dawo kuma har muta ne uku ya kashe. ta na isa ta tar da uban ƴan sanda a ciki, ciki ta shiga suna sara ma ta, sun dau 30mnt su na magana sannan meeting din ya tashi cikin ɓacin rai ta nufa office din ta, ko da ta zauna akan kujeranta kifa kanta ta yi tana tina maganan shugaban na su

"Nan da 24h mu ke son a sa mu ko da makama ɗaya ne na kama Rash, abin ya yi yawa a ce gaba ɗaya jami'an mu a ban za tin da mutum ɗaya rak ya gagara muku." tsaki ta ja a fili ta na imagine yadda idan ta ka ma Rash za ta mai, Za ma za tay i ta feɗe shi sala-sala, ta dinga ɗaye mai fata sannan ta yayyan kashi gida-gida sannan idonsa da wuƙa zata cire hmmmm abubuwan da yawa ta ke misaltawa a ranta.

END
Daga alƙalamij pretty SK
Sakeenat Abdullahi
Mrs I (insha Allah)
[6/13, 22:30] ᑭᖇᗴTTY ՏK ✍️✍️✍️: https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

💪 JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIAION (J.W.A)💪
Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi.✍️

𝐑𝐀𝐒𝐇 Ɓ𝐎𝐘𝐀𝐘𝐘𝐄𝐍 𝐌𝐀𝐒𝐇𝐄Ƙ𝐈

ᑭᖇᗴTTY ՏK
ꜱᴀᴋɪɴᴀ ᴀʙᴅᴜʟʟᴀʜɪ

Page 16

*********** **************

Kuka take tayi cikin ƙunan rai da jin zafi a ranta a ce har mutum uku aka kashe wanda by-mistake ta danna video din ash mugun gani za ta yi, ƙarshe dai wayan faɗin ya yi har sai da ta fashe ya ci screen, da sallama ya shigo a bakinsa ganin yadda ta ke kuka ya sa ya ƙara danna gudun Wheelchair din sa ya nufo in da ta ke

"Me ke damunki? Waya taɓaki? Meyafaru?." duk ya jero mata tambayoyin amma babu amsa, sai da kukan na ta ya tsaya tukun ta samu ta ɗago fuskanta da ya yi ja, bayan ya cire hannunsa a kan na ta, cikin kuka ta fara magana

" Mutane uku duk ka ya kashe fa, meyasa?." sai wani sabon kukan ya kwace mata, sa ku ya yi ya hau kan kujeran da take ya rungumota ya ja shafa bayanta alaman rarrashi, a hankali ta sa mu ta natsu, ya bata haƙuri, be san meyasa ba, baya son ganinta a cikin damuwa, lallaɓata ya yi har barci ya ɗauke a gurin, kallon fuskan ta ya dinga yi gwanin sha'awa. sai misalin 4pm ta farka da mamaki ta ganta akan gadonta, a haka ta tashi ta yi alwala ta na idar da sallan ta fita ta shiga kitchen girki ta yi mai rai da lafiya, sannan ta jera akan daining, wanka tayi sai ta ɗanyi kallo a TV har magrib ya yi, sai lokacin ta ji dawowarsa, part dinsa ya shiga sai 9pm ya fito dan a ɗaki ya yi sallan isha'i din sa bo da kanshi ya na mai ciwo sosai. ko da ya fito zama ya yi shikaɗai ya ci abincin nabsa sannan ya nufi part dinta a dai-dai ƙofan ɗakin na ta su ka haɗu, kowa ya sakarwa ɗan uwansa murmushi, ba su wani daɗe ba amma sun shaƙu sosai kuma sun fara ƙaunar juna, tare suka zauna a Parlour suna kallo sai ya ke ce mata

"Zuwa gobe zan fara zuwa aikin dabsu Pazars suka ne man mu, na so subarni da Online business, tin da ina samu sosai, wai a cewan su hutun na wa ya yi yawa dan ha ka zanfara aiki amma gaskiya ba zanyi aikin gommaniti ba kawai zan jira in dai na ci requesting din da nayi shikenan zan fara zuwa aiki a bank kawai."

"Allah ya za ɓa abin da yafi zama alkairi."

" Ameen, yau na ga kinyi kyau sosai ne, me ya sirrin?." sai da ta yi murmushi sannan ta ce

" Ha ka dai ka ke gani."

"Haka ne ma Kifaty." satan kallon shi ta yi sai ta yi saurin juya kanta dan sun haɗa ido gu ɗaya

"Zawji Pls ina son gobe na je gidan mu da na yayanta sannan na je na ga ƙawata a badikko kaji." ta kai ƙarshe ta na marairai ce mai fuskan ta re da daidaita muryan cikin ɗan shaƙwaba, salon maganar na ta sai yaji wani irin daban haka, dan haka ya yi shuru na wani lokaci sai ya ce

" Bayan la'asar in na dawo zamu fita sai na kai ki duka shike...." be ƙara sa ba ta rungumesa cikin murnan, shima abin sai ya bashi dariya, sannan yaƙara raɗa mata a kunne ce wa

"Next week za ki fara zuwa school Poly, dan haka in munje ki haɗo takaddunki." kukan jin daɗin ta fashe mai ta na mai godiya a ha ka su ka shanye rabin dare suna soyayya mai tsafta dan zuwa yanzu sunysan su kansu a buƙace suke da juna amma suna sharewa sai dai shi ya kan tuna ma 'ta cewa ya kusa samun lafiya, be san me ya sa ya ke ma ta ƙarya ba ya na son suyi sunna amma ba yanzu ba duk da suna ƙaunar juna, ya na da babban dalili a kan ha ka, da ƙyar su ka rabu ko wa ya huce part din sa sai da ya yi minti 30 ya na jiƙa kansa a ruwa ya san duk ran da by-mistake ya kwana ta re da ita me afkuwa na iya faruwa, shiyasa ya ke taka tsan-tsan.


********** ************ *********

" Omry ki bar damuwa a kan case din nan, gobe zan haɗa babban taro na jami'ai kuma zan sa Zaki ya dawo nan domin ku haɗu ayi binciken cikin sati biyun nan, abin ya yi ya wa sosai mu kanmu ya taɓa mu dole mu san abin yi." ya faɗa ya na zama a gefanta in da ta bi ta haɗe rai kaman an aiko mata saƙon mutuwa, tin da ya shigo ma taƙiyin magana sai faman kumbure-kumbure take yi ko Uniform din ta ki cirewa

" Farsi wallahi duk ranar da Rash ya shigo hannuna sai na sheƙe shi da wannan bindigan ko bindiga ai ya sami sauƙin mutuwa, Allah ne me a zaba da huta dan haka da knife zan mai nawa." da ɗora bindigan a saitin kanshi ta na haki, dariya ta so kwace mai sai ya danne ya na cewa

" Omry ba shi ne ba ai, yi haƙuri gaba ɗaya hukuma yanzu ta shiga case kinji." ɗaga mai kai ta yi tana aje bindigan, rungumota ya yi ta baya ya shiga fa ra mata kalamai masu ratsa zuciya harta rage fushin na ta. tukun ta miƙe ta yi abin da ya dace, a tare suka yi wanka, sai shirin barci, a ƙirjinsa ta yi barci shi kuma ya nata shafa gashin nan na ta mai laushi da ƙamshi

*************** ************

Ƙofa ta buɗe ta shiga ɗakin nasu, tsaki taja mai tsayi wanda duk kan su suka kalle ta, hijab ta cire ta ajiye a kan sofa zama ta yi kusa da Beasty wacce ke waya da saurayi ta wanda sati biyu baya suka haɗu, ɗan masu kuɗi ne ga kyau sosai, ya na sonta sosai amma yana son rayuwan shagala da ya wa, abin da ba ta son kenan tana son ta canza shi kuma ɗan zata more in dai ta aure sa, dan ta cire tuta, katse kiran ta yi ta na ce wa

" Baby excuse me." ta na yanke wayan takalli Kandy wacce take ɗan huci ta ce " Sister what happened?."

"I think is Uncle Adamsi? Mrs Love ce fa." Faɗi Hasty ta na kashe datan wayanta, sai Karis ta ce

" Maybe wani ne, kun san ba ta fushi da shi ai."

" Bashi ba ne Aunty ce."

"Me Aunty ta yi." faɗin Baby jin an ce Mamanta ce ta taɓo Khadija, ga ba ɗayan su kuma suka natsu suna jinta sai ta ce

" Wai aurar damu zata yi nan da wani lokaci kuma za ta faɗama Pazars, wai ai mun haɗe da matan gidan ba'a gane su waye iyayen, kuma wai ai mun da ɗe da yaa Adam kawai karatun za ta tsaida." dariya wasu suka sa, wasu kuma murmushi, sun san Kandy ba ta san aure yanzu ta fiso ta kammala karatun ta tukunna, shiyasa ta su ta zo ɗaya Adam

"To ai yaa Adam ya shirya shi be da damuwa." harara Kandy ta dallama Husty, sai Fancy ta caf ke da faɗin

"Uhmmm wa ya ga ranan auran Kandy ƴar a halin ƙanƙara akwai buduri." Dariya suka kwashe sai Kandy ta shaƙa aikuwa suka hau gujeguje a ɗakin cikin wasan da suka sa ba, sai da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login