Showing 57001 words to 60000 words out of 93691 words
su je tare da Pretty dan gaisheta ƴan uwan sa na can ɗin, da yake yanzu motan da yake amfani tsohon na Aliyu ne, shi yasa ya shiga gidan, safiya ce yawan cin ba su ta shi ba. Babban palourn ya shiga bayan jami'ai sun gaida shi. Babu kowa dama haka ya yi tsammani, za ma ya yi ya na son tina jiya wa ya ba key ɗin motan daya dawo duk da sai da Aliyu ya ce ya barshi amma yaƙi kuma be son ɗauko motan station ne. Shuru ya yi sai ya tina Aunty ya ba dan ita ya samu a compound ɗin jiya, ga time na ta tafiya dan yanzu 7:23am kuma ya na son ya yi wani muhimmin aiki ne kuma zai je coat akan kai wani me laifi. wayansa ya ciro kafin ya fara latsawa sai yaji Butter na gaida shi, ya amsawa ya yi da sakin fuska.
" Fadila har an shirya school ɗin?."
" Eh Uncle Zaki." Take Baby da Karis suma suka fito cikin shirin Uniform iri ɗaya, suma gaishe shi suka yi ya amsa yana mai kallon wayan sa sannan ya ce.
" Fatan kunyi breakfast ko?."
" Eh lunch za mu ida haɗawa mu sa a lunch back." Suna kawai nan suka shiga kitchen dan juye jollof spaghetti wanda yake kan huta. dan yanzu girki abin da zasu ci suke yi da kansu umarnin Babban yaya, tin basu iya komai ba amma da taimakon Baby wacce ke koyowa a gurin Ramlat. Butter ce ta zu ba mu su a babban flask, sai Karis ta farfasa boil eggs guda shida, a wani roba me huji-huji ta sanya, ita kam Baby snack ta ke zu ba wa a gefan basket da zasu tafi da shi, take suka ji horn na mota fitowa suka yi a lokacin har Zaki ya huce. Motan suka hau suka nufi school, a yanzu shirin Waec suke.
*************** ***************
Kallon ƙafarta ta yi wanda duk sun kumbura duk da duk bayan magrib suna za ga ye gidan ita fa Ramlat, duk ta yi duhu dama ba haske gareta ba, sannan ta yi wani ƙira amma kyaunta ƙaruwa ya yi.
" Omry da kinji wani yana yi Please ki yi gaggawan faɗa mutanen gidan." Murmushi ta yi mai dan kullum abin da yake ce mata kenan idan ze fita. Tsugunnowa ya yi saitin tulelen cikin na ta sannan ya sunba ce shi, daga haka ya fice dan bayan ya ma ta addu'a. Yana fita ya haɗu da su Pazar M da Pazar R suma sun fito, mota ɗaya suka hau direct sai office anan kuma kowa ya huce na sa ɓangaren. Tin daga ne sa ya hango Askira wato sabon sactary dinsa, a tare suka ƙarasa babban office din Gomna, Aliyu na za ma ya ce.
" Ga wannan list din na ga ma tsarashi kuma yadda na ke so komai ya tafi a tsare." Askira ya amsa yana karanta paper sannan ya ce.
" Sir an gama." Da ga haka ya fice abin sa, Aliyu miƙewa ya yi yana kallon haraban cikin compound ɗin wanda tin da ya shigo ya hangi wasu mata su uku daga gefe sun rakuɓe, ganin ɗaya daga cikin jami'an sa ya nufeta yana koransu irin na rashin imani haka, Telephone ya janyo yana dan na kiran number Askira, bugu biyu ya ɗauka yana mai miƙo gaisuwa.
" Ina da ga be ne yanzu haka, ina hange wasu mata su uku, a turosu office di na."
" Sir ba wajanka suka zo ba, ɗaya daga cikin su ce take son ganin yaron ta dan ɗaya ne daga cikin jami'an tsaron gidan nan, amma ba mu gan shi ba, an tambaya abokansa su ka ce tin shekaran jiya be zo ba." Askira ya kai nan yana mai fatan Aliyu ya yadda, sai dai me kafin ya gama firar zuciya ya ji ya ce.
" Turo su." Daga haka ya katse kiran yana kallon su, dan har sun fara tafiya, baya jin wannan ne ya kawo su, domin last week ma yaga fuskan ɗaya ta zo ta huni a filin gurin. Ganin an kira me korasu ya sa ya koma ya zauna yana ɗauka home phone na sa tare da kiran Omry, amma hatta katse ba ta ɗauka ba, sai a kira na biyu ta ɗauka da sallama ya amsa yana mai sakin fuska.
" Maman Babyna."
" Na"am Baban baby, ya aikin toh?."
" Alhamdulillah, ya jikin na ki?."
" Lau mu ke, Ramlat na miƙo gaisuwa."
" Ina amsawa."
"Za ta ji, ita ma Sk haka dan gata gefe na."
" Ma sha Allah ki ce nan aka zo hira yau, ba ra zan kira ki bye take care please dear." kafin ta amsa ya ba da umarnin shigowa, ya aje kiran sannan ya kalli wanda ya kawo mata ukun ya yi mai nuni da ya fice, gurin za ma ya nuna musu duk suka zauna suna mai jin daɗin yau dai sun ga His Excellency Aliyu Haidar. Duk da su ne manya amma su suka gaishe sa sai ya mai da mu su gaisuwa.
" Ina son na ji lafiya tin ba yau ba na ke ganinku a gurin nan."
" Yallaɓai wata ɗaya kenan kullum sai mun zo amma haka muke koma wa watara su koremu wata rana su haɗa da duka, amma haka muke dawowa dan san ganin ka." ɗaya takai nan sannan ta tsakiyan ta ce.
" Mu ƴan tsaunin da wa ne, wanda ke cikin Rigasa, muna cikin mawiyacin hali, muna neman taimakon ka Yallaɓai." sayi ta hau kuka, gyara za ma ya yi yana ce wa.
" Karku damu inajin ku."
" Yallaɓai ka san damuna ta kama ƙasa, mun yi shuke-shuke a gaba ɗaya filayenmu, wata biyu baya, wasu jami'ai da manyan mutane suka kawo mana ziyara, bayan sunyi mana kyaututtuka sai babban cikinsu ya ce mana, ya na so mubar tsakanin dawa domin ze gina Company agurin ne." Takai nan tana nun fasawa sannan ta da sa " ya ce ya bamu sati biyu, da muka yi gardama akan ba za mu bari ba saboda nan ne duniyar mu kuma munyi shuka, take ya sa wani ya babbaka gaba ɗaya gonan na mu." Sai kuka ya kwace mata, sannan ɗaya ita ma ta da sa da ce wa.
" Abu kaman a Film, Yallaɓai duk wanda ya ƙalu balan ce su to ka sh eshi su ake yi, rayuwa acan yana bamu tsoro." sai da ya sauke kwaron numfashi sannan ya ce.
"Yanzu ku faɗamin sunan unguwan, zan so na bincika amma kun tuntuɓa shugaban da ke wakiltan arean na ku?."
" Yallaɓai har dashi a cikinsu, sannan da wasu manyan Mutane." Shuru ya ratsa sanann ya amsa location dinsu, kuɗi ya basu me ya wa da cewan gobe zai shigo ko ya turo, Huce wa suka yi suna fatan da su samu sauyi a rayuwansu. rufe idanuwan shi ya yi yana jin babu daɗi.
END.
𝕻𝖗𝖊𝖙𝖙𝖞 𝕾𝕶
[7/8, 06:07] 𝐏𝗿𝗲𝘁𝘁𝘆 𝐒𝐊..............: https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 ᴊᴀᴊɪʀᴛᴀᴛᴛᴜ ᴡʀɪᴛᴇʀ'ꜱ ᴀꜱꜱᴏᴄɪᴀɪᴏɴ (ᴊ.ᴡ.ᴀ)💪
ʀᴜʙᴜᴛᴜ ʙᴀɪᴡᴀ ᴄᴇ ᴅᴀɢᴀ ᴀʟʟᴀʜ, ᴊᴀᴊɪʀᴛᴀᴛᴛᴜ ɴᴇ ᴋᴀᴡᴀɪ ᴋᴀɴ ɪʏᴀ ᴀᴍғᴀɴɪ ᴅᴀ ᴡᴀɴɴᴀɴ ƙᴀꜱᴀɪᴛᴀᴄᴄɪʏᴀʀ ʙᴀɪᴡᴀ ꜱᴜ ꜱᴀᴜʏᴀ ᴛᴜɴᴀɴɪɴ ᴀʟ'ᴜᴍᴍᴀ ᴄɪᴋɪɴ ꜱᴀᴜƙɪ.✍️
𝐑𝐀𝐒𝐇 Ɓ𝐎𝐘𝐀𝐘𝐘𝐄𝐍 𝐌𝐀𝐒𝐇𝐄Ƙ𝐈
ĎĂĞĂ ĂĹƙĂĹĂМĨМ РŔĔŤŤŶ ŚĶ
✿◡‿◡✿ [Sakina Abdullahi] ✿◡‿◡✿
typing....
Page 48
**************** *****************
Opposite ROYAL HOSPITAL WHITECHAPEL, RD. LONDON E1, 1FR, UK.
Taxi ce ta yi parking a bakin baban hotel din, fitowa ta yi daga ciki ta na mai biyan me Taxi kuɗin sa, ya amsa ya wuce, cikin hotel din ta shiga direct room din su ta shiga, wanka ta yi sannan ta yi sallah, addu'oi ta shi ga yi yadda A.A ya koya mata, tana gamawa ta miƙa ta kunna TV tana mai kallon wani Nigeria Film Rich mom and poor mom. tana jin wayarta ta kira sallan magrib, a cikin app din V-muslim dan ba masjeed a kusa da su. Bayan ta idar ta ɗauki sabuwar wayanta ƙiran Galaxy A05, data ta kunna ta hau internet dan yi assignment din ta. tana cikin yi aka buɗo ƙofan, A.A ne ya shiga bakinsa ɗauke da sallama, amsawa ta yi tana mai miƙewa ta nufesa da murmushi, rungumesa ta yi yadda suka sa ba, sai a lokacin ya buɗe bakin sa ya ce.
" Fatan kina lafiya?."
"I'm fine Monceur." sai ya riƙon hannuta suka ƙasara cikin palourn, zama suka yi, ta taimaka mai gurin cire safan ƙafan sa, tare suka shiga bedroom sai ta fito bayan ya shiga toilet danyin wanka, da yake ba irin ƙananun hotel ba ne, wannan ya na da komai a ciki, mutum ba ma zai ce hotel ba ne in dai kana cikin room. Bayan ya fito tare suka yi sallan isha'i sannan mai kawo mu su abinci ta kawo, ci suka yi suna hira kwanin sha'awa, ɗago idanunta ta yi ta kalli AA, ƙura mai idanunta ta yi tana ƙare mai kallo, kyakkyawa ne sosai, duk da be da yawan fara'a da surutu, gashi iya rayuwarta da shi taga ya na fa halaye na gari. taimaka mata ya yi suka yi sauran assignment dinta dan ya sa ta a wa ta makaranta anan din, ba University ba ne kawai school ne akayi dan ƙarin ilimi, kuma Alhamdulillah dan daga shigarta ta kware da English kuma irin na UK. Dan kafin suyi hausa yanzu su kan ju ma. Sai bayan da suka kwanta a bed ya ke mata albishir da ce wa nan da 1 month za su koma Nigeria ta ga familyn shi kuma ba zasu dawo UK ba. ita ce ta fara barci wanda kanta ta ɗaura kan ƙirjinsa, shi kuma yana kallo fuskarta, a hankali ya za me daga gadon, miƙewa ya yi, ya kunna globe take madaidaicin haske ya gauraya bedroom din, mirrow ne daga gefansa tsayawa ya yi yana ƙare ma kansa kallo, ji yake tamkar ba shi ba, wai A.A shine ya faɗa soyayya, ya yi aure ba tare da sanin kowa ba, rayuwan sa a yanzu ya mugun sauya, kaman ba shine ke rayuwa cikin ɓata garin yara ba, kaman ba shine shagalan duniya ya sa be ɗaukan mutane da daraja, kaman ba shine me shan abin da addininsa ya yi hani ba wato Alcohol, kaman ba shine ya yi sanadiyyan mutuwan mutane da yawa ba, amma tin da ga ranan da Airah ta shiga rayuwarsa duk ya sauya, ta mai dashin kamilin mutum mai yawan bauta ba tare da sanin ita Airan ce ta can za shi da soyayya ta ba. A yanzu abu ɗaya yak e tsoro shine idan ƙwaƙwalwan ta ya dawo, mai yuwa ta na da saurayi ko aure..... "Inaaaa" ya yi saurin katse zuciyar sa da wannan tunanin, yasan shi ya fara saninta a matsayin mace, yana fatan da ta samu ƙaruwar ciki ta haihu kafin komai na kwakwalwanta ya dawo...........
END.
[7/8, 06:07] 𝐏𝗿𝗲𝘁𝘁𝘆 𝐒𝐊..............: https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 ᴊᴀᴊɪʀᴛᴀᴛᴛᴜ ᴡʀɪᴛᴇʀ'ꜱ ᴀꜱꜱᴏᴄɪᴀɪᴏɴ (ᴊ.ᴡ.ᴀ)💪
ʀᴜʙᴜᴛᴜ ʙᴀɪᴡᴀ ᴄᴇ ᴅᴀɢᴀ ᴀʟʟᴀʜ, ᴊᴀᴊɪʀᴛᴀᴛᴛᴜ ɴᴇ ᴋᴀᴡᴀɪ ᴋᴀɴ ɪʏᴀ ᴀᴍғᴀɴɪ ᴅᴀ ᴡᴀɴɴᴀɴ ƙᴀꜱᴀɪᴛᴀᴄᴄɪʏᴀʀ ʙᴀɪᴡᴀ ꜱᴜ ꜱᴀᴜʏᴀ ᴛᴜɴᴀɴɪɴ ᴀʟ'ᴜᴍᴍᴀ ᴄɪᴋɪɴ ꜱᴀᴜƙɪ.✍️
𝐑𝐀𝐒𝐇 Ɓ𝐎𝐘𝐀𝐘𝐘𝐄𝐍 𝐌𝐀𝐒𝐇𝐄Ƙ𝐈
ĎĂĞĂ ĂĹƙĂĹĂМĨМ РŔĔŤŤŶ ŚĶ
✿◡‿◡✿ [Sakina Abdullahi] ✿◡‿◡✿
typing....
Page 49
***************** **************
Air Force Base
"Maa wai dan Allah yaushe za mu je gun malamin nan, ya ka mata tin yanzu mu san abin yi, daga tafiya ta wai ya yi aure, Maa a gaskiya ko wan can ta fita na shiga ko naje a matsayin kishiyar ta." Faɗin Hafsat tana kallon Maa, sai Maa ta ce.
" Kar ki da mu Hafsat, ba ra gobe ta yi za muje da rana, ni kaina ina son na ga duk kan ku kunyi aure, ke Halima wai har yanzu baki gama tsara wannan yaron da ki ka ce kin so?."
"Maa yaron ya ƙi bani hankalinsa, gashi a yanzu ba ya Kaduna ma, na ji an ce yaje Bauchi dan can ne family house na su ya ke."
" To abin da zai faru dukka mu ukun zamu je muji me Malam Bulala zai ce." shuru ya ratsa parlour, sai murmushi ne ke sauka akan fuskan Hafsat wacce take ji kaman har ta auri saurayin na ta ne wanda take son sa, ji take kaman wannan shine auranta na farko ma, dan ma wan can 5month kawai suka rabu da shi.
"Yunwa na ke ji sosai fa." faɗin Halima sai Hafsat da ke latsa waya ita ma ta ce.
" 9:45am amma ƴar iskan can ta ka sa kammala breakfast." kafin Maa ta ce wani abu sai Fatima ta fito daga cikin kitchen ɗauke da plate a hannu ɗaya sannan ɗayan hannun tana riƙe da waya ta na chart da ƴan uwanta wanda suka haɗu a group dinsu, hira suke yi kwanin jin daɗi, dan a yanzu har zuciyoyin su sun salula akan maganan talauci dan sun yi haƙuri su kuma sun falwala ma Allah, gashi ita Fancy da ke cikin dukiya amma a ban za, sannan har Ramlat sun kira sun ba ta haƙuri kuma ta haƙura, Beauty ce ta rubuto
'Fancy ki dai bi a hankali, na san ki wani lokacin ba kya aiki da lissafi ba ki san mai ze je ya dawowa' kafin ta fara typing har Kandy ta turo sticker na tinani, murmushi ta sa ki sai taji Maa na magana ta na ce wa.
"Ke wai ba ki da hankali ne ace goma saura baki kammala breakfast ba dan ma yau Sunday." hatta hau step 1 sai ta dawo ba ya ta ce.
" I'm sorry Maa, wallahu tin ɗazu na kammala ya na kitchen....."
" Uban wa zai kawo kan dining ɗin?." Faɗin Hafsah ta katse Fancy ta ce.
"Duk uban da ke jin yunwa, mtwwws." ta ja tsaki tare da haurewa sama, tana jin Halima ta fara masifa ta banko ƙofan ɗakin ta, Indomie da fry egg ne ta haɗa ma kanta, ci take sunata hira abin su. A parlour kuwa Maa cikin fusata ta da Katar da Halima wacce ke ƙoƙarin bin Fancy.
" Hmmm Halima bar ta, mu karya sai mu yi mata hukunci." daga haka Hafsat ta shiga kitchen dan fito da abincin da suka umarci ta yi, da mamaki ta ƙarasa ciki ganin babu alaman an yi wani girke-girke a ciki, dan ita wainar flawer da tea ta ce ta na so, ita kuma Halima yam, egg and pepper suop and bread sai Maa custard da Bons. da sauri ta koma palourn ta kirasu, a tare suka shiga kitchen wanda babu komai a gurin dan sun sha za su zo suga kulolin abincin, babban tukunya suka gani a gefan gas, halima ta buɗe sai sukaga Macronnie fari, sannan gefansa soyayyen oil ne. in ran su ya yi dubu ya ɓa ci. su ukun suka je bakin ƙofar ta suka fara Knocking, ta na jin su sai da ta kammala cin tukun ta miƙe tana vioce da ce wa "Jama'a sun iso bara na ji dasu ina zuwa." Daga haka ta a je wayan tana buɗe ƙofan, ko a fuskokin su ta san sun shaƙa kafin su yi magana ta ce.
"Yaji ku ke ne ma?."
"Barkono mu ke ne ma." cewan Halima tana ta muzurai, sai a lokacin Maa ta buɗe bakinta ta fara magana cikin ɓacin rai.
"Wato ke gaki mara kunya, mu na zaman jiran breakfast ashe kina zaune a kitchen ɗin dan hulaƙan ci, ma za ki fito ki koma, na biki 30mnt da ki kammala komai ko ranki in ya yi dubu wallahi sai ya ɓa ci."
" Maa wai ya kike mata magana a hankali ne, kyen shi mufara ma ta shegen duka tukun." ce wan Hafsat, sai Fancty ta saki shu'umin murmushi ta na ce wa.
" To ai ni in ba ku sa ni ba ku sa ni, da ne na girkin gandun, na san ki na da hannu Bismillah ko wa ya shiga ya koya, balle ke Hafsat maybe shiyasa aka sako ki, baki iya girki ba. "Hafsah da ranta ya kuma ɓaci ta janyo Fancy wacce ke tsaye ko ge zau ba ta yi ba, hannunta ta ɗaga da niyyan ta mareta sai Fancy ta rige hannun ta na ce wa.
" Kul Hafsat, wallahi karki so ma, kaf cikin ku babu mai buguna ya zauna lafiya, banza kawai." Take Halima ta matso dan su yi mata duka sai Maa ta dakatar da su da ce wa.
" Karku duketa, muje mujira M.d daya ajiye ta, yau ta sa ni a gidan ubanta za ta kwana."
" Bara na je na fara haɗa kaya na, Allah ya sa ya dawo da wuri." daga ha ka Fancy ta koma ɗakinta tare da banko ƙofa, tsaki ta ja ta na ce wa "Uban wa ke tsoron saki.", za ma ta yi ta ko ma koma online suka dasa hira da cewan gobe dukkansu za su zo gidan na ta.
---------- "Maa wai meyasa ba ki bari munyi mata shegen du ka ba?."
" Halima ke yarin yace, tin da Maa ta hana akwai abin da take shirin aikatawa ne."
" Shi yasa ba na wasu abubuwan a gaban Halima saboda har yanzu ke yarin ya ce, kubari gobe ta yi kusha kallo, ko in ce anjima."
"Yanzu Maa ya zanyi? yunwa nake ji." Halima ta ƙarasa cikin ɗan shaƙwaɓa sai Maa ta ba Hafsat umarni da ta yi musu order, cikin jin daɗi ta yi order din amma sai nan da 20mnt za su kawo.
" Gobe za muje Malali bayan min fara zuwa gidan Malam Bulala."
"To Maa." suka amsa a tare, Halima wacce tafi kowa jin daɗi, ta tashi ta shiga bedroom din ta, wayar ta ta ciro ta kira numbern Salma, budu biyu Salma ta ɗauka cikin magagin barci sai Halima ta zauna a dressing mirrow ta na mai ce wa.
" Salma gobe za mu zo, kin ga ba wani wahalan ki yi raping kwayoyin nan dan ba Maa, ki dai tanadar min da ya wa kawai, dan kwana biyun nan ban yi charji ba ji nake kaman ba ni ba." Daga cikin wayan Salma ta ce.
"Ƙawata kenan, ba ki da matsala, akwai story amma sai kin zo."
"Okh kina barci ban san na dame ki, sai kin ganmu gobe din."
"Okh Haleemzee." Daga haka ta yanke kiran tana shigewa toilet danyin wanka.
End.
𝕻𝖗𝖊𝖙𝖙𝖞 𝕾𝕶
[7/8, 18:37] 𝐏𝗿𝗲𝘁𝘁𝘆 𝐒𝐊..............: https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 ᴊᴀᴊɪʀᴛᴀᴛᴛᴜ ᴡʀɪᴛᴇʀ'ꜱ ᴀꜱꜱᴏᴄɪᴀɪᴏɴ (ᴊ.ᴡ.ᴀ)💪
ʀᴜʙᴜᴛᴜ ʙᴀɪᴡᴀ ᴄᴇ ᴅᴀɢᴀ ᴀʟʟᴀʜ, ᴊᴀᴊɪʀᴛᴀᴛᴛᴜ ɴᴇ ᴋᴀᴡᴀɪ ᴋᴀɴ ɪʏᴀ ᴀᴍғᴀɴɪ ᴅᴀ ᴡᴀɴɴᴀɴ ƙᴀꜱᴀɪᴛᴀᴄᴄɪʏᴀʀ ʙᴀɪᴡᴀ ꜱᴜ ꜱᴀᴜʏᴀ ᴛᴜɴᴀɴɪɴ ᴀʟ'ᴜᴍᴍᴀ ᴄɪᴋɪɴ ꜱᴀᴜƙɪ.✍️
𝐑𝐀𝐒𝐇 Ɓ𝐎𝐘𝐀𝐘𝐘𝐄𝐍 𝐌𝐀𝐒𝐇𝐄Ƙ𝐈
ĎĂĞĂ ĂĹƙĂĹĂМĨМ РŔĔŤŤŶ ŚĶ
✿◡‿◡✿ [Sakina Abdullahi] ✿◡‿◡✿
typing....
Page 50.
***************** *****************