Showing 78001 words to 81000 words out of 93691 words
haka har aka kai ni asibiti a ka sauyamin sabuwar ƙoda. ***** Sai kuka ya kuma ƙwace mata, a hankali Abbu ya buɗe baki ya ce.
" Me ya sa baki nemi mijin ki ba?."
" Ta ya zan ne me shi, rayuwan wahala nake yi a gidan, sam bai damu da ni ba, a ce mai na mutu, shine ya tafi da ƴar da muka haifa, ai sai ya nemi gawata ko." Kowa jikin sa yayi sanyi balle Doctor, a hankali ta ce.
"Nasan na yi kuskure dan Allah ki yafemin, Please, sannan ina ji a jikina wannan ƴar ki ce." ɗaga ido ta yi ta kalli Sakeenat dake zubar da kwalla, sai a lokacin Sakeenat ta buɗa baki ta ce.
"Ni ba ƴar ta ba ce." take ta basu labarin rayuwarta dana Ramlat wacce har yau shiru abu ya kusa rufa shekara.
"Innalillahi wa'inna ilaiyi raji'un." Abin da Doctor ta faɗa kenan sannan ta miƙe da ga tsugunne, gaban Sakeenat ta tsaya sai ta janyo ta sannan ta duba hannunta, take wannan tambarin ya bayyana ya ƙara girma da kyau, duk da ta na da duhu amma gashi nan ya yi raɗau, rungume ta tayi ta na cewa.
" Wallahi ƴar ki ce wannan, na aikata babban zunubi a rayuwata a cikin manya-manyan shine wannan mugun aikin da na miki, twins mata ki ka haifa, Hassana ta na da wannan alaman a hagu sai Hussaini mai wannan alaman a hannun dama, ni na hana a ba mijinki dukka saboda na san ba zai iya raunon su ba, sai na ba ɗaya daga cikin nurses da ta kai ta gidan marayu, sai dai aka kawo min labarin tayi accident, na zaci har da jaririyan ne ta rasu...." , sai saɓon salati daya cika gurin, take Doctor ta zuɓe a gurin, nan hankali ya kuma ta shi, abu mafi razar da su shine, bayan minti biyar a lokacin da wata Doctor Shamsiya ta sadanar da su rasuwarta Doctor Mariya.
************ *************
_______ Ganin har gitsin ya yi yawa, ya sa duk suka wuce zuwa family house ɗin ƙanƙara, dan abin ya shafi Mama Zulaihat da Sakeenat, sannan ance musu kar kowa ya dawo saboda suna damun mara sa lafiya, nan da kwana uku sai su dawo ɗaukan Ramlat ɗin.
______ Maa suma dare na yi su ka koma gida dan ba ta farfaɗo da wuri ba har ankai ƙawarta makwancinta, rayuwa kenan, duk ciwon da Salma ke ji sai ta ji ta dawo lau dan mutuwan ya dake ta sosai, ta sha kuka kaman ranta zai fita, haka Halima ma.
Itama Hafsat da ta dawo da ƙuncin soyayyan Yusuf, gashi Boka ya ce in ba'ayi sa'a ba zai dawo kan ta , to duk a ruɗe take gashi gidan nasu ya hargitse, duk ta shiga damuwa sosai.
End.
Daga alƙalamin pretty SK.
[6/12, 2:46] ᑭᖇᗴTTY ՏK ✍️✍️✍️: https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIAION (J.W.A)💪
Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi.✍️
If your Mum is alive, may she have a long life to witness your success🤲
𝐑𝐀𝐒𝐇 Ɓ𝐎𝐘𝐀𝐘𝐘𝐄𝐍 𝐌𝐀𝐒𝐇𝐄Ƙ𝐈
ᑭᖇᗴTTY ՏK
Page 63.
************** *************
_____ Fancy ce zaune gefan Airah, sai A.A da ke ƙara duba jikin ta.
" Matar Yaya kije gida kawai, ai ina nan karki damu."
"A'a ƙanin miji, ni na janyota nan dan Allah ka barni na kwana."
"To ai kinga in kika koma da safe sai ki tawo mana da abubuwan da muke buƙata, dan ta shiga doguwar suma, amma wai su waye ta gani ne haka?." ya ƙa ra sa maganan cikin jimami.
"To kawai miƙe wa tayi sannan ta yi ihu shike nan, da ya ke muna da yawa bana ce ga wanda ta ga ni ba."
"Hmmmm okay." sai ya fita, ba yadda ta iya haka zuwa 10pm, M.d ya zo ya ɗauke ta a motar ta.
**************** ***************
____ Nan ma su biyu ne kawai, Ramlat da Meerah dan an yi an yi ta wuce gida Aunty ta zauna ta ƙi yadda, dan haka suka bar ta.
" Yanzu fa shike nan Doctor Mariya, Allah sarki, Allah ya jiƙanta da Rahma."
"Ameen ya Allah, abu kaman wasa da ka zubewa, takwara wallahi gani nake kaman mafarki, Allah sarki Sakeenat, Allah ke nan." Sai ga hawaye a idonta, sharr sharr, hannu ta sanya ta share sannan ta shiga toilet, da ido Meerah ta bi ta ɗan ta san ta tina Ramkat ne.
************ *************
_____ Tin bayan da suka koma gida kowa ya shiga jimami sosai, sannan aka watse, Kandy,Beauty,Beasty da Zubee su ka wuce gida, dan su Baby sun ƙi binsu, Abbuu shima tafiya suka yi da yamma shi da Mama Zulaihat bayan ta sha rarrashi sosai, haka Sakeenat ma sai da Zaki yazo tukun ya samu ta natsu.
**************** **************
SAUDIYYA
Hajiya tin 9:00pm ta yi barci, su biyu ne zaune a parlourn suna hira amma hankalinta sam ba ya jikinta domin gida kawai take tinani, gashi matar Boss ta haihu za ta so a yi suna ta nan.
" Baby what's wrong?." Sai da ta ɗan firgita dan unexpected ta ji muryan na sa.
" Nothing Dear, take your medicine, and start with Bismillah be for you drink." Ta faɗa ta na miƙa mai ruwan zam-zam daya sha addu'oin karya sihiri. amsa ya yi sannan ya yi yadda ta ce ya sha, ya na ga ma wa ya miƙe da niyyan shiga bedroom sai kuma ya zauna yana sakin phone ɗinsa ƙasa sannan ya dafe kansa, yana faman kiran sunan Allah, a ruɗe take tambayan sa.
" Dear what happen?". Bai ma san ta nayi ba, addu'a ta fara tofa mai cikin ikon Allah cikin minti biyar sai ya fara atshawa sai da ya yi sau bakwai a jere sannan ya kalleta ya ce.
" Menene a cikin kai na wanda yau aka ya ye min, na ji kaman an cire min blanket mai zafi a cikin kai na, wait..... why are you crying." ta san waraka ta zo dan an ce sau uku in kasha an gama, kuka ta fara yi sannan ta shiga ɗakin Hajiya, barci take yi amma Hasty ta fara bubbuga ƙafarta a hankali ta na ce wa.
" Hajiya! Hajiya!! Hajiya tah Please wake up, Hajjaju." cikin kuka take magana sai Hajiya ta farka ganin irin kukan da take yasa Hajiya ta watstsake ta na miƙewa sannan ta ce.
"Innalillahi wa'inna ilaiyi raji'un, Hassana me ke faruwa? Wa ya mutu? Ko jikin Hassan ne?." ba amsa sai ta rungumeta sannan ta ce.
" Hajiya Hassa...." Sai kuma ta yi shuru, amma ganin har Hajiya zuciyarta ta fara bugawa da ƙarfi ya sa kuma ce wa "Alhamdulillah ya samu lafiya, sihirin ya karye Hajiya."
" Alhamdulillah, amma shine za ki tsora ta ni haka."
"I'm sorry Hajjiyatah." Sai kuma ta saki murmushi, tin shigowar ta yake bayanta, duk yaji zan cen su. A hankali ya ta ko har zuwa gaban su sannan ya ce.
" Malama kar ki karyamin tsohuwa ta.".
" Uhmmm ai Hajiya ta ce."
" A'a sakar min wiyarta haka kawai kin shaƙo min ita." Sai ta sake ta, baki ta turo, Hajiya ta riƙon hannun ta sannan ta ce.
"Ƙyale shi, ke ce ƴata ai."
" Haba Hajiya to ni fa?."
" Tafi ka bani guri, kasan......" Sai hawaye, labarin abin da ya faru aka ba shi duk da akwai wanda yakan sani amma bai san dalilin yin shi ba. Haƙuri ya basu sannan ya ce su shirya jibi za su koma gida.
*************** ***************
Air Force Base
________ Gaba ɗaya gidan babu daɗi, Maa tana cikin yanayi mara daɗi, ta so a bar mata Salma amma ƴan uwar Doctor Mariya sun tafi da ita Bauchi, gidan sam babu daɗi, ko da Fancy ta dawo ta yi mata gaisuwa ba ta jira mai za ta ce ba ta wuce part ɗin ta dan yanzu ita fatanta Airah ta samu lafiya.
Washegari da safe Hafsat na zaune a parlourn ta na latsa waya sai ga Fancy za ta shiga kitchen dan haɗa breakfast, har ta wuce Hafsat sai ta jiyo ta na cewa.
" Ki haɗon min lemon tea yanzu." Kamar Fancy za ta tanka sai kawai ta shiga kitchen, haɗa girki ta yi mai rai da lafiya, sannan ta zu ba ruwa a flask, haɗawa ta yi a Basket sannan ta kai motan ta, bayan ta koma kitchen ɗin ta tadda ta Hafsat a ciki ta na buɗe-buɗe.
"Lafiya kuwa?."
" Lafiyar ce ta kawo haka, ina tea ɗin?." Sai da Fancy ta saki murmushi irin na kin mai da kanki banza.
"Wa ki ka haifa? Wa kika aje da zai making tea for you?."
"What..?." Hafsat ta riƙo hannunta, fizge hannun ta yi ta na ce wa
"Ke dalla gyale ni, ina da aikin yi yanzu, na ga kaman neman rigima ta kike yi, so mind your self."
"Hehehehe, who are you?."
" Your Aunty." Kafin Hafsat ta kuna mai da magana, ta ji kaman an buga ma ta guduma a kwanyar kanta, ihu ta sanya mai razanarwa ta na toshe kunne, Fancy ba ya ta ja sai kuma ta nufeta ta na ce wa.
"Subuhanallah meneme?." Take Maa, Dad da Halima suka shigo a ruɗe dan har lokacin ta na ihu, tin daga kallon da Maa ta yi mata ta ji ajikinta tasan hala ace ta mata wani abu ne.
"Fatima me ya sa me ta?."
" Dad ni ma ihunta kawai naji." Abin da ta ce kenan sannan ta fita dan basu guri, da ƙyar Hafsat ta yi shuru sai ta ɗauke huta gaba ɗaya, da ƙyar a ka Kaita parlourn, bayan an kwantar da ita, Maa ta ɗibo ruwa aka yayyafa mata duk da idanunta suna buɗe. Dad addu'a ya fara tofa mata, amma ta ƙafe cak. Bayan sun ɗau lokaci a haka, Maa da Halima sun fara kuka, sai ta saki wani ihu sosai wanda yasa suka toshe ƙunnuwan su, take ta miƙe daga kwance ta na bin su da kallo ɗaya bayan ɗaya, sai ta fashe da dariya mai sautin kuka.
" Hahahahaha ni ce, wallahi ni ce, kalli Maa ashe ni ce fa, ke ma taɓani kiji ai ni ce ko?." ta kai nan ta na kallon Halima, Dad ne ya riƙo hannunta ya ce
" Hafsat! Hafsat!! Hafsat!!! Are you okay? What's wrong with you?." Sai Hafsat ta kallesa ta ce
" Waye kai, na ce kalle ni, ai ni ce ko, ni zan aura shi, wallahi ni ce koh haka Boka ya ce min ai." Salati suka ɗauka ɗan ya tabbata Hafsat hauka ya sa me ta, hatta Fancy wacce ke tsaye jikin step, jikin ta ya yi sanyi sosai.
***************** *****************
Bayan kwana huɗu
______ Yadda kasan ana wani babban shagali ne a gidan, sakamakon dawowan Maman twins, Mutane uku ne suka je suka ɗauko ta, Hajiya, Mama Zulaihat da Karima, ko hour ba suyi ba, suka dawo da ita dan Meerah ta gama haɗa musu komai da suke buƙata, kafin su fito suka leƙa Fancy dan ganin me jiki, sai dai har lokacin ba ta farka ba, suka ma Fancy gaisuwa da fatan ta samu lafiya.
Ko bayan sun iso gida kowa sai murya ya ke, part ɗin ta sauka akan ta tadda Hajara, Maryam, da Zainab, farin ciki kaman me agunta, yinin ranan sai hamdala dan kowa yana cikin farin ciki.
Bayan kwana biyu
_____ Pazar Q, Pazar M, Zaki, Abbu, Mama Zulaikha, Sakeenat sai Hajiya, sune zaune a parlour madaidai ci, bayan ɗan lokaci Maman Rabi ta kawo musu pure water, sannan Baba shima ya fito dan wanka yake yi aka ce yayi baƙi. Koyan sun gaisa aka gabatar mai da dalilin zuwan su, ya yi mamaki ganin Zulaikha na raye amma abu na Allah, kuka ya sha sosai tare da neman yafiyansu, sannan itama Maman ta ne ma tafiya cikin ikon Allah Mama Zulaikha ya tafe tare da musu fatan Alheri. Pazar Q da Zaki suka ma Baba kyuata kuɗi masu yawa sannan suka bar gidan.
RASH
______ Zaune yake akan kujera mai juyi sai ya kalli Adamsy ya ce
"Ina jinka." taka Adamsy ya buɗe wani babban littafi ya fara magana.
"A yadda Spider ya bincika shine, Sunan sa Nura Isma'il, yana da yara biyu maza, matar sa ta rasu tin shekaru uku da suka wuce, yana koyarwa a wata Secondary School anan Barno, ɓata yara mata shine babban aikinsa, doka ba ta aiki akansa sam dan ya na kuɗi da manyan mutane a bayan sa." Sai ya yi shuru, sai Boss ya ce.
"Zuwa gobe na ke so aka wo min shi, ba kisa yanzu amma zamu koya mai darasi." Daga haka ya miƙe sanann ya shiga room ɗin sa, Spider da ke kallon Adamsy ya ce.
"Dole team ta haɗu nan dan lokaci, dan na ga alama idan ba Rash ya bayyana ba ba za'a dena wanna aikin ba."
"Hakane amma kasan ƙasar nan, sai ace za a kama shi ɗan ko a yanzu ne mansa ake." Faɗin Skiddo da ke gyefan su, sai Adamsy ya ce.
"Hmmmmm mu na da ƙarfin iko ai, Babu mai iya shiga gonar mu."
"Skiddo wai nan mu jami'ai ne koh? da wannan kakin kwanda wannan." Ya faɗa yana nuna tambarin Rash a jikin rigan da ke gyefan sa.
"Sosai ma kuwa dan wannan ta ce ƙasar muke.....
END
Daga alƙalamin pretty SK.
[6/12, 12:46] ᑭᖇᗴTTY ՏK ✍️✍️✍️: https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIAION (J.W.A)💪
Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi.✍️
If your Mum is alive, may she have a long life to witness your success🤲
𝐑𝐀𝐒𝐇 Ɓ𝐎𝐘𝐀𝐘𝐘𝐄𝐍 𝐌𝐀𝐒𝐇𝐄Ƙ𝐈
ᑭᖇᗴTTY ՏK
Page 64.
Ranar Suna.
_______Gida ya cika sosai, mata kowa ta sha lalle da kitso, haka aka wuni ranan gidan yasha taro, rago shida, shanu biyu aka yanka, Ramlat ta sha kyau sosai, bayan an gama walima zuwa yamma ladies suka baza M.P a cikin gida, sun shashe sosai, amma banda Fancy, dan ita ba ta jima ba ta wuce asibiti, Hasty ma ta zo dan a daren suka dawo dan sun tsaya shirin ne a natse. Zuwa dare duk an watse sai mutan gida, Ladies dai su 8 wai anan zasu kwana gobe za su tafi.
Hajara da Maryam suma sun leƙo amma Abbuu tin 5pm ya ce su huce dan duk bayan two days sai sun zo. Doguwar riga less ɗinkin dogan riga ta cire dan sanya masu nauyi, bayan ta sanya mai ɗan sauƙi, ta ɗauki wayarta sabuwa da daren jiya Babban yaya ya sauya mata, kiran shi ta yi amma bai ɗauka ba sai bayan ta aje wayan sai ga kiran shi.
"Ina kaje?."
"Hmmmmm ko sallama ai kyamin, amma an fara min tambayoyi kaman ɗan yaro, I'm father now." Murmushi ta yi sannan ta ce.
"Tom Baban Twins ina kaje, tin 3pm ka bar gidan nan."
"Ki ce yanzu kin samin ido, na je wani gu ne."
"Ohhh ina ke nan."
"Kifayaty zan kira ina zuwa." Kafin ta ce komai ya katse kiran, ita har ranta tasan Shuraim ba zai bar aikin kasada ba amma ta na mai fatan ya de na.
************** ***************
Air Force Base
_________ Maa ce zaune ta yi jugum tana kallon ƙanana ta Hafsat da Halima, Hafsat hauka kullum gaba yake yi, ita kuma Halima wasu mugayen ƙuraje ne ya fito mata a dukkan jikinta, su na da ƙaiƙayi sosai, ga su sunyi ruwa idan kuma ta fashe akwai azaba sosai, kallon su take cikin son gano shin itace silan wannan yaruwan ta su ko sune, da iyayenta na raye sam ba za su zo ganin wannan lokacin ba, sannan yaranta maza babu mai shiga harkan su, balle Dad da ko ɗaki ba su haɗawa, so ta ke tama kanta karatun ta natsu amma ta rasa ta ina za ta fara. Shurun ne ya katse da shigowan Fancy.
"Maa sannu da gida." Ba tare da Maa ta amsa ba Fancy ta wuce, da idanu ta bi ta tana mai son gano ai bunta amma ta kasa, Hafsat ce ta mike tsaye tana sosa kanta wanda duk ya hauka ce.
"Ke ina zuwa?." Sai ta kwashe da dariya ta na daka tsalle da hayewa stairs, Halima idanu ta buɗe idanu da ƙyar sannan ta ce.
"Maa." Da sauri ma ta nufeta ta na cewa
"Halima menene, me ke damunki?."
"Maa ki ya femin mutuwa zan...."
"Kul Halima in sha Allah za ki samu lafiya kinji." Sai ga hawaye sun wanke mata fuska, sai ga Da sun shigo shida A.A, bayan sun shigo sai ga wasu mutane a bayan su.
"Baban Muhammad kalli Halima, wayyo Allah na ban san ta mutu."
"Yi shuru, Maa kin yadda da ƙaddara ko a'a." cikin kuka ta ce.
"Na yadda."
"To muje." Kafin ta kuma magana ya ja hannunta suka shige part ɗin su, A.A dake tsaye jikinsa a mace ya ce.
"Wannan ce mara lafiyan, ku ɗauke ta." Wasu mata suka dauki Halima akan wani gado, ta so tayi magana amma ta kasa sai hawaye kawai, take M.d ya sauko riƙe da hannun Hafsat, yana isowa ya ce.
" Ga ta." nan ma wasu suka riketa suka yi waje da ita.
" Allah ya sa a da ce."
" Ameen brother, Halima na ta ne guarantee."
"Hmmmmm Allah sarki rayuwa, ya jikin matarka, ɗazu na shigo a kace ka fita."
" Jiki Alhamdulillah."
_______ Dad ya kalli Maa ya ce
"Muna sane da halin yaran nan, sai muka sa miki ido, domin kisan irin isharan da Allah ya musu, kina dai kallo kuma kina saurare, rayuwa sam ba gurin dawwama ba ce, ke sheda ce a yau ina ƙawarki Mariya, ba ta duniya, ke kanki baki fi ƙarfin Allah ya ɗauki ki yanzu ba." Sai ya nisa sannan ya da sa. " Aboki na tin na yarinta Askira, tin daga mutuwar sa ya gane hanyar da nabi, Allah ya so ni da rahma, ke ma haka amma kin ba sar neman shiga wata halakar kike, dan Allah ki natsu kisan abin da ya dace ki yi."
"Kai co na Bababn Muhammad, wallahi na tuba na bi Allah." Sai ta fashe da kuka, rungume ta ya yi ya na ce wa.
" Is okay, by now ki san me ya dace ki yi a rayuwa, and kin yadda da mijinki?." Da daga mai kai sai ya da sa da ce wa "Ban san ki tambaya ina Hafsat da