Showing 6001 words to 9000 words out of 93691 words

Chapter 3 - RASH ƁOYAYYEN MASHEƘI. COMPLETE HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

205

Baba ya fito da ga ɗakin, can sai Ado me chemist ya fito, Baba ya biya shi kuɗin sa, sai ya ko ma gurin Ramlat din, su dai su Rabi na su ido, sun san halin Baba idan ɗan suna ciwo su na shan kula. Ramlat ta kalli Baban na ta wanda ke mata ya jikin.

"Baba inajin yunwa, zan sha tea." bai ce komai ba ya kuma fi ta, dariya ta sanya har su Umar na ji, sai su ka shigo suna kallon ta.

"Yarinyar nan kin riƙa" cewan Radiya ta na riƙe Kwankwaso, kafin Ramlat ta yi magana su kaji sallaman Baba cikin sauri ta ko ma ta kwanta ko da ya shigo ya umarci Radiya da ta ha ɗa ma ta tea din aiko ta haɗo ta ba ta. amsa ta yi ta kai baki da ƙyar, rabi ta sha sannan ta mi ƙa ma Umar sauran dan sun fi shiri yaron be da damuwa, amsa yayi ya koma ge fe ya na sha, a ranan Aunty ta sha faɗa haka su Rabi akan abin da su kayi ma Ramlat, ita dai ta na jin su hankalinta kwance.


******** ******* *********

*KIKINAU*

"Maryan ɗan turamin Film ɗin nan na kalla" Maryam amsa wayan Ramlat ta yi ta tura ma ta wani Nigeria film ɗin da Maryam ta yi download dan sun ga poster kuma an ce ya yi daɗi sosai, Hajara ce ta shigo da sallama da ɗauke da babba plate a jewa ta yi ta na ce wa.

"Bisimillah ga ma ra imani dukka na Annabi ya ce ya ƙoshi." suna jin ta faɗa ha ka su ka kalli plate ɗin, alkaki ne wanda yaji ruwan sugar ya ga ma jiƙa shi kuma yana ta walwal kwanin sha'awa, ta ke su ka sauka su ka fa ra ci, Zainab ma na shi go wa ta ɗauka biyu ta ce ya ishe ta dan ba ta wani cin sugar.

" Mama ta yi?." Ramlat ta yi tambayan sai Hajara ta ba ta amsa

" A'a Abbuu ne ya ka wo."

" Gaskiya ya yi daɗi." Maryam ta faɗa ta na lasan ruwan zaƙin.

******** ********* ***********

"Wallahi sai sun san ɓoni akan me dan na ba da shawara shi ke nan, aiko sun taɓo match, dole na san abin yi."

" Ka din ga kai zuciyan ka ne sa Abdulmasheed kaji."

" How? Hmmmmmm dole salon wasan ya sauya." wayan shi ya ci ro ya yi kira bu gu uku aka ɗauka

" Gobe inaso na ganka sanann ka faɗa ma Babban yaya shima ya zo gobe nasan kai kaɗai ne zaka iya samun numbersa." ya na kaiwa nan ya kashe wayan. Baba Abdulqadir ya yi murmushi dan gobe ze ga yaran shi da ma so ya ke su dawo balle ma Babban yaya yana son ganin ya lafiyan shi ya ke, amma be san da munsu gashi Abdulmajeed ya kira su da ya ke shi ne ya san dole gobe za su dawo Nigeria. cikin faɗuwar gaba ta re da sauri-sauri ta nufi part din su bayan ta aje ma su Pazars drinks, yanda ta buɗe ƙofan da rufewan ya sa dukka su ƴan matan suka yi saurin ɗago wa, ko wacce da abin da ta ke yi amma kusan su hudu waya su ke latsawa

" Baby lafiya kuwa?." cewan Hasty ta na du ba littafin karatunta, dukkansu kallon ta su ke yi dan ha ka ta buɗe baki a hankali ta ce.

" Na zo da labari gu da biyu, bad one and good one." ta faɗa ta na ƙara sawa cikin su, zama ta yi kusa da Husty, sai Fancy ta ce.

" Start with good one than bad din."

" Ok, firstly tommorow Uncle ze dawooooo." yadda sautin kalman ƙarshe ya yi sai yai kaman a tare su ka ƙarasa cikin ihu da murna, su na ta hamdala sai Beasty ta ce

" Ki ce mu shirya zamuga Uncle wayyo daɗi, dama banda ko sisi..."

" Mayyan kuɗi kawai, ai sai mu ji bad din duk da ba ze tsora ta mu ba tin da munji maganar kuɗi." Kandy ta kai nan ta na mai da Idon ta ga Baby wacce annurin fuskarta ya ɗauke lokaci guda, dukkan su suka sassauta jin daɗin su su na sauraro ta

" Pazar M ya umarci da a sanar mai shi ma ya zo goban nan."

" Baby wa kenan?." Butter ta tambaya sai da baby ta ja dogon numfashi sannan ta furta kalmomi masu harɗe harshenta

" BABBAN YAYA." daram, durum, dam, daan, zuciyoyin su ya bu ga sannan zu fa ya fa tsatstsa go mu su duk da A.C da ke aiki, duk cikin su Hasty ta fi kowa jin tsoro dan ta san case ɗin ta da Babban yaya.

" Mun shiga uku, mun mutuuuu." kaman za tai kuka ta faɗa, sai Kandy ta ce

" Me ya sa Pazar M, ze ma na ha ka, Allah ya soo munji, me ya ka mata mu yi toh?."

" Two Hijjab gareni kawai , wayyo Allah." Hasty ta faɗa da muryan ƙasa-ƙasa, sai Beauty ta tari numfashi ta.

" ke nima biyu gare ni ya kama ta mu je kasuwa amma banda kuɗi, wake da kuɗi a account dinsa?" dukkan su suka ce babu sai Kandy ta ce

" I have 7k but ......" Ba ta ga ma magana ba Baby ta katse ta da ce wa

" Mukira Uncle ya turo mana sai mu je amma yanzu 7pm yamma ya yi, ko an barmu sai dai mu ari motan Pazar Q."

" Eh, ai muna da ke Baby, za kije ki riƙon mana Pazar. "

" No Kandy wata ta je Pls "

" Ke fa za ki tambaya, dan ko gun Pazar B ne tsaf ze ba ki key" a jiyan zuciya ta sauke sannan Besty ta ƙira Uncle Video call aikuwa cikin ɗan lokaci ya ɗa ga, da ya ke a system ne sai ta aje yadda zasu din ga ganinshi dukkansu, motsi wayan nashi ke ta yi sai kuma ya aje wayan ta ke fuskan shi mai kyau da ƙawa ya bayyana ya na mai sakin murmushi, fari ne ƙal kaman dukkan su, tweens ne kawai haske su be kai na su ba dan su hasken Mom su ka ɗauko, ga hancin su duk irin ɗaya mai tsayi dai-dai wa dai da, da an gansu an ga jini ɗaya sak ɗan dukkan su sun ɗauko fuskokin Pazars ne, fararere ƙwawawa ma su ka ma da shuwa-Arab, gaishe shi su ka yi, ya amsa da kai kawai ya na ta blushing abin shi ya na kallon ƙannan na shi ma su kama da juna wanda za'a iya za ta Babansu ɗaya ha ka Mama ɗaya, cikin murya shi mai daɗi da ɗan gurɓace wan yaran nasara ya fa ra magana

" Gobe zan da wo Sister's." ganin babu wanda ta yi alaman farin ciki ya sa ya kuma magana sai suka ɗa ga kai alaman sunji sannan ya kuma magana.

" Babban yaya koh?." a tare su ka ɗa ga mai kai sai ya yi murmushi ya san ƙannan na shi sam basa son Babban yaya ya da wo, Baby ta bu ɗe baki a hankali ta ce.

"Uncle Plsssssss we need some money immediately." ya ri ga ya ma san dalilin kiran, a ta gefan shi aka mai magana dan ha ka ya kalle su ya na magana da sauri-sauri saboda ze koma bakin aiki.

" Sister's am sorry kiran gaggawa amma karku damu, balallai Babban yaya ya dawo gobe ba sa bo da ga ba ɗaya Numbers din sa basa shiga na different countries, samun shi ze yi wahala sosai and zan tura muku kuɗin a account din Fatima sai ku raba." kai suka ɗaga sannan suka mai godiya ya kashe kiran. Walwala su ce ta da wo ta re da murna sai su kai hamdala su kaci ga ba da harkokin su tin da an ce Babban yaya balallai ya da wo gobe ba.


******* ********** ******* **********
*BADIKKO*

Yau tin da ta wayi gari babu wanda ya shiga harkanta sa bo da abin da yafaru jiya, Aunty har kuka tayi saboda Baba in ranshi ya ɓaci sai haƙuri kawai, sukan su Rabi da yau bakinsu ya mutu, wanka ta fito sannan ta shirya ta sa kayanta tare da Hijjab, fitowa tayi ta kalli Aunty dake shara ta ce.

"Mama ina kwana" harara ta maida ma ta sai ta fi ce abinta ta na murmushi tare da tina rayuwar baya.

Labari

***** Baba mai suna Harun haifaffen Kaduna mazauni Kinkinau layin masallacin Ustaz sai kuma ya siya gida a badikko suka dawo sa bo da yafi kusa da gurin kasuwancinsa, ta yi missing ƙawarta aminiyar ta dan a gidan su take wuni, harta kowa na unguwan ya sheda ƙawancan su, tin ta na jaririya Mahaifiyata ta rasu a cewan Babanta, gurin Maman su Rabi ta taso cikin wahala da azaba sam basa raga mata ita
da yaranta, ga shi ita yarinya ce me natsuwa da girmama na gabanta, ta na musu biyayya iyakar yinta, da ƙyar ta samu ta kammala junior level, islamayi kuwa a aji hudu ta bar zuwa, Mama ba ta bin Malamai amma tasan kan sharri babu ranan da ba zasu jamata duka ba shi kuma Baba baya bincike sai duka, shekara 3 kenan da dawo warsa unguwan sannan wata 7 kenan da ta fara zuwa aiki gidan wata Hajiya ta na ba ta 5k duk wata sai ta kaima Mama amma ko sisi bata ba ta. cikin kwanankin da be fi wata ɗayan ba ta fetse da zama ma ra kunya ba na gida ba har da ƴan layi da su ka tsane ta duk da sai wanda ya shiga gabanta ta ke mai raddi, Mama wanda a yanzu ta ke ce ma ta Aunty sai dai in agaban Baba ne. ta ɗaura ɗammaran nan da sati 3 wanda shine bikin su Radiya sai ta baƙan ta mu su kafin subar gidan, sunyi ma ta abubuwa da yawa, sharri babu wanda basa mata, a yanzu tsayinsu ɗaya dasu harma ta huce su, ta dai san a duku ba za ta bugu musu ba, yanzu ko ta zo da abinci ita da Umar kawai ke ci da kuwa su ta ke ka wo ma wa su ra ba, ta rantse kuɗin watannan idan an ba ta ba zata ba yarda ko sisi ba za ta sissiyan abubuwan buƙa ta ne, Mama in zata hana ta sai ta ce za ta faɗa ma Baban dan dama be san ta na zuwa ba rufa-rufa aka mai, ta yi shuru ne kawai sa bo da ba ta don su samu matsala da tini ta tona abin da ke faruwa.

Cigaban labari

A dai-dai ƙofan chemist ta tsaya dan ganin akwai wani aciki bayan ya fito ta shiga tana gaishe Ado, amsawa ya yi sannan ya miƙa ma ta 1k amsa ta yi ta mai godiya ta futa ta na jin daɗin dan kuɗin Alluran jiya ce sukai ra ba dai-dai da me chemist din ko wa ya dau 1k. ta na ta zance zuci harta shiga gidan Hajiyar domin yin aikinta.

END
*Daga alƙalamin Pretty Sk*

[6/1, 15:56] ᑭᖇᗴTTY ՏK ✍️✍️✍️: https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

💪 JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIAION (J.W.A)💪
Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi.✍️

𝐑𝐀𝐒𝐇 Ɓ𝐎𝐘𝐀𝐘𝐘𝐄𝐍 𝐌𝐀𝐒𝐇𝐄Ƙ𝐈

story & written -------
ᑭᖇᗴTTY ՏK
ꜱᴀᴋɪɴᴀ ᴀʙᴅᴜʟʟᴀʜɪ

page 7

************* **********

************** ******************
KINKINAU

yau ma kamar kullum ta dawo da ga islamiyya kenan ta shiga gida anan ta tadda Zainab da wani suna hira wato sabo saurayinta, dogo ne mai ɗan duhun fa ta, sai faman hira suke suna murmushi ƙara sawa ta yi ta gaishe shi aiko ya amsa cikin sakin fuska kaman ya san ta, sannan ta shige gida abinta

" Masha Allah ashe ƙanwarki ta fiki kyau duk da tana sanya da niƙaf amma masha Allah kawai." Muhsin ya yi maganan da si gan wasa dan ha ka Zainab ta ce

" Uhmm na ji ai da ma nasan ni banda kyau." sai ta miƙe tsaye ta na turo baki duk cikin wa sa

" Ha ba gimbiya, ita ta isa ta fiki kyau wasa na keyi na janye kalman, My haƙarƙari zauna abin ki" sai suka kwashe da dariya dukkan su, ta zauna suka ci ga ba da hiran su ita kuma Ramlat ta shiga ɗakin su.

****

" Sis gaskiya Zainab ta yi sa'a nasan wanda nagan ta dashi a wajen nan." Ramlat ta faɗa ba ya ta cire hijab din ta sai Hajara ta ce

" A ina kika san shi?."

" ya na kawo wasu yara islamiyyan mu, gaskiya mutum ne mai kyauta da sakin fuska ba shida da mu wa."

" Ma sha Allah ha ka ake so, naso nima na ganshi amma akwai wata ran ai ba zan fita yau ba."

" Hmmmmmm ai Yaya Muhammad da Yaya Usman sun fishi kyau." Zainab ta faɗa a lokacin da take shigo wa, sai maryam ta ce

" Uhmmm bawani nan Usman fa be da tsayi." sai suka kwashe da dariya sannan Zainab ta kuma magana ta na kallon Ramlat

" Ramlat ta shi ki faɗa mana wane ne yafi kyau aciki tin da duk kin san su." sai su ka mai da hankali akan ta sai ta ce

" Yaya Muhammad na Hajara shi be da damuwa, salihin ba wa ga kyauta, toh na baki 70%, shikuma na Maryam ya shin 20% zan bashi mutum sai uban kishin tsiya....."

"Tab ana nuna min wariya anan gurin amma ai fari ne dai." Maryam ta faɗa ta na dan hararan Ramlat

" Eh amma kinsan dai halin shi ga faɗa, ba gaira ba dalili za kisha fa ma Husaina." cewan Hajara

"Uhm sai Yaya Muhsin shi kuma na ba shi 95%...."

" Iyyema yarin yar nan ba bu mai 100%?."

"Gaskiya babu ana wa result din sis Hajara"

" To Allah Ubangijin ya baki mai 100% ƴar autan mu."

" Ameen Zainabu tahhhh."

" Ramlat ba ma kunya , ah to ya yi ma na." Hajara ta miƙe ta fita dan du ba girki, su kuma su ka ci gaba da hiran su kwanin sha'awa.

********* ************* *************
Babu wanda ya fita agidan yau sa bo da suna shirin tarban Uncle, misalin 1:30 Uncle ya da wo kar kuso kuga yadda familyn ke nu na mai ƙauna da kulawa, wanka ya yi sannan ya fito su ja haɗu a daining danyin lunch, su 18 ne ko wa da yalwataccan murmushi, Uncle mutum ne mai wa sa da dariya, do go ne mai cikan haiba da kamala be san abubuwa biyu a rayuwan shi, rashin kunya da tsiwa shi yasa su ke shira da ƙannan na shi duk da akwai ma su wannan halin

"Ya maganar BABBAN YAYA." faɗin Pazar M ya na shan ruwan kwakwa, sai da hantar ƴam matan suka, dan jin sunann Babban yaya, sai Uncle ya ce

" har yanzu duk ka numbers din ba sa tafiya kuma last call dimu ya ce china za shi."

" Okh ai wallahi idan ya dawo gidan nan, ya shigo kenan ba shi ba barin ƙasar nan, kusan 2yrs be zo ba ba shi da aiki sai ya wo zuwa neman magani, ni fa ba yadda da wannan yaron da suke ta re na ke ba kawai shaƙa tawa su ke zuwa ƙasashen duniya." Pazar B ya kai magana ya na jan tsaki sai Pazar Q ya ce

" Wai Adamsi?."

" Eh mana shi, basu da na yi sai ya wo hmmmm."

" Pazar M Insha Allah za mu sa mu numbers din shi.

" Shike nan Allah ya sa." wayan Uncle ne yahau Ringing ganin new number ku ma True-caller be yi identifying number ba ya sa be ɗauka ba, sai da ta katse har sau biyu, dan abinci suke ci ne, su na ga ma cin lunch, su ka ko ma Main parlour suna hiran su, Baby sai labari take ba shi ya na ta dariya, ya na son familyn shi, su Pazars kallo su keyi a babban T.V su kuma Momcy na su hiran suke na manyan muta ne,, take aka fara haska labarin da ya girgiza Nigeria a satin nan, Video ne wanda aka saki yanzu a Social Media, hakan ya sa kowa na Parlour ido ya koma kan T.V dan jin cikakken rahoton abin da kunnuwan su su ka jiyo, cikin majigin TVn wani mutum ne ke zaune kan wani dogon gujera, ya na san ye da baƙaƙen kaya wanda ko ina na jikin sa a rufe ya ke harta kwayan idon shi ya sa glass magana ya fara yi ciki wani kalan murya mai amo da cika kunnan me sauraro.

" Ƴaku mutanen Nigeria barkan ku, ni ne wannan ɓoyayyen masheƙi wanda ku kafi sani da RASH masheƙi, a yau ma zan dauki ran wannan shahararren dan kasuwan nan mai suna Ibrahim Sani Greto ...."

"Ibrahim greto kuma, wai ni waye wannan ɗan Iskan yaron ne, kaman babu hukuma a ƙasar na, ha ka last week ya nuna ya kashe wani Doctor a kebbi state" cewan Pazar Q ya na jin ba bu daɗi har ransa, ai kafin ya maida idon shi ga T.V RASH ya yan ka Ibrahim Sani Greto, sai jini ke zu bowa da ga jikinshi, salati su ka hau yi dukkan su suna ta duba wayoyin su ganin ko ina an haska wannan mugun videon dan direct ne, kuma masheƙin yakan kashe kowa sannan ya datsi tashoshin TV ya musu ƙurar, daganan sai muta ne ɗauka a sa me dukka Media sai abin ya yaɗu.

" RASH! RASH!! shi ne babban matsala muta ne a yanzu, kashe mutum a gunsa ba bu wahala, gashi sai bincike akeyi amma ko ma kama ɗaya ba'a samu ba, ya kashe babban ɗan kasuwan na Nigeria wanda ya ke zaune a Abuja wato Ibarahim Sani, kuma kafin shi ya kashe wasu, shin wai wanene RASH? RASH, RASH masheƙi sunan dake ta yawo kenan a media, hankalin mutane da ya wa ya na ta she

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login