Showing 60001 words to 63000 words out of 93691 words
Unguwan mai dabino
___________ Ranta a haɗe take kallon sa shi kuwa ko ajikin sa, hannu ya sa ya amsa wayan sa a hannunta sannan ya ce.
" Madam ba zan kai dare ba na yi alƙawarin."
" Ba wani amma ce min ka yi ai ba za ka ko ina ba, shine ka shirya wai za ka fita ."
" Sorry Sweetie, My Sweet Kandy ta, kiran Babban yaya ne shi yasa."
" Okh, karka manta da fura da nono irin na jiya."
" Allah ya kawo kuɗin, zan siya mi ki, kar ki yi girkin dare da ni." hannunsa ta sa ki dan sun kai ƙofa in da zai fita, a hankali ta ce
" Me yasa kar na yi dai?, Ba ya yin daɗi koh?."
"Haba ai da ne baki iya ba amma yanzu kin kware ai, ba Maman zul-yadain na koya miki ba."
"Uhmm yanzu su snacks za mu fara ma."
" Kandy ki fara kwarewa a jollof dai." murmushi suka yi ma juna sannan suka rabu, maimakon ta kwanta kaman yadda ta sa ba, sai ta hau gyaran ko ina sannan ta kwanta tana jiran Maman Zul-yadain.
************* ************
"Ka manta wannan." faɗin Beauty tana miƙa ma Skiddo wanda ya ke amsa waya kuma ya na tsaye dan amsan jakkansa ta baya. amsa ya yi sannan ya sauƙe wayan daga kunne ya ce.
" My Haulat ba ra na je in kinga ban kira ki ba to kiyi girki amma in na sa mu da ma zan siyo mana."
" Toh Allah ya tsare, Please take care of yourself to me." Murmushi ya sa ki mai sanyi sannan ya fita daga gidan, har za ta shiga ɗaki sai ta fasa ta shiga kitchen, soya doya ta fara yi wanda zata yi breakfast, sai masu ɗiban ruwa suka shigo, cikin da ra ha ta musu iso, dan a yanzu ba ta damuwa, rayuwa ta ke ta riƙe Allah kawai da auranta.
" Maman takwara, idan takwara ta dawo makaranta dan Allah ta zo na aika ta siyan kayan miya." Faɗin Hauwa'u tana fito da wanke-wanke tsakar gidan daga gefe guda, Matar da ta yi ma magana ta ce
" To shike nan, za ta zo Allah yasa karta tsaya wasa idan an tashi."
"To Ameen dan takwaran akwai son wasa kaman me." suka yi dariya,a haka har ta gama ɗiban ruwan, ta ɗi ba na ƙarshe kenan sai Beauty ta ɗiban mata soyayyen doya ta sa mata a leda ta ba ta, ta amsa da godiya tana hucewa har ranta take jin daɗin mu'amala da Hauwa'u dan akwai kyauta, gashi ba ta da rowa, ta dai san ta sauya ba yadda aka kawo ta ba dan a lokacin ko kallan su ba ta yi, sai ta kulle gidan ta hana ɗiban ruwan, amma daga baya sai ta can za, ta lura in dai ta san mutum ne take sakin jiki da shi..
********************* *********************
__________ "NEPAAAAAA." Gaba ɗaya unguwan ta dauka dan an kawo hutan lantarki, da gyar ta buɗe idonta dan wani mugun barci ne ya ɗauke ta, ganin hutan lantarki yasa ta tashi t ajona wayan ta da power bank, sannan ta fita parlour ganin Almajirin ta na zaune daga bakin get din gidan ta ce.
" Shazali yaushe ka zo?."
" Aunty tin ɗa zu, na gama ɗiban ruwan ai."
" Okh yanzu ka je gidan yayata ka ce ta ba ta power bank na yi ma ta charji."
"To." Shazali mai kimanin shekara 11 ya tafi dan zuwa gidan Beauty, ko da yaje ya gaida ta, ta amsa cikin sakin fuskan dan ta san Beasty ce ta aiko shi, saƙo ya faɗa ma ta sai ta ce.
" ka ce mata na ba da a nan maƙota kawai, sannan ka ce mata gobe ne, kar ta yi halin na ta." Shazali ya amsa da "To.", sai da ta ba shi abinci ragowan na jiya ya ci sannan ya wuce, faɗa ma Beasty abin ta ce ya yi, sai ta yi murmushi tana ti na gobe shine zasu je gidan Fancy sannan halin ta shi ne barcin safe.
END.
*****𝐏𝗿𝗲𝘁𝘁𝘆 𝐒𝐊****
[7/9, 10:36] 𝐏𝗿𝗲𝘁𝘁𝘆 𝐒𝐊..............: https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 ᴊᴀᴊɪʀᴛᴀᴛᴛᴜ ᴡʀɪᴛᴇʀ'ꜱ ᴀꜱꜱᴏᴄɪᴀɪᴏɴ (ᴊ.ᴡ.ᴀ)💪
ʀᴜʙᴜᴛᴜ ʙᴀɪᴡᴀ ᴄᴇ ᴅᴀɢᴀ ᴀʟʟᴀʜ, ᴊᴀᴊɪʀᴛᴀᴛᴛᴜ ɴᴇ ᴋᴀᴡᴀɪ ᴋᴀɴ ɪʏᴀ ᴀᴍғᴀɴɪ ᴅᴀ ᴡᴀɴɴᴀɴ ƙᴀꜱᴀɪᴛᴀᴄᴄɪʏᴀʀ ʙᴀɪᴡᴀ ꜱᴜ ꜱᴀᴜʏᴀ ᴛᴜɴᴀɴɪɴ ᴀʟ'ᴜᴍᴍᴀ ᴄɪᴋɪɴ ꜱᴀᴜƙɪ.✍️
𝐑𝐀𝐒𝐇 Ɓ𝐎𝐘𝐀𝐘𝐘𝐄𝐍 𝐌𝐀𝐒𝐇𝐄Ƙ𝐈
ĎĂĞĂ ĂĹƙĂĹĂМĨМ РŔĔŤŤŶ ŚĶ
✿◡‿◡✿ [Sakina Abdullahi] ✿◡‿◡✿
typing....
Page 51
**************** ******************
__________________ "Yanzu duk kansu ne a nan." Zaki ya faɗa yana ɗa ga papers ɗin da ke kan desk, sai Sakeenat ta ɗago Idanun ta da ga kallon computer, wanda take operating cikin kwarewarta.
"Eh su ne, yanzu abin da ka ke zargi ya tabbata a kan Rash."
"Amma ya shiga hatsari sosai, dan babu wanda zai iya fahimtar abin da mu ka fahimta mu."
" Haka ne amma zan tura mai secret sms."
"Na ƙa gu na haɗu da shi." ya faɗa ya na koma wa kan sopa.
"Ni kai na ina son ganin shi, ina son nasan wanene shi." Zuciyar ta ɗaya ta faɗa hakan ba tare da tasan maganan ya da ki zuciyar Zaki ba dan mutum ne shi me kishin gaske, sam ba ta lura da yanayin sa ya sauya ba sai da ta miƙe daga in da take ta kalle sa.
"Baby what's wrong?." Ta tambaya ta na zama gyefan sa, be kula ta ba haka be kalle ta ba, aka karo na biyu ta da fashi tana kuma ce wa.
"Lafiya?." Kafin ta ce wani abu ya sa hannunsa ya cire na ta hannun da ta dafa sa, Ita dai a iya sanin ta ba ta yi komai da zai sauya mood ɗin sa ba, miƙewa tsaye ya yi sai ya koma parlour, ganin haka sai ita ma ta bi bayan sa, zaune ya ke amma sai ti na kalaman ta yake yi.
"Daga yau za ki bar wannan aikin na ki na bincike." Ya faɗa da kakkausar murya, sai ya dawo ainiyin Zaki na gurin aiki.
" Baby ban gane ba? Wani aikin zan de na?."
" Abin da na ce kenan." sai ya nufa ƙofan fita har ya buɗe ƙofan ya ji ta na ce wa.
"9:10pm dare ya yi ina za ka je?."
" Ni kaina ina so na gansa, ina son na san wanene, hmmmmm." abin da ya ce kenan ya banko ƙofan da uban ƙarfi bayan ya fita, murmushi ta sa ki dan ta fahimci in da zance ya dosa wato kishi ya motsa. miƙewa ta yi ta kunna T.V ta sanya wani shiri da ta ke bibiya a Star Life TV.
___________Ya na fita ya shiga giɗan su Aliyu, gaishe shi guard suka din ga yi ya na amsa wa har ya shiga main parlour, Hajiya, Momcy da Mom ne ke hira cikin ra ha abin su, gaishe su ya yi suka amsa sai sannan ya zauna a gefan Mom dan sunfi wasa da ita.
" Ango Ango, idon ka ke nan ?." cewan Mom sai da ya sosa kan sa kafin ya ce.
" Mom wani ango kuma, ai mun tsufa mu kam."
" Tin da aka yi bikin nan sau biyu Amarya ta shigo ta gaishe mu fa, why ba ka barin ta ta shigo?." Hajiya ta kan nan tana kallon Zaki, kafin ya yi magana Momcy ta ce.
"Ai da an yi mai magana sai ya ce tana aiki ne babu lokaci, wa ya mutu wa ya tashi."
"A'a Momcy ba ha ka ba ne, amma gobe za ta zo In sha Allah."
"Allah ya sa da gaske, yanzu ma mai ya hana ku zo tare?." Mom ta tambaya sai ya ce.
"Ta yi barci ne." Sannan ya miƙe dan tambayoyi ne zasu yi ta mai kan an aiko su, hannu ya miƙa ma abokin sa wanda ya fito tare suka yi musabiha.
" Ba ra mu shiga ciki."
" Ashe gun aboki ka zo ba gaishe mu ba."
" Mom a'a, yanzu zan dawo ai, zan duba Meerah an ce ba ta jin daɗi." Daga ha ka su ka shiga part din Aliyu, za ma suka yi a kan sopa sai Aliyu ya miƙe ya shiga kitchen bayan dan lokaci ya fito ɗauke da babban plate, ajiwa ya yi akan center table ya na ce wa.
" Yau za ka ci girki na fa."
"His Excellency da kan sa ya ke girki, wow."
"To ya zanyi sai haƙuri ai Madam ba lafiya jiya sai da mu ka je asibiti amma Alhamdulillah." Kafin Zaki ya yi magana sai ga Ramkat ta fito, tafiya take da ƙyar saboda nauyin ciki, sanye take cikin hijab blue har ƙasa amma a kallo ɗaya za ka ga ne kumburan ta da tayi da duhu, sai da ta zauna da taimakon Aliyu, sannan Zaki ya yi mata ya jiki, ta amsawa ta yi ta na sakin murmushi wanda iya fuska ne kawai dan ba ta jin daɗin jikinta.
"Haidar ka san zargin mu akan Rash gaskiya ne." Ramlat ta za ro ido ta ce
" For real Zaki?."
"I'm very sure." yadda Sakeenat ta faɗa mai haka ya zayyana mu su, shuru ya ratsa gurin sai Aliyu ya ya ce.
"Ikon Allah, wane ne wannan Rash ɗin, ka ce ta tura mai saƙon sai mu jira mu ga abin da zai ce."
" Ya dau babban kasada da rayuwan sa."
"Allah ya sa mu da ce, yauwa Aliyu gobe sunday muna da meeting da president Bola Ahamed Tunubu a Abuja, zan bi flight amma dole na ɓa ta lokaci, sannan ban san zuwa na fiso na tura a ɓoye." Take ya ba Zaki labarin wa'inda suka zo ɗazu office din sa sai Zaki ya ce.
"Allah ya kai mu zanje, dan gobe ina free " Daga haka suka dinga hira har Meerah ta shiga dan yin barci, sun jima ba su haɗu sunyi hira sai yau.
" Kai wai har 11:10pm ya yi." Faɗin Aliyu yana duba wayan sa, sai a lokacin Zaki shi ma ya an kara duk da so ya ke ya yi dare sosai.
"Bara na je, na bar ƴar muta ne a gida ita kaɗai."
"Gaskiya kam duk da akwai get-man amma be ka ma ta ba." Da ga haka su ka jera har main parlour, sannan Zaki ya ce.
"Ka ga koma abin ka, zan ɗan gai da Aunty kan na wuce." Daga nan kuma suka yi sallama ya koma part ɗin sa, main parlour ɗin babu kowa sai Aunty wacce ta fito daga part ɗin ta, a duk lokacin da ya ga Aunty cikin farin hijab sai ya ga sak Mahaifiyar su dan ita ma'abociyar farin hijab.
"Auntynah, Mamanah." ya faɗa yana isa gaban ta, za ma suka yi a akan kujera ɗaya, sai ya ɗauka kan sa kan cinyarta ya na ce wa.
" Ina kewan Mama."
"Nima ha ka Asad." Ta ke kalman 'Asad' ya sa Ramlat ɗin sa ta faɗo ma sa duk da kullum ita ya ke gani a tare da Pretty Sk.
" Allah ya gafarta mu su, Baba da Mama." sai ya yi murmushi.
" Ameen ƙanina." Hira suka ɗan yi suna yi tana sosa mai gashin kan sa, a haka har Pazar Q ya fito daga part din su yana ce wa.
" Daga ɗauko min drink sai na jiki shuru, ashe Zaki ne ya riƙe ki."
" Ya Allah, I'm sorry Baban Baby wallahi na sha'afa ne." Ta faɗa tana so ta miƙe dan tini Zaki ya ɗaga kan sa daga cinyar ta.
"No bar shi har na sha wancan ai." Ya zauna ya na kallon su sai kuma ya ce.
"Sai na ga kaman Zaki yana so ya fiki kyau ne."
" Uhmmm ai na fishi, dan har yanzu angon cin ne be sa ke shi."
"Aunty ango kuma, kin dai san ko a ɗa na fiki kyau sosai balle yanzu, dan ma ban hutu kaman ke da hmmmmn, Ni bara na wuce ma "
"A'a zauna abin ka ni na shige ba ra na je na kwata." Faɗin Pazar Q ya na miƙewa, sannan ya wuce, sai Aunty ta ce.
" Kafi Mama kyau koh?"
" Ni awa, Mama ta fini ma na." Ya yi saurin ba ta amsa sai ta saki murmushi sannan ta ce.
"Kuma ka ce sak na ke da Mama, to ni ban fahimta ba?."
"Aunty ɗan kama ne kawai ku ke yi."
"Kai wai lafiya 12:04pm ka na nan?, dare ya yi sosai fa."
" Ok bara na wuce, ai nasan tayi barci ti ni." Jin hiran su Baby ya sa suka kalli in da suka fito, ta ƙofan ɗakin Babban ya suka fito, gaishe shi suka yi ya amsa sai Aunty ta ce.
"Sai yanzu ku ka ga ma karatun?."
" Eh Aunty, ba ra mu shiga, good night." Faɗin Karis, sannan suka shiga part din su, Butter ce ta kashe globe bayan ko wacce ta hau bed ɗin ta, sai Karis ta ce.
" Allah yasa gobe muji alheri akan JAM result."
"To ameen, kin ga idan mun ci sai mu roƙa zamu je gidan Fancy idan Pazars za su bar mu."
"Haka ne Allah ya kai mu, kin san karatun yau ya ta shi kai na."
" Baby muna ɗaya nifa har kunya-kunya Aunty Ramlah na dinga ji." sai suka kwashe da dariya dan ti na yau fiƙihu suka yi sun sha dariya, da yake yanzu kullum suna part ɗin ta dan koyan karatu da girki, da Baby ce kawai ke zuwa daga ba ya su ma su ka fa ra zu wa, kuma suna matuƙar jin daɗi karatun balle na yau.
______ "Hadith ne duk da ya na da rauni, (Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Miskini ya ce! Miskini ya ce!! Miskini ya!!!. Sai Sahabbai su ka ce : Wa man ya Rasulullah?. (wa ye). Sai Manzon Allah (s.a.w) ya ce: Almar'atul lati laisa laha zawjun, walau ka nat ganiyyatun minal maaa).. Baby wallahi aure akwai daraja sosai, marta ban matar aure da ban da na budurwa, ga Bonus na la da. Karima da ki ran kwaɗa kwalli ki sha turare, ke kin ƙure kwalliya, kin ya fa ƙaramin Vail kin fita, wallahi duk haram ne, babu kyau, amma ni kam, ko a yanzu ace na ran kwaɗa kwalli wa Babban yaya na sha turare, ke idan ma Swimming dress na yi, la zan samu sosai fa." Sai da suka kwashe da dariya, Ita kam ko a jikinta ta kuma ci gaba da misalai, wani su yi dariya, wani kuwa su yi murmushi. Barci ne ya ɗauke su dan sun gaji ba laifi.
END
Daga Sakeenat Abdullahi.
[7/9, 19:51] 𝐏𝗿𝗲𝘁𝘁𝘆 𝐒𝐊..............: https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 ᴊᴀᴊɪʀᴛᴀᴛᴛᴜ ᴡʀɪᴛᴇʀ'ꜱ ᴀꜱꜱᴏᴄɪᴀɪᴏɴ (ᴊ.ᴡ.ᴀ)💪
ʀᴜʙᴜᴛᴜ ʙᴀɪᴡᴀ ᴄᴇ ᴅᴀɢᴀ ᴀʟʟᴀʜ, ᴊᴀᴊɪʀᴛᴀᴛᴛᴜ ɴᴇ ᴋᴀᴡᴀɪ ᴋᴀɴ ɪʏᴀ ᴀᴍғᴀɴɪ ᴅᴀ ᴡᴀɴɴᴀɴ ƙᴀꜱᴀɪᴛᴀᴄᴄɪʏᴀʀ ʙᴀɪᴡᴀ ꜱᴜ ꜱᴀᴜʏᴀ ᴛᴜɴᴀɴɪɴ ᴀʟ'ᴜᴍᴍᴀ ᴄɪᴋɪɴ ꜱᴀᴜƙɪ.✍️
𝐑𝐀𝐒𝐇 Ɓ𝐎𝐘𝐀𝐘𝐘𝐄𝐍 𝐌𝐀𝐒𝐇𝐄Ƙ𝐈
ĎĂĞĂ ĂĹƙĂĹĂМĨМ РŔĔŤŤŶ ŚĶ
✿◡‿◡✿ [Sakina Abdullahi] ✿◡‿◡✿
typing....
'
*Page 52.
A parlour kuwa, Zaki ne da Aunty suka yi sallama sannan ya koma gidansa. Ya saka key ya buɗe parlour ɗin, sai ya tarar da babu kowa, sai T.V da ke aiki. Ya kashe shi, yana addu’ar Allah yasa ba barci ta yi ba.
Da yake a ɗakin shi suke kwana, sai ya fara shiga, amma bai ganta ba. Ya wuce ya yi wanka, bayan ya fito ya sanya PJmas. Ya shiga ɗakinta, sai ya hange ta kwance cikin bargo. Ya murmusa sannan ya zauna a bakin gadon.
Ya so dai yazo ya ganta tana jiran sa ta ba shi haƙuri, amma sai yaga barci take sha. Shuru ya yi, sai yaji ta motsa. Ta rungume shi ta baya, bakin ta kusa da kunnensa tana ce wa:
> “Bazan iya barci ba alhalin Babyna na fushi da ni. Fushin ka kan janyo min tsinuwan Allah da Mala'iku. Wallahi ba da wata manufa na faɗa ba. Kai ma ka sa ni, a duniyar nan banda wanda nake so sai kai. Kai kaɗai ne Zakin Zaku na, masoyi abin so na.”
Har ransa ya ji daɗin wannan kalaman. Ya rike hannayenta yana ce wa:
"Ba komai, kawai raina ne ya ɗan sosu. Please, ki rinka kula da kalamanki. Kinsan ni mai kishi ne.”
> “Insha Allah, Baby. Kishi ai halal ne. Manzon Allah ya ce: *‘Wanda bai da kishi ba, ba zai shiga Aljanna ba.’* Sannan ina so ka janye kalmanka akan aikina, ka ji?.”
> “Shike nan, ya wuce. Matata abar ƙauna ta.”
Daga nan ta zagayo gaban sa. Kallon ta yake yi cikin ƙauna mara misali. Suka koma ɗakinsa, bayan sun zauna sai ta ce:
> “Bari na kawo ma ka abinci nan.”
> “A’a, Alhamdulillah, na ƙoshi,” ya faɗa. Sai ta dawo baya tana ce wa:
> “A ina ka ci abinci?”
> “Gurin Meerah.”
> “To ni wallahi ban yadda ba! Ina jin yunwa, na ƙi cin komai ina jiranka. Amma shine... uhmm uhmmmm.” Ta faɗa tana kifa kanta a gado, ta fara kukan shaƙwaɓa.
> “Ya-salam! Daga cewa na ƙoshi sai kuka? To ya ƙuri, My Pretty,” ya faɗa yana ɗaga ta daga kwanciya. Ya shiga rarrashinta har ta yi shuru. Ta ɗauko abincin, duk da yana ƙoshe, sai da ya ci don zaman lafiya.
*********************** ******************
RASH
_____________________Cikin wannan gidan na sa motoci guda uku su ka fito black suka ɗauki hanya har suka hau kan titi, motan gaba da ba ya dukka matasa ne masu sanye da kaya kala ɗaya, kuma ko wannen su a bayan rigan sa sunan mamallakin mai sanye da shine sai harafi ɗaya a cikin sunan RASH, wani A, wani H haka dai suke, Airport suka nufa gaba ɗaya su goma sha shida ne (16), privet jet suka hau ba su sauka a ko ina ba sai Abuja, suna sauka a airport motoci da yawa suke jiran su, ha wa suka yi sai wani babban gida suka nufa, motoci bakwai ne suka yi parking a haraban babban gidan fitowa suka yi wanda a cikin su har da Shuraim, shiga su kayi wasu kuma suka tsaya a compound ɗin, gidan sai ma sha Allah, komai ya haɗu, ga ɗakuna ma su masifar yawa, wani room su ka shiga wanda na'urori ne kawai a ciki nan suka je suka hau aiki a ciki, Rash kam zama ya yi a wani kujera ya fito da wayan sa yana kiran number Ramlat, bugu uku ta ɗauka, a hankali yaji sanyaryar muryan ta, ta cikin wayan.
" Ina kwana." sai da yaja fasali tukun ya ce.
" Lafiya, kinga ban dawo ba koh?."
" Uhm fatan Lafiya?, Ina ta kiran number ka baya shiga."
" Ina wani babban aiki ne, kuma zuwa