Showing 48001 words to 51000 words out of 93691 words
kafin lokacin ta bayyana."
" Bakya sona ko?."
" Hmmmmm Ƙaunarka kawai na ke." Daga haka ta shige bedroom ɗinta, lumshe idanu ya yi, yayi Istikara kan wannan lamarin amma Sk ita kaɗai yake gani shi yasa ya zaɓi faɗa ma ta ha ka.
************* *****************
Air Force Base
Jigum jigum suka yi dukkansu su biyar ɗin suke zaune, Dad, Maa, M.d, sai mata 2 wa'inda a kallo ɗaya za ka ga tsananin kama su da Maa, dan ƙannanta ne, ita ce babba sai Hafsa da Halima, amma ta girme su sosai, tsakanin su shekara biyu ne, Hafsat 26 sa'ar A.A sai Halima 24. Tin suna yara suka dawo gurin Maa da za ma dan iyayen su sun rasu, ta riƙe su tsakani da Allah dan ita kaɗai mahaifarta ta haifa sai ta mutu, gurin Hajiya Baraka ta taso cikin kulawa a lokacin Baraka na da shekara 18 amma ta koma ma Maa mahaifiya, da yake yarinyar ƙanwar Mahaifarta ce, bayan wani lokaci sai kawai ta auri mahaifinta ko a lokacin Maa na da shekara 8, sannan ba ta haihuwa har Maa ta yi aure dan sun fidda tsammanin za ta haihu.
" Yaron nan wai me ke damunsa ne? Tin jiya ya bar giɗan nan kenan, na ra sa ya zanyi da Auta wallahi, yanzu ya wuce London din kenan babu sallama?." Maa kaɗai ke ta zazzaga masifarta ita kaɗai babu wanda ya ce ƙa la, dan duk yadda A.A ya za ma ta na da sa hannu dan ita ba ta kwaɓa ma yaro balle shi.
" To ya za muyi sai addu'a kawai amma be kyauta ba gaskiya." faɗin M.d sai Hafsat ta ce
" Allah ya tsare mana shi." dyaga haka ta gyara veil ɗinta wanda da shi ta shigo gidan sannan ta nufi part din su ita da Halima.
" M.d je ka kwanta dare ya yi." a tare shi da Halima suka miƙe tare da barin gurin. Sannan Dad ya ci ga ba da ce wa.
" Tinda ya ce mana ze tafi ai yayi ƙoƙarin ma, hala yanada babban aiki a can din ne."
"Hmmm Alhaji yaron nan maganin shi zanyi da wuri, kafin ya dawo zan sa ka daura mai aure da Salma, sai na ga ta tsiya."
" Maa duk yadda ki ka ce ai."
END
𝕻𝖗𝖊𝖙𝖙𝖞 𝕾𝕶
[7/3, 19:27] 𝐏𝗿𝗲𝘁𝘁𝘆 𝐒𝐊..............: https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 ᴊᴀᴊɪʀᴛᴀᴛᴛᴜ ᴡʀɪᴛᴇʀ'ꜱ ᴀꜱꜱᴏᴄɪᴀɪᴏɴ (ᴊ.ᴡ.ᴀ)💪
ʀᴜʙᴜᴛᴜ ʙᴀɪᴡᴀ ᴄᴇ ᴅᴀɢᴀ ᴀʟʟᴀʜ, ᴊᴀᴊɪʀᴛᴀᴛᴛᴜ ɴᴇ ᴋᴀᴡᴀɪ ᴋᴀɴ ɪʏᴀ ᴀᴍғᴀɴɪ ᴅᴀ ᴡᴀɴɴᴀɴ ƙᴀꜱᴀɪᴛᴀᴄᴄɪʏᴀʀ ʙᴀɪᴡᴀ ꜱᴜ ꜱᴀᴜʏᴀ ᴛᴜɴᴀɴɪɴ ᴀʟ'ᴜᴍᴍᴀ ᴄɪᴋɪɴ ꜱᴀᴜƙɪ.✍️
𝐑𝐀𝐒𝐇 Ɓ𝐎𝐘𝐀𝐘𝐘𝐄𝐍 𝐌𝐀𝐒𝐇𝐄Ƙ𝐈
ĎĂĞĂ ĂĹƙĂĹĂМĨМ РŔĔŤŤŶ ŚĶ
✿◡‿◡✿ [Sakina Abdullahi] ✿◡‿◡✿
typing....
Page 39.
**************** **************
ROYAL HOSPITAL WHITECHAPEL RD, LONDON E1, 1FR, UK
Sanye yake cikin kayan likitoci, shi da wani doctor ne suke magana cikin yaren turanci.
*"Mr. Alexander, you know I didn’t specialize in matters of the brain, that’s why I brought her to you, because I trust your professional experience."
" Mr. AA don't worry." Daga haka ya mai da fuskan sa kan Airah wacce ke kwance, nunfashi kawai take saki a hankali. Fucewa ya yi ya koma masaukinsa wani hotel da ke opposite da asibitin.
*******************************
BAYAN WATA BIYAR
A yau ne aka ɗaura auren ƴammata shida daga Familyn ƙanƙara, Hassan, Husaini, Fatima, Khadijah, Hauwa'u da Hajara. Har dar da Zaki shi ya aure Sk bi sa tsayawan Pazars da Aunty, An sha shagali na kwana bakwai, sai dai akwai abubuwa da ke kewa da wasu acikin ƴam matan wanda ba su sa ni ba. Zuwa yanzu Ramlat da Merah sunyi nauyi sosai. Taro ya tashi lafiya sai dinner daza'a gabatar kafin ko wacce a kaita gidan auren ta.
************* ***************
Tsaya wa baku labarin gurin taron ɓata lokaci ne, amare na gyefe guda haka angwaye ma. hatta Babban yaya yana zaune daga gefe guda, shagali ya kai shagali, amare sun so su sha rawa amma babu dama Babban yaya ya hansu sa kewa. Hatta Gomna guda da wasu manya manya mutane sun halacci wannan taron.
" A ganina ba sai ka hukunta su ba ka barsu da halinsu dan Allah Baby." Ramlat ta faɗa da sigar roƙo, Shuraim da ke kallon ta ya ce.
" Karki damu Khadijah, Hauwa'u da Hajara kawai ne, banda Fancy a cikin su dama banda twins."
" Please."
" Hmmmmm na ɗan watan ni ne kawai." Daga haka ta bar magana.
Misalin 10pm aka tashi sannan motoci suka ɗauki amare. Kandy a iya saninta ta san iyayen Adam sun rasu dan Babban yaya shine ya tsaya mai akan komai. Ita aka fara kai wa wani ƙaramin gida mara fasali, gidan zaman mutum ɗaya ne, Babban yaya shi ya musu kayan ɗaki, dan haka ba suje ganin gida ba sam. Ƙawaye sai ƙananun magana su ke, dan ace wan Kandy babu country da be je ba sai gashi an kawo ta gida wanda babu nepa aciki. Layi ɗaya ne tsarkin su da Hauwa'u zan iya cewa kwanda gidan Kandy ma dan ita Hauwa'u gidan ba ruwa sai well sannan ba nepa, ƙananun ɗaki biyu, kitchen da ba yi duk suna waje. a layi ɗaya suke da Hajara, dama dama na ta dan ita get ne a gidan amma ciki kuwa sai a hankali, amma bayinta na ciki sai dai ita ma babu nepa babu ruwa har rijiya babu. Kowa abun ya ɗaure mai kai ganin yaƴan manya amma sun ƙare gidaje marasa fasali
Alhamdulillah Fancy cikin gidan su Chul aka ajeta, gida mai rai da lafiya, sai dai uwa uba shine in da aka kai Twins wato gidan su Meerah KK GRA..
Tin a mota Meerah da Ramlat ke ta dariya ƙasa ƙasa har aka mai dasu gida, part din Ramlat meerah ta zauna suna yin dariya san ransu, sun san ba komai yaja musu haka ba sai tsabar raina Ramlat da su ka yi suna ce mata ƴar talakawa, harta a gaban friends dinsu suna wulaƙanta, shi kuma Babban yaya ya na son ya koya musu darasi me kyau. Yaso harda Fancy amma ita ya barta, abin da be sani ba shine ita Fatima Allah ne da kansa zai nuna ma ta ishara.
Aunty da wasu ne suka kai Sk sabon gidan da Zaki ya siya a gefan na Familyn ƙanƙara, cikin aminci suka barta sannan su Aliyu aka raka ango gurin amarya.
************* **************
Unguwar mai dabino
Gidan Kandy, kuka take yi kaman ta yi hauka, yanzu wai a wannan gidan za ta rayu, tina abin da Babban yaya ya ce musu ɗa zu da rana tayi "Ni Shuraim a yau mun aurar da ku kuma ina mai janyo hankalin akan aure dan kunsa shi aure bautan Ubangiji ne, ko da wasa kar naji complain akan ku, duk in da Allah ya kai mutum ya yi hakuri dan yafi wasu, ba zan ɗauki yaji da mata ke yi ba haka saki duk wanda ta sa aka saketa to ta ne mi wani gidan, sai dai in da babban dalili ne." Sa ke rushewa ta yi da kuka, tana mai jiran Adam, aikuwa can sai gashi cikin manyan ka ya, abokansa na wucewa ta cire mayafin na ta sannan ta ce
" Ya Adam bangane ba, me na ke gani? Ina ne nan?." Har ranshi wannan hukunci Babban yaya ya yi mai tsauri, duk da darasin rayuwa yake son ya musu amma be so ta haka ba.
" My sweet Kandy, wannan shine gidan da na mallaka, na so na ne mi haya amma banda kuɗi duk a lefe suka ƙare."
"So kake ka ce anan zanyi rayuwa, babu fanka babu AC. How?."
"Kandy sa ta kikeso na yi ne ko mene?....."
" Ina kuɗinka? Duk aikin da kake da Babban yaya ba'a biyan kane?." Dariya yake son yi amma ya haɗe rai ya ce
" Ni ɗan rakiya ne, kuma nasiya fili ai karki damu zanyi gini soon." Kuka ta ci gaba da yi mai sauti, sai ya ajiye ledan ɗaya sannan ya buɗe ɗayan dan guda biyu ya shigo da shi,
" Kinga shi yasa na siyo mana fitila me chargi, a cike yake ma." ya faɗa yana kunnawa take hasken sa ya bayyana dan dama wayarta ta kunna flashlight.
" Ya zanyi na shiga uku na, Ya Adam meyasa ba ma faɗamin ba ko Pazars na tambaya su baka wani gida amma nan sam be yi ba."
" Khadijah ke ba yarinya ba ce, idan kina so na to idan kuma ba kyau sona, auran ai ba dole bane kuma......" da sauri ta toshe mai baki da hannunta wanda ya ƙawatu da zanen lalle mai shegen kyau sannan ta ce.
" Shike nan naji kasan ina sonka dai." Ya daga kansa, Rungume ta ya yi yana ƙara ƙaunata, har shi ze so ta sauka akan ƙyaman talakawa, ze so ta dawo yadda ya ke fata da Babban yaya.
**************** ********************
Abin da ya faru a gidan Kandy shi ne ya faru a gidan Hajara da Hauwa'u, gashi sun kamu da soyayyan Skiddo da Spider, haka suka kwana suna kuka, tare da jin babu daɗi akan ƙaddaran da ya faɗa musu.
END.
[7/4, 17:53] 𝐏𝗿𝗲𝘁𝘁𝘆 𝐒𝐊..............: https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 ᴊᴀᴊɪʀᴛᴀᴛᴛᴜ ᴡʀɪᴛᴇʀ'ꜱ ᴀꜱꜱᴏᴄɪᴀɪᴏɴ (ᴊ.ᴡ.ᴀ)💪
ʀᴜʙᴜᴛᴜ ʙᴀɪᴡᴀ ᴄᴇ ᴅᴀɢᴀ ᴀʟʟᴀʜ, ᴊᴀᴊɪʀᴛᴀᴛᴛᴜ ɴᴇ ᴋᴀᴡᴀɪ ᴋᴀɴ ɪʏᴀ ᴀᴍғᴀɴɪ ᴅᴀ ᴡᴀɴɴᴀɴ ƙᴀꜱᴀɪᴛᴀᴄᴄɪʏᴀʀ ʙᴀɪᴡᴀ ꜱᴜ ꜱᴀᴜʏᴀ ᴛᴜɴᴀɴɪɴ ᴀʟ'ᴜᴍᴍᴀ ᴄɪᴋɪɴ ꜱᴀᴜƙɪ.✍️
𝐑𝐀𝐒𝐇 Ɓ𝐎𝐘𝐀𝐘𝐘𝐄𝐍 𝐌𝐀𝐒𝐇𝐄Ƙ𝐈
ĎĂĞĂ ĂĹƙĂĹĂМĨМ РŔĔŤŤŶ ŚĶ
✿◡‿◡✿ [Sakina Abdullahi] ✿◡‿◡✿
typing....
Page 40.
******************* *****************
Air Force Base
Zaune take cikin babban mayafi, tana tsugunne ne a gaban wacce ke amsa sunan Uwar mijinta da ƙannanta biyu, sai mijinta a gefe, tamkar ba ita ce wacce suka taɓa zuwa dan gaishe ta ba, ta dinga rawar ƙafa akansu ita da Fancy da Beauty ne suka zo a lokacin. Tin da M.d ya kirata tun daga murya sa taji ya sauya mata dan cikin taushi yake mata magana amma ɗa zu kamar ba shi ba. sannan tin data fito zuciyarta ke ci gaba da bugawa sannan balle da Maa ta fara furta.
" To a wannan gidan dai dokana ne ke aiki sai na Auta wato ƙanin mijinki, idan na ce abu to ba'a mu sa wa, kije ki kwanta yanzu gobe misalin ƙarfe 7am ki fito kisame ni dan jin dokokin na wa da fara aiki da su."
" In sha Allah Hajiya Maa." Daga haka M.d ya ɗa gota suka nufi part din su, suna shiga ya ce.
"Please Fancy love, ki bi uwata sau da ƙafa kinji." baƙara min haushi ya ba ta ba dan haka ɗaga kai kawai tayi, shi kan sa be san meke damun sa ba, za ma ya yi yana da fe kansa, sai ta ce.
" Ba ka da lafiya ne?."
" A'a lafiya na ke kawai naji kaina na ɗan min ciwo ne." ya faɗa yana riƙo hannunta, ido cikin ido suke kallon juna, irin kallon soyayya nan kallon ƙauna, kallon me isar da zazzafan saƙo.
*************** ******************
Sallah suka idar sannan ya kama kanta ya yi mata addu'a wanda ya zama sunnah ga ko wani ango, abubuwa akan addini ya tambaye ta kuma cikin natsuwa ta ba shi amsa, har rashi yana mai farin cikin samun ta a matsayin mata, ya na da kyakkyawan yaƙini akan ta domin kuwa ya na so ya haskaka rayuwar ta da haske me yawa, ya wanke wannan duhun da ya ke cikin rayuwarta. Bayan sun ci abinci sai ta kalle sa ta ce.
" Na tina Ramlat baiwar Allah, haɗuwan mu uku kawai amma sai nake ji kaman jini na ce ita, komai na mu ɗaya, murya, jiki, tsayi abu biyu kawai na iya fahimtar banbancin mu shine na fita zafi dan ta fini tsoro, sai yawan sakin fuska dan ko da yaushe murmushi za ka ta nayi."
" Haka ne, na so da muka koma gurin Babanta ya ce kema ƴar sa ce sai dai ya ce shi Matarsa mace ɗaya kawai ta haifa, baiwar Allah ba ta ƙarewa."
" Ina mata addu'an idan tana raye Allah ya bayyana mana ita, idan kuma ta rasu Allah ya haskaka makwancinta da Rahman Allah." Sai suka haɗa baki suka ce 'ameen'. Sannan suka shiga faranta wa juna har Allah ya basu ikon mallakan juna, jini ya gauraya, sunnah ta afku cikin tsarin shari'an addini.
(Daga pretty SK 😍 Amare fatan Alheri, sai na zo cin chinchin da dubulam 😋)
******************* *******************
" Allah sarki Abbuu, Allah ya sanya alkairi." shuru ta yi tana sauraran na cikin wayan sannan ta kuma ce wa
"Shike nan tin da ka sanar musu, yauwa a huta lafiya Abbuu." Daga haka ta katse wayan tana jin farin ciki a ranta, Abbu ya aura wata baiwar Allah a saudiyya dan watansa 4 da koma wa can dan ƙaro ilimin addini kuma yana koyar da ƴan sanawiyyah (ss Islamic level).
**************** ***************
Unguwan me dabino
Tsaye take jikin window tana hange matan da suka yi layi a bakin rijiyan gidan suna ɗiban ruwa, mamaki take yi yadda ta ga mata duk cikin yanayin ƙazanta, ga kwata daga gefan rijiyan, tana so ta fita dan shiga kitchen ko tea ta haɗa, amma ta kasa fita koma wa bedroom ta yi tana mai jin kaman ta koma gidan su, kwance yake yana barci hankalinsa kwance, tsaki taja a fili tana kallon Sunusi mijinta, tana son sa tana ƙaunarsa amma sam ba ta san talaka ba ne sai jiya da aka kawota ace kamar ita Beauty amma ya za tayi haka Babban yaya ya so ai, zama ta yi gefansa ta ɗauki wayanta, take ta shiga contact ta kira Beasty. Bugu biyu ta ɗauka, gaisawa suka yi sannan suka hau wa juna jaje gashi Babban yaya ya umarci ko meke faruwa kar su kira kowa a gida. Beasty wacce ita yanzu Mubarak Skiddo ya ga ma ɗibo mata ruwa a ɗan wani fanfon maƙotan su.
"Ni beauty babban matsalan shine girki wallahi ban iya ba, ya zan yi?."
"Beasty kenan ai sam mun cu ci kanmu, muna kallo Twins suka dage da koyan girki, mu dai sai ce wa ai gidan Naira zamu gamu ai." taji hawaye ya gangara mata,
" Hakan nan za mu daure ko ya ya ne mu girki, na kira Kandy ita ma abun babu da ma." Daga haka suka katse kiran na su.
END.
[7/5, 14:27] 𝐏𝗿𝗲𝘁𝘁𝘆 𝐒𝐊..............: https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 ᴊᴀᴊɪʀᴛᴀᴛᴛᴜ ᴡʀɪᴛᴇʀ'ꜱ ᴀꜱꜱᴏᴄɪᴀɪᴏɴ (ᴊ.ᴡ.ᴀ)💪
ʀᴜʙᴜᴛᴜ ʙᴀɪᴡᴀ ᴄᴇ ᴅᴀɢᴀ ᴀʟʟᴀʜ, ᴊᴀᴊɪʀᴛᴀᴛᴛᴜ ɴᴇ ᴋᴀᴡᴀɪ ᴋᴀɴ ɪʏᴀ ᴀᴍғᴀɴɪ ᴅᴀ ᴡᴀɴɴᴀɴ ƙᴀꜱᴀɪᴛᴀᴄᴄɪʏᴀʀ ʙᴀɪᴡᴀ ꜱᴜ ꜱᴀᴜʏᴀ ᴛᴜɴᴀɴɪɴ ᴀʟ'ᴜᴍᴍᴀ ᴄɪᴋɪɴ ꜱᴀᴜƙɪ.✍️
𝐑𝐀𝐒𝐇 Ɓ𝐎𝐘𝐀𝐘𝐘𝐄𝐍 𝐌𝐀𝐒𝐇𝐄Ƙ𝐈
ĎĂĞĂ ĂĹƙĂĹĂМĨМ РŔĔŤŤŶ ŚĶ
✿◡‿◡✿ [Sakina Abdullahi] ✿◡‿◡✿
typing....
Page 41.
******************* ********************
Air Force Base
Sai 7:30am ta samu barchin ya bar idanunta, miƙewa ta yi dan ita abin da Hajiya Maa ta ce ma ta, da sauri ta zura hijab dinta ta nufi stairs, a Parlourn ta hangi Maa da Halima, gaishesu ta yi amma basu amsa ba, cikin kakkausar murya Maa ta ce
" Wato ke ƴar iska in ce 7am kifi to sai 7:30am, kika shanyani kamar wat
ta dabba."
"Hajiya Maa Please ki ya ƙuri, makara na yi." Ta furta dan a samu lafiya kuma ɗan jiya ta shigo gidan.
" Ki ɗaga mata ƙa fa yau dan Allah amarya ce da." ce wa M.D yana sauko wa daga stairs, ta ra sa gane me ke faruwa a gidan wai meyasa haka ne, jiya ta zo gidan amma ba ta shiga a sa'a ba sam. Hawaye ne ma su zafi suka gangaro mata ta share tanajin dokokin Maa gareta.
" Girki safe, rana da dare ke ce, mu ɗauke miki shara amma wanke-wanke ke ce, kowa da abin da yake son ci dan haka list ne abinci kowa ya kan ja mark ne da daddare akan abin da yake son ci da safe, a ƙalla 8am agama breakfast, 1pm na rana, sai 6:30pm na dare." Jita yi zuciyarta har ta tsinke akan wannan dokan, shikam M.d yana ji a ranshi babu daɗi amma sam babu daman ya ce ƙa la.
" Yarinya ta kin ta shi lafiya?." Da sauri ta ƙalla Dad wanda tin ba yau ba, ta san shi, a da can har gidan su yana zuwa, murmushin da ya yi mata ne ya sa ta ɗanji release. Zama ya yi yana kallon Maa ya haɗe rai.
"Amarya ce fa ya ka mata kibarta ta huta na wasu lokacin ko ba haka ba."
"To in ta huta na yau wa zak girka mana abinci dan tin jiya na sallami larai mai mana girki." ƙarara yya fahimci Maa ba ta ma ra ba da ita, shi kuwa M.d yana daga gefe kaman saƙaƙo ko tari baya yi.
" Shike nan zan shiga amma zan so na masu me ta ya ni dan ban iya girki ba, ba na yi a gida, karatu shine......."
"Ashe da aiki, ba ki iya girki ba?, Maa karna makara na wuce." Halima ta miƙe ta fice.
" Lallai ma, shiga kitchen din ganinan zuwa." Daga ta miƙe ta nufi in da take sa ran nan ne kitchen ta shiga, ita za ta iya rantsewa ko ɗauka abu ba ta yi a kitchen sai dai ta aika su Baby, ta so ace ta daure ta koya girki dan wata uku me koya musu girki ta zo ta yi, amma ba ta ta ɓa zuwa ba. A parlour kuwa Dad ne ya kalli Maa ya ce
" Ya yi wuri Maa ina laifin kibari ta yi 1 week, dan Allah kibari ta shaƙu damu na wani lokaci dan komai ya tafi yadda ya da ce."
" Shike nan kai M.d ja ta ku nufi part din ku, amma 1 week kawai na ba ta." har ranshi yaji daɗi dan haka ta sauri ya shiga kitchen, ganinta a tsaye tana zubar da kwalla yasa ya rungumota ta ba ya ya na ce wa.
" Muje ɗaki." hannunta ya ja har suka ratsa Maa da Dad suka shiga part dinsu.
" Me ke faruwa da ni ne?, Shin dama Maa ba ta sona ka aure ni? Meyasa na ke ganin tsana ƙarara acikin kwayan idanunta?." Ta jero mai tambayoyin ta na fizge hannunta, shi kanshi be san mai ze ce ba sai kawai ya zauna kan sopa ya kulle idanunsa.
******************** **********************
RHYENO ESTATE MILLINIUM CITY
Gida har yanzu a cike yake dan yau wasu duk za su wuce, Aliyu da Meerah ne na hango a gefan Main parlour suna magana ƙasa ƙasa, saboda kar su da me mutanan da ke kai da kawo.
" Please da naje zan ɗauko na dawo."
" A'a ki dai aika driver kawai, kin san kin shiga watan haihuwa, so kike ki haifamin Baby a mota, shekaran jiya kin fita haka jiya sannan yau ma, ni dai a'a