Showing 54001 words to 57000 words out of 93691 words

Chapter 19 - RASH ƁOYAYYEN MASHEƘI. COMPLETE HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

225

ta bi komai, ba laifi a bakin ta yi daɗi amma a ido sai haƙuri ɗan ta caɓe sosai.

" Queen kukan me kike yi ne.?"

"A ce ina Amarya amma ka fice tin safe sai yanzu, nai ta kiran number ka ba ta shiga, ga dare ya yi haka na zauna a tsakar gida sai na ga wata mage ta akan katanga shine na shigo....."

" Wayyo Queen ki ya ƙuri kin ji, ba zan sa ke da ɗe wa ba. Yanzu dai ga Power bank sai kidinga charge tin da nan ba'a wani samun huta." amsa ta yi tana mai godiya dan ita sam ba ta da raini kaman yayarta Hauwa'u, amma akwai bincike da kure mutum, a palourn ya zauna ita ma haka ta zauna ta na aje flask ɗaya, ya san ba ta iya girki ba amma be son kwasale ta ya ce.

" Amarya da girki wa ya sa ki? Fisabilillah."

" To tin da Ango ya fice ai dole na samar ma kaina abin da zan ci." a ƙoshe ya ke amma ya amsa taliyan wacce ke ta tiriri, a kallo ɗaya ya ga jakwalkwalon ta, murmushi ya yi har ze aji ya ta ce.

" Ban ga ne ba, ai na san ba ka so na shi yasa ba za ka ci abinci na ba." Sai ta sa kuka saurin ɗauka ya yi ya ɗaura kan table ya na jujjuya fork ɗin hannun sa, share hawayen ta yi ta zuna akan table din sannan ta amsa plate ɗin " Kulle idanun ka." Yba musu ya kulle sai ta kai abincin bakinsa ai kam a natse ya amsa yana taunawa a hankali, sai ya ji ya yi ɗanɗano a baki, ai kuwa a haka har ya cinye plate din, leather water ya sha.

"Wato girki queen a ido subuhanallah, amma a ba ki Alhamdulillah." Murmushi ta yi sai aka ka wo nepa, take unguwar aka hau Nepa! . sai suka kalla juna suka kwashe da dariya.

*********** ************
Zau ne su ke kowa rai a ɓa ce, dan tin da ya shigo Beauty ke neman maganan sa dan suyi dambe har ɗammara ta ci abin ta, wai ita akan me ye zai kawota gida kaman kejin dabbobi, yadda ya fita haka ya dawo ya ga gidan, sai ma tsakar gida da ya ci uban dau ɗa, shi kansa zai so ta yi hankali kafin nan da wata ukun, be bi ye mata ba ya yi kwanciyarsa, ita kam ko Power bank din daya ba ta anan ta ajiye ta na ta faman huci, chinchin din da su Baby su ka kawo mata shine ta ci ta ƙoshi abinta. ganin zaman ban za ta ke ya sa ya shiga ɗakin ya kwanta gefansa, har barci ya ɗauke ta.


END

[7/5, 14:19] 𝐏𝗿𝗲𝘁𝘁𝘆 𝐒𝐊..............: https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

💪 ᴊᴀᴊɪʀᴛᴀᴛᴛᴜ ᴡʀɪᴛᴇʀ'ꜱ ᴀꜱꜱᴏᴄɪᴀɪᴏɴ (ᴊ.ᴡ.ᴀ)💪
ʀᴜʙᴜᴛᴜ ʙᴀɪᴡᴀ ᴄᴇ ᴅᴀɢᴀ ᴀʟʟᴀʜ, ᴊᴀᴊɪʀᴛᴀᴛᴛᴜ ɴᴇ ᴋᴀᴡᴀɪ ᴋᴀɴ ɪʏᴀ ᴀᴍғᴀɴɪ ᴅᴀ ᴡᴀɴɴᴀɴ ƙᴀꜱᴀɪᴛᴀᴄᴄɪʏᴀʀ ʙᴀɪᴡᴀ ꜱᴜ ꜱᴀᴜʏᴀ ᴛᴜɴᴀɴɪɴ ᴀʟ'ᴜᴍᴍᴀ ᴄɪᴋɪɴ ꜱᴀᴜƙɪ.✍️

𝐑𝐀𝐒𝐇 Ɓ𝐎𝐘𝐀𝐘𝐘𝐄𝐍 𝐌𝐀𝐒𝐇𝐄Ƙ𝐈

ĎĂĞĂ ĂĹƙĂĹĂМĨМ РŔĔŤŤŶ ŚĶ

✿◡‿◡✿ [Sakina Abdullahi] ✿◡‿◡✿

typing....




Page 45.

After eight days

***************** *****************

ROYAL HOSPITAL WHITECHAPEL, RD. LONDON E1, 1FR, UK.


______ "Doctor A.A, you can go now. Everything about your discharge has been completed." Wani bature ya faɗa yana miƙa ma AA file, amsa ya yi ya mai godiya sannan ya kalla ƙofan toilet din da yaji alaman buɗewa, a hankali ta futo daga ciki tana goge fuskanta da alaman wankewa ta yi, kallon kallo suke yi da juna sai kuma ta sakar mai murmushi ta ke yaji hankalin shi ya kwanta, za ma ta yi gefan gadon ta na ce wa.

" Na shirya za mu iya wuce wa." yaune karo na uku da ya ji muryanta mai daɗi, kallonta take yi yadda y aga duk ta rame saboda watannin data yi cikin doguwar suma, a ƙalla wata 8 da sati biyu kenan, kuma Alhamdulillah ta dawo nomal sai dai komai na brain dinta ya goge, fita suka yi cikin natsuwa suka shiga hotel din nan dan dama ya kwashe komai na su ya mai da, Room F13. suka shiga, za ma ta yi a kan gado tana bin ko ina na bedroom din da kallo dan komai sabo ne a idanunta, hatta fararen fatan da suke yawo a ko ina na garin.

" Ba ra na sa mo mana abinci" kai kawai ta ɗaga mai ya fice, tafiya yake yi cikin farin ciki mara misaltawa ya rasa da me zai kira da wannan al'amarin, tina abin da doctor Alex ya ce mai ya yi 'Idan har kana so ta tina komai na rayuwarta ta baya dole ta dinga ganin manya manyan abubuwan da suka same ta na rayuwanta na ba ya, idan tana yawan gani komai za ta tina kaman mahaifarta, ko wani kalma da ta sa ba faɗa da ba ta labaran rayuwata da dai sauran su.'

"Ina har abada ba zan bari ta tina ita wace ce ba." ya furta a fili yana shiga restaurant din hotel din.

Kallon kanta take yi a mirro, budurwa doguwar kyakkyawa fara ƙal, mai zubin surar jiki dai dai wadaita. ji yake kaman ba ita ba, an ce mata komai na kanta ya goge sai ɗan abin da ba'a rasiaba, yanzu an ce brain dinta ta koma na yara dan empty take, sai wanda ta fara gani wai shine mijinta wanda ta ji ana ce mai Doctor AA. shigowan shi ya sa ta kai idanunta kansa, ya na da kyau fiye da misali, dogo wanda ya fita tsayi, gashi kaman zubin ƴan ƙasar nan, ga wannan baƙin gashin na sa sai shining ya ke, za ma ya yi yana miƙa mata abinci da yake yunwa take ji, amsa ta yi, sandwich ne ji ta yi ɗanɗano be ma ta ba amma haka ta ci dan yunwa sosai ta ke ji.

*"Nigeria,"* ya amsa yana ɗago kai daga kallon screen ɗin wayarsa.

*"Ni ma ina da 'yan uwa a can?"*

*"A'a, ke ba ki da kowa sai ni."*

*"Toh, I want to learn the language everyone here is speaking, ni ban iya sosai ba"*

*"Just get better first, I’ll enroll you in school soon."*

*"What is school?"*

*"It’s a place where you’ll learn how to read and write."*

*"Oh, so what did you say my name is?"*

*"Airah."

*" Meaning?."

" Mai daraja ko wacce take da haske mai kyau."

*"Okh and you, what’s your real name?"*

*"A.A."*

*"A.A? I don’t understand." Ya sauke numfashi, yana jin gajiya da tambayoyinta, sai ya ce:

*"Abdullahi Anas. That’s enough questions for today, okay? We’ll continue tomorrow." Daga kai ta yi tana bitan duk abin da tattauna yanzu.


**************** ********************

Air Force Base

Tin asuba ta fita zuwa kitchen sai yanzu 10am ta kammala komai shine ta shiga dan ta huta, kwanciya ta yi dan jikinta duk ya yi tsami, babu laifi zuwa yanzu har ta fara sabawa, wahala sha take kaman me, kuma ba ta da ikon mu sa umarnin kowa a gidan, rayuwa take kaman ƴan aiki, dan har gyaran gidan ita ce, a da Dad ta sha yana son ta ne amma zuwa yanzu ta fahimci shima ba ya ƙaunarta, gashi M.d ba ya iya komai akan haka sai dai ya yi ta ba ta haƙuri kawai. Har zaman gidan ya ishe ta amma a duk lokacin da wasu suka zo gidan sai Maa ta yi ta nuna ma ta ƙaunarta, har ta kwammaci rayuwa irin ta su Kandy na talauci akan wannan rayuwan da take yi, dan har ɗa rama ta yi shuru ta yi tana ta wasiƙan jaki sai taji an banko ƙofar parlour na ta, ta san Maa ce dan haka da ƙyar ta miƙe ta fita, a parlour ta samet a tana haɗe fuskan kaman hadari, tsugunnawa ta yi ta ce.

" Maa ga ni, me kike buƙata?." Kaman ba za ta ce komai ba sai ta ce.

" Na ji ban sha'awan Rice and beans ne, ina son ɗan wake kaɗan sai custard da akara."

" Ba ra na watsa ruwa sai na....."

" Yunwa na na ke ji, dalla tashi." Ta ƙarasa cikin tsawa sai ga hawaye a idon Fancy ya gangaro, fita ta yi ta nufi kitchen tana shiga ta share hawayen tare da yin shu'umin murmushi ta na ce wa.

" Wallahu kun gama mora ta daga yau sai dai ni na more ku, sannan zanga idan za ki iya cin abincin na wa." cikin sauri ta yi komai dama ba ta iyaba gashi ba ta yi niyya ba, tana gamawa ta kai daining sannan ta sanarma Maa, da yake yunwa take ji da gaske sai ta je ta zauna, sannan ta kalli komai, custard din yellow ne zar alaman be ji ruwan zafi ba kaman ƙullu ha ka yake duk da ta sanya milk amma be can za colour, akara din kuwa waken ko niƙuwa a blander be yi ba ya wani iri hakan nan, sai shi dan wanke wanda shi nomal ne amma ya yi mugun tauri, shuru ta yi ta rasa abin ce wa, wayanta ne ya fara ringing tana dubawa ta na new number WhatsApp voice call ne, accepting ta yi ta kai kunne ta, jin muryan auntan ta wanda tin da ya tafi be kira ba, a maimakon su gaisa ta haushi da faɗa, miƙewa ta yi ta dhige room din ta. Ganin haka Fancy ta wuce na ta ɗakin tana ai yana da Maa ta ce wani abu ta sun kwashi ƴan kallo. tina wayan da suka yi Babban yaya ta yi.
(Kuka ta ke yi, ta faɗa mai komai, abin da ya ce ma ta shine ya faranta mata sosai * Fatima kar ki za ma shashasha ma na, ke fa mace ce na yadda da tarbiyyan da muka ba ki, ke kanki za ki iya gyara gidan auran ki, ki natsu za ki samu mafita*. A cikin kalaman sa ta ɗauki haske.



***** "Ban ga ne ba? ba za ka dawo ba ka ce?." Faɗin Maa ta na ɗan hu ci,

" A'a zan dawo amma 1 week zan yi domin aiki ya main ya wa."

" Ina yawan fa ɗa ma ka, da ka dawo nan ka fara aiki, menene amfanin asibitin ka, ga ma na ƙawata Maman Salma in baka son na ka."

" No Maa kawai kibar maganan. Next week zan zo du ba ku."

" Toh naji ya maganar Salma?." tana fatan ya ce ya amince sai dai ya ce.

" Maa kibar maganan salma sam yarinyar ba ta min ba."

" Kamar ya Autaa....." Ƙit ya kashe wayan, ta bi kiran amma offline, tsaki ta ja tana jin ta ƙoshi ma ga ba ɗaya dan ba za ta iya sa komai a bakin ta ba.
END.
[7/5, 14:19] 𝐏𝗿𝗲𝘁𝘁𝘆 𝐒𝐊..............: https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

💪 ᴊᴀᴊɪʀᴛᴀᴛᴛᴜ ᴡʀɪᴛᴇʀ'ꜱ ᴀꜱꜱᴏᴄɪᴀɪᴏɴ (ᴊ.ᴡ.ᴀ)💪
ʀᴜʙᴜᴛᴜ ʙᴀɪᴡᴀ ᴄᴇ ᴅᴀɢᴀ ᴀʟʟᴀʜ, ᴊᴀᴊɪʀᴛᴀᴛᴛᴜ ɴᴇ ᴋᴀᴡᴀɪ ᴋᴀɴ ɪʏᴀ ᴀᴍғᴀɴɪ ᴅᴀ ᴡᴀɴɴᴀɴ ƙᴀꜱᴀɪᴛᴀᴄᴄɪʏᴀʀ ʙᴀɪᴡᴀ ꜱᴜ ꜱᴀᴜʏᴀ ᴛᴜɴᴀɴɪɴ ᴀʟ'ᴜᴍᴍᴀ ᴄɪᴋɪɴ ꜱᴀᴜƙɪ.✍️

𝐑𝐀𝐒𝐇 Ɓ𝐎𝐘𝐀𝐘𝐘𝐄𝐍 𝐌𝐀𝐒𝐇𝐄Ƙ𝐈

ĎĂĞĂ ĂĹƙĂĹĂМĨМ РŔĔŤŤŶ ŚĶ

✿◡‿◡✿ [Sakina Abdullahi] ✿◡‿◡✿

typing....




Page 46.

******************** ********************

Malali

Baban gida ne mai kyau dai dai, mota ce ta yi parking ta ke wata budurwa ta bayyana, ba duguwa ba ce can amma ba laifi tana da tsayi, skin din ta me duhu ne amma saboda shan gyara da hutu sai glowing yake yi, wando crazy tasa sai riga ƙarami me dogon hannu, ga uban attach wanda ya zubo a kafaɗarta, a kallo ɗaya za ka sha ba musulmai ba ce sai dai in kaji an kira ta dq SALMA. shiga gidan na su ta yi ta na aje jakkanta kan kujera tana cire hill shoes din ta, za ma ta yi kan kujera ta na latsa wayanta sannan ta kai kunne.

"Jubby yaushe za ki dawo?." Ana ba ta amsa a cikin wayan ta katse tana ajiye wayan, sai ga ƴan mata biyu sun nufota suna mata barka da zuwa.

"Aunty Salma me kuke buƙata.?" Duk da wacce ta ce ma Aunty ta girma salman sai ta ce

" Ku je ban buƙatan komai a yanzu
" Daga haka suka bar gurin cikin sauri sauri. tsaki ta ja tana nufa party din ta. tana shiga ta ba je kan makeken bed din ta ta hau bancin asara dan tin 5pm sai 9pm ta tashi, wanka ta yi sannan ta sanya kayan barci fitowa ta yi tana kallon Hubby wacce ta je zaune ta ja duba file.

" Hubby kin dawo?."

" Eh Salma tin ɗa zu,na leƙaki kina barci ai."

" Okh Hubby, Dady ya shigo kuwa?." Wanda aka kira da Hubby ta ɗago fafaren idanunta wanda suke cikin farin glass, kallonta tilon ƴarta ta yi wanda ita ce komai na ta ta ce.

" Ya dawo amma ya ɗan fita ne."

" Hubby ina son wasu kuɗaɗe Please." Ta haɗa hannayenta na ba roƙan Hubby din, shuru ta yi tana mamakin kashe kuɗin Salam ko 1 week ba ta yi da tura mata 3 hundred thousand ba, ta rasa me ke kanta kwana biyun nan.

" Me kika yi da kuɗin da na tura miki five days back?."

" Hubby kawai in zan samu toh in babu na kira Dady na.'

" Ba zan b ada ba." Tafada cikin haɗe fuska dan sam ba ta son yadda ƴar ta ta ke mata magana,

" Ƴa ta na wa kike buƙata?." Da sauri ta kalli Dady wanda shugowansa kenan, da sauri ta nufesa kaman wata yarinya ta rungume, cikin ƙauna ta ce.

" 100k ne fa kawai Dady."

" Don't worry my only one daughter."

" Sannu da zuwa Abu-salma."

" Yauwa Ummu-salma." haka suke kiran junan su har wasu ma kance haka.

" Me yasa kake ƙara san garta Salma ne?."

" Kamar ya ɗan ta tambaya kuɗi, ni fa gaba ɗaya dukiya ta ƴa ta ce Salma Nura Askira."

" Na sa ni amma kashe kuɗin ya yi yawa." ita dai Salma shuru kawai ta yi dan in dai kanta ne sun sa b jayayya.

" Ki barta ta huta da kuɗin Baban ta, ban san ki na shiga abin da babu ruwan ki." System da files din ta, ta ɗauka ta wuce ɗakin ta a fusa ce.

"Dady ban san kuna samun misunderstanding a tsakanin ku."

" Hmmmm za ta sauka ai, oya check your phone." wayarta ƙiran iPhone 16 ta du ba, da sauri ta duba ganin 500k ya sa mata, fa sa ihun daɗi ta yi, tana rungumesa sannan ta shige part dinta da sauri, tana shiga ta ta kira ƴan team dinsu, ta sanar da su ta samu kuɗin. Daga haka ta yi kwanciyarta cikin nishaɗi.


**** "Ban son kina shiga rayuwarta, ke doctor ce, ni ɗan siyasa kuma ɗan kasuwa duk dukiyan mu ta Salma ce kawai,ki yi ƙoƙarin faranta mata."

" Sam ka kasa fahimta ta shin ka san yanzu ƴan mata da samari wanda suke samun kuɗi shaye-shaye suke yi a ɓoye, sai ya ci yaro sai iyayen su ke sa ni, kafin ka ce wani abu ƴan hanji sun sa mu matsala ko wani abu haka."

" Mun san ƴar mu ai." Daga haka ya shiga toilet ɗauke da towel, hawaye ne ma su zafi suka zu bo mata sannan tana ta furta 'Astagfirullah' a cikin ranta.


************** ***************
KK GRA

" Hajiya yau za muga ko da gaske kike yi akan za ki banban ce Hassana da Husaini." faɗin Husain (Yunus),

" Ha ba na gane ku balle ma su." Take suka fito Hasty da Husty cikin shigan Abaya Black sunyi rolling da vail kaman hijab, su kansu Twins din sai dai suka ce ma sha Allah ganin yadda suka yi matuƙar kyau. dayake kullum sai Hajiya ta ce ai tana gane su. Abin da ko su Yunus da gyar suka fara banbance su.

" Wannan ita ce Husaina sai ga Hassana." Ta nuna su, sai suka yi dariya, da ya ke muryan su da ɗan banbanci ita Husty ta na magana da slow sannan magana ɗaya biyu sai ta yi english, amma Hasty ba ta cika yi ba sai in ta je school ko suna wani hira haka, Husty ta ce

" Wow Hajiya, ya kika ga ne cikin sauƙi ha ka?."

" Ha ba aiku yara ne abu biyu na rige kuma da shi na ke ga ne ku."

"Explain more..." a tare Yusuf da Yusuf suka faɗa hakan sai Hajiya ta ce.


" Yadda kuke suka haka suke, Hassan ko ka yi murmushi ba ya amsan fuskanka haka Hassana take, fuskan ku be da fara'a me yawa, kuku ma yana amsan na ku fuskan wato murmushi."

" Kaji baiwa malam...." Yunus ya faɗa fa sigan wasa sai Hasty ta ce.

" Ba komai kwanda mu nuna mu manya ne a ko ina " Sai suka yi dariya sannan Husaina ta ce.

" To Hajiya sai kuma ne ne kike me ne.?"

" Uhmm, launin ku ya ɗan banbanta sannan giranku ma haka, shike nan." Hajiya ta kai nan tana kai colanut bakin ta. Zama suka yi duk kansu su na ta hira da cin abinci kwanin burgewa. Hajiya fatanta Allah ya basu ƴan bibbiyu su ma, dan har ranta take son Hassana da Hussaina saboda sun ba ta respect kaman mahaifiyar su.

END


[7/7, 18:34] 𝐏𝗿𝗲𝘁𝘁𝘆 𝐒𝐊..............: https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

💪 ᴊᴀᴊɪʀᴛᴀᴛᴛᴜ ᴡʀɪᴛᴇʀ'ꜱ ᴀꜱꜱᴏᴄɪᴀɪᴏɴ (ᴊ.ᴡ.ᴀ)💪
ʀᴜʙᴜᴛᴜ ʙᴀɪᴡᴀ ᴄᴇ ᴅᴀɢᴀ ᴀʟʟᴀʜ, ᴊᴀᴊɪʀᴛᴀᴛᴛᴜ ɴᴇ ᴋᴀᴡᴀɪ ᴋᴀɴ ɪʏᴀ ᴀᴍғᴀɴɪ ᴅᴀ ᴡᴀɴɴᴀɴ ƙᴀꜱᴀɪᴛᴀᴄᴄɪʏᴀʀ ʙᴀɪᴡᴀ ꜱᴜ ꜱᴀᴜʏᴀ ᴛᴜɴᴀɴɪɴ ᴀʟ'ᴜᴍᴍᴀ ᴄɪᴋɪɴ ꜱᴀᴜƙɪ.✍️

𝐑𝐀𝐒𝐇 Ɓ𝐎𝐘𝐀𝐘𝐘𝐄𝐍 𝐌𝐀𝐒𝐇𝐄Ƙ𝐈

ĎĂĞĂ ĂĹƙĂĹĂМĨМ РŔĔŤŤŶ ŚĶ

✿◡‿◡✿ [Sakina Abdullahi] ✿◡‿◡✿

typing....




Page 47.

***************** *******************

"My Pretty SK, yanzu kin ga ki na daga ɗakinki za ki dinga komai da ya dan ganci binciken." Zaki ya faɗa yana kunna socket din da zai ba dukka na'urorin gurin huta, Sk da ke ɗauke da wani Flash ta jona ta na ce wa.

" Haka ne, so now I need ......" Ta katse magana saboda ganin wani paper me ɗauke da kalmomi hudu na babban maƙiyin ta wanda take ne ma ruwa a jallo, dan shi ne sanadin rasa ƴan uwan ta 'Rash' shine ta rubuta ta na ta har haɗa sunaye ko zai fito da asalin sunan wannan mugun amma ta ka sa.

"Pretty zuwa yamma na ke son ki haɗa komai da komai a kan list ɗin." Ɗaga kai kawai ta yi ta na ganin ai aikin ko 1hours ba za ta ɗauka ta na yi ba, tare suka kammala haɗa komai, anan ɗakin yana aiki tana feeding na sa breakfast, miƙewa ya yi ta mai rakiya har bakin get, da yake motan shi na Abuja ya tsara nan da sati ɗaya za

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login