Showing 87001 words to 90000 words out of 93691 words
na ɗan lokaci, ba komai ne ya haska a kanta ba sai abu biyu, imagine yadda ta ya sadaukar da komai na shi a kanta, be sonta ba amma ya nemo mata lafiya, sannan rayuwar su ce ta baya ta haske a cikin kanta, rasa abinyi ya sa ta rungume sa ta na ce wa.
"Ya zanyi? Ji nake Ya Umar kawai na ke so, faɗa min yadda zanyi...."
"Ya isa, ki natsu da kyau kinji, ba zan yadda ni kaina na cuce ki ba, amma ki sani kina ɗauke da ciki na, ki kula bara na kira miki shi." Be bari ta ce komai ba ya fice, ji tai jikinta ya mutu, haka dai ta jaa ƙafarta ta zauna akan kujera sannan ta faɗa kanta da hannu ɗaya, ɗaya kuma ta sha cikinta.
Tare ta suka shigo, bayan sun zauna, sai ta ɗago ta kalle su, Sakeenat da Zaki, wanda sun yi matukar match.
"Ƴar uwa, matso kusa." Take ta matsa kusa da ita, kallon juna suke yi kaman yau suka fara haɗuwa.
"Kallon kai na nake yi, hmmmm Allah na gode ma, shin za ki iya faɗa min wannan bawan Allah yana kula min da ke yadda ya kamata?." Sunyi mamakin jin abin da ta faɗa dan baka suka yi tsammani ba sam. hawaye ne suka gangaro a fuskan Sakeenat dan sai ta ji wani iri, ɗaga kai ta yi.
"Faɗa min dai, idan akwai abin da ya ke miki tin yanzu na sa ni."
"Babu." ta faɗa sai ta miƙe tare da fice wa da sauri ta na kuka. Ko da ƴan Parlour suka haka sai suka ce kar kowa yaje, amma zuciyar A.A har ta rayomai ce wa 'Airah ta sa Umar ya saki ƴar uwarta ne'.
________ sun dau lokacin sai ya kalle ta ya ce.
" Bayan lokaci mai tsayi kin bayyana, Alhamdulillah, Ramlat ki ya femin wallahi ban yaudare ki...."
"Kar ka damu Ya Umar, wallahi ya wuce, ina ji a raina haka Allah ya so, ba mu isa mu sauya ƙaddan Allah ba, ina so ka rike ƙanwata da kyau kaji."
"Hmmm insha Allah, kin ya femin kenan?."
"Ba komai, ya kamata na ci girma akan ka."
" Ta ce ita ce babba ke ma haka to waye ni kam."
"Haka ko a ido ai ansan ni ce. Ya Umar."
"Na'am ka najin wani abu a ranka ga ne da ni?." Sai da sauka a in da ya ke sannan ya matsa kusa da ita amma akwai ta zara a tsakanin su ya ce.
" Eh, na kasa fassara yanayin."
"Nima haka ne amma mu sa a ranmu, ƴan uwanta ka ce kawai, harga Allah na haƙura domin a yanzu Doctor ke faɗamin ina da juna biyu, rabo kenan mu ƙaddara rabo ne duk ya kawo haka."
"Insha Allah........" Kafin ya kuma magana sai ga A.A dan ya kasa haƙuri, sannan ya ji hiran su na ƙarshe. yana shigowa ya kalla Umar ya ce.
"Ɗan Uwan ka ta yani neman yafiyarta kaji." Murmushi mai ciwo ya yi dan harga Allah sai ya ji kaman kishi ya ke yi amma ya danne komai ya ce.
"Kar ka damu, ƙanwata mai yawan yafiya ce, ta yafe ma amma kamin alƙawarin kula da ita kaji."
"Insha Allah, Zan kula da ita." Rungume juna suka yi, Zaki ya bar ɗakin cikin ɗan ɗauriya, A.A ya kalla Airah ya ce.
"Airah ki....."
"Monceur dai." Ta faɗa ta na murmushi, sai ya riƙe hannunta sanann ta kuma ce wa.
"Da gaske yanzu anan akwai baby." Ta nuna cikin ta sai ya ce.
"Eh, za ki bini muje gidan mu." Sai ta ɗaga mai kai. Tare suka fita suka tadda kowa yadda suke.
" Fatan kun sulhunta kan ku." Abbuu ya faɗa sai Airah ta ɗaga masu kai. Komai murna ya shiga yi don ba son ace an yi saki. A gidan suka wuni sai gurin yamma suka wuce dan sai da suka je gidan Maman Rabi, suma aka basu labari, harda kuka Maman Rabi tayi sannan suka rabu nan ma A.A ya ba su kuɗi sosai.
END.
Page 71.
**************** **************
_________ Baban labarin da ke trending a yau shine : Rash ya dawo, da sabon salo dan ya bayya kuma ya umarci duk ɗan Nigeria mai ƙofari da ya turo saƙo a wata number nan take za'a bi mai haƙƙi.. kowa labaran ya ke duba wa aka waya. Beauty da itama ke zaune a gefan Beasty ta ce.
"Beasty yanzu wai duk kisan nan ashe Rash taimakon ƙasa ya ke. amma idan jami'ai suka kama shi fa? Kin san halin ƙasar nan."
"Hmmm ai yanzu asirin shuwagan nin mu ya gama tonuwa kodan haka za su ƙulla mai sharri sosai."
"Allah dai ya biya shi, amma yana cikin matsala tin da naji ance anƙaro jami'ai akan case ɗin, kuma President ya zauna da Governor's akan haka." Kafin Bauty ta ce wani abu sai Kandy ta shigo dan ita yanzu ta dawo daga gurin aiki.
"Sannu kin shawo hanya fa."
"Kedai bari Beauty, kin san yau mun sha wiya kuwa, rahota aka ce mu nemo akan Rash, yanzu haka zan kammala abin yi ne, na zauna dan duba wasu abu."
"Wai sannunki, ashe yanzu Rash mutumin kirki ne? Imagine ashe taimakon mu ya ke yi."
"Kedai bari Beasty, sai ma kinga channel ɗin mu yau, rahoto ne kowa da na shi."
"Ina Zubee ta kawo miki drink ki ɗan sha. Zubee, Zubee." Sai ga Zubee ta fito da sauri.
"Aunty Beasty ga ni."
"Kawo ma Kandy abu mai sanyi." Take ta nufi kitchen sannan ta kawo mata pop cola da glass cup, sai ta amsa ta na cewa.
" Ya school fatan karatun ba bu wiya." Sai Zubee ta zauna ta na ce wa.
"Alhamdulillah gaskiya, makaranta ya yi, sai dai Aunties akwai dokiki next week za mu yi matriculation."
" Dan Allah ki maida hankali, su kansu Uncle's ɗinki za su yi alfahari da haka."
"Insha Allah Aunty Beauty."
"Idan kuma akwai assignment da baki ga ne ba ki tun tuɓe ni."
"An gama Aunty Beasty."
************* ************
Bayan sati ɗaya
_______ a yau za ta koma school, shirya wa ta yi dan karta ɓata ma Fancy lokaci, tana gama shiri ta kalla A.A da ke bin ta da kallon ƙauna, yau ba zai fita da wuri ba dan haka yana kwance abin shi.
"Monceur zan ta fi." Ta faɗa ta na ɗaura niƙaf, sai ya ce.
"Please take care kinji." Ɗaga kai ta yi sannan ta fice tana kashe mai globe dan barci ya ke ji sosai. Bayan dawowanta wata sabuwar soyayya suke mai tsafta da kula da juna.
Tana saukowa ta tadda Maa ta shirin shiga kitchen, gaisheta ta yi ta amsa cikin kulawa sannan Airah ta ce.
" Maa ai Fatima ta kammala break fast."
"Masha Allah, Allah ya muku albarka." 'Ameen' sai Maa ta koma ɗaki, zama ta yi dan jiran Fancy.
* "Baby 8:00am zan shiga lecture fa, kuma Airah na jira na." Ta faɗa kaman tai kuka sai ya sake hannuta sannan ya ce.
"Ni ma ai 8:00am ina da class, kawai kallon kyakkyawar fuskar ki na ke yi."
"Baby please."
"Okh kiss me." Ba jira ta mai peck a kumatu sannan ta fice, shi kuma ya kalla agogo 7:38am, kuma text zai ma wasu, cikin sauri ya ɗau car key ya fito, motan su Fancy na fita shima ya bi bayan su.
_____ ko bayan da ya farka, wanka ya yi, sannan ya yi breakfast ɗin da ta aje mai, sai 10am ya bar gidan a lokacin har Dad ya fita Maa ce da wata Rashida mai aikin gida.
************* **************
________ Tin a daren jiya suka iso Saudiyya, a yau kuma Abbuu ya zaga da su cikin babban burinin Saudiyya, su kansu cikin nishaɗi suke, sai bayan la'asar suka koma gida, da a hostel za su zauna Abbuu ya ce sam, tare za su zauna dan suma koma wa za suyi, dan haka suka dawo jiya, abin da ya ma su Pazars daɗi ɗaya a in da Abbuu ke koyarwa anan makaranta su Baby aka sanya su.
************** *****************
Meerah da Sakeenat ne tsaye jikin ƙofar gidan Ramlat, ba su jima ba ta buɗe suka shiga, ɗauke ta ke da Husaini da ke faman kuka, Sakeenat ta amshe shi tana jijjiga shi.
"Ina Hassan hala ana sana'ar barcin koh." Meerah ta faɗa tana ajiye small Ammee kan sopa.
"Aikam tin ɗazu ya ke barci, gaskiya ki faɗa min menene sirrin, naga Ammee kullum fresh ta ke ƙarawa ne, ga ta ɓulɓul." Sai suka yi dariya sannan Sakeenat ta ce.
"Nima haka na tambaye ta, tubar kalla kullum sai za ma wata babban mace ta ke." Sai suka kwashe da dariya. Hira suka wuni suna sha abin su, sai suka wuce, Ramlat da duk ta shiga da muwa saboda Shuraim ya ƙi barin wanann aiki, jiya har faɗa suka yi akan haka dan haka ya fice yau da wuri, ganin kar mala'iku su tsine mata dan faɗa sukai sosi har da kuka ta yi. Wayarta ta ɗauka ta kira number sa, 3 miss call ta mai amma bai ɗauka ba kuma bai bi kiran ba.
_______Sakeenat tsaki ta ɗan ja, domin ta samu ta ɗauko number Babban yaya sannan ta haɗa da na Ramlat, so ta ke ta ji wayan da za suji and duk kiran da zaiyi za ta datsa dan ta ji. Jin Earphone ɗin kunnin ta na ƙara sai ta gyara zama ta na cin popcorn abin ta.
_______Ɗaukan kiran ta yi da sallama sai ya amsa.
"Baby uhmm uhmmmm ni uhmmmm."
_____ Jin hakan sai Sakeenat ta cire a kunnin ta aje a gefen ta. ( Hmmmm Sakeenat Allah ya shirya, ashe akwai sense Awwwnnn 💓, kunsan akwai mu da hankali wallahi.)
"Ina jinki." Ya furta sai ta kuma kwantar da murya ta ce.
"Ka de na so na koh?."
"Ni ban ce ba......"
"To me yasa kamin faɗa, ka sa ni kuka, nifa maraini ya ce." Sai ta fashe da kuka dan tina Ammee.
"In kin gama kukan ki kirani." Daga haka ya katsen kiran, jitai takaici ya mata sosai, sai ta shiga contact, number da ta sanya 'My Yaya for ever' shi ta kira nan ma ba'a ɗauka ba.
_______ Sakeenat ta duba kiran sai ta ga ya katse, saita abu ta yi sannan ta koma Parlour ta hau kallon T.V abinta.
________ kwanciya ta yi sai ga kiran ya shigo da farin ciki ta ɗauka ta na share hawayen ta.
" Yayana ƙara na kawo maka." Ta najin sai da ya saki ɗan murmushi sannan ya ce.
"Tom ƙanwata ina jinki."
"Dama mijina .....mi..ji...." Sai kuka, rarrshin ta ya shiga yi sosai, har ta yi shuru, sannan ya ce.
"Kimin bayani so that na baki sharawa kinji." Labarin faɗan su ta bashi tsaf ko abu ɗaya bata manta ba, bayan ya gama ji sai ya ce.
"Da fari ina mai baki haƙuri a madadin shi, bara na faɗa miki abu ɗaya, kinga mijinki mutum ne mai son taimako, ki natsu ki kalla komai da idanun basira, kyanshi ki dinga taimaka masa da shawarori akan haka, ƙasa gaba ɗaya yake taimako, ko bakyaso ne?"
"Ina so."
"To ki dinga mai addu'a dan Allah. Shike nan ko a kwai wani complain ɗin."
"Eh, dama ni ka kira shi ka ce mai karya kuma zuwa da bindiga gida, jiya na gani na tsorata sosai."
"Hmmm me ya kaiki ɗakin sa, bana ha na ki shiga ba."
"Eh yaya kawai dai na ɗan shiga ne."
"Karki sake kinji."
"Tom, Nagode a huta lafiya." Daga haka ta katse kiran. Take ya kuma kira da ɗauyan number, haka suke idan ya mata abu to ɗayan number ta ke kira ta faɗa mai komai har shawara ya ke bata sai kuma su koma dayan number.
"Ina jinki." Ya faɗa bayan ya daga, ita kanta sai da ta yi mamakin sa amma ta basar ta ce.
"Ka ya ƙuri."
"Naji, komai sai kin kai ƙara na koh?"
"Uhmmm to ai laifi ka yi ne."
"Kin kyauta, fatan kin ɗau shawaran Yayanki."
"Eh na ɗauka."
"Na lura kina ji da Yayanki fa."
"Sosai ma kuwa, baya min faɗa shi."
"Ohh shike sangartaki kenan."
"Yep, kuma ya ce in ka kuma ɓatamin rai za ku haɗu." Sai sukai dariya gaba ɗaya.
"Kin iya drama, aiki na ke yanzu zan kira zuwa anjima."
"Dan Allah Yayana na ke so ya zo yau."
"Lallai ma, bakya son Mijin ki kenan."
"Uhmmm ni dai ban ce ba. Bye." Ta faɗa tana kashe wayan sai ta kifa kanta akan pillow take Hassan ya farka dan haka ta miƙa ta ɗauke sa.
END.
Page 72.
**************** ****************
K.K G.R.A
__________ Sai yau na ta saƙon motan ya iso, itama irin na su ne, hawa tai suka ɗan ɗana, sai suka dawo gida, itama kamar Husty ta fara attending class.
"Hajiya na fi Hasty iya driving mai kyau."
"Wai Hussaina ai ni na kuma hawa motan ki sai wani ikon Allah, kaɗan ya rage ranan ki ƙarasa ni." Hajiya ta kaina ta na tina ranan da suka fita.
"Hajiya haka ake fama da ita, shi yasa nima ban yadda na hau motan ta, akwai ganganci."
"Haba Hasty ai da ne yanzu kuwa na canza, driving na ke cikin kulawa."
"Ai da kulawa shi yasa naga har motan ki ta fara ƙoƙewa and Babban yaya sai da ya miki magana."
"Uhmmmm nikam Bara na shiga ciki na kwanta." Ta miƙa ta shiga part ɗin ta.
"Husty manya." Hajiya ta faɗa tana mai da idonta ka T.V.
************** ************
_________ Meeting room ɗin ya dau shuru saboda jawabin da shugaban gayya ke yi wato His Excellency Haidar.
"Maganar gaskiya, manyan shuwaga bannin ba su da haɗin kai, na lura da haka, ya kamata ace an nemo Rash an saka mai da halacci amma mene wai an bada dokan gani da harbi akan sa, menene shawarorin akan haka dan yanzu zan shiga meeting da jami'an tsaro." Ya kai nan ya na kallo mutanen gurin sai wani ya ɗaga hannu sannan aka bashi permission sai ya ce.
"His Excellency ya kamata mubi komai a natse Rash mutum ne mai wayo da sunada, ba zai yadda a kamashi cikin sauƙin ba, kawai dai a yi yadda president ya zartar." Sai Da shima ya ce.
"A ganina mu yi yadda ka ce Sir, fatan sa'a."
************ ************
_______ " Sir a yau kawai mun samu saƙo sama da dubu 1, Nigeria sai a hankali." Adam ya faɗa yana kallon saƙon nin kowa da na sa matsalan.
"Mutum 20 a kullum ya isa, ki tashi ku koma gida dare na yi, nima yanzu zan wuce." A tare suka fito sannan suka hau mota suka bar wannan gidan da yanzu ya sha gyara fiye da daa.
________A haraban gidan ya tadda Aliyu da Zaki, bayan ya isa in da suke zaune shima ya zauna, ba su ɗau lokaci ba suka bar hiran tare da shigewa gidajen su.
Da sallama ya shiga part ɗin sa, ganin ba kowa a Parlour ya zauna, bai jima ba sai ga ta ta fito cikin dogon hijab, kusa da shi ta iso sannan ta ce.
"Rash ne ko Yayana?. " Sai da ya yi murmushi sannan ya ce.
"Rash na can, yanzu yayan ki ne, Shuraim." Sai ta saki murmushi mai sanyi tana zama daga gefan sa.
"Ina kewanki, ina yaran su ke?."
"Sun yi barci ti ni ai."
"Kifayaty ina son ki sosai da sosai."
"Nagode Yayana, nima ina son ka."
"Kin biya da tikwicin yara maza har biyu, kai Alhamdulillah kullum na tina wai ni ne mai yara sai naji wani sanyi na ratsani."
"Ba komai, fatan ba ka jin yunwa dan yau na ce kar a ko."
"Why?." Ya faɗa ya na kallon fuskanta mai wani sheƙi.
"Kawai dai, mu kwana da yunwa."
"A'a wallahi sam, ni a ƙoshe na ke muje kitchen ɗin." Kafin ta fara musu ya ɗauketa suka nufa kitchen ɗin.
________ Da Meerah har Small Ammee sun yi barci, gyara musu kwanciyar ya yi, sannan ya ɗauka system ya hau ɗan dube dube cikin dare, a yanzu ya samu sauƙin sosai dan wasu ayyukan Rash ke aikatawa.
_______ Neman ta ya shiga yi bayan ya fito wanka amma bai ganta ba, ko ina ya duba amma ba ta babu labarin ta, harya fara tinanin ko dai ta fita ne, sai ga ta ta fito a bayan labule, haɗe rai ya yi dan yasha ne manta sai ta saki murmushi ta ce
"Sorry Baby wasa ƴar ɓuya na ke so muyi." Kwafa ya yi ya koma room ɗin sa, sai ta bi bayan shi, tana shiga ko ya ɗamƙota, kunninta ya ɗan murɗa hatta saki ɗan ƙara.
"Auuchhh."
"Ban san kalan wasan nan."
"To ni na, uhmmm shike nan, ba zan kuma yi da kai ba." Ta faɗa ta na ruba baki, ya na sakin ta sai ta fice daga ɗakin, shareta ya yi ya gama shirya barci sannan ya dawo Parlour, T.V ya kunna dan a ƙoshe yake, ko da yana jin yunwa ba zai ci ba sai ta rarrashe shi, ita kuma sai an ce ta ke yin abu, ko haƙuri wani lokaci sai ya ce tukun ake bashi.
Tana kallon sa ta window yadda ya ke shashshan ƙamshi, dariya ma ya ba ta, dan haka ta miƙa da sauri kaman wacce aka kira, ba tatsa a Parlour ba ta nufi kitchen, dama kaman ta san haka ta ƙi yin girki so ta ke ta musu indomie ganin haka ta dafa guda ɗaya shafshaf, sannan ta soya egg, sai kaman ƙamshi abincin ke yi, fita Parlourn ta yi ta zauna a kujera da ke gefe guda ta fara ci a natse, saboda neman rigima ta miƙa ta ɗauki remote sannan ta mai da channel ɗin Zee world 'Barr Anu' shi ake yi, ƙara volume ta yi, shikam bai ce ko ƙala ba, ta ci gaba da cin indomie ta na kallo, guri ko da ba abin dariya bane sai ta yi. Zaki ya cika ya yi fam, sai ya miƙe tsaye, waje ya fita, take hutan nepan ta ɗauke, shuru ta yi duhu ga shi wayarta na ɗakin bincike, kuma ba ta ƙaunar duhu, da wiya kaga rauninta sai kun mungun sabo, rauninta ɗaya duhu sam ba ta juran zama a ciki.
______ bayan ya cire hutan gidan sai ya koma ciki amma ta ƙofan kitchen ya shiga, hangen ta ya yi zaune a in da ya barta ta na kiran sunan sa da cewa.
"My husband ka na ina, an ɗauke huta wayana ya na kitchen, please ka shigo ka aramin na ka hasken." Murmushi ya saki sannan ya tawo cikin sanɗa ba tare da ta ji sound ba, amma kafin ya aikata abin da ya yi niyya sai ya ji ta