Showing 30001 words to 33000 words out of 93691 words

Chapter 11 - RASH ƁOYAYYEN MASHEƘI. COMPLETE HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

210

ɗauke ta.


*********** *************

Ko da ya gama komai a cikin wannan ɗakin nasa na sirri, sannan ya fita zuwa gurin matarsa, daƙin ta ya shiga yasa mu ta na barci, ha wa gefan gadon ya yii ya na kallon Beauty face dinta me sheƙi da annuri, ya rasa me take ci da sha kwana biyun nan ta ƙara kyau da jiki, ga skin dinta sai glowing shi ma yake yi, ji yake kaman ya mai da ta cikinsa sa boda tsananin ƙauna, ya na sonta kuma ya na kishinta dan ko da wasa ba ta fita ba tare da ta kulle ko ina na jikinta, sannan ga muta ne biyu masu kai ta da jiranta a iya saninta amma a zahiri kuwa su goma ne har da mata wanda suke a aji ɗaya, haka duk ka ƙannansa kowa ya zuba mai secret guards like 5 people, haka su Pazars ma, sai Aliyu Haidar wanda na shi yafi na kowa sa bo da aikin daya ke yi dan wa'innan securitys din duk ya musanya ma su, harta matarsa Meerah be bar ta ba ita ma yasa mata dan akwai abubuwa da ta ke fuskanta a kan aiki. Ganin barcin nata ya yi nisa ya sauka a Wheelchair dinsa ya miƙa tsaye, in ya dawo RASH komai na sa sauyawa yake yi, freezer ya buɗe na ɗakinta ya dauka drink me sanyi ya koma kan sopa ya buɗe yana sha tare da buga wa brain dinsa lissafin wasu abubuwa, a nan gurin barcin ya ɗaukesa.


****************** ****************

Kwana biyun nan ba ta jin daɗin sosai hakan ya sa jiya taje asibiti dan a du ba ta, kwajin farko aka samu ta na da juna biyu, ta yi farinciki sosai ma ra misaltawa, sai dai me bayan Aliyu ya dawo da ta faɗa mai shi ma yaji daɗin fi ye da na ta sai dai a in da matsala take shine ya ce tin yanzu ta fara neman hutun gurin aiki dan sau biyu za ta dinga zuwa a week nan ga ba kuwa dole ta haƙura ma, abin da ya sa yau duk ta bi ta haɗe fuska, ta san baya cin taliya aikuwa shi ta da fa, mai da yaji kuwa, kallonta kawai yake yi yasan neman rigima take yi aikuwa ya ɗaure ya ci har da ce wa ya yi daɗi, ba haka ta so ba ta so ya yi complain ta hau masifa sai ta ga ya basar duk da tasan ƙarfin hali ya yi gurin ci, ta rasa me ya ka mata ta yi wanda shi ma za ta ɓa ta masa rai, bedroom dinta ta wuce ta yi kwanciyarta, shi kuwa sai da ya kai 12pm ya na kallo da ga bisa ni ya gyara kwanciya akan sopa sanyin A.C na ratsa shi, ko da cikin dare ta farka sai ta fito a can parlour ta hangesa sai ta koma ta ci gaba da barcinta, ko da gari ya waye bayan ta idar da salla ya higo dan su gaisa kawai ta haushi da faɗan ƙarya, faɗan da babu gaira babu dalili wai dan ya kwana a parlour.

"Wato barci kasha, ko damuwa da ni baka yi ba, hmmm ya yi kyau sosai, haka jiya ka gama cin abincin kabarmin kwaninka agurin na gode." Ta kainan tana cire hijab din jikinta, kallonta ya yi sai ya share yasan jira take yi ya kula ta su hau tuhuma dan shi be ma ta ɓa ɗauke kayan abinci ba idan ya ga ma ci sai dai ranan da shi ya dafa, sannan ta da sa da ce wa.

"Wato ina magana ka share ni, ni wai....." duka iya ƙarfin sa ya sa ya janyo ta, ta faɗo jikinsa ba tare da ta gama maganan ba.

"Ashhhh za ka karya ni, na san baka sona yanzu ai." nan ma be ce ko ƙalaba sai da ya ɗauki minti 10 a haka, sai ya kai ba kishi saitin kunnan sannan ya ce

"Gaba ɗaya week din nan ki na gida babu inda za ki....." ta yi saurin to she mai bakinsa tare da marairaice fuska ta na ce wa

"Uhmmmmm ni ban son na ɗauki hutu da wuri, nayi ma alƙawarin duk ranar da muka gama case din Rash zan ɗau hutu sai time to time zan dinga zuwa, amma be ka mata ka ce za ka hana ni zuwa ba."

"Na ji kinga sai kusa mu ku yi da wuri dan da yarona ya yara zama mutum ba zaki ɗaura mai pressure ba."

"Toh, amma ka taya ni da addu'a kawai duk da binciken ba'a samun ci gaba ko kaɗan, ga lokaci sai tafiya yake." da ga haka suka shiga wani hiran daban na su na masoya.

END
ĎĂĞĂ ĂĹƙĂĹĂМĨМ РŔĔŤŤŶ ŚĶ
[6/24, 17:41] Ameeratul Khairy❤️❤️: https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 ᴊᴀᴊɪʀᴛᴀᴛᴛᴜ ᴡʀɪᴛᴇʀ'ꜱ ᴀꜱꜱᴏᴄɪᴀɪᴏɴ (ᴊ.ᴡ.ᴀ)💪
ʀᴜʙᴜᴛᴜ ʙᴀɪᴡᴀ ᴄᴇ ᴅᴀɢᴀ ᴀʟʟᴀʜ, ᴊᴀᴊɪʀᴛᴀᴛᴛᴜ ɴᴇ ᴋᴀᴡᴀɪ ᴋᴀɴ ɪʏᴀ ᴀᴍғᴀɴɪ ᴅᴀ ᴡᴀɴɴᴀɴ ƙᴀꜱᴀɪᴛᴀᴄᴄɪʏᴀʀ ʙᴀɪᴡᴀ ꜱᴜ ꜱᴀᴜʏᴀ ᴛᴜɴᴀɴɪɴ ᴀʟ'ᴜᴍᴍᴀ ᴄɪᴋɪɴ ꜱᴀᴜƙɪ.✍️

𝐑𝐀𝐒𝐇 Ɓ𝐎𝐘𝐀𝐘𝐘𝐄𝐍 𝐌𝐀𝐒𝐇𝐄Ƙ𝐈
ĎĂĞĂ ĂĹƙĂĹĂМĨМ РŔĔŤŤŶ ŚĶ
✿◡‿◡✿ [Sakina Abdullahi] ✿◡‿◡✿

Page 22

**************** ************
kamar kullum in ya zo kwanciya sai sun yi waya da babynsa amma yau tin da zu yake kira ta ƙi ɗauka, ya san duk yaran can ne suka sa ta yi fushi, gashi gobe su Pazars za su je su kai sadaki da tsaida rana, ya so ƙananan baban shi su zo daga Abuja, amma Pazar Q ya ce ba sai sun zo ba, damuwa duk ya'ishe sa, hawa online ya yi da mamakinsa ya ganta a online, 'Slm' ya yi mata sai bayan 2mnt ta yi mai reply da "wslm." sai kawai ya kira ta voice call dan ba ta ɗaukan video call ba, haƙuri ya fara ba ta, sai ta nuna babu damuwa da haka suka dinga hiran yadda rayuwan su na aure ze tafi dan Ramlat ba ta ɗaukan abu da zafi balle ma ta sani Lion dinta yana son ta sosai

"Baby ki zaɓa a ina kike son mu zauna?, a nan familyn ƙanƙara tin da akwai part part dan haka Pazars suka cemin amma in kina so zamu iya neman wani gurin na, so can Abuja zamu koma amma babu dama da yake acan ɗin ina da gida gadon babanmu.' ai kaman ta na jira ta ce

"A nan dai yafi kodan ƙawata ka ga ni." amma a zuciyarta ta na cewa ko dan ta nuna ma su Khadija, ba a zaginta a zauna lafiya, gashi akwai ya da mugun riƙo, da haka suka yi sallama suka rabu bayan sun sa ƙauna sosai.


************** **************
A yau 9 wednesday\4\2025 misalin 11:33am, abin da ya faru ya hargiza muta ne da yawa domin yara ɗaliban ilimi, kuma zallan ƴan mata su talatin (30) a wannan babban makaranta nan wato EVANT INTERNATIONAL SCHOOL, wacce ke cikin hajar Kaduna, makaranta mai ji da kanta domin duk yaran masu hannu da shuni ne a ciki, tin jiya a ka kwashe su duk da ba'asan taƙa maiman lokacin da aka kwashe su ba, sannan iyayen yaran sun kai ƙara gurin jami'an ƴan sandq harta hukumar makarantar ta shiga alhini, abu mafi razanar wa shine a safiyar yau 11am sai ga video an saki na RASH kan cewa garkuwa ya yi da su kowa ya shirya kuɗin fanasa, gaba ɗaya muta ne cikin zullumi suke ballan tana wa'inda ba suga yaransu ba. harta shi wanda ke zaune yana kallo a T.V baya cikin tsaro in dai a wannan ƙasar ne, muta ne suna tsoron kar ƴan matan su shiga matsala domin duk kan babu wacce suka haura 20yrs, kuma abin mamakin shine kallaman da ake kira RASH ya faɗa kan biya kuɗin fansa." Matashin saurayin da ke cikin maginin TV ya gama kowo rahoto cikin alheri kuma ta je suka canza shirin zuwa wani abu, Shuraim da ke zaune ya na kallon tunani ya shiga yi mai zurfi dan sai da Kifaty ta na yi magana a karo na biyar shine ya dawo da shi cikin tunaninsa.

"In sha Allah a sirin RASH ya na gab da tonuwa, kwana biyu ya bar kisan shine ya koma satan yara mata, Allah ya sa babu abin da ze musu." Sai ga hawaye sharrrr ta mike ta nufi part din ta, be da katar da ita ba har ta shige, ya rasa meke mai daɗin be ma bi takan Wheelchair dinsa ba da ƙafafuwan sa ya nufa na sa ɗakin ta re da kira a waya bugu biyu aka ɗauka

"Ina son ganinku yanzu nan." Ya kashen wayan yana murɗa handle din ƙofan sannan ya kukkule ko ina tare da nufan wannan lungun, already sun iso dan jin labarin da ke yawa a media su kansu sun san akwai meeting na gaggawa. ya na shiga ya zauna ya na faɗin

"Kunga me ke faruwa ai, ina son na sa ke ganin wannan video din da a kace an saki." take Spider ya kunna flash tare da so ka wa a magic TV, sai hotan ya bayyana mutum ne sak me irin shigan da Shuraim yake yi yana zaune sai ya miƙe ya fara tafiya tare da yin alama da hannu sai ga yara mata su talatin, dukkansu suna sanye da Uniform iri ɗaya amma duk an rurrufe masu fuska, magana ya fara yi da irin muryansa sak

"Nasan kun san Ni wane ne, to ko wani mutum ɗaya a cikin yaran nan za su bani number ɗaya daga gidansu tanan ne zaku biya kuɗin fansa, nabarku lafiya da ga ni RASH."

Ƙet Videon ya ƙatse, gaba ɗayan su shuru suka yi suna mai tinanin waye wannan da ke neman sa kanshi a hatsari sosai, sau uku Shuraim ya kalla videon sai ya saki shu'umin murmushi ya na mai ce wa

"Ɗayan biyu ne ko dai plan ne jami'ai suka haɗa domin kamani kodai wani ne ya fito domin samu kuɗi da sunana."

"Boss yanzu yake so ayi, in kace zuwa gobe mu binciko sa zamu kawo makashi." Cewan Adamsi cikin haɗe fuska, sai Skiddo shima ya ce

"Haka ne Boss, aiki nan ko wani kalan hatsari ne mu masu shiga ne balle a kanka RASH kai ne gatan mu na duniya da Allah ya ɗaura maka."

"Ga duk kan alamu koma waye sunyi dubara da kuma sunyi ƙoƙarin dan harta muryata sun ɗauka sai dai ga dukkan alamu na ɗan fishi tsayi amma zamu samo shi, kubari muga iya gudunsa kawai." daga ha ka ya fice suma suka fita, ko da ya hau kan bed dinsa sai ya tina be ɗauko Wheelchair dinsa ba nan take ya ti na ɗazu da safe da suka tashi da ga barci

''''''' Muryan ta ne ya doki kunnansa ta na ce wa "Baby ya aka yi ka iya zuwa kan sopa ba tare da Wheelchair dinka ba?." Ko da ya watstsake sai ce mata ya yi. "Keken ai me tafiya da kanshi ne idai an danna to shine yake matsawa." Bata kuma ce wa komai ba kuma ta yadda 100%,'''''''''''

Amma be san me ze ce mata an jima ba, dan ba ya yana yin da ze iya fita yanzu, cikin sa'a barci ya ɗauke shi bayan ya kwanta.

END.
❤(。◕‿◕。)❤ [ᑭᖇᗴ𝙏𝙏𝙔 Տ𝙆] ❤(。◕‿◕。)❤

[6/25, 13:01] sknt6428: https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 ᴊᴀᴊɪʀᴛᴀᴛᴛᴜ ᴡʀɪᴛᴇʀ'ꜱ ᴀꜱꜱᴏᴄɪᴀɪᴏɴ (ᴊ.ᴡ.ᴀ)💪
ʀᴜʙᴜᴛᴜ ʙᴀɪᴡᴀ ᴄᴇ ᴅᴀɢᴀ ᴀʟʟᴀʜ, ᴊᴀᴊɪʀᴛᴀᴛᴛᴜ ɴᴇ ᴋᴀᴡᴀɪ ᴋᴀɴ ɪʏᴀ ᴀᴍғᴀɴɪ ᴅᴀ ᴡᴀɴɴᴀɴ ƙᴀꜱᴀɪᴛᴀᴄᴄɪʏᴀʀ ʙᴀɪᴡᴀ ꜱᴜ ꜱᴀᴜʏᴀ ᴛᴜɴᴀɴɪɴ ᴀʟ'ᴜᴍᴍᴀ ᴄɪᴋɪɴ ꜱᴀᴜƙɪ.✍️

𝐑𝐀𝐒𝐇 Ɓ𝐎𝐘𝐀𝐘𝐘𝐄𝐍 𝐌𝐀𝐒𝐇𝐄Ƙ𝐈
ĎĂĞĂ ĂĹƙĂĹĂМĨМ РŔĔŤŤŶ ŚĶ
✿◡‿◡✿ [Sakina Abdullahi] ✿◡‿◡✿


Page 23

*********************

Jami'ai duk hankalin su a tashe yake tun ganin me ke faruwa, an rarraba jami'a duk gidan da aka yi garkuwa da ƴarsu, gidaje 22 ne don wasu yara biyu ne a gida ɗaya suke, zuwa yanzu har an biya kuɗin fansan mutum 6 ta wani account a GT Bank sai dai be da suna, 1M ne a ka cazi ko wani yaro, harta GT bank su Zaki sunje amma basa'a domin ana sa kuɗin ake cire wa a take, sunata binciken POS din da ake cire kuɗin amma basa gani, hakan ya ƙara tabbatar musu da RASH mayen na'ura ne, sam ba su da sa'a a haka har sai da aka gama tura mai kuɗin duk ka dan RASH ya ce cikin 3h yake so a gama biya shi ya sa kowa ya samu ya biya, yanzu a nata jiran sakon yaran dan a tare suka ce zasu sake su, sun san jami'a na an kare amma idan Allah ya so taimakon mutum cikin ikonsa da buwayarsa ya na taimako. Misalin 12pm na dare, babban mota ta nufa cikin gari direct makarantan EVANT INTERNATIONAL SCHOOL suka nu fa sannan suka shiga dan sun sai ta komai da shigansu cikin baban makarantar wanda babu kowa a ciki, fitowa wasu muta ne biyu suka yi daga motan suna sanye da baƙaƙen wando da riga, ko ina nasu a rufe, haka suka nufa hanyan fita amma da takun farko na biyu na uku, suka ga an zagaye su tare da danjan bindigu ajijunsu dan haka suka ɗaga hannayen su sama ƙirjinsu na matsanancin bugu, polisawa su suka rarratso ta a ina da suka ɓoɓɓoye, Zaki ne a gaba har hamdala yake yi akan yau sun samu nasara cafke RASH cikin jin daɗi ya ba da umarnin banda harbi sannan ya matsa jikin babban motan sannan ya sa wasu suka buɗe take ya hangi mata duk suna sume...........



******************* ****************

Cikin barcinsa ya jiyo a na buga ƙofansa a haka ya miƙe ba tare da tinanin komai ba ya nufa ƙofan hannu ya sa ya cire gaba ɗaya lock din da ke jiki, sannan ya buɗe, ganin ta ya yi tsaye tare da Wheelchair dinsa, fuskansa a matuƙar haɗe take babu annuri kuma babu rahama, kallon-kallon suke yi dan ita suman tsaye ta yi ganin gurgun mijinta a tsaye da ƙafafunsa magana take son yi amma kalmomin sun maƙale a maƙoshinta baya-baya tafara yi cikin zafin nama yaruƙo hannunta aikuwa ya cafkota amma sai da ta suma, ɗaukan ta ya yi cak kaman baby ya nufa Parlour kwantar da ita ya yi kan kujera sannan ya ɗauko ruwa a fridge ya yayyafa mata cikin ikon Allah sai ta farka suna haɗa ido ta zabura tana miƙewa daga kwanciya ta na ce wa.

" Dama kana ta fiya ne?." ya ɗaga mata kai yana zama a gefanta, gaba ɗaya duk ta ruɗe zabura ta kuma yi tamiƙe dan nufan ɗakinta, yasa hannu ya mai da ta ta zauna juyowa ya yi suka fuskanci juna ya na ce wa.

"Ban san magana, and ban san tambaya." abin da ya ce kenan sannan ya miƙe ya nufi room dinsa da idanuwanta ta bisa ta na kallon yadda ya ke tafiya cikin natsuwa, a yau take ƙare mai kallon, yana shiga be jima ba ya fito ɗauke da magani, kallonsa take yi ko ƙyafta ido ba ta yi, gashi besan riga ba wannan faffaɗan ƙirjinsa na waje mai ɗauke da yalayalan baƙin gashin da suka kwanta.

"Wannan kallon fa, na mene ne?." Ya na furtawa ta ɗauke idonta ta na mai tinanin iri-iri a ranta, maganin ya ballan mata aikuwa ta amsa ta sha, zama ya yi ya na mai ce wa.

"Na yadda da ke, ni dama ainiyin ba masaki ba ne lau na ke, so na ke kiriƙemin wannan sirrin sannan na lura ki na da brain sosai ina son na baki wani aiki ne." Jita yi kaman mafarki take yi sai ta ce

"Pleasr ka ta dani da ga mafarkin da nake yi." Yadda leɓen nata suka matso sai yaji har zuciyarsa domin irin me pink lip din nan ce, ba ta an karaba sai ya haɗe ba bakinsu guri ɗaya ya hau kissing na ta cikin rashin sabo, a hanli ya za me bakinsa ya na ce wa.

"Bansan tambaya yanzu kin yadda a zahiri kike koh ?" dasauri ta ɗaga kanta tana mai taɓa bakinta danjin ko yananan. miƙewa ya yi ya koma ɗakin na sa ta bisa da ido kawai, can sai gashi ya fito da wani trolley a jewa ya yi ta re da ce ma ta

"Kule ƙofofin gidan nan." da sauri ta miƙe ta nufa ƙofan fita takukkule harda ƙafan da ze sa da ka da Main parlour, isowa in da ya ke ta yi, ya mata nuni da in da za ta zauna aikuwa ta zauna babu musu, buɗe jakkan ya yi ya fiddo na'urori kala-kala take ya haɗa wanda ya keso ita dai bin sa kawai ta ke da ido, ta ke wayansa ya yi Ringing janyowa ya yi daga gefan Pillow ya ga Adamsi, yana katsewa ya kira sai ya ɗaure, speaker ya sanya sai ya ajiye a gefan sa sai na cikin wayan ya fara magana.

"Boss abubuwa na ta ta'azzarafa, a halin yanzu 1million for each person." kaman Shuraim ba ze ce komai ba sai ya ce

"Karku da mu kubarsa zan haɗa mai tarko kawai kudaiyi sab gan gabanku kawai." ya na cewa haka ya katse kiran tare da kallon Ramlat wacce ke kallon shi ita ma, murmushi ya yi mata mai sanyi, ta mai da mai da yaƙe, operating system ya fara yi cikin kwarewa, sannan yace ta musu girki haka dai suka wuni yana aiki da na'ura ita kuma tana kallon yadda yake yi sai 7pm ya ɗauki wayansa tare da kiran wani number bugu biyu aka ɗauka.

" Zaki."

"Na'am Babban yaya."

"Kunna location na ka zan ha ɗaka da wani red light karkuyi komai sai idan sun fara tafiya sai ku bi su amma hakan ze sa su gane, nan da 1h zan kajini, before the time make sure get ready."

" Godiya mu ke Babban yaya.", ya katse kiran, Ramlat ya bawa wani abu ya ce ta yi ta matsa shi aiko shi ta ke ta yi, zuwa na 9pm ya kuma kiran Zaki.

"Ku nufa EVANT INTERNATIONAL SCHOOL, cikin shigan kayan gida, kuɓoye motocin ku, idan kunje sai ku sauya me gadin sannan kumai dubara dan ɗan team dinsu ne, idan kun shiga ku ɓoye har sai sun zo." Be jira me Zaki zai ce ba ya kashe wayan tare da kwanciya kan sopa sannan ya ce "Ya isa matsawan ki barshi haka." aiko ta tsaya dayin, miƙewa ta yi ta shiga ɗakinta ta rufe, lumshe idanuwansa ya yi dan ya gaji sosai da ƙar ya samu makama, ita

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login