Showing 72001 words to 75000 words out of 93691 words

Chapter 25 - RASH ƁOYAYYEN MASHEƘI. COMPLETE HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

220

kina da TV a part ɗinki, sai ki koma can. Masu gida sun dawo."

Fancy da takaicin abin da suka mata ɗazu ya dawo ƙal a ranta, kawai ta tsinka ma Halima mari har sau biyu. Hafsat yake tayo kanta. Nan fa suka hau fada sosai. Maa dai tana kallon ikon Allah. Sun jibga juna babu laifi, balle Hafsat – har bakinta ya fashe. Fancy kuwa duk ta ta sha yaƙushi dan Hafsat akwai farce masu tsayi.

Da yake window ɗin glass ne, ganin M.D ya a batanan gidan sai Fancy ta saki shu'umin murmushi. Kafin handle ɗin ƙofa ya yi ƙara, ta zube ƙasa tana kurma ihu:

"Don Allah ki yafeni, Maa ki ɗauki za ta kashe ni. Wayyo Allah!" Ta na kuka da ihu. Su dai ido suka zuba mata. Sannan suka lura da wanda ya shigo – M.D ne. Nan suka fahimci in da zancen ya dosa.

"Hafsat, kina hauka ne? Uban me ya sa ki dukan matata?" Ya furta cikin fushi, sannan ya ɗago Fancy daga ƙasan. Sai ya tsinka ma Hafsat mari ta ke ma ta buɗe baki tare da nufansa.

"Uwarka ce ta sanya ta! Akan wannan kake maran ƙanwata Muhammad? Kana hauka ne? Za ka bugata akan wannan yar iskar? Wai da me take taƙama ne? Ita ɗin wata tsiya ce.".

"Maa, babu ruwanki a ciki. Tunda kina kallo za ta kashe min mata kuma tana ɗauke da juna biyu, salan ta zubarmin."

Maa ta buɗe baki tana maimaita:"Juna biyu?." cikin sauri Muhammad ya ɗaga mata kai ɗan ƙara tabbatar da hakan.

"Wannan hayaniyan fa dan Allah, mutum shi ba zai huta ba wani lokaci in dai yana gidan nan."Suka ji saukar muryar A.A. Maa da su Halima suka yi mamakin ganin sa.

"Auta, yaushe ka dawo?" Maa ta faɗa tana kallon shalelen ɗanta cike da so da ƙauna.

Sai da ya iso gabanta sannan ya ce:"Maa, jiya na dawo. Na yi kewarki sosai." Ta riƙe hannunsa, suka zauna."Allah sarki. Ashe za ka dawo. ni kam har na cire rai, Yaya kake?"

"Lafiya, Maa."

"Shine ka kasa faɗa mana dawo wan ka? Uhmmm Sirikin ka Allah ya rasu." Ta kai nan maganar tana kallon Muhammad da fushi tare da dalla mai harara.

"Maa, na sani ai, Sun faɗa min."

"Shine ba ka zo ba?."

"Ai na yi masa addu'a."

"Ayya. To ai ko Doctor ka je, ka ma ta’aziyya. Sannan ka ga Salma. kar kaga yadda ta ko ma baiwar Allah duk ta sauya."

"No, Maa. Ni fa ki daina haɗa ni da Salma. ba zan aure ta ba." Take ta saki hannunsa, annurinta ya ɗauke.

"Ban gane ba. So kake ka ce ba za ka aure ta ba? Why?"

"Because I have a wife. I'm a married man."

Ba Maa kaɗai ba, har sauran na parlour jin zan cen suka yi daga sama. Hatta Dad da ke saukowa ya tsaya.

"Me? Ban gane ba. Ka yi aure da iznin wa?" Maa ta tambaya da faɗa.

"Eh, na yi aure, da iznin kaina."

"Enough!" Maa ta faɗa da ƙarfi. A.A ya juya, ya nufi stairs da sauri. Sun yi zaton ba zai dawo ba, sai gashi ya dawo da hanzari, wata kyakkyawa yarinya na biye da shi.

Fara ce ɗal, doguwa, tana da kyau sosai. Sanye take da doguwar riga ta material, tana kallo kamar baturiya, balarabiyya ko shuwa-arab.

"Baturiya ka aura?." Hafsat ta tambaya, amma bai ce komai ba.

Bayan sun gama sauka, A.A ya ce:"This is my Dad and my Mom, then my brother, his wife, and my sisters."

Ya nuna mata su duka. Sai ta saki murmushi, ta gaishe su:

"Good evening Dad, Good evening Mom and all together."

"A.A kana hauka ne? Wa ya ɗaura maka aure da kafira?"

"I'm Muslim. My name is Airah Abdullahi." Airah ta faɗa da mamakin yadda ba su san ta ba.

"Innalillahi. Abdullah ka cuce ni? me zan faɗama Doctor da Salma? Next Friday mai zuwa zan aurar da ita ko kana so ko ba so, yadda zaka yi da wannan kai ka sani."

"Hmmmm. Never! Ba zan auri wannan yarinyar ba, Kuma in baki sani ba, Maa, ki sani yanzu, Salma tana shaye-shaye. Salma tana bin maza. Salma na—" abin da ba ta taɗa yi masa ba shine yau ta mai, mari, Hannu ya ɗaura a gurin sannan ya ce:

"Na san haka zai faru. Ba zan zauna a cikin gidan nan ba. Wuce wa zan yi, zan bar muku gidan."

"Auta, kul! Koma ɗakin ka, ja matar ka ku tafi." Dad ya faɗa cikin fushi da tausayi. Hannun Airah ya ja, suka koma ɗakinsu.

"Ya nuna bai son Salma. To ki haƙura mana."

"Haba! Ai wannan cin fuska ne." Ta ja jakarta, ta nufi ɗakinta...

END.

𝐏𝗿𝗲𝘁𝘁𝘆 𝐒𝐊

Page 60.


**************** **************

___________ "Why? Why?" Zaki ya ja da baya daga in da taron jama’a ya cika wajen. Zuciyarsa cike da rudani, ya buɗe motarsa ya shiga amma ya kasa tuka ta. Ya dafe kansa sannan ya zaro wayarsa ya kira Sk, Pretty a ɗauka bayan bugun biyu.

" Wai abin da nake ganin a live, is true?."

" Eh Pretty, imagine Rash ya kashe kansa, ga ba ɗaya hujjojin na daga gefan babban motan, sannan ga gawan sa ya ƙone ƙurmus abin ba bu daɗi sam."

" Wayyo Allah."

" Ina zuwa zan kira ki an jima." daga haka bai ce uffan ba, ya kashe wayar. Ya jingina da kujerar motar yana shakar iskan wake.



**************** **************

__________ "Ina alfahari da kai amma waye ka kashe last? na san wani ka kashe."

" Wani pastor ne?." Daga haka ya miƙe ya shiga part ɗin sa, da ido ta bisa kawai. yana shiga ɗakin sa ya kwanta kan bed da latsa wayan da ya ciro a cikin aljinun sa, take kiran Skiddo ya shigo bayan ka katse sai ya kira.

“Sir, done,” ya faɗa cikin girmamawa. bayan sunyi sallama wa juna.

“Good,”

"Boss mun god....."

“ Enough, Ku tabbatar komai ya taxi nomal kamar yadda na tsara.”

“Understood, boss.”

Yana kashe wayar ya juya zuwa matasan da suka fi dari uku da ke zaune a wata unguwa ta sirri. Ya ɗaga murya da ƙarfin.

“Ku tashi!.” Suka miƙe kamar sojoji.

“Yau ƙungiya za ga je huta, da zaran kunji kira to ku amsa, ko wa anan Boss ya zaɓa muku abin da ya da ce, jami'an mu mutane 50, ku an baku hutun sati biyu, mutane 150 wanda Boss ya kuɓutar in ma a prisoner ko a wani gu, duk ya ba ku aikin yi, a ciki akwai mutane 50 wanda ya tura karatu zuwa ƙasar waje, ko dai da nasa a yanzu kuma zamu cika umarnin sa idan har laifuka suka yawaita dole mu dawo, wake tare da ni?." take suka hau faɗin.

" Mune! Mune!! Mune!!.".

******************* ******************

Gaba ɗaya wannan babban labarin shike treading a gaba ɗaya yinin jiya da yau, sannan mutane da yawa sun yi farin cikin wannan al'amarin na mutuwan Rash.

" Yanzu mai ya kamata mu aikata?" faɗin His Excellent sai Zaki ya ce.

" Komai ya ƙare ai, sai dai mu mai fatan alheri sannan Allah ya sa ka mai, ya ce ci ƙasar nan."

" Haka ne da bai kashe kansa ba da mu zamu wanke shi a gaban duniya." Meerah ta faɗa ta na gyara kwanciyar Small Ammee, sai Pretty Sk ta ce.

" Ba ma wannan ba, shin mai yasa ya ƙona kansa? Why? Da fari mu ma har yanzu bamu da tsayayyen in da za mu sa me sa balle mu ce ko yaga mun sani ne ya gudu, than ba wanda ya san shi balle ace a na neman ransa"

" Haka ne maganar ki, amma tin da kowa ya yadda mu ma mubar zan cen kawai."

" His Excellent shike nan, bara na ta ka maka." su biyu suka fita sai Meerah ta kalli Sakeenat ta ce.

" Yanzu duk wahalar bincikenan ya tashi a banza, koma waye Rash mutum ne na daban gaskiya."

" Sosai Maman baby."

" Allah ya kyauta."

" Ameen ya Allah."

****************** ***************
Air Force Base

Rayuwan giɗan yanzu sai a hankali kullum cikin rikici ake yi balle da Airah ta kulla ƙawan ce da Fancy, kullum suna tare har school ɗaya suke dan anan A.A ya sanya ta, kamar kullum a sabuwar motan Fancy suka zuwa, yau ma daga schoo suke, bayan sun shiga ciki kowa part ɗin ta ta shiga, Fancy ta fara sauko wa dan neman abin da za ta ci, tana cikin soya plantain sai Airah ta shigo, tare suka kammala sannan suka ci a dining area. Sosai jinin su ya zo ɗaya sannan Fancy na koya mata abubuwa da yawa, Airah ta rasa dalili da ya sa take jin kaman ta san fuskan Fancy a cikin brain ɗin ta amma a duk lokacin da ta matsa a kwakwalwanta akan ta tina sai kanta ya hau ciwo.

" Maa ki yadda da ni, ƙawance kawai muke yi amma bana shan........"

" Halima shuru ki bari mu shiga ɗaki mana, kin san ba mu kaɗai ba ne." Maa ta faɗa da ɗa ga murya, Part ɗin Maa suka shige, Fancy da ta bisu da ido ta saki ɗan murmushi da bai kai zuci ba, ba dan komai ba sai dan yadda rayuwa ke gwara Maa yanzu, a gun mijinta babu daɗi haka yaran ta sannan su sirikan ta, kuma ga dukkan alamu Halima ma tayo wani tsiyar dan yadda ta ga sun shigo abin ba daɗi.


Shuru ne ya ratsa madaidaicin parlourn, a karo na biyu Maa ta kuma sauke ajiyan zuciya ta na kallon Halima wacce take zub da hawaye.

" Halima." ta furta cikin sanyi, hakan ya sa Halima ta ɗago jajayen idanunta ta ce

" Na'am Maa."

" Ki faɗa min gaskiya, shin ke ma kina shaye-shaye kaman Salma sannan da bin maza."

" Maa ni ƙawance kaɗai muke yi, ban san ta na wannan halin ba."

" Gobe za muje asibiti, fita ki bani guri." da sauri ta bar ɗakin, Maa jin gina kanta ta yi jikin sofa ta na fatan kar ace abin da Salma ke yi ita ma Halima na yi.


********************* *******************

_________ Kwana biyu saboda rasuwan Askira ba ta zuwa gurin aiki domin kullum sai sunje, ta kan kira number Yusuf amma sam ba ta tafiya, yau ta zo aiki kuma tin safe ba ta gan shi ba, ta yanke shawaran in bai zo ba to direct giɗan shi za ta je ta ji shin lafiya. misalin 4:20 suka gama waya da Maa akan an kwantar da Salma, domin rashin lafiya ya ka mata yau, daga zuwa asibi aka ce shan manyan kwayoyi ya huda wasu jangin cikinta, sannan ta na ɗauke da juna biyu. Hankalinta duk ya tashi akan haka, knocking aka yi sai ta ba da permission sannan aka turo ƙafan aka shigo, shin sauri ta miƙa tsaye ta na kallon yusuf da ke sakar mata murmushi.

" Wai ina ka shiga ne, My Barrister?." ta tambaye shi ta na gyara vail ɗin abayarta.

" Nayi busy ne and wayata tan ya faɗin ne, so sai da na yi welcome back ɗa zu."

" Okh, ya kake?"

"Steady." ya faɗa ya na ƙarasawa zuwa gaban ta sannan ya miƙa mata file ya ce.

"I need ur signature for all this document." Ba tare da ta ce komai ba ta kammala sign din sannan ta miƙa mai amsa ya yi tare ta nufan ƙofa zai fita sai yaji ta ce.
"Yusuf." cikin murya mai rauni, zuciyarta na bugawa, ya tsaya ba tare da ya juyo ba.

"Ya maganar auren mu ne?."Shiru daga can sai ya ce:
"Hafsat... ki bar wannan yanzu. Yunus bashi d lafiya ba na cikin natsuwa." Sai ya fice, yana barin dakin da sauri, zama tayi fuskanta ɗauke da damuwa mara misaltuwa.

****************** *****************

__________ A gidan suka wuni, a tare su ka shiga gidan Sakeenat ta gaidasu Mom sannan suka shiga part ɗin Babban yaya, yau ne karo na farko da Sakeenat ta fara gani Babban yaya, gaishe shi suka yi ya amsa ya na fita daga gidan gaba daya, da gyar Ramlat ta iya fitowa tsaɓar nauyin ciki, gashi ko scanning ba ta zuwa wai ba ta so babu yadda ba'ayi da ita ba, sai dai ta kanje amsan magunguna da wasu kwaje-kwajen.

" Ya jikin na ki?."

"Alhamdulillah Sakeenat, ya Zaki."

" Lpy lau."

" Ma sha Allah, barci take yi ne?." ta tambaya ta na kallon Meerah da Small Ammee

" Aikam tin ɗazu ta ke yin barci, amma Namesake anya month dion Haihuwan nan bai wuce ba, at least yafi 9 month."

" Eh yafi gobe 10 month dai-dai, goben za ni hospital duk da jikina lau ya ke."

"To Allah ya raba lafiya, Sakeenat ba ra na barku, mai za ki ci yau?."

"Alhamdulillah, yau ki huta, Babban yaya zwi tawomin da shi." daga haka suka yi sallama ta wuce, duk abin Ramlat ke so Meerah na girka mata wani lokacin kuwa su Baby ke mata. a nan ta bar Small Ammee gurin Sakeenat, hira suka sha sosai, can sai Ramlat ta ce.

"Wallahi idan ina tare da ke, ƙawata na ke tunawa da rayuwar da muka yi, Allah sarki."

" Allah ya bayyana mana ita in dai tana raye, ameen, amma dan Allah Ramlat kin san mahaifiyar ta?."

" A'a, amma mahaifiya ta ce, ta santa ta ce ma na, dukka shekaran ta ɗaya 1 kawai ta yi a layin sannan babu wanda ya santa dan ba ta fita, ita ce dai takan leƙa su gaisa, to tin gun haihuwa ta rasu."

" Allah sarki na za ci kunyi rayuwa tare ne."

" Ko kaɗan, lokacin ni ina jaririya kenan, dan na girma Ramlat ƙarara da wata 1, amma mahaifar mu ta ce, sak Ramlat haka mahaifarta ta ke, kenan sak dai ke, idan na haifa mace ni zan zaɓa sunan idan kuma namiji ne to Babban yaya ne, da ba sunan mu iri ɗaya ba da sunan ƙawata zan sanya, dan ina ƙaunarta sosai."

" Ai za ki iya sa wa sai ki sanya nickname mai daɗi kawai."

" To, mayyuwa na sanya, Please ki ta yi nemo nickname masu daɗi da ma'ana mana."

" Shike nan Auntyn, zan ma duba miki na masoya na haɗa sunan ki da na Babban yaya."

" Wai to hakan ya yi amma mai ma'ana"

" To ya sunan Babban yaya na gaskiya."

" Shuraim."

" Nice name."

" Uhmmm ai Umar yafi wannan daɗi." Sai da Sakeenat ta yi murmushi sannan ta ce.

"A'a gaskiya." Hira suka ɗan kuma yi sannan tayi mata sallama.

END.


age 61.

******************* ***************

_________ Fuskar Malam gaba ɗaya babu annuri, kallonta ya kuma yi ya ce da ita:

“Mar’atussaliha, dole gobe mu koma Nigeria. Ƴar auta ta tana asibiti, sannan yara na biyu duk sun haihu, Hajara yaronta ya kai wata biyu, Maryam kuma wata uku, dukkan su maza kuma sunana suka sanya musu, Ina son naje na gansu, Ramlat kuma kwance take, rai a hannun Allah, domin C.S za a yi mata.” Zuciyarta ta buga da sauri, sai dai yanayin Malam ɗin bai mata daɗi ba. A hankali ta buɗe baki ta ce:

“Shike nan, amma zamu dawo nan ko?.”

“Eh, tunda kina so.” Daga nan suka fara shiri. Ta shiga gidan maƙon ta domin yin sallama da Hajiya. A parlour suka gaisuwa cikin mutunci, kasancewar ba su daɗe da zuwa ƙasar ba. Hajiya kuma ba ta da damuwa sam, sai dai har yau ba su haɗu da ɗanta da kuma sirikarta ba domin kullum suna makaranta.

“Allah ya tsare hanya, a gaida kowa idan kin je can,” cewar Hajiya.

“In sha Allah Hajiya, ba rana je, dan jirkin safiya zamu bi,” ta amsa da "To madallah" Har haraban gidan Hajiya ta rakota kafin suka rabu. Da ta koma gida ta zauna tana kallon shiri a T.V, sai ga su Yusuf sun shigo.

“Hajiya ya gidan?” inji Hasty bayan sun yi sallama. Ta amsa mata tana murmushi.

“To ya ya zan yi, ai gobe zan biki ne. Matar da muke ɗan hira da ita gobe za su tafi Nigeria. kinga ba zan zauna ba.”

“Allah sarki. Har yau dai ba mu haɗu ba, amma in ta dawo zan je, musamman na gaida ta” Yusuf ya ce yana zama kusa da ita. Hasty ta kalle shi.

“Tare zamu yi girki yau da kai fa,” ta faɗa. Shiru yayi sannan ya ce:

“Ki huta, ni zan yi kawai.”

“Yauwa, thanks.”

“To ni ban yadda yarona ya yi girki ba,” Hajiya ta faɗa da sigar wasa.

“Uhmm uhmm uhm, ni dai wallahi a’a Hajiya,” Hasty ta furta tana bubbuga ƙafa, ta miƙe ta shige bedroom. Dariya suka sa..

***************** *****************

FRONTIER CONSULTANT CLINIC

________ zaune yake a ofishinsa yana duba agogo, ya ga saura minti ashirin time ɗin operation. Ya ɗauki waya ya kira lambarta, amma har ya yi miss call uku ba ta ɗaga ba. Daga bi sni sai ga kiran na ta, cikin sauri ya ɗaga.
“Ina kika ajiye waya ne? Na san dai yanzu kun koma gida ai.”

“Sorry, wanka na shiga yi ne.”

“Okay, ya home ɗin?”

“Alhamdulillah, Monceur kasan menene?” ta rage murya, kaman me raɗa.

“ Sai kin faɗa."

"Won’t you scold me if I tell you something?"

"No, go ahead. I'm listening."

"Earlier when we got back from school, that your sister Barrister, insulted me. Honestly, I don't tolerate disrespect, that’s why I avoid people’s matters, because I have little patience." Sai ta yi shiru shi kuma ya ɗan saki murmushi mara sauti sai ya ce.

"What did you do to her?"

"I gave her three slaps, then warned her seriously."

"Hmm, aren’t you afraid she might retaliate?"

"Never. Honey, I’m feeling hungry. Uhmm, I’ll go to the kitchen now."

"Okay. I need one peck."

"Ummaath. Take care, please..


Bayan kwana ɗaya.
************** ***************

“Sir, komai ya kammala. Sign ɗinka kawai ya rage,” ya ajiye wasu takardu. A hankali Haidar ya duba takardun sannan ya sa hannu. Ya ɗago ya kalli saurayin:

“Nuruddeen, in the next five minutes, get ready. We're heading to a village near Jaji. Assemble the team and pack the equipment, take everything to its proper place.”

“Okay, Sir,” saurayin ya amsa. sannan ya fice, Haidar ya bi shi da ido. Yaron akwai biyayya, ji yake kamar Askira ne babban matsalar shi tun da ya rasu komai ya koma nomal, harta Chul yana mai biyayya da bin tsari ya da komai. Ya ce “Alhamdulillah.” A kullum idan matsala za ta ɓullo, kafin ya yun ƙura sai ya ga an riga an magance ta.

************ **********
Tun da safe ta kammala aikinta, zama ta yi tana duba wani app na sunayen musulci da ma’anarsu, take zuciyarta na raya mata: “Mai zai hana na haɗa sunan Babban Yaya da Ramlat? Sai na samu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login