Showing 75001 words to 78000 words out of 93691 words

Chapter 26 - RASH ƁOYAYYEN MASHEƘI. COMPLETE HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

214

suna mai daɗi da ganan sai na duba ma'anarsa.”

Ta ɗauki takarda, ta rubuta Shuraim da Ramlat. Ta duba haruffa bibbiyu, har sai da ta samu “Shura.” Ta ce, “Shura ai sunan sura ne.” Daga nan ta fara na Ramlat, ta rubuta “RASHU.” Sai ta ce, “Gaskiya bai yi mana ba, bara na cire U.” take ta goge harafin sai idonta ya sauka kan sunan “RASH.”

Zaro idanu ta yi, ta kuma kalla. Sai kuma ta dubi Shuraim. Ta haɗa kalmar Rash a cikinsa. Shiru ta yi, sai ta ɗauki wayarta, ta kira Zaki, amma bai ɗauka ba. Nan take kiran Meerah ya shigo, ta ɗauka.

“Assalamu alaikum.”

“Wa’alaikas salam, Sakeenat. Muna asibiti yanzu, mun samu twins maza daren juya, ki shiga gidanmu ki ku tawo da su Mom da abinci.”

“Ma sha Allah! Amma ai da baku faɗa min da wuri...”

“Ke dai ki bari. Hankalin mu ya tashi. Yanzu haka jini ake ƙara mata don ta zubar da jini sosai.”

“Subhanallah! Ga muna zuwa.”

Nan da nan ta shiga gida domin shirya kayan atafiya..


*********** ************
_______ Yau lecture ɗin ya yi zafi sosai. kai ma ciwo yake mata. Ta duba agogon hannunta 10:12am. bai jima ba lectural ɗin ya fita, ko note ɗin ba ta gama ba, ta yi snapping a waya ta fice, ta rasa mai ya sa ko da yaushe sai maza sun tare ta, wasu ko tace tana da aure sai su ƙaryata, kun san farar mace, mai tsayi hmmm sai ma sha Allah, haka yau ma wasu sai da suka tare da bakin class ɗin su, amma ta wuce ta naji suka biyo ta, can kuma suka koma ganin ba za ta kula su ba, can ga hangi Fancy tsaye da wata ƙawarta, ko da ta ƙasa gaisawa suka yi sannan ya shiga mota dan jiran ta, nan da nan Fancy ta shigo motar ta na cewa

"Na jiki shiru, a raina na ce, ko Oga bai barki ba ne."

" Ai ina shiga class na kira shi, sai ya ce ba bu damuwa." Sai da motan ta hau kan kwalta sannan ta fara gudu, dan so take ta riga su Kandy ganin twins, Meerah ta kira da safe ta ke faɗa mata, ba ɗan text ba da ba ta je ba school ba.


*************** **************

_______ Tin a jiya suka iso, sannan giɗansu Zainb ta sa a gyara sosai, hatta girki ta yi musu, bayan sun iso, ita da Muhsin suka je da daddare suka gaidashi Abbuu, da yake yana da mota shiya ɗauko har asibiti a safiyar yau, sannan ya ce an jima zai zo ganin yara ɗan yasan akwai mutane sosai. Babba ne ɗakin haihuwar, Ramlat da barci ya ɗauke ta sannan jinin na ta shiga jikin ta wanda ake ƙara mata, Shuraim ne ya bada na shi, Bayan su shiga gaishe shi su Aunty suka yi ya amsa cikin walwala da ɗan damuwa ganin ƴar sa kwance, jarirai aka bashi ya amsa cikin ƙaunar su, jarirai ne amma kamarsu ɗaya sannan abin Allah komai ɗaya ya yi sai ɗayan ya yi, har ta kwanciya kusan iri ɗaya suke yi, nan fa sai ga su Kandy, Beauty, Beasty, Karis, Butter, Baby da Zubee, Dan har kayansu sun ɗauko wai zasu taya Ramlat raino.

Suna da yawa amma babu me magana saboda a na so ta samu hutu, A A ne ya shigo ya kuma duba jikin na ta sannan ya fita, bayan yayi ɗan nisa ya shiga wani ɗakin, Maa, Halima da Hafsat ne ya gani suna zaune jigum-jigum.

" Result ya fito ne?" Ya faɗa ya na gyara class ɗin sa sai Maa ta ce.

" Nan da 10mnt za mu koma Lab ɗin." Kafin ya ce wani abu Doctor da Salma sun fito daga restroom, kallo ɗaya ya musu ya fice dan bai ma san ganin Salma, shi duk iskan cin da ya yi sai ya ga ta fishi don shi baya neman mata amma ita kam za ta nemi mutum kuma ita ke biya. Zama Salma ta yi da ƙyar dan duk ta fita hayyacinta, ta yi duhu, ga rama da ta yi, Halima duk a tsora ce ta ke akan result domin tana shaye-shaye amma bada yawa ba sannan ita babban ƴar bariki ce, dan ta zub da ciki sau uku ba tare da sanin kowa ba.

" Maman Muhammad, kin ga yadda rayuwa ta mai da ni koh?, tuba nake ga Allah babu dare babu rana, hmmm alhaƙi ƙwiƙwiyo ne ga aya ina gani akan rayuwata, domin ni kaina ina ɗauke da ciwon zuciya."

"Nasa ni kibar damuwa dan Allah, ki na da ni zan gyara rayuwar ku in sha Allah."

"Momyna ki yafe min dan Allah, wallahi na gane kuskure na in sha Allah daga yanzu zan za ma mai miki biyayya." Salma ta kai nan tana rushewa da kuka mai ciwo, hatta Halima sai da hawaye suka zubo mata, ita fatan ta ɗaya ace ba ta ɗauke da HIV dan taga alamomi da yawa na ciwon akan ta.

END.



Daga alƙalamin pretty SK.
[6/12, 1:34] ᑭᖇᗴTTY ՏK ✍️✍️✍️: https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

💪 JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIAION (J.W.A)💪
Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi.✍️

If your Mum is alive, may she have a long life to witness your success🤲
𝐑𝐀𝐒𝐇 Ɓ𝐎𝐘𝐀𝐘𝐘𝐄𝐍 𝐌𝐀𝐒𝐇𝐄Ƙ𝐈
ᑭᖇᗴTTY ՏK


Page 62
*************** ****************

A hankali ta buɗe idanunta, sannan idanun suka sauka akan ledan jinin daya ƙare, ƙoƙarin miƙewa ta ke sai Aunty da Hajiya suka taimaka mata har ta zauna, a hankali ta ke bin ƴan ɗakin da kallo, suna da yawa sosai, a hankali ta kalli maccen da ke kallon ta fuskanta sanye da niƙaf tana mata sannu, sannan ta kalli mahaifinta, murmushin ƙarfin hali ta sakar mai sai ya miƙe ya nufota.

" Ramlat ya jikin." 

" Abbuu Alhamdulillah." ta faɗa ta na riƙe hannunsa.


“I see the babies, may Allah keep you safe and bless them. Two babies are a great blessing from Allah, so be thankful.”

“Alhamdulillah. Thank you. When did you arrive?”

“Last night. Your mother and I came,” ya faɗa yana nuna Zulaihat, sai ta kalle su ta yi murmushin sannan ta kalli Zainab.

" Daure kisha wani abu ƴar nan." Mom wacce ba su jima da zuwa ba ta faɗa.

" Momcy ina Sakeenat?." Meerah ta tambaya tana miƙa Hassan gurin Butter.

" Muna shigowan haraban asibitin nan, ta ce ta na zuwa wai za ta amso saƙo."

"Okay. Baby, do you see how beautiful the babies are?."

"How can babies be beautiful? Look at me, am I not beautiful, Aunty?" Karis ta faɗa tana kallon Aunty sai tace

"Definitely, my dear niece. Leave them. Even Babban yaya agrees, you’re the most beautiful."

"Honestly, not me! If Karis is prettier than me, then I'm in trouble," Beasty ta faɗa take suka kwashe da dariya.
Hasty ce ta kira Husty Video call ita ma ta ga yara ma sha Allah, yara wa'inda suka ci Hassan Abdulrahman sai Hussain Abdulraheem dan ɗazu Babban yaya ya raɗa musu, ganin ba ta tashi ba ya sa ya ɗan fita.

****************** *****************

___________ Tin shigowar su asibitin ta hangi Babban yaya ya na fitowa daga ciki, ta rasa mai yasa yaji ta na son ta ɗan biyeshi dan a tsakanin ɗa zu zuwa yanzu tinanin sa ta ke yi, tasan ba shine Rash ba amma ta na zargin sa.

"Momcy ku shiga bara na amso saƙo." ta faɗa haka ta na miƙa ma Mom Basket ɗin hannun ta, amsa suka yi sai ta dinga kallon Babban yaya har ya shiga wata mota, driver daya kawo su ta bashi umarnin ya bi motan da ke gaban sa, cikin kwarewa driver ke bibiyan sa, bayan sun shafe tsawan lokaci suna tafiya har dai ya isa wata unguwa sannan motar ta shiga wani babban gida, sai ta juya ta dawo asibiti, bayan ta sallami driver sannan ta fara ta ka wa haraban asibitin wanda ke da yalwan jama'a.

************* ***************
___________ "Bara na fita na shigo da Fancy wai ba ta gane gurin ba." Meerah ta faɗa sannan ta nufa waje bayan ta ajiye Small Ammee gurin matar Abbuu.


*************** ***************

________ "Excuse me, Maa and the others will soon be back, let me quickly check on some patients," Salma replied, without much softness in her voice, tin da aka kwantar da su Momynta ke duba wasu a cikin asibiti, hijab ta sanya sannan ta fita ta na fatan su Maa su dawo daga Lab komai ya tafi nomal.

************* **************

_________ Tin da suka sauka a mota, Airah ta matsa ma Fancy da ta fara rakata gurin A.A, ba yadda ta iya, haka ya sa ta rakata a waje ta tsaya ita kuma Airah ta shiga, a zaune ta gansa ya na aiki a system.

" Have you arrived." Be ɗago ba ya furta ɗan ya san tana hanya zuwa.

"Yes, I came to get my medicine."

"What’s bothering you?"

"I feel headache and a little dizzy." He quickly looked at her, standing up in concern.

"Subhanallah! Since when have you been feeling like this?."

"Uhmmmm, since the morning," ta faɗa tana ƙara sawa kusa da shi.

"I’ll take your blood for testing. look at your skin, it’s turning yellow, and your eyes have a bit of redness. now, let me call a nurse..."

"Okay, but let me walk Fatima to see the babies. I’ll come back to the test, I think it’s malaria."

"Ok you can go?."

"Uhmmmm, go ahead, please, take care of yourself." Sai da ya ɗan taka mata sannan ya koma ciki.


_______"Sorry sis, I stopped you." ta faɗa tana isa gaban Fancy

"No, babu damuwa, yanzu Aunty Meerah nake jira ta fito dan kaimu room din, ya baki medicine ne?."

" Wai idan mun gama za'amin text."

" Gaskiya kam, dan kin sauya sosai kodai-kodai." tai murmushi ta na shafa cikin na ta. Hannu Meerah ta ɗago musu sai suka isa gunta.

" Cewa na yi hawa na uku, amma ina kuka tsaya."

" Sorry Aunty duk na ƙosa na gansu, na san su Baby sun iso."

" Tin ɗazu ma." suka jera suna hira, bayan sun gaisa da Airah.

" Nace ba." a tare suka ƙalla matar da ke magana, ta ke fuskan Meerah ya faɗa ɗa murmushi.

" Laa Doctor ina wuni."

"Lafiya lau, ina baby girl."

"Ta na lafiya, kin dawo nan asibitin ne?."

" Eh, waye ba lafiya?."

" Uhmn wannan sister tawa ce aka ma C.S, ta haifa twins maza."

"Ma sha Allah, wani room ne na zo ganin babies?."

" Ai gashi can mujera kawai." daga haka su huɗu suka jera. sai Fancy ta ɗan raɗama Aira

"Wannan ce friend ɗin Maa, Doctor, Maman Salma."

" Oh, to ba tana idda ba."

"Maybe wani abun ne ya kawota nan."


_________ Tana tambyan ɗakin haihuwa kenan ta hangi Meerah da Fancy sai wasu, sannan ta hanji in da suka shiga.


******* Cikin jin daɗi da murna, Fancy ta ga yara sannan aka ba Doctor itama ta musu fatan alkairi, Airah da ke tsaye bayan sun gaisa da kowa, brain ɗin ta ya shiga tsalle kaman zai fita, dan mutanen da take gani sai suke mata gizo a cikin kanta, amma ta ɗaure ta zauna.

Mama Zulaihat da ke jiran Malam ya dawo su wuce dan ɗakin ya cika da mutane sosai, idonta ne ya kai kan Airah wacce ta kifa kanta akan cinyarta, sai kuma ta mai da kan Zainab da ke mata magana.

" Assalamu alaikum." Sakeenat ta faɗa ta na shigowa.

" Ke wai ina kika je? Kin san kira na wa Zaki ya miki?." Hajiya ta faɗa ta na miƙa mata wayan ta, sai ta ce

" Na ɗan tsaya ne kawai."

" Yayi kyau ai kyamai explain, kusan 40mnt da kiran sa." Faɗin Meerah. Doctor ta ɗago kai ta ƙalla Sakeenat, take gabanta ya faɗi ganin wannan yarinyar a karo na biyu, ta nufo ta amsan Hassan ta yi a gun Doctor itama ta na kallonta.

" Ya sunanki?."

"Sakeenat." ta faɗa ta na zama a gefan ta, Doctor ɗin jikinta a mace yake, jiran Ramlat ta ke dan an ce Momcy na gasa mata a toilet. Jim Sakeenat ta aje wannan ta nufa in da ɗayan jaririn ya ke.

"Ɗan na ga Hussain." ba ta kalleta ta fara miƙa mata Hussain ɗin sai dai mai idanunta ne suka kalli yarin yar, a matuƙar tsoro ce ta. da sauri ta miƙe tana ƙare ma Sakeenat kallo, kowa na room ɗin sai kallon ta suke dan yadda ta miƙe ɗin ma abin kallo ne.

" Wacece ke." Jin irin tambaya da matar ta yi mata yasa ta miƙa ma Zainab yaron ta ce.

"Kin san ni ne?." take ta fizge niƙaf ɗin fuskanta, ba Sakeenat kaɗai ba kowa sai da ya miƙe ganin fuskan Mama Zulaihat, tsayi, kama, skin colour iri ɗaya sai dai ana kallo an san Zulaihat ba yarinya ba ce dan za ta haifa Sakeenat.

"Zulaihat." Doctor ta faɗa da ƙarfi mai haɗe da firgice da tsoro, Zulaihat ɗin ta kalli mai magana wanda sai da take tayi baya-baya, Momcy tayi saurin tare ta fe cikin faɗin.

"Innalillahi wa'inna ilaiyi raji'un. Innalillahi wa'inna ilaiyi raji'un, innalillahi wa'inna ilaiyi raji'un.'

Doctor Mariya ita ma zaunar da ita a kayi sannan suka kalli juna, ita dai Sakeenat jin gina tai da bango, a karo na biyu ta ga mace mai kama da ita sai.

______ Momcy da Ramlat ne suka fito suna tambyan lafiya, sai a lokacin Airah ta ɗago taga mai ke faruwa dan tini ta yi nisa da tinani, fuskokin uku ta gani a jere, Mama Zulaihat, Sakeenat da Ramlat, ihu ta sa wanda kowa ya mai da ido kanta sai ta tafi luuuu ta faɗi ƙasa.

Ana wata ga wata, abu sai addu'a kawai, dan Abbu na shigowa yaga faɗin Airah, shi ya kira Doctor's suka tai maka mata amma ina ta shiga doguwan su, ko da A.A ya ji, hankali ta she ya nufa room ɗin da aka kwantar da ita, abu biyu sun haɗe mai, dan Halima an gano ta na ɗauke da HIV, sannan Maa ta suma amma bata farka sai dai ana sa mata drip.

 

__  After 1 hour __

Babu mai motsin a ɗakin sai ƙafan fanka da kuka small Ammee, Doctor Mariya ce ta miƙe da ƙyar sannan ta nufi Mama Zulaihat da ta rufe idanunta sai hawaye ke zubowa, durgusawa Doctor ta yi sannan ta haɗe hannunta tana ce wa

"Dan Allah ki yafemi, ji nake alhakin ki ne keta bi na, tin ba yau ba nake neman ki amma ban sameki ba, na sani na miki......" Sai kuka ya kwace mata sannan ta ci gaba da ce "A lokacin duniya na ruɗata fiye da tinani mai tinani." kowa dai kallonsu yake yi, sai Abbu ya ce.

" Mar'atussaliha me ke faruwa ne? Sam ban gane in da kuka dosa ba, wace ce wannan matar?." sai a lokacin ta ɗago, jajayen idanunta ta kalli Abbu ta ce.

"A lokacin auren mu na ɓoyema ai niyin labarin aure na, badan komai ba sai dan ba na so tinawa da wannan rayuwan na har a ba da." Sai ta mai da idonta kan Doctor ta ce "Ban mutu ba, Allah ya yi ina da tsawan rai a gaba." Bara na baka labari na


   Labari

--------- cikin dare naƙuda ta ya tashi, a napep ɗin maƙocin mu aka kaini wani ƙaramin asibiti, aka bani gado, a dokan su ba'a zama da majinyaci dan haka, Malam (mijina), ya koma gida da niyyan washegari zai tawo da kayayyakina, bai so ta fiya ba amma nurses fin nan suka sa ya wuce, alluran aka min wanda ni kai na ban san na menene ba, haihuwar fari ce ko ya ye ne ina buƙatar wani a kusa dani, ciwo sosai na keji a kowa ni sassa na jiki na, bayan na ɗau lokaci a haka sai na ji muta ne sun shigo, ban shedi su waye ba sai naji suna ce wa.

" Doctor Mariya munyi mata alluran sannan mun kwada lafiya lau ta ke."

" Yauwa yanzu kuje room 17 Aminity, ki ce ma Hajiya mun samu kidney ɗin, ta shirya tiyata yanzu." da ga nan ban kuma jin su ba sai bayan wani lokaci mai tsayi, na ji na dawo dai-dai amma jikina ya na min ciwo sosai, ko bayan na buɗe idanuna ni kaɗai na gani sannan babu cikin nawa gashi babu motsin kowa a kusa da ni, ta ɓa cikina nayi in da na ga ɗinkin guri biyu, komawa nayi na kwanta dan motsi ma wahala ya kemin, ban san dalilin ba amma ko da wasu suka kuma shigowa na kasa motsi sai dai abin da na ji suna faɗi ya sa na ɗauke wuta

" Allah sarki, baiwar Allah nan abin tausayi, gaskiya Doctor Mariya ba ta ɗa tausayi in dai akan kuɗi ne, da wanne za ta ji c.s ko musanya mata kidney."

"Nurse Harira abin takaicin ma na wata wacce na ke zatan tafi 50yrs, aka sanya mata."

"Duk talauci ne ya kawo haka fa, mijin ya bani tausayi da ya bar nan yana kuka tare da baby a hannu."

"Hmmm Allah ya isar mata kawai, amma abu bai yi daɗi ba, mu kan mu muna cikin hatsari dan idan kalma ɗaya ya fita mune." Da ganan sabon hawaye wa gangaromin take na suma bayan na fara, mutane ne uku na gani a biyu da kayan nurses sai ɗaya da kayan gida amma ta sa lab-coat.

" Ya jikin." da kai na amsa mata sannan na ji tace "Harira ɗauko wannan injection ɗin P.I.D." 

"Okh." har ta kai ƙofa sai ta juyi ta ce "Doctor Mariya P.I.D A1 ko A1q."

" A1q." Da ido na bisu sannan a hankali na ce.

" Ina mijina?." 

"Bai zo ba, sannan ina miki ta'aziyyar ƴar da kika haifa ta koma ga Allah." Rintse ido na yi sannan na ce.

"Doctor Mariya koh?." Matar da nake kallo ta ɗaga min kai, sai na ce "ina buƙatar wayana?"

"Sorry babu dama ki bari zuwa anjima." Ganin basu da niyyan ba ni wayan sai na yi shiru, daga nan ban kuma farkawa ba sai bayan sati ɗaya, in da na tsinci kai na cikin birnin Saudiyya, gurin wata baiwar Allah, ita ke bani labarin yaron ta ne ya tsinci ni a cikin bola, da yajin ina da rai sai ya tawo da ni Saudiyya, daga nan na ci gaba da rayuwa a can cikin ciwo a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login