Showing 84001 words to 87000 words out of 93691 words

Chapter 29 - RASH ƁOYAYYEN MASHEƘI. COMPLETE HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

233

tsaye sannan ta fita daga room ɗin, sai a lokacin Airah ta ga ne ashe asibiti ne, ba ta jima da fita sai ga ta ita da ƴan gidan su, sannan da wanda a kallo ɗaya ta ji sam ta tsane sa balle da yake yawan taɓa mata jiki. Idon ta ne suka sauka akan Sakeenat sai hawaye ya gangaro daga idanunta, gyara zama tayi sannan Fancy ta ce.

"Ƙanin miji ka mata bayani, kan mu a kulle ya ke sosai, kai ne kawai za ka iya warware wannan case ɗin, sam cikin mu ba musan mene faruwa ba." Shuru yayi sanann ya ɗan taka zuwa gabanta sai ya furta.

"Airah, Monceur ɗin kine fa....."

"Waye kai Please?." Ta kuma wurga mai tambayan tana mai da kanta ga Sakeenat da ke tsaye gefan wata mai maka da ita again, shuru ta yi dan shine abin da zai fi mata akan ta yi magana.

"Airah wannan Mijin ki ne fa." Faɗin Fancy bayan ɗakin ya ɗau shuru.

"Miji, Fancy wai hauka kike ko me, wait natina ashe Fancy ce, Uhmmm Hasty da Husty na san ku kuna sona ai, ba kwa ƙyamata Please ku fitar da ni a cikin duhu dan Allah." Ganin idan bashi ba, ba bu mai warware wannan case ɗin, kafin ya furta wani abu sai Aunty ta ce.

"Doctor Abdullahi, me ke faruwa, wace ce Airah? A ina kasanta? ta ce ita ce Ramlat ɗin mu, Please ka ma explain ko ka faɗa in da iyayen ta suke da mu nemo su, mu kuma ku koma gida."

"Gaskiya zancen ki, ke Fancy a ina kika santa?." Fancy ta kalla Momcy tukun ta ce.

"Matar shi ce." Ta faɗa tana nuna A.A.

"Muna jinka a ina ne gidan su Airah."

"Ya isa, wannan dai da kuke gani itace Ramlat ɗin da kuke magana, ita ce dai sak wancan yarinya, ita ce dai." Ya kaina ya na nuna Sakeenat.............
END



Page 69.
****************** *************
_____________ "Bara na baku ainihin labarin wanne A.A da wace ce Airah." A.A ya faɗa yana mai fargaban kar Airah ta dena son shi, amma bara dai ya gama faɗi. Kowa shuru ya yi dan ya na son yaji labarin, duk su 10 ne, Ramlat, Fancy, Aunty, A.A, Husty, Hasty, Sakeenat, Mama Zulaikha da Momcy, sauran sun zauna a gida.

Labari na

A.A - Abdullahi Anas chul, haifaffen ɗan Kaduna ne, Ni ne ƙarami gun iyayena, na taso cikin gata sangarta da wadata, Mahaifiya ta wato Maa, ta sangartan da ni fiye da misali, ban damu da ilimin addini ba sam duk da ina zuwa saboda Yayana Muhammad dake tilasta min akan naje, ni mutun ne mai son shagala da duniya, yau ni ne wannan club ɗin gobe wannan, nakan sha shisha da giya wani lokacin, ban taɓa na daman wani abu ba saboda iyayena sun tsayamin, amma ban taɓa zina tinda nake, a baya ban taɓa tsammanin akwai ranan da Ni zan faɗa soyayya, dan ni ban kula ko wacce mace. A qata rana bayan na sha nayi ta tul, na shiga mota ta dan na koma gida daga club, a hanya ta wani babban iftila'i ya faru dan accident ɗin da ban taɓa gani ba na ci karo da shi......." Sai ya yi shuru tare da kallon Airah wacce itama ta zuba mai idanu kaman sauran mutan ciki. Ci gaba da magana ya yi cikin taushin halin sa.

" Banyi au ne ba, wasu matasa sun tawo a cikin napep ga gudu, nima na danno gudu, haka wata babban mota ma haka, ba na ce nasan me ya faru ba dan ban cikin hayyaci na, na wayi gari ne na ganni a wani ɗan garamin gida, bacin na miƙa tsaye da ta hangi rigata a gyefe guda na sanya sanann na fita waje, wani ɗan dattijo na su zaune a tsakar gidan, da ganina ya miƙe tsaye ya na mun Barka da fitowa. Bayan na natsu ya bani labarin hatsari ne ya kafku sosai, ni da mata ne kawai iska ya kaɗamu wani gangare hanyar da ya sada ƙauye su, shi ya tsince mu sannan ya kawo mu nan dan ba mu kulawa, ashe har kwana biyu nai a doguwar suma, bayan matarsa ta dawo shine ta kaini ɗakin wacce suka kira da Mata ta, hankali ya mugun tashi da na ga yadda da take, ba tare da tinanin komai ba na ɗauke ta d taimakawan su nafita da ga wannan unguwan, na kaita Asibitin mai kyau, bayan kwaje-kwaje aka ce sai an mata aiki dan gefan fuskanta ya lalace, daga ƙasar waje aka zo aka wanann aiki daga bi sani na kaita aka sauya mata fuska sannan aka bata wasu ƙwaya wanda take mutum kan sauya kala, haka akai mata aiki a brain, 8 month tana kwance ina jinya ta....." Sai ya tsagaita tare da kuma kallonta, sam ba zai iya karanta komai dan gane da ita ba. Sai kawai ya da sa.

"Tin bayan ranan da nakaita asibiti wallahi wallahi ban taɓa jin ina son ka sance da kowa ba sai ita kawai naji na kamu da soyayyarta, dan haka da na koma gidan wannan Baba na faɗa mai ni ban santa ba amma ina son na taimaka mata, take yace to na aurenta, na ce bansan ko da auren wani a kanta ba, haka dai muka tsaida musu, a ranan aka ɗauramin aure da ita bayan na biya sadaki, domin gasgata ni ga ma su nan." Yana faɗin haka sai ga bayin Allah nan sun shigo, ƙara jaddara magarsa suka yi, da gode ma A.A dan ya maimake su sosai, yanzu haka yaran shi maza biyu ɗaya yana karatu ɗaya kuma ya samar mai aikin soja, kuma sun bar gidan nan ya musu sabo. Baban ne ya faɗa haka.

" Ko bayan faruwar abin jami'ai sunyi bincike a in da aka ce wasu matasa sun sake wata budurwa sai tsutsayin ya afku. Duk sun mutu, su biyu Allah ya tsaratar.."

"Mama wannan itama ƴar ki ce." Sakeenat ta faɗa tana isa gaban Airah, sai ta rungumeta, tana kuka.

"Ramlat ashe mu twins ne, ashe....."

"Sakeenat ba a nan ba, ki bari ta samu hutu Please." Aunty ta katseta da faɗin. Ramlat da hannunta ke cikin na Airah ta ƙara matsawa tare da sumbatar shi. Mama Zulaikha itama ta matso ta rungume Airah wacce ake ce ita ta haife ta, tayi ko kwanto kafin ga rungume ta amma bayan ta rungume ta take ta gasgata ƴar tace sai ka ta da ga wannan ta bon a hannunta haka kuma ga wani abu a saitin wiyarta sak irin na ta, safan gun tayi ta sake rungume abarta.


*************** ***************
7:30pm suka dawo gida, anan Mama Zulaikha ta ga Hajiya wacce sam ba su haɗu ba, sun yi murna da ganin juna haka haka taga sirikarta harda yaranta twins, wanda suka dawo bayan magrib dan su wuce. Allah ke nan sam ba ta kawo nan kusa zasu haɗu ba sai gashi.

Kafin Pazars su dawo ko wacce ta wuce zuwa gidan ta, Mama Zulaikha itama ta wuce da Abbuu ya zo ɗaukan ta, ta so Airah ta bi ta amma Ramlat ta ƙi yadda. hatta Meerah ta yi farin ciki da bayyana Ramlat ɗin. A part ɗin Baban Yaya suka raba ɗare kafin Meerah da Sakeenat suka bar gidan. suna fita Airah ta kalla Ramlat ta ce.

" Pure white, abu na cin rai na, wai yanzu Zaki ya yi aure, ya aure ƴar uwata?." Ta faɗa cikin taushin hali da fatan ace wani Zaki ne ba Saurayinta ba.

" Ki ya ƙuri, abu yafi 1yr yanzu, be yi aure ba sai bayan kin fi wata 8 tukun ya yi, sabon Aure ne wanda bai jima ba. Dan Allah kar ki tashi hankalin ki kinji......"

"Ya yi aure. Zaki na ya aura wata, Za...." Sai kuma sannan ta miƙe tsaye ta ce. "Na rasa shi wai !, Inaaa sam ina son sa, babu kowa acikin nan sai shi." Ta nuna zuciyar ta. Sai ta nufi in da zata kwana kafin ta shiga ta ja jakkanta, ta na kam shiga ta garƙame ƙafan. Zama ta yi jikin gadon ta sa ka sukuni da walwala. Misalin 1:21am na dare ta kunna wayarta, saƙon ne ya far shigowa a jera kuma duk na mutum ɗaya wato Monceur 💖, buɗewa tayi amma na ƙarshen kawai ta karanta.
*** Daga ni mijinki Airah, ina miki so na gaskiya, dan Allah dan Allah kar ki ce za ki gujeni, ki sani ni bazan taba gudun ki ba insha Allah, ki ɗauki duk lokacin da kike so ki huta acikin familyn ki amma ki kulamin da kanki....***** Ji tai kaman ta fashe da kuka, sai kawai ta shiga contact take ta fara sanya number da ta mai wani mugun hadda, saɓo ta tura kamar haka.

" A. Asad, kayi aure, ka manta da ni, Allah sarki, ya zanyi da dakon soyayyar ka da ke cin zuciyata...." ta tura tana mai jiran reply sai kawai taga ya kira ta. Take ta dauka.



Zaune yake ya kasa barci tinda Sakeenat ta gama bashi labari, barcin yaƙi zuwa sai ya koma bedroom ɗin sa amma sam barcin ya guje shi, ba komai ya ke tinawa ba sai rayuwar su ta da, ya zo ace zai iya auren ta amma ina a yanzu babu aure a tsakanin su. Ganin sms ɗin ta sai ya kira, take ta fara kuka wanda ya ke ji har cikin zuciyar sa.

"Ramlat is okay, Dan Allah ki shuru kinji." Ya faɗa shima kaman ya yi kukan, sai da yi mai isarta sannan ta yi shuru. sai ya dasa da ce wa.

"Har yanzu wai kina sona?."

"Har abada." Ta faɗa ta na share sabon hawayen idanta.

"Ki na da aure ai......."

"Ya sakeni wallahi ban son sa, bansan auran kowa in ba kai na." Sai kuka abinka da uwar kuka.

"Innalillahi kin san ban san wanan kukan koh? Sai da safe tin da ba za ki yi shuru ba." Take ta sassauta kukan sai ya ci gaba da magana.

"A kullum ban da maradi sai na ga kin dawo, na jira na jira, daga baya na fidda rai nai aure amma a kullum kina cikin rai na....."

"Ka aure ni in dai da gaske har yanzu ka na so na."

"Hmmmm dan ba kiji yadda ƙirji n yake bugawa ba ne, matsalan a yanzu babu aure a tsakanin mu." Ya faɗa da duk ka dauriyan sa sai ta ce

"Ba aure mai ya sa?."

"Saboda ina auren ƴar uwanki kuka uwa ɗaya uba ɗaya......"

"Na gode." Tana faɗin haka ta kashe kiran tare da kashen wayan. A na shi side ɗin ya san haka zai faru, da shi har ita babu wanda ya rintsa har gari ya waye..

END.

Tab ana abu, Ke Airah ai da auren ki kuma shi A A ya mutu a kanki sosai, haka kuma Zaki ya na ƙaunar Sakeenat amma duk da haka akwai sauran ɗanɗanon First Love AIRAH 🥰..

Ko ina Rash ya ke da tawagar sa ........ Mudai je akwai tafiya fa.

Page 70.

************** *************
__________Gari na waye wa Ramlat ta koma jikin ƙofan Airah ta fara bugawa, sai ta ga ashe a buɗe ƙofar take, shiga ta yi sai ta hangeta zaune tsakiyar ɗaukin, da sassarfa ta nufe ta tana ce wa.

"Why? Ba ki yi barci ba na sa ni, Airah ya kamata kisan komai ya wuce." Ta faɗa tana da fa ta, miƙewa ta yi tsaye ta ce.

"Ya wuce, ban san a kuma magana, shike nan." Ta faɗa tana ƙaƙalo murmushi, duk da Ramlat ba ta yadda ba amma sai ta basar suka ci gaba da harkokin su amma sam jikin Airah a mace ya ke.



***************** **************
___________ Bata buƙatar tambaya ta san waye Zaki, tin a kallo ɗaya ta fahimci yana cikin damuwar da ta barshi a ciki. Bed ɗin ta hau tare da daura kanta akan cinyar sa, ta na ce wa.

"Faɗa min menene matsalan." Ta faɗa tana wasa da yatsun hannunsa, a rayuwar su babu ɓoye ɓoye dan haka bai ja dogon magana ya ce.

"Na ka sa barci, sannan Airah ta kira ni a daren jiya, shin ni na zama azzalumi kenan tinda har na cuce ta, na kasa aurenta, sam na kasa barci saboda damuwa ta ishe ni." Murmushi Sk ta saki dan ta san dawari zan cen. Sai da ta gyara kwanciya ta yadda take kallo fuskan sa ta ce.

"Babynah sam baka yaudara kowa ba, ba ka cuci ƴar uwata ba, ina so kasa wannan a ranka, a yanzu zan iya baka shafa ɗaya tak idan ka na so."

"Why not, ina jinki Jaririyatah."

"Ka sa mu kai da ita ku zauna kuyi magana ta fahimta, insha Allah itama za ta fahimta."

"A'a bazan iya kallon cikin idanun ta ba......"

"Ban sanka da tsoro ba Zaki, be a man nan." Ta faɗa da sigar wasa dan sai da ya yi murmushi, sai ta kuma ce wa.

"Idan kuma ba ta yadda ba kasan mai ya kamata ka yi?." Sai ya kaɗa kai Ita kuma ta koma ta bayan shi yadda baya iya ganinta sai ga ɗaura kanta a kafaɗar sa sannan tai maganan cikin wani salo amma iyanka a baki dan ta san waye Zaki

"Sai ka sake ni ka aur......." ta sauri ta rufe mata baki tare da ce wa.

"Kul na ƙara jin wannan maganar, akan menene zan sa ke ki."

" Baby in ba haka ba babu wata hanya ai." Da hannun sa ya sa ya zagayo da ita saitin sa sai ya ce.

"Kalla cikin idanuna ki maimaita abin da kika ce." Cikin idon ta kalla babu kyaftawa, na tsawon sec amma ba ta ce komai ba sai can ta ce.

"Karanta saƙon da kake gani a cikin wannan idanun nawa." Ba tare da ya ƙyafta ba ya ce.

" Zallar soyayyar mijinki na ke gani."

"Good, shin kaga wani tsoro a ciki."

"No, sai dai na ga fargaba kaɗan." Murmushi ta yi sai ya kuma ce wa.

"Ni fa mai kike iya gani a cikin idanuna."

"Ban iya ganin komai sai tsabar gajiya da barci, gashi ina so na sanya ka babban aiki yanzu."

"Kan ki tsaye My Queen, faɗa na cika aiki."

"Yauwa so nake ka goyani muje kitchen, sai ka haɗamin abinci bayan na ƙoshi, sai na karaka gun ƙanwata dan ni ce Yaya."

"Baby son girma koh, shike nan, hau." Babu musu ta hau sannan suka nufa kitchen....



*************** **************
________ Ko bayan ya koma gida part ɗinsa ya shiga tare da rufewa, sai Fancy ce ta faɗa ma su Maa komai da ke faruwa, sunyi sunyi da ya fito ya musu ƙarin bayani amma yaƙi fitowa, gari na waye wa suka kammala komai, Dad, Maa, Fancy da M.d suka shirya sannan suka fito da sun so su tafi suka ɗai, sai A.A ya ce shima zai je. Tam kar Airah shima haka ya kwana bai yi barci. Mota biyu suka yi sannan suka nufa gidan su Fancy.

************* *************
________ Adam ne ya kalli Spider ya ce.

"Kai posting ɗin sannan ta tabbatar komai ya yi daidai, sai kai Skiddo Oga ya ce work ɗin ka ya yi sosai, a taro tawaga zuwa gobe.

" Ba case, yanzu zan tura ma kowa saɓon." Faɗin Skiddo yana cin Shawarma.

"Allah ya saka ma Boss, har yau na rasa ta ya zan nuna godiya ta gare shi."

"Hmmm kwanda ku, nikam zan iya cewa saboda ni ya za ma RASH, dalilin iyaye na, gashi ya zama shugaban taimako, na yi imani da Allah aikin da Shuraim ya ke gaba ɗaya Nigeria babu mai kwatan sa. ina g kwanda ya fito da ainiyin sa wa muta ne dan a gyara ƙasa."

"Haka ne Adam, fatan mu da mu riƙe ƙannan sa da kyau." Skiddo ya faɗa yana kiran wata number, bugu biyu aka ɗauke sai ya ce "Gobe za a dawo bakin aiki, a faɗa ma kowa."

" Masha Allah gamu nan tafe." Daga haka ya katse kiran ya na duban Spider ya ce

" Ka dubi yadda rayuwa ta yi da mu, mu marayu ne amma Shuraim ya mana gata sosai, na yi rantsuwa da Allah babu wanda zanga zai cuce shi na tsaya sai ƙarfina ya ƙare."

"Insha Allah." Spider ya faɗa da kakkausar murya.


**************** *****************

____________ magana ce ta kai har gun Pazars, Pazar Q dan haka ya nemi da aka kira Abdullahi Ustaz da Mama Zulaikha, dan su Maa sun iso, haka Zaki da Sakeenat, sai su Ramlat da Airah, ba su jima da haɗuwa ba Mama Zulaikha suka iso. Bayan an gaisa, Pazar M ya ce

" Yanzu ba wani abu ne ya tara mu anan ba face sulhu tsakanin Ramlat ko in ce Airah da Abdullahi, dan Allah ku bani a ron hankalin ku, a yanzu dai shi Abdullahi ya na son da ki koma gidan sa tinda ba sakin ki ya yi ba, dan ku ci gaba da rayuwar ku cikin aminci." Ya faɗa yana kallon Airah wacce kowa na gun ita ya ke kallo. sai ta buɗe baki a hankali ta ce.

" Dan Allah za ku iya bani dama da na yi magana da Ya Umar cikin sirri." take fuskan A.A ta haɗe fiye da tsammanin dan yaji shine wanda zai aureta dan ya biya sadakin ta.

"Ki tambaya mijin ki dan shi ke iko da wanna." Ta ke ta maida idon nata kansa sai ta ga ya haɗe fuska, maimakon ta tambaye sa sai tace.

"Zan so na fara da kai." tana faɗin haka ta miƙe sanann ta shiga wani ɗan ɗaki daga gefan parlour, ba musu A.A ya bita, dan shima ya na so suyi magana.


A zaune ya sa me ta kan kujera dan haka ya zauna a gefan ta sannan ya ce.

" Airah......"

"Akan meye bai faɗa min gaskiya ba?, Ashe kai kanka baka san wacce ni ba amma ka zauna da ni, harda aure na, hmmmm yanzu ka sa ke ni a lalama kawai dan bazan......." Bata ƙarasa ba ya yi saurin haɗe bakin su guri guda yana zubar da kwalla, sai da yasan ta haɗiye sauran magana tukun ya cire bakin sa sannan ya riƙe hannunta ya ce.

"Airah wallahi wallahi ina sonki ina ƙaunarki, amma idan kika umarci da na sake ki zanyi, ina da kishi akan ki, ko da wasa ban yadda kifi minti uku da Umar ba." Sai ya miƙe tsaye, hannu ta sa ta riƙo hannunsa tare da kallon fuskan sa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login