Showing 39001 words to 42000 words out of 93691 words

Chapter 14 - RASH ƁOYAYYEN MASHEƘI. COMPLETE HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

219

fita cikin gidan nan ba ze bani wahala ba, sannan katangar ƙarama ce tsab zan tsallake ta be da wani tsayi, duk da akwai jami'a daya wa amma tsab zan fece."

" Hmmmm da gaske."

"Kwarai kuwa, na kwada maka ne?" Ta faɗa tana ɗaga girarta ta da ma.

"A'a bana so, na san za ki aika kin san ke WANTED ne, kuma am ba za hoton ki a ko ina."

"In dai wannan ne karka da mu zan sauya shiga ta da yadda na ke, and faɗa min me ya sa Camera ya yi yawa a gidan nan, gurin shigowa iya wanda na gani sun kai 15, sannan Parlour din nan akwai, duk saboda Gomna ne?" cikin rashin fahimta ya ce

"Cameras kuma!? Ban san waye ya sanya su ba, amma ya aka yi ki ka ga ne su?."

" Hmmmmm ba ka san wace ce SK ba akwai kwanya."

" Mayyuwa saboda tsaro aka sanya su."

" Haka ne amma har a cikin ɗaki abu mara daɗi ma, masu record ne da kansu kuma ko da yaushe suna aiki sai dai ban san ko me anfani da sola ba ne ko na nepa ne."


"Yanzu bara dai na je masallaci ina zuwa." ya miƙe yana mai nufan ƙofan ya fita, aikam yana fita ya murza keys, murmushi ta sake sananan ta shiga bedroom hijab din da matan ɗa zu suka ba ta, shi ta sanya ta yi sallan a wajen ta zauna har taji shigowan shi, amma ba ta motsa ba, shima ko da ya shigo zaman shi ya yi a Parlour yana mai tinanin yadda ze ceci ƴan uwanta. Knocking ya ji yasan su Ramlat ne dan ha ka ya ce

" Bisimillah." aikam suka buɗe suka shigo bakin su ɗauke da sallama, ya amsa yana mai sakin fuska sosai, sanann ya gaida matar Boss aikam ta amsa, zama suka yi sai Babynsa ta fara magana

"Wai mafin ka zo da kan ka kai shine ka sa mu zo, toh gamu ai, mene ne surprise din." Har ran shi yana son Ramlat sosai komai na ta na burge shi yake sai dai akwai wani yanayi dabam da ya keji akan waccan Sakeenat din wanda komai na su iri ɗaya ne harta muryansu abun ya bashi matuƙar mamaki, sai dai in ya tuna waye ALLAH da girmansa sai dai yace 'ma sha allah'.

"Gajen haƙuri, surprise din yanzu zan nu na muku." kafin su yi wata magana sai ya miƙa ya nufa Bedroom, Kifaty ita dai kallon TV take abinta, amma Babynsa da idanu ta rakasa tana mai godiya da Allah ya bata wannan amatsayin saurayi kuma nan da ɗan lokacin za su yi aure, Zaki mutum ne kyakkyawa mai duhun launi, mai faɗin ƙirji ga tsayi, tafiyarsa ma abin kallo ce. Gani take duk duniyan nan Zaki yafi kowa a wajen ta, gashi da addinin ga ilimin boko, sannan ya iya za ma da muta ne abu mai jan hankali ma shine akan aikinsa akwai riƙo da gaskiya. Sai da ya shiga ta bar kallon gurin, ita ma ta mai da Idonta ga TV.

Yana shiga ya hangeta zaune ta na tasbeehi, tana ganinsa sai ta shafa addu'an ta miƙe tare da cire hijab ɗin ta kallon sa ta yi tana mai ce wa

"Dare na yi ina son na wuce gaskiya, sannan ina neman wani taimakon ka guda ɗaya kawai."

" Faɗin kan ki tsaye."

" System nake so, kun kwashe min kayayyakin aikina wanda ƙoƙarina da hazaƙa ta na ciwosu."

"Kayan ki sunanan na a dana miki domin da su za ki yin aikin da zan saki." idanuwa ta ware tana mai jin daɗi sannan ta ce

" Na gode sosai bawan Allah, idan ka ba ni da su zanyi anfani na ce to su Kahu."

" Da gaske?."

"Eh mana."

"To yanzu dai mu je na nuna miki surprise din, na san tunda aka haife ki baki taɓa ganin wannan surprise din ba." ta ɓe baki ta yi sannan ta taƙo gabansa wanda duk taku ɗaya yana ji har ran shi, a gabansa ta tsaya sannan ta ce

"kafin nan faɗamin aikin?."

"Secret ne, ban san ko wa ya san ke ce mayyan na'urace, kullum daga 9am zuwa 5pm, za ki dinga zuwa gurin da zan miki kwatan ce."

" An gama tin da ka ce ci raina komai zan ma ka."

"Mu je." Daga haka ya fita ita ma ta bishi, ko da suka isa Parlour din, sai ya yi ma Ramlat nuni da ta ɓoye a bayansa fuskanta a haɗe dan ita ba ma'abociyar son wasa ɓa ce, ta na da dariya amma ba a gani sam saboda ɗauke fuska.

END.


𝐏𝗿𝗲𝘁𝘁𝘆 𝐒𝐊
[6/29, 19:27] sknt6428: https://chat.whatsapp.com/lqfbwo1tifs84zut6x2xs9
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rs40ab7s9ucbxw6v


💪 ᴊᴀᴊɪʀᴛᴀᴛᴛᴜ ᴡʀɪᴛᴇʀ'ꜱ ᴀꜱꜱᴏᴄɪᴀɪᴏɴ (ᴊ.ᴡ.ᴀ)💪
ʀᴜʙᴜᴛᴜ ʙᴀɪᴡᴀ ᴄᴇ ᴅᴀɢᴀ ᴀʟʟᴀʜ, ᴊᴀᴊɪʀᴛᴀᴛᴛᴜ ɴᴇ ᴋᴀᴡᴀɪ ᴋᴀɴ ɪʏᴀ ᴀᴍғᴀɴɪ ᴅᴀ ᴡᴀɴɴᴀɴ ƙᴀꜱᴀɪᴛᴀᴄᴄɪʏᴀʀ ʙᴀɪᴡᴀ ꜱᴜ ꜱᴀᴜʏᴀ ᴛᴜɴᴀɴɪɴ ᴀʟ'ᴜᴍᴍᴀ ᴄɪᴋɪɴ ꜱᴀᴜƙɪ.✍️

𝐑𝐀𝐒𝐇 ɓ𝐎𝐘𝐀𝐘𝐘𝐄𝐍 𝐌𝐀𝐒𝐇𝐄ƙ𝐈

ďăğă ăĺƙăĺăмĩм рŕĕťťŷ śķ


page 30.


" bismillah ga surprise din...." a tare suka wai go ramlat da ramlat din, shi dai sun ga mace wacce ta ɓoye a bayansa, dan ta juya fuskan ta ne.

" lafiya ta ɓoye? ohhhh ita ce surprise din wai?." sai ya ɗaga ma babynsa kai alaman eh, sai ya matsa gefe guda take fuskokin su suka yi arba da juna, ita kanta kiyaty sai da ta ɗan razana, tsakanin sakeenat da baby ramlat an rasa wayafi shiga firgici take ramlat ta zuɓe ƙasa sumamma, sakeenat kuwa kanta ta dafa a matuƙar tsora ce jitai kaman ta kurma ihu, mace tagani sak ita, tsayi, jiki, skin colour, murya, abin da ya banbanta su shine kayan jikinsu sai kuma ta lura ta fita tsoro, a lokacin ramlat ta farka bayan ta kwararta ta yayyafa mata ruwa, tana buɗe idanu sai suka ƙara haɗa ido guri ɗaya da sakeenat, a tare suka yi kan juna suka rungume dan ƙarin tabbatar wa, mamaki da almara sun cika su, sai bayan 10mnt aka samu su ka natsu, zaki har ran shi yana tinanin ko dai tweens ne, labarin juna suka ba juna, kowa kallon photocopyn sa kawai yake.

" dan allah matar boss, ta kwana a wajenki zuwa gobe za ta wu ce."

" ayya babu damuwa." daga haka suka yi sallama suka wuce, taso su shiga main parlour amma ta ce su huce kawai, suna shiga ɗakin ta ramlat ta sauka nan ita ma ta kaita, da ƙyar suka iya cin abincin daren, haka dai ta barsu ta koma na ta ɗakin tare da ɗaukan wayanta ta kira boss, kiran na katsewa sai ga na shi ya shigo, sai da ya kusa katse ta ɗauka tare da yi mai sallama, ya ko amsa,

" honey ba ka dawo ba dare na yi fa, kana ina yanzu?."

" kifaty ku kulle ko ina, sai gobe zan dawo, naje ganin doctor ne, mun haɗu amma akwai abin da zemin ne shiyasa in kuna kina so na dawo cikin dare toh."

" a'a goben ka dawo." sai da ya sassauta murya saboda har na ta muryan ya kashe mai jiki

" kisan mene ne?"

" a'a honey sai ka faɗa."

"alhamdulillah yanzu na sa mu lafiya sai ki shirya zuwa gobe dan na kai ƙarshe, zan ta wo da kazar amarci." shuru ta yi ba tace komai ba, ta ji daɗin samun lafiyansa amma ba ta shirya gobe ba sam ba ta shirya ba.

" shike nan mu kwana lafiya."

" har za ki kwanta."

"eh"

" make sure ki kulle ko ina, please." dayga haka ta kashe wayan, kallon time ta yi ta ga 10:00pm sai ta shiga contact ta lalubo meerah wanda tin tini suka yi exchanging number, kira ta yi aikuwa bugu biyu ta ɗauka da sallama sai ta mai da mata sallaman

"fatan ban tashe ki ba koh?."

" haba ina ni ina barci tin yanzu, ai sai anjima ko dan akwai abubuwan da zanyi, lafiya dai koh?."

"eh lafiya amma ƴar taimako nake so kimin kinji kuma sirri ne fatan ke kaɗai ce?." take ta ɗago daga cinyan aliyu wanda da ɗaura kanta, ta shiga bedroom sannan ta ce

" eh toh na matsa yanzu, inajin ki."

" pls sis takwara magani nake so ki taimakamin da shi."

" magani ? me ke damunki?."

" ba komai ba ra na raɗa mi ki." nan fa tayi kuskura wanda meerah ce kawai ta iya ji me ta ce, sai meerah ta yi murmushi ta na ce wa

"wai dama shine kawai, karki damu ina da su kala kala, yanzu dai yamata tin yau kifara shansu, na aiko miki guard ne kawai."

"a'a sis ba ra mu zo da ƙawata amma ta ƙofan main parlour zan shigo." daga haka suka yi sallama, sai ramlat ta miƙe ta nufi ɗakin baƙi, samun su ta yi suna hira, sai ta ce

"ramlat plsssssss sa ƙo zabki rakani na amso gurin meerah ta main parlour"

" okh." tabko zura hijab dinta dan dama ne man haɗuwa take da fatima ta gasa mata magana, sakeenat sai ta miƙe tana mai ce wa

" muje tare sis, aunty babba ki zauna kawaim" kamar ta ce a'a sai ta barsu, ta main parlour suka bi wanda babu kowa sai tv dake aiki, ita dai sakeenat abun sun ba ta mamaki ace ko ina cameras, suka zo daidai ƙafan meerah sai ramlat ta ce

" sk zanje wancan ɗakin, ki shiga ki amso saƙon sai ki jirani anan." kafin sakeenat ta ɗaga mata kai, ramlat kuma ta nufi ɗakin su fancy. knowking tayi sai aka ce 'shigo' hakan yasa tashiga kanta tsaye, tanata lura da gidan da abubuwan da ke cikin gidan, duk da gidan gomna ne amma securitys din sunyi yawa, babu kowa a tanƙamemen parlour wanda ya ƙawatu sosai, sai can wata tafito sanye da dogon hijab, a kallo ɗaya ta gane police din can ce , abu ta ba ta sai ta amsa, sai tamata sai da safe sannan ta fice. tsayawa tayi a inda ramlat tace har ta ga ta fito tana murmushi, tare suka jera ba dan sakeenat tasan meyasa ramlat din ke murmushi ba. ko da isansu part din boss, kifaty na kallonsu ta ce

" takwara kinje ɗakin su fancy ko?."

" na je amma ba gunta naje ba, gurin baby naje." ta faɗa tana za ma sannan ta ci gaba da ce wa "kema kinsan ni, naje nayi mata baƙaƙen maganganu ne da za su hanata barci."

" allah ya shiryeki dai." sakeenat dai shuru ta yi tana buga lissafi a cikin kanta. a ɗaki ɗaya suka kwanta.


end.


ďăğă ăĺƙăĺăмĩм рŕĕťťŷ śķ
✿◡‿◡✿ [sakina abdullahi] ✿◡‿◡✿.


[6/30, 09:17] sknt6428: https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

💪 ᴊᴀᴊɪʀᴛᴀᴛᴛᴜ ᴡʀɪᴛᴇʀ'ꜱ ᴀꜱꜱᴏᴄɪᴀɪᴏɴ (ᴊ.ᴡ.ᴀ)💪
ʀᴜʙᴜᴛᴜ ʙᴀɪᴡᴀ ᴄᴇ ᴅᴀɢᴀ ᴀʟʟᴀʜ, ᴊᴀᴊɪʀᴛᴀᴛᴛᴜ ɴᴇ ᴋᴀᴡᴀɪ ᴋᴀɴ ɪʏᴀ ᴀᴍғᴀɴɪ ᴅᴀ ᴡᴀɴɴᴀɴ ƙᴀꜱᴀɪᴛᴀᴄᴄɪʏᴀʀ ʙᴀɪᴡᴀ ꜱᴜ ꜱᴀᴜʏᴀ ᴛᴜɴᴀɴɪɴ ᴀʟ'ᴜᴍᴍᴀ ᴄɪᴋɪɴ ꜱᴀᴜƙɪ.✍️

𝐑𝐀𝐒𝐇 Ɓ𝐎𝐘𝐀𝐘𝐘𝐄𝐍 𝐌𝐀𝐒𝐇𝐄Ƙ𝐈


ĎĂĞĂ ĂĹƙĂĹĂМĨМ РŔĔŤŤŶ ŚĶ


✿◡‿◡✿ [Sakina Abdullahi] ✿◡‿◡✿

Page 31.

**************** ****************
Da sauri-sauri gudu-gudu ta haɗa tana shiga part dinsu tana mai zub da hawaye, ba ban Aunty ta ce ta je ta kira Zaki ba, da ba za ta sake zuwa part din shi ba, Aunty ce kawai a parlour sam ba ta lura da yadda ta shigo ba har sai da Fancy ta bige wani flawer class har ya fashe, sai ta shige part din su, da mamaki a fuskan Aunty tana mai tinanin lafiya kuwa dan wayan Zaki baya shiga ne da sunyi waya amma ta na fatan ba wani abu ya yi mata ba, ta na shiga guri guda ta samu ta zauna tana kuka mai sauti, gaba ɗayan su suka kewaye ta suna son jin ba'asin me ke damunta amma ta kasa magana dan kuka yaci ƙarfin ta, sunyi sunyi amma taƙi magana, dan haka suka barta dan ta wuce. Sai bayan kaman kusan hour sai aka musu knocking sannan Baby ta ba da izinin a shigo, tana buɗo ƙofan suka hada ido da Kandy take fuskanta ta sauya, shiga ta yi da Baby da Tweens ne kawai suka gaisa, sai Hasty ta ce

" Ƴar uwa shine sai yanzu kika leƙo mu, Tom ki kwana anan ma na."

"Ayya karki damu a can zan kwanta kinji."

" Please da kin kwanta ana ......"

" Ba mu da masaukin wannan ƴar iska anan ɗakin." Tin bayan shigowar ta ba ta furta komai ba sai yanzu, ta faɗa tana nufo Ramlat, ita kam Ramlat din jin daɗi ta yi dan an zo in da ya da ce.

" Hmmmm ke ƙaramar mara kunya ce, faɗamin arziƙin da ke cikin gidan nan na ki n ko na babank......"

" Wallahi idan ki ka zagan mana Pazars sai munci mutun cinki anan."

" Beauty bar ɓaƙar ƴar iska mana." ji tayi Ramlat ta wanke ta da mari sannan Beasty ita ma ta tsinka mata mari, take Kandy ta yo kanta a fusa ce nan ma ta wanke ta da mari sannan ta ce

" Wallahi ban ga me ta ɓani a cikin ku ba, ku fita a idona na rufe wallahi."

" Sisters ku gyaleta kun sani rainon talauci sai haƙuri." Faɗin Karis tana daga zaune abinta, har Ramlat ta juya za ta fita sai ta dawo ta matsa kusa da Fancy ta raɗa mata abu akunne sannan ta fice tana murmushi.

*************** ******************

ko da safiya ta yi misalin 9am tara na safe, Sakeenat ta shirya bayan ta ara kayan Kifaty ta sanya, sanyawa ta yi da yake dogon riga ce kuma yama Kifaty ɗan tsayi sai Sakeenat ta shanye ta, a tsaye ta yi breakfast sannan ta fice, bayan ta ce ma Ramlat za ta je har gida dan taga gidansu kuma su ƙalla ƙawan ce, dukkansu sunajin har ransu suna da dangan taka a tsakanin su.

Direct cikin wajen ta shiga in da ya yi mata kwatan ce, ta na shiga ta hangesa zauna cikin manyan kaya wanda haibarsa da kamala sun bayyana mai sosai, gaisuwa suka fa ra sanann ta ce

" Kasan menene?."

" Sai kin fa ɗa."

"Akwai wanda ke bibiyan familyn ku agani na." sai da ya gyara zama sannan ya ce

"Kamarya?." Miƙa mai ƙananun Camera ta yi ta ce

" Ga ka irin wa'innan sunfi 100 a gidanku, ina ji akwai me sa ido akan ku."

"Za mu yi wannan magana daga ba ya, yanzu zauna kifara aikin na ki." zama ta yi kan kujera sanann ya miƙa mata jakka wanda abubuwan ta ne a ciki, tana gani ta hau daɗin murna harda pi to.

"Na gode sosai Zaki, yanzu dai ina son sanin location ɗin da aka kaisu kahu." Take ya ciro wayansa da karanto mata, nan da shiga operating cikin matuƙar kwarewar daya ba Zaki mamaki, cikin ƙanƙanin lokaci ta nemo station din da kaisu amma abun da ya matuƙar ba ta mamaki shine wani babban al'amari ta gani wanda yasa zuciyarsa tsayawa cak.

END.


𝕻𝖗𝖊𝖙𝖙𝖞 𝕾𝕶
[6/30, 09:25] sknt6428: https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v


💪 ᴊᴀᴊɪʀᴛᴀᴛᴛᴜ ᴡʀɪᴛᴇʀ'ꜱ ᴀꜱꜱᴏᴄɪᴀɪᴏɴ (ᴊ.ᴡ.ᴀ)💪
ʀᴜʙᴜᴛᴜ ʙᴀɪᴡᴀ ᴄᴇ ᴅᴀɢᴀ ᴀʟʟᴀʜ, ᴊᴀᴊɪʀᴛᴀᴛᴛᴜ ɴᴇ ᴋᴀᴡᴀɪ ᴋᴀɴ ɪʏᴀ ᴀᴍғᴀɴɪ ᴅᴀ ᴡᴀɴɴᴀɴ ƙᴀꜱᴀɪᴛᴀᴄᴄɪʏᴀʀ ʙᴀɪᴡᴀ ꜱᴜ ꜱᴀᴜʏᴀ ᴛᴜɴᴀɴɪɴ ᴀʟ'ᴜᴍᴍᴀ ᴄɪᴋɪɴ ꜱᴀᴜƙɪ.✍️

𝐑𝐀𝐒𝐇 Ɓ𝐎𝐘𝐀𝐘𝐘𝐄𝐍 𝐌𝐀𝐒𝐇𝐄Ƙ𝐈

ĎĂĞĂ ĂĹƙĂĹĂМĨМ РŔĔŤŤŶ ŚĶ


✿◡‿◡✿ [Sakina Abdullahi] ✿◡‿◡✿


Part 32.

************* ***************

Tun jiya ranta ke ɓa ce, saboda kalaman da Ramlat ta yi mata a kunnuwa, a haka dai suka shirya dan zuwa makaranta, ko da suka fito Parlour sai da Mom ta tambaye ta

" Fateema me ke damunki?."

" Kaina ke ɗan ciwo." tana faɗin haka ya sa dukka su huɗu iyyaye matan na su suka zuba mata ido, ta so zuwa school amma Aunty ta ha na ta tare da ba ta magani ta sha ta kwanta, ba ita ta tashi ba sai 11am, ta yi wanka tare da fitowa, a lokacin walwala ta ɗan dawo, za ma ta yi tana kallo sai wayanta wanda ke Ringing ganin number ne ya sa taƙi ɗauka saboda umarnin Babban yaya, amma da ta ga an kira sau 6 yasa ta ɗaga tare da sallama, amsawa tayi badan tawayi muryan namijin ba.

"Nasan baki gane ni ba, ni ne Sir Muhammad Anas, M.D." yana faɗin haka ya sa ta waro ido, dan daga faɗan sunan na sa ta gano muryan sa, malamin English ne, wanda gaba ɗaya makarantan su suke ji da shi, gaye ɗan wanka, matashin mai ƙananan age, ko wacce mace so take taga ya kulata dan ko magana ya miki ranan ji za ki yi kaman an miki bushara da gidan aljanna.

" Na gane, Good morning Sir M.D"

" Morning beautiful how was your day."

" Alhamdulillah."

" Ma sha Allah ban ganki a school ba, hope everythings is 5ne?." ƙirjinta har dukan uku uku yake yi, wai Sir M.D ne ya kira ta, sai da ta kwantar da murya sannan ta ce

" I feel headache."

" Ya Allah. Sorry wishing you quick recovery beautiful."

" Thank you Sir."

" Don't worry, excuse me , I will call you letters." kafin ta ce komai ya katse kiran, da idanu ta bi wayan tana mai mamaki sosai, wai Sir M.D shine ya kirata, "Fatan ba wani abu na yi ba, Maybe na samu carryover ne a English?." Ta tambaya kanta ganin babu mai ba ta amsa yasa ta koma ɗakinsu. Tana tuna kalaman Ramlat

"Gaskiya ajin ki ya zuɓe anan, kuɗinki ya siya miki soyayyan My Asad, please adinga ka ma kai dai."

*************** ****************

Hannu ya sa ya rigo na ta hannu ganin ta yi baya kaman zata faɗin, ya riƙota amma firgici data shiga sai dai mumfashinta ya ɗauke hakan yasa ya janyota jikinsa, be wani tsaya yi mata wani abuba saboda shima yaɗan tsorata da yanayin na ta, direct yasa aka shiga da ita asibitin da ke kusa da station din, alluran barci yasa aka mata don ta samu natsuwa. komawa ya yi in da ya fito ya tattara ta kaddun gun tare da ƙara kallon abin da ya janyo mata wannan razanan, system din ne kunne wanda yake nuna wani babban guri na ci da huta, in da suka tabbatar station din da aka sanya su Kahu ne.


****************** ****************

"Labarai da ɗumi ɗumin sa, a yanzu rahota ya iso ma na, na cewa Staion ɗin (Right and peace) wanda ke burnin Abuja, Unguwan Sultan Hakimin ƙaramar hukuma, wannan station din wasu matasa ɓa ta gari sunyi daran mikiya sun cinna mai huta in da ya janzo mutuwan wannan masheƙin me suna RASH da ɗan uwansa wanda a yau ake so amiƙasu a kurkukun dake Kazaure, sannan da wasu wa'inda suke kulle, jami'an 5 suma sun ƙone da wasu iyali wanda shigansu kenan ciki dan an kama yaransu a daren jiya." matashin saurayin wande ke zaune yana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login