Showing 66001 words to 69000 words out of 93691 words

Chapter 23 - RASH ƁOYAYYEN MASHEƘI. COMPLETE HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

216

Hajiya ba za ta bari ba..."

" Ka saki matar mana." ta na faɗin haka ta katse kiran sannan ta saki shu'umin murmushi, tattara kayanta ta yi ta wuce gida. A hankali ya leƙa tagar office ɗin, motanta ya hanga ta fita a coat ɗin, miƙewa ya yi jiki ba bu ƙwari sai ya tsaya ya na mai ciro wayan sa, number da aka sanya 'Hasty' ya ƙira, bugu uku ta ɗauka ta na kai kunninta, sallama ta yi ya amsa sai ya ce.

" Hajiya Hassana mata ga yaya na Hassan, daga ke ba bu ƙari a cikin zuciyar sa." dariya ta sa ki ta na ce wa.

" Wannan duk tatsuniya ce, ya aikin?."

" Komai nomal yanzu ta wuce."

" Hmmmm da ni ta ke wasan, sai ka han zarta nan da 35mnt zai farka kuma zai buƙaci wayar sa."

" Nan da 20mnt In sha Allah za ki gan ni." da ga ha ka ya kashe kiran ya na tattara komai na yayan shi wanda yau a nan ya zauna dan wasa da hankalin Hafsat.

(Toh fa???)


****************** *****************

_______*Zaune suke a cikin parlour jikinsu duk ya mutu, sakamakon abin da suka kalla yanzu, wato manyan-manyan asibitoci goma sha biyar daga jihohi daban-daban. A daren jiya aka konasu, abin mamaki shine ko rai daya ba rasa ba, sannan a gaba daya in da aka kona an ijiye babban banner wanda ke dauke da sunan RASH.*

"*Innalillahi wa'inna ilayhi raji'un, wai wannan wani irin mugun mutum ne." fadin Hajiya sai Momcy ta ce.

"*Allah ya isar ma masu hakkin su, kinga har da Asibitin da Meerah ta haihu.*" Jimami suka din ga yi, Meerah dake kwance a sopa, ta mike cikin sauri-sauri ta shige part ɗin ta, hannun ta wanda ya sha lalle suna dan sunyi babban shagalai wanda yarinya ta ci suna Surayya, amma suna ce mata small Ammee sabo da sunan mariganya Maman su Babba yayye ne. Wayanta ta dauka ta na latso number Zaki, wanda jiya ya dawo daga Abuja.

"Umar ka ga abin da ke faruwa kuwa? " ta faɗa bayan ya ɗaga kiran.

" Eh yanzu na ke shirin fita sai Sakeenat ta ke nuna min a waya."

" Dan Allah kuyita tatara hujjoji akan komai, ina ji a jiki na akwai wani abu a ƙasa ayi bincike akan asibitocin."

" Shike nan zuwa dare zan leƙo da hujjojin." daga haka suka yi sallama.


____________ Zaki kuwa kallon Sakeenat ya yi wacce ke jiran ta ji mai zai ce,

" A tattara hujjoji sannan ya ba tun saƙon da ki ka tura."

" Okh, ya je amma no reply." ta faɗa ta na ɗaure mai igiyan kalminsa.

" Ka san kuwa asibitin da aka haifa
a small Ammee har da shi."

" Menene sunan shi.?"

" SALMA CONSULTANT CLINIC." ya jin jina kai sannan ya ta rakasa har ya shiga sabuwar motarsa, sai ta koma ɗaki, kwanciya ta yi ta ɗan yi barci kafin nan brain ɗin ta ya yi refresh sai ta hau kan na'ura.

END

𝕻𝖗𝖊𝖙𝖙𝖞 𝕾𝕶

https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

💪 ᴊᴀᴊɪʀᴛᴀᴛᴛᴜ ᴡʀɪᴛᴇʀ'ꜱ ᴀꜱꜱᴏᴄɪᴀɪᴏɴ (ᴊ.ᴡ.ᴀ)💪
ʀᴜʙᴜᴛᴜ ʙᴀɪᴡᴀ ᴄᴇ ᴅᴀɢᴀ ᴀʟʟᴀʜ, ᴊᴀᴊɪʀᴛᴀᴛᴛᴜ ɴᴇ ᴋᴀᴡᴀɪ ᴋᴀɴ ɪʏᴀ ᴀᴍғᴀɴɪ ᴅᴀ ᴡᴀɴɴᴀɴ ƙᴀꜱᴀɪᴛᴀᴄᴄɪʏᴀʀ ʙᴀɪᴡᴀ ꜱᴜ ꜱᴀᴜʏᴀ ᴛᴜɴᴀɴɪɴ ᴀʟ'ᴜᴍᴍᴀ ᴄɪᴋɪɴ ꜱᴀᴜƙɪ.✍️

𝐑𝐀𝐒𝐇 Ɓ𝐎𝐘𝐀𝐘𝐘𝐄𝐍 𝐌𝐀𝐒𝐇𝐄Ƙ𝐈

ĎĂĞĂ ĂĹƙĂĹĂМĨМ РŔĔŤŤŶ ŚĶ

✿◡‿◡✿ [Sakina Abdullahi] ✿◡‿◡✿

typing....



Page 55.

*************** ***************

"Kai ne ka aikata wannan aikin?." Ramlat ta yi tambayan ta na kallon Shuraim da ke kan kekensa, a hankali ya kalli fuskanta da babu wasa ta haɗe kaman ba ta san menene walwala ba, ya ce.

"Ohhh Kifayaty kin san Ban san tambaya koh."

" Na sani amma mai suka yi?."

" Sirri ne." da ga haka ya shiga part ɗin sa akan keken, shiru ta yi ta rasa mai ya ka mata ta yi, ganin ya fito cikin sauya kayan jikin sa sannan ya nufa ƙofan da zai sa da shi da main parlour, kafin ya sa hannu ya murɗa handle ya ji ta ce.

"Babban yaya." hakan yasa ya juya direction ɗin sa ya kalle ta, ita kam ta ci gaba da ce wa.
"Dan Allah, Rash ya bar gangan jikin ka, aikin da ka ke yi mai kyau ne, amma babu wanda ya sa ni, dan Allah ka kiyaye ba zan iya rayuwa babu kai ba, kar ka cutar min da kan ka dan Allah." Duk da nauyin cikin ta amma a haka ta tashi ta shiga bedroom ɗin ta cikin gudu-gudu murmushi ya sa ki mai tarin ma'anoni, shi ko mutuwa zai yi sai dai ya mutu amma ba zak bar wannan aikin ba, zai ma iya ciwa salon ne zai sauya zai bayyana ma kowa amma babu wanda zai iya kashe shi, amma zai rage ka sa da.


______________ Karis na ganin Baban yaya ta miƙe ɗan guduwa ɗakin su amma taku biyar ta yi ta ji wannan muryan ta sa na.

" Kiramin sauran kuzo." sai da ta haɗiye miyau sannan ya juyo ta gaishe shi amma bai amsa ba sai ta kuma ce wa

"To Baban yaya." Room ɗin ta shige, shi kuma ya tsaya a gefan kujeran da Aunty ke zaune, gaishe ta ya yi ta amsa cikin sakin fuska, sai ga Hajiya ta fito da ga part ɗin Haidar dauke da baby, amsan ta ya yi yana gaida Hajiya ta amsa sai ta shiga kitchen, da yake kowa kwarji Shuraim ke ma sa babu mai wani zaman hira da shi ko wasa da dariya, shi ɗan serious at all the time, bayan sun fito su ka zauna kallon baby ya yi wacce ke kama da ƙaninsa kuma kama da ɗan sun biyo Pazar Q ne.

"Ina kwana Yaya Shuraim." su kai gaida shi, da idanu ya bi ƙannan sa ukun wanda ya jima bai gan su ba sai yau.

" Bilƙis je ki parlour na, jikin TV stand za ki ga wani leda ki ɗauko min." ta amsa ta na nufan in da ya aiketa, ba ta dau lokaci ba ta fito ɗauke da wani leda aje mai ta yi ga ban sa sannan ta koma in da ƴan uwanta ke zaune, wayan Aunty ne ya shiga ruri dan haka ta ɗauka ta na ba su guri,

"Na ga result ɗin ku sannan jiya waec result ya fito." gaba ɗaya addu'a suke yi a cikin ransu.

" Allah yaso ku , kuma kun so kan ku, gaba ɗayan ku kunyi kokari sosai, Allah ya ƙara basira." cikin farin cikin da ya wanke fuskokin su, suka amsa da 'Ameen'.

"Karima kin ba Fadila 2 month dan haka zo ki sanya hannu a ledan ki ɗauki abu ɗaya a ciki." Da dan sauri ta matso ta sanya hannu tare da ciro wani abu da aka yi raping, sannan ya umarci Fadila da ta ɗauka sai Bilƙis, kowa kallon abin yake wanda yake kaman gift harda flower, Bilƙis na ta pick ne, Fadila Sky blue sai na Karima orange.

" Kowa ta buɗe na ga." ai kan ya gama maganan sun fara warware raping ɗin, Karima da ta riga su han zari idanuwanta ta zaro, suma haka dan sun kammala buɗewa, waya ce dukka iri ɗaya Galaxy A05, amma ko wacce da kalan jacket ɗin ta, sai Sim pack wand duk ya sanya sim ɗin, sai kuɗi rafan dubu-dubu, sun ma rasa mai za su ce da sauri duk suka ajiye suka nufesa rungumesa suka yi suna mai godiya.

"Ku karya jaririyan kunji." ya furta ya na murmushi, a ransa ya guɗira sauya rayuwar sa na gida, ya na so ya dawo kaman Haidar.

" Mun gode, Mun...."

" Kun san ban san godiya koh, In sha Allah da ga yanzu za ku ji daɗin rayuwa da ni, tin da kun dawo yadda na ke maradi, zuwa nan da 3 month za ku fara zuwa makaranta amma ba'an nan ba a Saudiyya za ku ƙarasa karatun, burin ku karatun nursing amma kun san me na ke so ku cimma?." da sauri suka amsa da "a'a" gabansa suka zauna suna mai jiran su ji abin da zai furta, sai da ya gyara kwanciyar Small Ammee sannan ya ce.
"Ina da burin na ga kun za ma malamai akan addini, so nake ku karanci Islamic, kun yi hadda kun yi already da wasu littattafan, so na ke a kaiku can kuƙara bun ƙasa karatun na ku."

" Babban yaya na amince dan ni ma zan yi alfahari da za ma na Malaman addini." faɗin Baby sai Karis ta ce " Ni ma na aminci In sha Allah za mu dage." sai suka kalli Fadila wacce bata yi magana ba,

" Idan bakya so babu dole zan iya kaiki U.S dan ki yi na ki karatun likitancin." Babban yaya ya furta sai Fadila ta ce
"A'a Babban yaya, ina so, ji na ke kaman mafarki na ke, wai da kai muke hira akan rayuwan mu." sai kuka ya kwace ma ta, sai da ya sauke a jiyan zuciya sannan ya ce.

"Na sallame ku, and ku shirya gobe za'a kaiku hutu wani gida, wata 1 za ku yi sai ku harhaɗa kayan ku." suka amsa sannan suka shige Room ɗin su, murna duk ya cika su, sun rasa ina zasu sanya ransu dan murna, har sun cire hijabs ɗin jikinsu suka mai da sannan suka fita kowa ni part sai da suka je suka nuna musu, Hajiya, Mom, Momcy, Aunty, Meerah, Ramlat sannan suka je gidan Zaki ita ma Sakeenat suka nu na mata.


***************** *************

_________ "Gaskiya Babban yaya yana ji da ƙannan sa fa." faɗin Sakeenat wacce ke kan kujera ta tsaya da duba saƙon da ya shigo ta na kallon wayoyin na su,

" Bamu number ki Aunty SK." Karanto musu ta yi suka yi saving sannan suka koma gida san su ba ta guri ganin aiki take yi, Idanu ta zaro ganin saƙon da ta tura ma 'Rash' an yi reply da 'mun gode amma ku sa ni Rash baya neman taimako gun kowa sai Allah, kuma nan da kwana biyu zai bayya ma kowa.' abin da ta gani kenan, ai babu shiri ta janyo wayarta ta kira number Zaki, bayan ya amsa ta sanar mai da reply din sannan ta ce "Akan asibito cin kuwa ko sanne da mugun aikin da ake yi a ciki, a zahiri babu wani hujja amma a baɗini akwai abubuwa da yawa, SALMA CONSULTANT CLINIC ne kawai na gano na su, akwai wasu magunguna da suke amfani da su wanda babu sa hannun Nafdac a ciki, kuma ana zargin shugaban asibitin da safaran jarirai."

"Ya-salam zan kira zuwa anjima." Kashe wayan ta yi, tana godiya ga Allah ya turo mu su Rash.

End


𝕻𝖗𝖊𝖙𝖙𝖞 𝕾𝕶

[7/13, 06:32] ᑭᖇᗴTTY ՏK ✍️✍️✍️: https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

💪 ᴊᴀᴊɪʀᴛᴀᴛᴛᴜ ᴡʀɪᴛᴇʀ'ꜱ ᴀꜱꜱᴏᴄɪᴀɪᴏɴ (ᴊ.ᴡ.ᴀ)💪
ʀᴜʙᴜᴛᴜ ʙᴀɪᴡᴀ ᴄᴇ ᴅᴀɢᴀ ᴀʟʟᴀʜ, ᴊᴀᴊɪʀᴛᴀᴛᴛᴜ ɴᴇ ᴋᴀᴡᴀɪ ᴋᴀɴ ɪʏᴀ ᴀᴍғᴀɴɪ ᴅᴀ ᴡᴀɴɴᴀɴ ƙᴀꜱᴀɪᴛᴀᴄᴄɪʏᴀʀ ʙᴀɪᴡᴀ ꜱᴜ ꜱᴀᴜʏᴀ ᴛᴜɴᴀɴɪɴ ᴀʟ'ᴜᴍᴍᴀ ᴄɪᴋɪɴ ꜱᴀᴜƙɪ.✍️

𝐑𝐀𝐒𝐇 Ɓ𝐎𝐘𝐀𝐘𝐘𝐄𝐍 𝐌𝐀𝐒𝐇𝐄Ƙ𝐈

ĎĂĞĂ ĂĹƙĂĹĂМĨМ РŔĔŤŤŶ ŚĶ

✿◡‿◡✿ [Sakina Abdullahi] ✿◡‿◡✿

typing....



Page 56.
**************** ****************
Malali

____________ Motar Hafsat ce ta yi parking a bakin get ɗin gidan su Salma, ba su san me ke faruwa ba amma sun san babu lafiya, ciki suka shiga bayan sun gaida mutane maza da mata a cikin gidan kaman ana wani taro, sai dai taron kowa ya gani yasan ba na lafiya ba ne saboda fuskokin jama'ar gurin babu annuri. Ganin mutane da yawa a part ɗin Maman Salma sai Hafsat da Halima suka shiga na Salma, Salma ce kaɗai kwance kan babban bed ɗinta, hawaye na sauka a fuskanta, ganin su Halima ya sa ta tashi ta zauna, Halima ta matsa gaban ta tare da ce wa.

"Salma me ke faruwa ne a gidan nan?." wani sabon kukan ne ya kwace mata, sai da suka rarrasheta sannan ta faɗa musu.

" Baba na ya rasu sanadiyyar accident zuwa Abuja, ɗazu aka kawo gawarsa."

"Innalillahi wa'inna ilaiyi raji'un." Hafsat da Halima suka furta a natse sai ta kuma ce wa "Kafin a faɗa mana rasuwar mun wayi gari da Asibitin Momy na ya ƙono ƙur mus." Salati suka dinga yi suna jin tausayin Salma dan mahaifi babban bango ne na rayuwar ɗa, haka jigo ne mai ƙarfi, su ma sun ɗanɗana wannan raɗaɗi.

________ A part ɗin Doctor kuwa ta suma yafi sau biyar, da ƙyar ta samu hankalin ta ya kwanta, ta rasa ina za ta sanya kanka, komai baya ma ta daɗi, a ce abu biyu a lokaci ɗaya, duk da dukiyan da ke asibitin bai da me ta ba kaman mutuwan Askira.


_______Dady da wasu manyan-manyan mutane ne cike da babban haraban gidan dan ba su jima da dawo wa kai sa makwanci, hatta His Excellent Aliyu Haidar Abdulqadir sun halacci wannan jana'izan, Dady wanda ya ke ganin abin kaman a mafarki, dan jiya sun yi sallama amma sai gawan sa aka kira yaje ya ɗauko, mutuwa ta farar ɗaya ya yi, babban mota ce ta bi ta kan tasu motan, ta ke Askira da driver su ka mutu bayan sun yi fata-fata dan ko kallo ɗaya ka musu ba za ka ƙara ba, babu abin da yafi tsorata Dady fa ce sanadiyyar tafiyar Askira, sun yi plane ne da yaje Abuja gurin wani babban boka, gashin kan His Excellent Aliyu suka ɗauka za suka kai ayi tsafi da shi..

(Allah ya kyau ta, ya kare mu da mugun ɗabi'a da mutuwa akan hanyar da bai da ce ba---- Ameen ya Allah.)


******************** ****************
ABUJA

_________ Cikin gaggawan ta gama shiryawa, a parlour ta gansa, kallan shi ta yi ta ce.

" Dear na gama." bai ce komai ba ya ɗauki trolley ya yi waje, bayan sa da ta bi da ido ta ƙare mai kallo, bayan sa tabi ta shiga mota take motan ta hau tafiya.

" I'm sorry da ɓata maka rai, ɗan......"

" It's ok, yanzu direct Kaduna za mu je, kin ga ke kinyi barci, nima ki bari na yi yanzu."

"Okh." ta furta ta na sakin murmushi dan ta na jin wani sanyi a ranta, ba ta san mai ya sa ba amma har ga Allah ta na jin wani irin abu haka a cikin jikinta tin da suka shigo Nigeria a jiya.

**************** ****************
KK GRA

_________ 9:23pm, babu wanda ya tan kasa, kira na 8 kenan amma ba ta shiga number, Hasty ce ta ƙalla Husty sai ta yi ma ta alama da ido, take ta miƙe ta shiga part ɗin ta, kunna wayarta tayi tana zama kan sopa, take wayar ta hau ringing sai da ta saki shu'umin murmushi sannan ta ɗauka.

" Alhamdulillah." Yusuf ya faɗa da ƙarfi dan jin babynsa ta ɗau kiran, zama ya yi gefan Hajiya ya na ce wa, "Hajiya ta ɗauka ta ɗauka, Assalamu alaikum." Hasty da abu biyu ya haɗe mata dariya da kishi, ta na dariyan tarkon da suka yi mai sannan kishin kuma ta na tinanin ashe haka ya ke ma waccan ƴar iskan wato Barrister Hafsat.

" Yusuf." yaji ta furta, duk da number ta ce sai da ya kuma kallo sa bo da jin muryan kaman ba na ta ba.

"Mai ya sa mi voice na ki.?"

" Mura na ke yi." Hasty ta furta ta na gyara kwanciyar ta akan sopa tare da rage murya.

" Okh, ya kike ya yau?." Ya furta har jikin sa ya na rawa.

" Am fine what of you?."

" Steady, yanzu kin ganni kusa da Hajiya, dan Allah ki gaidata kin ji, kuma ki roƙe ta na aure ki kin...."

" Wait Yusuf, kasan mene ne?."

" A'a Queen, in ba za ki iya gaida ta ba babu damuwa kinji." ya furta da dukkanin gaskiyar sa, ba Hasty ba haryta Hajiya, Husty da Yunus sunji mamakin abin da ya faɗa.

"Ni zan ce ma wannan matar dalla gyaleni da maganar ka ba dai ka na so na ba."

" Sosai ma, wallahi i love you."

"Ina son gobe da kai da matar ka kuje Saudiyya, so nake ko izu 30 ka haddace a kan ka sai mu yi aure."

"Hadda kuma, ai na hadda ce Alqur'ani." Husty ta dai-dai kan ta sannan ta kuma magana.

" Eh na sani so nake ka dawo farko, kuma da wa su takaddun, zuwa lokacin sai muyi aure abin mu."

" Hakan ya miki."

" Sosai ma."

" An gama gobe zan tafi."

" So nake in kaje karka ƙirani har sai randa ka dawo, so na ke ka dawo Shaikh."

"Hajiya kin jifa, na faɗa miki ustaziya ce." ya kai nan ya na mai da wayan kunne, Hajiya dai dai ganin ikon Allah suke.

" Ka tafi da Hajiya maybe before ku dawo ta so ni."

" Insha Allah, sai dai ba zan iya tafiya gobe ba in ban gan ki ba." ta ke zuciyar Hasty ta buƙa sai dai jin abin da Husty ta ce ya yi ma ta daɗi dan wayan a speaker ya sanya

"Aure na ko gani na wanne kafi so?."

"Auran ki."

" Fine, good bye." daga ha ka ta katse kiran, jingina kansa ya yi jikin kujera ya na dafa kan na shi sai ya ce " Hajiya ina son Hafsat, bazan iya saɓa ma umarnin ta ba, gobe zamu je saudiyya, zanyi ma wani abokina waya yanzu da ya shirya min komai." Babu wanda ya tan kasa har ya gama, sannan ya miƙe ya shiga part ɗin su, da Idanu suke kallon juna, Hajiya har ranta ta kejin babu yadda za ta yadda ya aura yarinyar da ya ke so, ti na abin da Malam Zakari mai maganin Hausa da yazo ɗa zu ya ce musu "Sihiri ne ya ke wayo a gangan jikin sa, idan kuna neman lafiyansa to abu uku za kuyi Insha Allah komai zai yi dai-dai, na farko, a yi ne sa da shi, yadda karma su haɗu da wacce ta yi sihrin, na biyu ya yawaita karatun Alqur'ani da wasu Addu'oin, na ƙarshe shine ruwan zam-zam, kullum a dinga mai addu'a a ciki sai ya sha, babban matsalan ba musan da mene ne aka yi sihirin ba amma insha Allah in ku kayi yadda na ce za'a dace..'

" Hajiya gobe sai ta fiya, dama na gama shirya kayan ki, idan da akwai wasu abu da kike so sai ki faɗa." Hasty ta faɗa cikin sanyin hali sai Hajiya ta ce.

" Ban san na ga kin shiga damuwa, zo." tayi mata alama da hannu, miƙewa ta yi ta nufa sai ta rungume ta, take kuka ya kwace ma ta, Hajiya ba ta rarrashe ta har ta gaji da kukan dan kanta, sai da ta yi yadda ta ke so tukun ta yi shuru, Husty ta yi tsaye

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login