Showing 24001 words to 27000 words out of 93691 words

Chapter 9 - RASH ƁOYAYYEN MASHEƘI. COMPLETE HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

222

suka gaji kafin nan kowa ya kwanta tana mai da nunfashi.

"Da kunyi addu'a dan wlh ba ni kaɗai ta ce ba dukkan mayan nan." Kandy ta faɗa ta na nuna, Beauty,Besty,Hasty, Fancy,da Husty.

" Kina ruwa mu na wa muke toh ai sai dai ku uku banda mu koh Hassana"

" Dena ɓata miyan bakinki Husty mu muna nan ai"

" Kaji wani zan ce, wai har da ni gaskiya Kandy ni ma kin ce wani abu." cewa Fancy ta faɗa ta na miƙewa da ga kwanciyar

" Ai gaskiya ce ko Karis."

" Haka ne Kandytah, mu na mu shagali koh Baby da butter."

" Dama-dama a ce lokacin Boss baya nan, wallahi ni kai na sai na haɗa na wa shagalin na biki dan classmates dina duk zan gayyata muje special hole hmmmm."

" Butter mutumin da ya yi aure ina shi ina barin nan."

" Haka ne fa balle ma an haɗa shi da me ƙashin tsiya"

" Bansan meyasa Pazar Q yamana haka ba, Babban yaya da yake da matsayi sosai, gashi da kyau duk da ya na da na kasa amma dole akwai wa'inda suka son shi kuma ma su dukiya, kalli dai matar Uncle, jami'ace gasu da kuɗi...." Hasty ta katse Fancy da ce wa

" Toh me zeyi da kuɗi shi? nifa matar tana burgeni sosai ba ta da damuwa." ta ke Baby ta amshe zancen

"Naga dai talauci da arziƙi duk na Allah ne, ku daina izgili babu kyau sa...."

" To uwar wa'azi ko na kowa miki speaker ne?."

" Karis ai gaskiya na faɗa da ki yadda ko karki yadda ya rage naku." daganan suka bar maganan dukkansu.


END

Daga alƙalamim Sasakeeee (Pretty Sk)

[6/14, 07:13] ᑭᖇᗴTTY ՏK ✍️✍️✍️: https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

💪 JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIAION (J.W.A)💪
Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi.✍️

𝐑𝐀𝐒𝐇 Ɓ𝐎𝐘𝐀𝐘𝐘𝐄𝐍 𝐌𝐀𝐒𝐇𝐄Ƙ𝐈
ᑭᖇᗴTTY ՏK
ꜱᴀᴋɪɴᴀ ᴀʙᴅᴜʟʟᴀʜɪ

Page 17

****************** ****************

Gari na wayewa ta yi wani miƙa a kan katifarta wanda yanzu ita kaɗai ke kwanci a kai, aiki ta fara yi ta na gamawa ta yii wanka har lokacin Maman Rabi ba ta fito ba, ɗaki ta koma ta ɗauki wayarta ta na karanta Novel me suna DAGA INA TAKE by Pretty sk, a haka ta wuni a kan wayarta ƙiran Tecno A31, kusan wuni ta yi a haka aiki kaɗai ke fito da ita daga ɗaki, basa wani hira yanzu da Maman Rabi kowa harkan gabansa yake yi, ita duk da ta ƙosa Babanta ya samo mata makarantan da za ta koma ko waec ta yi. Misalin 7pm bayan ta idar da sallan magrib ta jiyo sallaman ƙawarta kaman a mafarki, da sassarfa ta nufi compound din aikuwa suka yi kicibis da takwararta cikin nishaɗi suka rungume juna suna mai jin daɗin ganinta, ɗakinsu suka shiga suna hiran yaushe gamo.

" Naji daɗin ganinki, shi to ba zai shigo bake nan?. "

" Eh ai gidanmu kaɗai ya shiga ya gaida su Abbuu, yanzu wai zaije ya dawo yabani minti 30 kawai."

" Allah sarki aiko ya kyauta ki ce har gidan Zainab kika je."

" Ai kuwa, ha ba takwara kibar abincin a ƙoshe na ke." harara ta watsa mata ta na ce wa ta re da ci ga ba da zuba abincin

" Ai nasan bakya son cikin abin gidan nan, alright karna ba ki guba koh." jin haka sai jikinta ya yi sanyi dama sun saba kullu in ta zo sai ha ka ta faru da su, ci ta yi ba sosai ba dan a ƙoshe take, hira suka sha da ga bi sani ta shiga ta gaida Maman Rabi wace yau zazzaɓi ke dukanta. Lokacin ya na cika ya ko kira ta a sabuwar wayan daya siyo mata jiya da amma ɗazu da safe ya ba ta, sallama suka yi a kan ya ka mata ta zo ta yi mata one week, har bakin motan ta rakata suka gaisa da Shuraim ya amsa cikin walwala. ta na komawa ledan da ta kawo mata ta buɗe dan ganin menene a ciki. Babban leda ne baƙi budewa ta yi nan fa ta fara tozali da abubuwan ci iri-iri madara, sugar, millo, bread, egg, dasu sweet da biscuit sai wani ledan daban, tana buɗewa ta ga tsohon wayarta ne ta re da paper, tabbas ta ga sabuwar wayarta har ta yi mata Allah ya sanya alkairi, paper din ya buɗe ta fars karanta wa tinda da Hausa a kayi rubutun

" Sis na gyara wayan sai ki riƙe babu abin da zanyi da shi, ba ta da matsalan komai, kiyi manage please kinsan bana son godiya koh, karki kirani akan wannan ɗan abun. Ina miki fatan alheri sai ki buɗe WhatsApp tin da dama wayanki bata yi kinga kullum muna online zan dinga turo miki data lokaci bayan lokaci." Hawaye ne ya zubo a idanuwanta tasan ƙawarta ta a kwai kyauta dan ko a da ba ta zuwa haka nan. jita yi ta ƙara ƙaunarta fiye da misali, ta san ko ta kirata ba za ta ɗaga ba dan haka ta tattara komai ta kaiwa Maman Rabi ta gani, cikin jin daɗi ta amsa ta a dana, ɗakinta ta koma taci gaba da godema Allah a kan abin da ƙawarta ta yi mata, da yi matan fatan samun rabo nan kusa, da farin ciki a rayuwar auran su.


************* **************

Ta ra da ina za ta sa ka kanta dan murna, satan kallon shi ta yi, waya yake yi kuma hankalin sa nakan System dinsa dan ko ina ya na tare dashi, a dai-dai nan Adam ya shiga Babban get dinsu dan shi ne ya yi driving dinsu. parking lot ya nu fa ya yi parking, sannan ta fita ba ta jira shi ba ta san masjeed se shiga dan an kira Sallan isha'i, aikuwa ta shiga Main parlour dan gaida su Momcy dan zuwa yanzu duk sun sa ba sosai harda Meerah dan ma ita ba ta wani zama saboda aiki. da sallama ta shiga cikin, samu ta yi dukkansu ƴan matan suna hira kwanin sha'awa. Twees da Baby ne kaɗai su ka gaisheta ta amsa ta na za ma a ɗaya daga cikin kujerun parlour, Kandy ta zabura ta miƙe ta na ce wa

" Talauci masifa ne, Allah ya shiga tsakanin mu dashi."

" Ameen dai." Beasty ta furta ta na taunar chewing gum, in da sabo ta saba da iskancin muta ne biyar dan duk zuwa yanzu duk ta shedasu, ita dai Butter ba ta wani yi mata iskan ci amma ta na team ɗin su, murmushin yaƙe ta yi sannan ta miƙe ta zo dai-dai gaban Kandy ta ce

"Hmmmmmm na lura ƙaramin hauka na daminki, dubeni da kyau babu talauci a jikina, idan kuma ni ce bakya so ki ce ma Shuraim din ya sakeni, so what, shi na ke aure ba ke ba, kuma zanyi maganin ku ba ra ya shigo." kowa na wajan shuru ya yi, ba su zaci za ta iya mai da martani ba, Meerah wacce ke fitowa daga Part ɗinta, ta ji abin da Ramlat ta faɗa kuma ta gano in da zance ya ke, tun kafin ta ƙaraso ranta ya ɓaci, buɗa baki ta yi da zafi-zafi ta ce

"Khadija hauka kike yi, me kika sha kike faɗa ma matar yayanki baƙaƙen magana."

" Ki barta so ta ke ta zubar manna da mutumci to yanzu Pazars za su shigo kuma yau sai a tantan ce." faɗin Aunty wacce ta fito daga kitchen, ta ke suka ji sallama dukkan su Pazars din harda Shuraim, suna isowa Pazar M ya tambayi ba'asin me ke faruwa, take Husty ta fa ra koro bayani har ta dire, wani irin kallo Pazar B da ya yi mata yasa ta ɗan ɗauke nunfashinta na seconni kuma ta dabur ce.

"Yayana shin kana sona ko baka sona? duk da ni ɗin ƴar talakawa ce, mara dukiya." Ramlat ta faɗa ta na kallon Shuraim wanda ranshi ya yi matuƙar ɓa ci

" Hmmmmm wallahi Kifayaty, ina sonki fiye da tinaninki, ke ma kinsan haka dan ha ka kowa ma ya sheda hakan. Ki yaƙuri da abin da ta miki." har cikin ranta ta ji daɗi dan haka ta kalli Kandy ta ce

" To kinji dai ya na son ƴan talakawa a haka, dan haka ki fita a idanuna nasan kin girmeni amma yayarki na ke a yanzu, ina da shuru-shuru amma idan aka kai ni bango banda kyau sam hmmmmm." ta nuna ma ta yatsa alaman warning ta re da sauran mata biyar ɗin, Juyowa ta yi ta gaida su Pazars sannan ta tura keken sa har bakin ƙofansu sai ya buɗe ba ki ya ce

"Kubiyo ni yanzu." daram zuciyar Khadija ta buga da sauran dan ita ba tai tsammanin za su shigo a wannan lokacin ba, sun sani yau za ta ci ubanta a kunsa harda su koda babu ruwan su, bayan shi suka bi Pazars Q ya na ce wa

" Kwanda ya yi maganinku marasa kunya kaji wani banzan zance, yara dai ta da shirme, Allah ya shirya mana ku."

"Ameen, ai ya ga ma su zo na musu nawa.' faɗin Pazars R, ƙara sawa suka yi suka zauna anan ne sauran matan suka fito dan ba suji wani hayaniya ba.

Suna shiga parlour din suka ga Shuraim ne kawai ya na zaune, ƙarasawa in da ke suka yi, cikin ladabi suka tsugunna a ƙasa suna facing na shi, ya ma rasa ta ina ze fara hukun ta su dan haka ya kira Ramlat tako fito bayan ta ajiye hijab dinta har tayi alwala.

" Yallaɓai gani."

" Me ya da ce na musu?." sai da ta saki murmushi sannan ta ce

"A musu haƙuri, idan kuma wata tasake ni na ishesu kasan kuwa yadda na iya rigima? Kawai ban san hayani ya ne amma Ramlat na ke fa."

" Hmmmmmmm."

" Kabarsu amma ka musu warning dan wallahi duk wacce ta kuma min haka sai na ji ma ta ciwo, kuma in nuna mata banbancin talauci da dukiya, Allah na tuba, hausawa suka ce kafini gidan uban na fiki gidan miji, waya sani sai ka ga wata a ciki Allah ya kaita gidan da babu duk da bana muku fata domin ku ƴan uwan na ne."

" Maganar haka yanke Shike nan Queen."

" Bara na yi sallah zan musu lecture me zafi, suma su ɗauko hijab suyi anan sai na musu wani karatu akan talauci da arziƙi."

" An gama, Baby ɗauko muku hijabs" miƙewa ta yi ta fice tanabjin daɗi dan ita Aunty Ramlat na burgeta, bayan ta ɗauko ta dawo ganin babu kowa a parlourn ya sa tanemi ɗakin da suka shiga, can ta shiga wani babban Bedroom, a nan ta sa mu wasu sunyi alwala, ta re suka yi sallan sannan suka zauna Fancy ta na ce wa

"Kandy kin janama raini agunta yanzu."

" Uhmmm mu kuma mana shuru ha ba, kubarmu muji da ɗaya mana." Husty ta furta sai sukaji sallaman Ramlat sannan ta ce su fito. Kaman kar wasu su motsa amma ha ka suka fito, a parlourn suka zauna dukkansu a ƙasa sannan Ramlat ta fara huɗuba cikin kwarewa, hadisai ta dinga kawo musu masu ratsa zuciya, amma a banza dan su Fancy haushinta suka ƙara ji.

"Aunty Ramlat please zan dinga zuwa ɗaukan karatu."

" Baby ni ma gaskiya harda ni" cewan Hasty, sannan Husty ita ma ta ce

" Gaskiya nima haka."

" Karku damu zan sa muku lokaci." take sukaji jiniyan motoci sun fara shigowa gidan nabsu, sunsan Aliyu ne dan zuwa yanzu cikin tsaro suke, saboda jami'an tsaro ta ko ina, sallaman su Ramlat ta yi suka fice.



Shigowa ya yi bayan jami'an shi sun mai rakiya har bakin ƙofan nasu, Hajiya da Momcy kawai ya samu dan haka ya gaishesu sannan ya shigw part dinsa, samunta yanyi tana kallo a TV, da sauri ta miƙa ta rungumesa ta na ce wa

" Barka da zuwa."

" Yauwa ya gidan."

"Alhamdulillah." daga haka ta rakashi ya shiga toilet danyin wanka.



****** suna fita Ramlat ta zame ta kwanta akan cinyar Shuraim wanda fitowan shi kenan ya zauna a gefenta.

"Zawjin baby cikina yamin zafi." ya najin daɗin sunan nan, cikin na ta ya kalla wanda yabke cikin hijab a shafe ya ce

"Meyasa ba ki faɗamin ɗa zu ba har muka dawo gida sai kitashi muje asibiti koh."

"A'a ba sai munje ba ze dena." ta faɗa Idonta a rufe sai ɗan hawaye yake gangarowa. sharewa ya yi da yatsan shi ya ce

"Kamar ya ba sai munje ba ko kin zama doctor ne?."

" Uhmmmmm ze dena kawai."

" How ko p.d ne. "

"No, abu ne nasha ɗazu....." sai ta yi shuru

"Me kenan kuma a ina?." gyara kwanciyar ta yi ta na canza hiran

"Baby me ya sa mi ƙafarka ne naji an ce lafiya aka haifeka kuma kaman shekarun ba ya ne hakan ya same ka."

"Uhmm Kifaty, Wata rana ne naje SIDI AND SONs Ina tafiya akan step ashe an yadda banana shell aikuwa na ta ka shine na zame na faɗo, kinsan ko ina tiles ne na bugu sosai dan tin daga saman haka na faɗin har ƙasa, Direct sai asibiti da ƙyar na farfaɗo, sai dai me anyi-anyi ƙafar ta hagu ta motsa amma ina, sam babu sa'a abu kaman wasa sai nakasa tafiya., naje country's dayawa amma babu sa'a at the end na haƙura kawai." jikinta sai taji ya mutu sosai, a hankali ta ce

" Ina mai baka haƙuri kaji, Allah yasa ya warke." wayan shine yaɗau ƙara ganin number dake kira yasa yasaki ɗan murmushi mai sanyi, wayan na katsewa saƙo ya shigo ya ko buɗe ganin me aka turo yasa farin cikinsa ya ƙara faɗaɗa, juyowa ta yi takallesa ta ce

" Baby wannan murmushin fa ?."

"Na samu aiki and gobe zanfara zuwa." murmushi ita ta yi tana hamdala, sai kuma ta ruƙo hannusa da ƙarfi jin cikin na ta ya karta, jita yi ya ƙulle sosai hakan yasa ta da burce, ya na ta mata sannu har ya la fa. ya dinga roƙonta suje asibiti ta ƙi, ɗakinta suka je ta kwanta kan bed ta na riƙe da hannunsa sannan ya ce

" Me kika sha?."

"Da na je gidan Zee ne ta ɓani wani abu kaman tamarin juice aikuwa nasha shinefa kawai."

" Juice ne ko mene ?."

" Na sha juice ne amma wai maganin ne."

" Maganin mene?" Shuru babu amsa sai da ya maimaita mata tukun ta ce

" Maganin sanyi ne."

" ban yadda ba, ƙarya ba ta miki kyau ina jinki."

" Uhmmm uhmmmm wai na matan aure ne fa kawai." ya gano zancan dan haka ya jingina kansa a jikin bed din ya na furzar da iska a bakinsa.

" Shikenan ki shirya yau zan biyaki haƙƙinki, ɗaukan alhakin ya isa haka." ya na kaiwa nan ya koma kan kekensa ya fice da ido ta bishi har ya fice, dariya ce ta kwace mata.

" Ashe na iya acting, wow a ta famin gaskiya." sai kuma jikinta ya yi sanyi da sauri ta miƙa ta sama ƙofan key ta ma dariya ta kwanta dama ta gaji barci kuwa ya yi gaba da ita.
END
Daga alƙalamin pretty SK✍️✍️
[6/14, 22:35] ᑭᖇᗴTTY ՏK ✍️✍️✍️: https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

💪 JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIAION (J.W.A)💪
Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi.✍️

𝐑𝐀𝐒𝐇 Ɓ𝐎𝐘𝐀𝐘𝐘𝐄𝐍 𝐌𝐀𝐒𝐇𝐄Ƙ𝐈
ᑭᖇᗴTTY ՏK
ꜱᴀᴋɪɴᴀ ᴀʙᴅᴜʟʟᴀʜɪ



page 18

************* **************
Zip ta zuge da ƙyar harda nishi, Wow ma sha Allah da ta kalli kanta a mirrow ɗinkin ya zauna tsam-tsam ya bi ko wani rami, tudu, lungu da kwari ya yi ɗas, ita kanta tasan manyan kaya su na ma ta mahaukacin kyau kawai ba ta son sa wa ne tafi so wando abin ta da riga. flat shoe ta sa ta nufa Parlour, in da yake zaune ta nufa ta na takunnan na ta kaman macen ɗawisu, tin kafin ya kalleta ya san ta haɗu, idanuwansa ya buɗe a hankali ya kalli yadda ta tsaya a gabansa, fuskan babu kwalliya amma ta yi kyau leshi ne ya ƙarbi fatarta, bakinnan na ta turoshi alaman rigima ta keji, matsar da abubuwan gaban shi ya yi ya miƙa mata hannu, kaman ba za ta kama ba sai dai ta kama aiko ya janyota ta faɗo mai ajiki

" Ma sha Allah OMRY kin yi kyau sosai."

" To ba ra na je na cire koh ai ka gani."

" Ai da ga yau ni dai kalan shigan nan nake so kidinga min in kin dawo aiki."

" Uhm Farsi a'a gaskiya ni dai damuna suke yi, kuma duk sun matseni sosai."

"A haka nake so." tin ɗazu ta ke jin barci amma ya ha nata wai sai ta yi mai kwalliya da manyan kaya, babu shiri ta yi amma ya sha ƙunƙunai kala-kala.

"Shi ke nan tinda bakya son abin da nake so jeki cire kawai na gode."

" A'a uhmmm uhmmmmm uhmm, zan dinga ma ka ba bu damuwa, I'm sorry." Murmushi ya yi sannan daga ha ka suka sha soyayyansu abin du.


***** ɓangaren Shuraim kuwa ko da ya shiga ɗakinsa, wanka ya yi yana tinanin yadda ze yi da Ramlat, koma wa ya yi jin ƙofan a kulle ya yi murmushi sannan ya koma na sa ɗakin ya kulle da keys guda biyar, ya sa sakata sannan ya kunna haske ɗakin madaidaici, a hankali ya sauke ƙafafunsa akan makeken carpet din da ya maƙale ƙasan ɗakin, cak ya miƙe tsaye da wannan ƙafafun na sa, ya tsaya ba tare da jin gina da komai ba, amma be ta ka ba, ɓalle butura rigansa ya yi, uay aje a gefe mirrow, ta ku ya farayi da ƙafan hagu wacce ita ce me ciwon kallon mudubin ɗakin ya yi ya na kallon irin halittan jikin da Allah ya yi mai jikinsa a murɗe ta ke, gashi da faɗin sosai, sak dai masu ɗaga ƙarfe, ta ku uku ya yi ya ɗauki yawan shi ya latsa number ɗa zu bugu biyu aka ɗauka, cikin kakkausar muryan wanda ɓantaɓa jin ya yi magana da shi ba ya ce "ku tawo yanzu." sannan ya katse kiran, close set ya nufa ya buɗe sai ga uban kayan sa wa, wa'inda suke a gare, hannu ya sa ya janye kayan ta ke bayan close set din ya bayyan cikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login