Showing 69001 words to 72000 words out of 93691 words

Chapter 24 - RASH ƁOYAYYEN MASHEƘI. COMPLETE HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

228

da ga gyefan Hajiya tana sauran kukan Hasty wanda ya ke karya mata zuciya sannan ta ce.

" Hasty ki yi haƙuri, daɗin abin munyi maganin komai cikin sauƙi." ta kai nan tana murmushi dan ti na ɗazu da suka sanya number ta a wanyan Yusuf sannan suka yi saving kaman yadda ya yi na Barrister Hafsat, sai sukai deleting bayan sun yi blocking ɗin ta.

" Yanzu Sim ɗin sa kawai ya rage na cire na ba Husain, bara na duba shi." da ga haka ta miƙa ta shiga part ɗin su, sauke a jiyan zuciya Hajiya ta yi tana mai ce wa.

" Koma wace ce Hafsat ɗin nan, ba yarin yar aure ba ce sam."

" Gaskiya kam, abin haushin ba ta biyo hanya mai kyau ba....."

" Wallahi Husaina ba yadda ma zan bari Yusuf ya yi ma Hassana kishiya yanzu, ba ta yadda zan yadda."

" Allah ya sa mu dace, yanzu Hajiya mu kaɗai za ku bari?." Faɗin Husty sai Hajiya ta ce.

" Eh mana, ko dan wan can ƴar iskan dole ku tsaya dan Yunus ya koya mata darasi."

End

𝕻𝖗𝖊𝖙𝖙𝖞 𝕾𝕶
[7/13, 12:13] ᑭᖇᗴTTY ՏK ✍️✍️✍️: https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

💪 ᴊᴀᴊɪʀᴛᴀᴛᴛᴜ ᴡʀɪᴛᴇʀ'ꜱ ᴀꜱꜱᴏᴄɪᴀɪᴏɴ (ᴊ.ᴡ.ᴀ)💪
ʀᴜʙᴜᴛᴜ ʙᴀɪᴡᴀ ᴄᴇ ᴅᴀɢᴀ ᴀʟʟᴀʜ, ᴊᴀᴊɪʀᴛᴀᴛᴛᴜ ɴᴇ ᴋᴀᴡᴀɪ ᴋᴀɴ ɪʏᴀ ᴀᴍғᴀɴɪ ᴅᴀ ᴡᴀɴɴᴀɴ ƙᴀꜱᴀɪᴛᴀᴄᴄɪʏᴀʀ ʙᴀɪᴡᴀ ꜱᴜ ꜱᴀᴜʏᴀ ᴛᴜɴᴀɴɪɴ ᴀʟ'ᴜᴍᴍᴀ ᴄɪᴋɪɴ ꜱᴀᴜƙɪ.✍️

𝐑𝐀𝐒𝐇 Ɓ𝐎𝐘𝐀𝐘𝐘𝐄𝐍 𝐌𝐀𝐒𝐇𝐄Ƙ𝐈

ĎĂĞĂ ĂĹƙĂĹĂМĨМ РŔĔŤŤŶ ŚĶ

✿◡‿◡✿ [Sakina Abdullahi] ✿◡‿◡✿

typing....



Page 57.
********************** *******************
Malali

" Hafsat ki ba ni key ɗin motar ki, ku bi Dady zuwa gida ni anan zan kwana." Maa ta faɗa cikin sanyin jiki sai Halima ta ce.

" Ni ma anan zan kwana saboda na ɗauke ma Salma kewa, Hafsat ta tafi kawai."

" A'a gobe ma wuce duk kan kawai." Hafsat ta faɗa ta na gyara zaman ta, sai Maa ta kuma ce wa.

" Shike nan ba ra na ce ya tafi, ku fito kuci abinci toh." da kai Halima ta ɗaga, sai Maa ta fita, Salma da ta fito wanka ɗaure da towel sai mayafi ta ce.

" Gaskiya na ji daɗi, ni har gobe ba zan bari Halima ki ta fi ba."

" To mai zan miki anan ɗin.?"

" Kawai dai, kin san kaf familyn mu banda ƙawa, gidan nan gaba ɗaya babu age mate ɗin na kinga."

" Gaskiya ko sati ɗaya ta miki, gobe sai ta yi ma Maa magana." Hafsah ta furta ta na kuma mai kira na biyar amma duk abu ɗaya ya ke ce wa, an yi blocking ɗin ta.


****************** *******************
Air Force Base

___________ Da ikon Allah ya isa gida, dan har yanzu mutuwan bai wani sa ke sa ba, parlour ya shiga bayan ya fito daga motan, babu kowa kamar yadda ya yi tsammani, Room ɗin sa ya shiga bayan ya yi wanka ya fito dan samun abin da zai ci, a kitchen ya samu Fancy sai ya ce ta kawo mai abinci, takaici ya sa ta kasa magana sai Indomie ta samu ta yi mai ta kai mai parlour.

" Dady Ina su Halima?." Fancy ta tambaya ta na jiran ya ce ga in da suke ta bi bayan su.

" Suna gidan rasuwa, sai gobe zasu da wo."

" Waye ya rasu?." M.d ya furta bayan ya gama sauka da ga stairs.

" Askira." kusan suman tsaye M.d ya yi ya na mai ƙara furta sunan 'Askira', Dad ya ɗago idanunsa ya yaƙara tabbatar mai da 'eh', salati M.d ya shiga yi a fili, Dad ya bashi labarin komai, mutuwar ta bigesa sosai hatta Fatima wacce ba ta san waye ba amma ta ji mutuwar.

" Allah ya jiƙan sa, na za ci sun dawo ne dan na kammala girki, na shiga yanzu na ga babu duk ka flask ɗin."

" Babu! to wa ya ɗauka, ko dai kin manta ne?." M.d ya yi maganan ya na kallon Fancy sai ta ce.

" Haba da hannuna na zuba amma kafin na dawo na ga babu, na za ci sune ai, ka duba......"

" Wait.. kodai an shigo gidan ne?."

" Dad sai a rasa mai za'a ɗauka sai Abinci, kawai ki sake du bawa dai." ta kaici ya sa Fancy ta yi shuru sai suka ji magana kaman daga sama, cikin zazzaƙan muryar sa da lafazi

" I'm sorry ban san na ki ba ne, ni na ɗauka." gaba ɗayan su kallon sa suke yi cikin mamakin yaushe ya shigo gidan, a hankali ya sauka ya na gyara agogon hannun sa.

" A.A yaushe ka dawo?."
.
" Dama surprise zan muku, ɗazu na shigo, bro na ga kayi ƙiba ne." Murmushi M.d ya yi ya ce.

" Gaskiya da ka faɗa mana mu tarbeka sosai, kai ne ai kayi ƙi ba sosai."

" Ina wuhi Dad." Ba Dad ka ɗai ba harta M.d sai da ya ware idanu, wai A.A ne ke gaishe da Dad yau.

"Me naji ka ce A.A?." Dad da yake jin kaman ƙunnuwan sa sun yi mai ƙarya ya tambaya sai A.A ya riƙon hannun Dad ya ce.

" A.A ɗin da, daban da ne da na yanzu, Dad na sauya fiye da tinanin ku, na dawo yadda zaku yi alfahari da ni." Dad rungume Auta ya yi ya na zubar da kwalla mai tarin ma'anoni masu yawa, A.A wai shine ya ke mai magani cikin taushi da na daman abubuwan da yake mai, M.d ma hawaye ya share ya na jin dama Maa suna nan ya san sai tafi kowa farin ciki. a hankali ya raba jikinsa da na Dad ya sa hannun sa ya share hawayen da ke zu daga idanun Dad.

" Ban san kana zubar da kwalla kaji." sai ya kalli Fancy wacce ke kallon sa, murmushi ya sakar mata ya kuma ce wa. "Amaryar mu ce?."

" Ina wuni." Fancy ta furta duk da tana jin haushin kwashe mata flask da ya yi ɗan lafiyayyen girki ta yi.

" Ai in na amsa na yi rashin kunya kina matar yayana ai ni zan gaishe ki, ina wuni." A.A ya yi maganar ya na miƙewa sannan ya ta ka zuwa gaban ta.

"Alhamdulillah." ta furta da gyar dan A.A irin mutane ne masu yi ma mutum kwarji a kallo ɗaya.

"Gaskiya Yaya ka iya zaɓe, she looks innocent, beautiful, wow me sunan aunty ta wa?." Ya kalli M.d ya mai murmushi, M.d da yake ganin abin da A.A yame yi kaman a mafarki ya ce.

"Fatima."

" Wow Fatimatul zahra'u, suna mai matuƙar daraja, sunan ɗiyar manzon Allah." Suka amsa da 'saw'

" Ban ga su Maa da su Hafsat ba."

" Suna gidan su Salma, mahaifinta Allah ya yi mai rasuwa." Dad ya furta annurin fuskansa na ɗauke wa, take shima AA annurinsa ya rage.

" Subunahllah, Allah sarki Allah yajikan sa."

" Ameen ya Allah."


********************* ********************

_____________ Tun safiyar yau suka kammala komai misalin 10:12am mota ta ɗauke su, su dai nasu ido kawai dan wani saɓon unguwa sukaga an kaisu, ko bayan sun shiga babban gidan wanda sukai ta kallon coumound ɗin gidan mai kyau sosai, bayan sunyi parking Baby ce ta fara fitowa sannan suma su Karis, fuskokin su ɗauke mamakin nan ina ne.

" Sani nan ina ne wai?." Butter ta yi maganan ta na kallon driver, sai ya ce.

" Oga ne ya ce na kawo ku na wuce, ni kai na ban sani ba gaskiya." fitowa ya yi ya firfito musu da kayan su, ba yadda suka iya babban ginin da ke tsakiyan haraban wargajejen gidan suke kallo, door bell Karis ta danna, sai su kaji an amsa, suna tsaye har aka aka buɗe, wata ƴar yarinya su ka gani sa'ar su tsaye tana gaida su, ta ce su shigo dan ta san da zuwan su, jikin su a mace suka shiga dan ita yarin yar ko ganinta ba su taɓa yi ba, ma sha Allah parlour ne wanda yake ɗauke da three seaters na kujeru, amma duk da haka akwai space a parlour, a haka suka zazzauna a kujerun, sai wannan yarin yar ta shiga musu da kayan su wani ɗaki.

" Ko dai munyi ma Babban yaya laifi ne shine ya kawo mu nan dan ya hora mu?." Karis ta faɗa idon ta cike da kwalla, sai Baby ta ce.

" A'a in sha Allah ba ha ka bane sister." Kafin Butter ta ce wani abu sai wannan yarin ta dawo parlour ta na murmushi sannan ta zauna daga gefan su ta ce.

" Yanzu zasu dawo, kafin nan mai za ku ci?."

" A'a Alhamdulillah a ƙoshe muke." ce wan Butter, babban TV da ke aiki ne aka sanya wani shiri mai daɗi, dan haka suka mai da hankali gurin kallon wani Nigeria Film me suna Treasure in the sky.

END.

𝕻𝖗𝖊𝖙𝖙𝖞 𝕾𝕶


https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

💪 ᴊᴀᴊɪʀᴛᴀᴛᴛᴜ ᴡʀɪᴛᴇʀ'ꜱ ᴀꜱꜱᴏᴄɪᴀɪᴏɴ (ᴊ.ᴡ.ᴀ)💪
ʀᴜʙᴜᴛᴜ ʙᴀɪᴡᴀ ᴄᴇ ᴅᴀɢᴀ ᴀʟʟᴀʜ, ᴊᴀᴊɪʀᴛᴀᴛᴛᴜ ɴᴇ ᴋᴀᴡᴀɪ ᴋᴀɴ ɪʏᴀ ᴀᴍғᴀɴɪ ᴅᴀ ᴡᴀɴɴᴀɴ ƙᴀꜱᴀɪᴛᴀᴄᴄɪʏᴀʀ ʙᴀɪᴡᴀ ꜱᴜ ꜱᴀᴜʏᴀ ᴛᴜɴᴀɴɪɴ ᴀʟ'ᴜᴍᴍᴀ ᴄɪᴋɪɴ ꜱᴀᴜƙɪ.✍️

𝐑𝐀𝐒𝐇 Ɓ𝐎𝐘𝐀𝐘𝐘𝐄𝐍 𝐌𝐀𝐒𝐇𝐄Ƙ𝐈

ĎĂĞĂ ĂĹƙĂĹĂМĨМ РŔĔŤŤŶ ŚĶ

✿◡‿◡✿ [Sakina Abdullahi] ✿◡‿◡✿

typing....





Page 58.
___________ "Honey, sai ka sauke ni a nan."
Ba tare da ya ce komai ba, ya yi parking sannan ya ɗago idanunsa yana kallonta. Hannunsa ya kai kan nata, tare da ja da rigarta, yana cewa:

"Don Allah ki yafe abin da su Maa suka miki. Suna gidan mutuwa amma babu Allah a ransu."

"Honey, kar ka damu, ya wuce, wannan Black car ɗin Babban Yaya ya ce na hau."

"To, don Allah ki kula da kanki. Idan za ki dawo, ki kira ni please, sai na zo na ɗauke ki."

"In sha Allah, Honey. I love you."

"I love you too." Ya sunbaci hannunta, sannan ta sauka. Ta ɗan yi tafiya kaɗan sannan ta shiga ɗayan motar. Sai bayan da ya ga motar ta hau titi sannan ya ɗauki nasa hanya. Tunani iri-iri ke yawo a ransa—har na abin da Maa suka yi wa Fancy. A gaban mutane suka tozarta ta da cin mutumci. Bai taɓa ganin ta zubda kwalla ba sai yau. Hijabi fari ne ta sa, suka zo ba mata manja. A hanya ya tsaya ya siya mata wani. Addu'o'in da yake yawan yi ne yasa yanzu baya jin daɗin halin su Maa balle yadda suke wa Fatima.

*************** ***************

"Ashe za ki iya tafiya ki bar ni, Hasty?"
Sai ta fashe da kuka tana rungume Hassana.

"Yanayi ne, amma da bazan iya ba, da zarar komai ya wuce zan dawo." Sannan ta saki ta, ta ja baya. Tun da suke tare suke rayuwa – dai dai da kwana gu ɗaya suke yi, sannan ba sa iya yi ba tare da juna ba. Idan ɗaya na rashin lafiya, tare ake kwantar da su. Allah ya ga ba za su iya rayuwa babu juna ba, shi yasa har ya ba su ƴan biyu kuma gida ɗaya.

"Menene abin kuka? Kun ga yanzu sai ku sha amarci ke da Husain."

"Amarci kuma, Hajiya?." Sai sabon hawaye ya zubo, Husain ne ya riƙo ta ya saka ta cikin mota sannan suka bar gurin. Shi ma zuciyarsa a karye take, ɗan uwan sa guda, wata mace ta sauya masa rayuwa. Hannunsa da ke dungule ya buɗe, ya kalli SIM card ɗin Hassan. A ransa ya ce, "Dole na koya miki darasi, Hafsat kin taɓo ni wallahi."

Har bakin get ɗin ya kaita. A lokacin har ta bar kukan. Dai dai nan Fancy ita ma ta sauko daga motar da ke gabansu.

"Zuwa yamma zan dawo. Babban Yaya zai sa a kawo ni gida."

"To shike nan. High Court za ni yanzu, akwai abin da zan yi a can." Sai ta ɗaga masa kai, Hawaye ya kuma gangarowa daga idonta, sai ya share ta yana cewa:

"Na ce ban so. Idan kuma za ki zubar min ne, to ki tara min wallahi. Ban yadda a zubar min da su a banza ba." Murmushi ta yi sannan ta fita daga motar. Ganin ta na zubar da hawaye, Fancy ta rungume ta tana cewa:

"Menene sister? Waye ya taɓa min ke?" Ina! Sai sabon kuka. A hankali ta zame jikinta ta nufi motar Husain da ke kallon su. Kafin ta ƙaraso, ya janye gilashin window, ya san da ɗan haka. Ya yi mata murmushi yana cewa:

"Fatima koh?, Kin san ban ga ne ku sosai."

"Eh, me ka yi mata?" Ta furta, ranta a haɗe. Murmushi mai sanyi ya yi yana cewa,

"Ni babu ruwana. Hasty ce." Take ta tuna da abin da suka tattauna ɗazu a group na tafiyar Hasty. Sai ta yi masa sallama ta koma wurin Husty. A tare suka shiga cikin gidan, shi kuma ya wuce.

Suna jin doorbell dukansu suka mai da hankali kan ƙofa. Yarinya ce ta je ta buɗe, sannan suka shigo. Su Butter suka hau murna ganin ƴan uwansu, sai hankalinsu ya natsu.

"Matar Barrister, me ya same ki?." In ji Karis—haka take ce mata.

"Sai haƙuri, Hasty ta bar ƙasan nan," in ji Fancy.

"Oh, toh. Allah ya tsare. Na manta ne ai," Butter ta furta. Take kuma aka buɗe ƙofa, mata uku suka shigo cikin ɗinkin atamfa iri ɗaya—Beauty, Kandy da Beasty. Suka hau ihu da murnan ganin ƴan uwansu kamar sun jima ba su haɗu ba.

"Wait! Wait! Wait! Wai nan gidan ku ne?" Karis ta faɗa tana kallon su Beauty. Sai suka ɗaga mata kai.

"Ai an ce kar mu faɗa muku ne. Babban Yaya ne ya siya mana wannan gidan sannan ya haɗa mu a guri ɗaya. Can na Beauty ne, wannan kuma na Kandy, sai wannan nawa."
Beasty ta faɗa tana nuna ɓangarori uku. Sai ɗaya da ke gefe, anan aka kai kayan su.

"Ma sha Allah. Allah ya saka da alheri, na muku murna, Sisters."

"Thanks, Fancy. Hmmmm, Husaina, za ki iya saki jiki da mu koh? Yadda kuka san an raba ta da ruhinta."

"Hassan ita ce numfashina, ji nake ba zan iya rayuwa babu ita ba."

"I'm sorry. Mun san yadda kike ji, sis. Dan shaƙuwarku na da ban ne."
Kandy ta kalli wata budurwa ta ce:

"Zubee, fatan kin yi arranging komai?" Da kai ta amsa sannan ta shige ɗakin.

"Ina kuka samu yarinya?" Fancy ta tambaya tana cire hijabin jikinta.

"Kyauta aka ba mu ita—marainiya ce. Babban Yaya ya ba mu ita. Sunanta Zubaida. Ba ta da damuwa. Komai ka saka ta, za ta maka, g son aiki da biyayya."

"Ma sha Allah." Daga nan suka shiga duba ko ina na gidan. Irin dukiyar da aka narka ba a magana. Gida ya haɗu har ya gaji da yaɗuwa. Bayan sun gama duba ko ina, suka zauna suna hutawa. Bayan nan suka tafi dining area—wasu tsararrun abinci da abubuwan sha na musamman ne a zagaye gurin.

"Ni yaushe za ku zo min hutu? Gashi nan da ɗan lokaci sai Saudiyya kenan," in ji Fancy.

"Da Babban Yaya zai yadda, ko one-one week sai mu zo," Baby ta ce.

"Mu kira shi to, mu ji," Karis ta ce tana ciro wayarta. Suka nuna mata lambarsa da aka ajiye da sunan Boss. Ta dannata, da mamaki sai ta ji yana ringing—abin da da wuya ka kira ka same shi. Bayan kiran ya katse, sai ya kira ta. D ta ɗauka, muryarsa ta daki kunnensu:

"Ina ji."

"Assalamu alaikum. Ina wuni. Da ma Fancy ce—oh sorry, Fatima ce. Ta ce tana so ko 2 days ne muje muyi mata kafin mu dawo." sai Karis ta yi shiru don jin me zai ce. Sai bayan kusan minti 2 sannan ya ce:
" Ba Husaina wayan." Da sauri ta miƙa mata, dan tana kwance a gefe ta kuma ta ƙi sakin jiki.

"Babban Yaya..."

"Hassan ta faɗa min komai. Me yasa ba ku sanar da ni ba? Ku fa ƙannai na ne, wanda nani muku kallon yara ba, Ni nan jagoranku ne. Ko wani irin damuwa gare ku, ku faɗa min kun ji? Yanzu dai na so a shigo da ku da surprise ɗin ku, sai dai na lura bakya so ke."

"A'a Babban Yaya, muna so."

"Ok, kibar damuwa, ban so, yanzu za a kawo muku."

"Mun god—"

"Ban son a godiya you know. Allah ne abin godiya, In ma godiyan ne, Auntyn ku za ku nawa, Ita ce ta sauya ni." Kafin su ce komai, ya katse kiran. Shiru ya ratsa wurin.

"Ni ban san me ya kamata mu yi ma Aunty Ramlat ba, dan mu saka mata," faɗi Kandy.

"Muyi mata fatan ta sauka lafiya kawai. Daga nan sai mu shirya mai za mu yi."

Misalin 6:10pm, bayan sun gama shirin tafiya, sai suka ji motoci na shigowa gidan.

"Ɓaƙin yamma kuka yi ne?" Butter ta faɗa.

"Ko dai su Ya Adam ne?" Karis ta ce, sai Kandy tace.

"Anya? Let’s go and check."Daga nan suka fita zuwa compound. Da idanu suke kallon matasa hudu—kowanne ya fito daga sabuwar mota mai ƙyalli, dukkan ƙira Bugatti.

"Assalamu alaikum."

"Wassalamu alaikum. Boss ne ya aiko mu."Ɗaya daga cikinsu ya miƙa key ya ce:
"Wannan na Madam Hauwa'u." Beauty ta amsa da mamaki. Sai na gefensa ya ce:

"Wannan na Madam Husaina." Kandy ta amsa mata domin su ba su fito ba. Haka suka ba su, sannan suka wuce.

Da gudu-gudu suka koma ɗaki suna cewa:
"Mota! Mota Babban Yaya ya siya mana!"
Gaba ɗaya suka fito—Beauty, Beasty, Kandy, Fancy da Husaina. Kowa ta shiga nata, suna dubawa a ciki kowa ta samu takardu, sannan suka duba.

Fancy da Husaina su na makaranta (HND). An gama komai. Fancy Polytechnic wanda ke opposite da Air Force Base. Husaina kuma a Malali, kusa da gidan su.

Beauty, Beasty da Kandy sun kammala karatu. Kandy Journalist ce a AIT TV. Beauty karatu ta yi a Fashion and Design, ta kaddun wani shago ne a wani plaza. Beasty kuma za ta haɗa aiki da karatu—likita ce ƙarama, za ta fara aiki a wani babban asibiti, daga nan kuma ta ƙara ilimi a fannin lafiyar mata.
End.


𝕻𝖗𝖊𝖙𝖙𝖞 𝕾𝕶

https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

💪 ᴊᴀᴊɪʀᴛᴀᴛᴛᴜ ᴡʀɪᴛᴇʀ'ꜱ ᴀꜱꜱᴏᴄɪᴀɪᴏɴ (ᴊ.ᴡ.ᴀ)💪
ʀᴜʙᴜᴛᴜ ʙᴀɪᴡᴀ ᴄᴇ ᴅᴀɢᴀ ᴀʟʟᴀʜ, ᴊᴀᴊɪʀᴛᴀᴛᴛᴜ ɴᴇ ᴋᴀᴡᴀɪ ᴋᴀɴ ɪʏᴀ ᴀᴍғᴀɴɪ ᴅᴀ ᴡᴀɴɴᴀɴ ƙᴀꜱᴀɪᴛᴀᴄᴄɪʏᴀʀ ʙᴀɪᴡᴀ ꜱᴜ ꜱᴀᴜʏᴀ ᴛᴜɴᴀɴɪɴ ᴀʟ'ᴜᴍᴍᴀ ᴄɪᴋɪɴ ꜱᴀᴜƙɪ.✍️

𝐑𝐀𝐒𝐇 Ɓ𝐎𝐘𝐀𝐘𝐘𝐄𝐍 𝐌𝐀𝐒𝐇𝐄Ƙ𝐈

ĎĂĞĂ ĂĹƙĂĹĂМĨМ РŔĔŤŤŶ ŚĶ

✿◡‿◡✿ [Sakina Abdullahi] ✿◡‿◡✿

typing....





Page 59.
************** ***************
Driving back home, take yi a natsa har ta isa gida. Ta shiga part ɗinta kai tsaye, ta gabatar da sallah sannan ta dawo parlour. Ganin fes ko'ina an gyara, ta yi mamaki sosai. Ta leka kitchen, ko za ta ga mai aiki, amma babu kowa. Sai ta dawo parlour.

Take aka buɗe ƙofa aka shigo – Halima, Hafsat da Maa ne. "Wato sai yanzu suka dawo," ta raya a ranta. Ta ɗauke kanta daga kansu, ta mai da hankali kan TV.

"Baki iya gaisuwa ba ne?" Hafsat ta faɗa cikin isa.

"Ban iya ba, Hafsat Ai na ga kin iya sallama." Fancy ta amsa a da ke.

"Yarinya nan ba ta da mutumci fa." Halima ta furta tana cire gyalenta. Sannan ta kashe TV ɗin da ke aiki, ta yi magana da zafi zafi :"Ai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login