Showing 18001 words to 21000 words out of 93691 words

Chapter 7 - RASH ƁOYAYYEN MASHEƘI. COMPLETE HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

213

wanda wani annurin ya sauka a fuskan shi, ya yi kyau sosai cikin ɗinkin babban rigan, shida ƴan uwan sune matasa kaman shi, dan shi be da friends duk suna U.S.

A cikin gida kuwa, mutane ne sosai ƴan uwa da abokan arziƙi, can ɓangaren ladies kuwa sun sha ɗinki iri ɗaya fitted gown sai na bayanshi wanda zasu sa saboda Boss. Masha Allah sunyi kyau sun sha make-up ga wasu ƙawayensu wasu sunyi ankon wasu kuma kayan nomal one jikinsu, Aunty ce ta shigo ɗakin ita ma cikin ango ɗinkin Buubuu sannan ta sanya hijjab ƙaramin, ta na shiga wasu suka fara gaishesta ta na amsawa sannan ta ce

"Kufito a ɗauki hotuna sun dawo." ta ke ƴan matan suka hau guɗa, sannan ta kuma magana "kunsan kuwa har da Babban yaya aka daura ma aure yau kuwa."

" Aunty wani babban yaya?." Cewan beauty

"Wanda kuka sani Yayanku Shuraim mana. muna sai yanzu muka ji mun daisan harda part ɗinshi aka gyara, sannan ɗazu ta ƙofan baya munga ana ta shiga da kawa." ta na gama faɗin haka ta fita tabarsu duk sun hangame baki, Hasty ce ta yi ƙarfin halin ce wa

" Mun shiga uku, Babban yaya, yanzu duk shirin event din dinner yata shi a banza in dai yaje kenan."

" Keta event kike yanzu ya yi aure kenan zaman gida dole wayyo allah na." Kandy ta kai nan ta na zama a kan gado, ji take kaman ta yi kuka, a haka suka fita dukkansu suka sha hotuna shi dai Shuraim fuskan nan a haɗe kaman hadari kuma yaƙi tambayan su Pazars akan maganan auran.

END

Daga alƙalamin pretty SK.
[6/12, 12:46] ᑭᖇᗴTTY ՏK ✍️✍️✍️: https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

💪 JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIAION (J.W.A)💪
Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi.✍️

If your Mum is alive, may she have a long life to witness your success🤲
𝐑𝐀𝐒𝐇 Ɓ𝐎𝐘𝐀𝐘𝐘𝐄𝐍 𝐌𝐀𝐒𝐇𝐄Ƙ𝐈
ᑭᖇᗴTTY ՏK


https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIAION (J.W.A)💪
Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi.✍️

𝐑𝐀𝐒𝐇 Ɓ𝐎𝐘𝐀𝐘𝐘𝐄𝐍 𝐌𝐀𝐒𝐇𝐄Ƙ𝐈
ꜱᴀᴋɪɴᴀ ᴀʙᴅᴜʟʟᴀʜɪ
ᑭᖇᗴTTY ՏK

Part 13
************* *************

K.K GRA

Nan ma gida ya cika ana ta shagali, can na hangi Amarya Ramlah (Meerah) cikin farin Less dinkin fitted me tattara ta baya da jela, wa'iyazubullah ɗinkin daram, tsam ta fitar da shape din ta sosai, ba ta yi make-up ba amma fuskanta sai hasken amare take yi, Polisawa ne can gefe guda suna cin abinci mata da maza, gurinsu taje tana musu godiya sannan ta fara tafiya sai ta jiyo muryan Zaki yana mata magana sai ta juya dai-dai nan ya iso gabanta

" Amarya bakya lefi kin ga yadda kikayi kyau kuwa, ma sha Allah, yabo da godiya sun tabbata ga mahaliccin wannan halittar." murmushi ta yi sannan ta ce

" Ai yanzu na gama neman ka, na sha baka zoba ne ai." sai ga kwalla a Idonta sai ta share da tissue ta ra sa hawayen me take yi tin safiyar yau kawai tana jin babu daɗi.

"Haba to ai na zo besty ta, tare da ango mu ke mun zo ganin ki."

"Ka ce su shigo cikin Compound." da ga ha ka ya fita sai gashi sun shigo da ango da wasu maza uku. tin da ga ne sa idonsa ya sauka a kan ta, be ta ɓa ganin dogon kaya ba kullum sai riga da wando, sai ya ga ashe manyan kayan suna mata kyau fiye da matsun da take sawa. ƙananan mamanta biyu da yaransu ne kusa da ita a haka dai a kasha hotuna har aka gaji, sai kuma aka basu guri dan suyi magana, za ma suka yi da ga can wani gefen idan babu yalwan muta ne da yake gidan yana da girma sosai.

" Please hawayen ya isa ha ka, ki yi haƙuri kinji, Insha Allah wannan shine hawayen ki na ƙarshen sai dai kiyi dan farin ciki." sai da ta share hawayen sannan ta kalle shi ta ce

" Kayi kyau sosai fiye da kullum."

" Ai kinfi Madam, a yau ma na ƙara tabbata da kyawun da Allah yamiki." sunan ta hira dai sama-sama sai ga yan biyu Yusuf da Yunus, gaisawa suka yi da ango sannan suka musu fatan alkairi

********* **********
KINKINAU

Nan ma sai ma sha Allah biki ya yi biki ga manya-manyan malamai, an ci an sha a gurin walima, amare duk sun sha hijabai har ƙasa, ko wacce mijinta ya zo sun yi hoto amma banda na Ramlat, hakan be yi mata daɗi ba amma ƙawarta ta nuna mata ba komai bane,'
hmmmm sai ma sha Allah kawai, sun yi kyau duk Hijjab da suka sanya su hau fatan su, ƴan uwa maƙil gida, ƙofar gida kuwa maza ne babu ma tsaka tsinke, misalin 3:30 Hajara ta shiga mota dan ita Katsina za'a kai ta sun sha kuka a haka aka rabu babu daɗi, can ma mislin 5 a kazo aka ɗauki Maryam Ita dai Zaria ne, can ma a kazo aka ɗauki Zainab wacce ita ba tada nisa da gidan su layi ɗaya ne ya raba. Har da Ramlat aka kaita sannan suka dawo, Kwance take akan cinyar Umma ta nata kuka Umma na ta ba ta haƙuri da nasiha.

" Ramlat ki yi haƙuri, da ma ita rayuwar mace haka ya ke, nasan har da ti nawa da Mahaifiyar ki koh?, Ki ya ƙuri wallahi Ramlat tun da na ke da ke banta tsanar ki ba abin da yasa bana sa ke miki sosai sa bo da Ummanki ta raine ki cikin sangarta sosai kuma na lura ke irin ta ce halinku ɗaya na sangarta shi ya sa bana sakin miki fuska sosai wasa-wasa na sa ba da hakan kinsan al'amarin sheɗan, duk da kina yarin ya ta rasu amma halin ya shiga jikin ki sosai, amma Alhamdulillah hakan dana miji sai kikafi sauran ma natsuwa sosai, ki yafemin idan hakan be miki daɗi ba." ta ƙara sa cikin kuka ita ma

" Na gode Umma Allah ya saka da Alkairi." abin da ta iya cewa ke nan cikin matsanancin kuka, a haka azo ɗaukan ta dan ita ta zaci babu me zuwa ɗaukan ta, motoci guda 15 ne, 14 Black sai white wacce tafi ko wacce kyau a tsakiya ciki aka sanyata ta nata kuka, sannan ƙawarta Ramlat ta shiga wata ta gaban ta amarya sai wasu ƴan uwansu. Sannan mota tabar unguwan, kowa ya sha mamaki ganin irin motocin amma da an ce musu ai yaron gidan su Alhaji Abdulqadir ƙanƙara ne zasu yadda subar maganan suna mata fatan alkairi, dan ko da aka kawo akwati an sha mamakin domin guda 24 a ka kai mata kowanne cike da uban kaya.

Dukkan su biyun kuka suke yi sai can suka yi shuru, Ramlat ta fara magana cikin shashsheƙan kuka

" Assalamu alaikum."

" Wa'alaikumul salam." da ga haka sukyayi shuru, dan ko ba'a faɗa ba sunsan dukkansu amare ne, a yanzu Meerah a tamfa ce ta sanya brown da milk sai babban gyalen kayan. Direct cikin Estate da ke cikin baban unguwa ta shahararrun muta ne wato Milinium City, aka shiga da su baban ESTATE din wanda ya sha saɓon fenti masu sheƙi, muta ne duk sun watse sai ƴan uwa na ne sa. a tare aka fito dasu aka kaisu Main parlour, ƴan uwa duk aka da bai baye su, da yake ita ma Ramlat ta janyo hijab dinta kanta na ciki, ita ma Meerah kyalan ya rufe fuskan na ta, a naso aga fuskokinsu amma babu hali, a bababn parlourn suka sauka dukkansu, in da ƴan uwan ko wacce suka ba da ammar ƴarsu, can dai a ka ce a kaisu su shirya za'a je dinner lokaci ya kusa, A part din Momcy suka sauka aka barsu su kaɗai bayan an aje musu kayan da zau sanya, shiryawa suka yi sai Ramlat ta ce

" Baiwar Allah, ni fa wlh banson zuwa."

" Karki damu baza'a daɗe ba kuma ina tare da ai, sannan sunana Ramlah ko ki ce Meerah duk da baiwar Allah din ce."

" Laaa ashe takwara ce ni ma Ramlat na ke."

" Uhmmm haka ne amma ke Ramlat ni kuma Ramlah kin ga ƙarshe da bambanci duk da ɗaya ne." dariya suka yi sunata ɗan hira har suka gama, ma sha Allah na rasa wacece tafi kyau a cikinsu, dogon riga ɗinkin gown ce, purple colour , ta yi musu matuƙar kyau, idan ka kalli Meerah sai na ce ta fi waccan kyau amma da ka kalla fara alƙabban mata sai dai ka yi hamdala, farar-farar ce haka choculate colour ɗin ma hmmmm. Su na gama shiri suka rufe kansu da kyale kayan sannan suka fita a ka kai su gurin babban gurin taro. Amare suna zaune a in da ya dace haka muta ne ma. sai ango Aliyu Haidar a gefan Meerah, MC yasa kiɗa mai sauƙin sautin "Aure daraja, marta ba ce mai tarin yawa..." ƴan mata sunka fara takawa abin su. Zaki shi ma zaune ya ke a gefe ya na ta kallon program din sai a ka zo gefan shi a dai-dai kunnunsa a ka ce

" Please minti biyu, amarya ce ta aikoni." ya ɗago ya kalli me maganan amma har ta yi hanyan waje, kaman ba zai je ba sai kuma ya miƙe ya fita, tsaye ya ga budurwa mai tsayi ta juya mai baya, sai ya nufe sallama ya yi ta juyo da sauri tare da mai da mai sallaman, sannan ta haɗe rai ta rufe Idonta ta fara magana cikin masifa kamar yadda ta sama idan za ta yi rashin mutum ci.
" Na lura kai ne abokin wancan angon, kuma ina zaton shima haka ɗayan, in ban da rainin wayo, ƙawata ba ta son ta zo amma muka lalla sheta mu kazo sai shi yaƙi zuwa, bani numbern shi in kira in zazzaga mai rashin mutum ci, ai wannan rainin sense." ta miƙa mai wayar Ramlat din, furzar da iskan bakinsa ya yi sannan ya sauke ajiyan zuciya ya ce

"I'm sorry ba ni ne abokin Shuraim ba and bansan ina ya ke ba."

" Oho ni ban number shi na kira na ji dalilin ƙin zuwan shi. "

" gaskiya be kyauta ba, kuma ban da number shi...." Fuuuuu ta wuce ta ko ma cikin gurin, ji yayi ta burge shi sosai, koma wa ciki ya yi, a gefan amaryan Shuraim ya hangeta, bini-bini sun haɗa ido sai ta dalla mai harara shi kuma sai ya yi murmushi.

Ganin Bababn yaya be zo ba yasa ladies su ka raƙashe suka shashe abin su, a haka har aka ta shi misalin 11pm, gida aka mai da su, ɓangaren daban-daban, aka kai Meerah part din farko wanda ya sha uban kuɗi da gyara, ita kaɗai aka bari kowa ya watse bayan an yi mata nasiha sannan an kaita gunsu Pazars suka sanya ma auran albarka, ita ma Ramlat na ta ɓangaren aka kaita wanda komai nasu iri ɗaya ne, ganin irin kukan da take yi akan kar ƙawarta ta wuce ya sa aka kaita ɗakin ladies.

Ramlat zaune ta ke tayi jugum dan ta gaji da kukan tayi shiru, har ɗaya na dare angon be shigo ba aiko tayi kwanciyarta cikin linzimin wani kalan miji ta aura, shin a haka zatayi rayuwa da shi, tin kafin ta sanshi taji bata kyaunar sa ko kaɗan, ace sai a card wedding ta ga sunan sa wai Shuraim (Babban yaya).

Su kuwa su Haidar bayan abokansa ko in ce ƴan uwansa sun kawo shi suka musu nasiha sannan suka wuce, sallah suka fara yi sannan suka zauna a Parlour suna ɗan hira tare da cin abinci, bayan sun gama suka shiga bed room, ya lura Merah gaba ɗaya a ɗan tsora ce take ga kuma taƙi sakin jikinta dashi dan haka ko hannunta ba riƙe ba a haka sukayi barci abin su.......

To Allah ya baku zaman lafiya ameen.

End

Daga alƙalamin pretty SK.

6/12, 12:46] ᑭᖇᗴTTY ՏK ✍️✍️✍️: https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

💪 JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIAION (J.W.A)💪
Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi.✍️

If your Mum is alive, may she have a long life to witness your success🤲
𝐑𝐀𝐒𝐇 Ɓ𝐎𝐘𝐀𝐘𝐘𝐄𝐍 𝐌𝐀𝐒𝐇𝐄Ƙ𝐈
ᑭᖇᗴTTY ՏK
Page 14

********** **********
Kiran sallan farko a kunnanta dan ha ka ta miƙe ta shiga toilet alwala tayi sannan ta fito ta na tinanin ina ne gabas, can sai ta hango prayer-mat wanda ya fuskanci gefe guda kuma a ta sama anvsa wani abu me ɗauke da sunan Allah wanda aka ƙawa tashi, take zuciyarta ta raya mata nan ne gabas aikuwa ta kalla ta gabatar da sallanta ta na idarwa gurin tayi raka'atanul fajr da Subh sai tabhau karatun alkur'ani cikin daddaɗan muryan nata kaman me busan sarewa.

Ɓangaren su Aliyu Haidar kuwa yana tashi ya tabsheta sannan ya fice masjeed, wanka tabyi sannan tabyi sallah duk abin ta ba ta wasa da ibada, lissafi ta hau yi yau satin ta ɗaya ba taje aiki ba kuma tasan sai nan da kusan 2weeks again za ta koma, abin da take ji sam ba zata iya ba, yana shigowa ta ɗago fararen idanuwanta ta kalle shi, sai kuma ta ɗauke kanta, da murmushi ya iso in da ta ke ya zauna gefan gadon ta re da ce wa

" Madam kin tashi lafiya?." gani yayi ta ɗauke kanta da ga kallon shi, hakan yasa ya ɗago hannunsa yajuyo da kansa ya na kuma magana cikin raɗa-raɗa. "me nayi to daga kaisuwa kuma?."

" Karka sa ke cemin Madam ....."

"Sorry Meerah." turo baki ta kuma yi sannan ta sanya hannunta wanda suka sha lalle suka ƙawata shi duk da duhun hannun amma ya fito raɗau sosai.

" To wanne kike so?."

" Uhmmm." ta faɗa ta na miƙewa da idanu ya bita, cire hijab din jikinta tayi ta sagale a anger, riga da wando masu laushi ne ta sanya sai wannan ƙashin amarci ke fita ajikinta me sanyin daɗi, ga wannan gashin na ta daya zubo baya dan ita ba tayin kitso, gaban mudubi ta tsaya tana gyarawa gashin sai kawai taji ya janyota jikinsa, kallon juna suka shiga yi kowa najin ƙaunar ɗan uwan nasa, a hankali ya kai bakinsa cikin nata suka shiga kissing juna cikin rashin kwarewar su, a haka har abu ya kan ka ma. Basu suka na tsuba sai misalin 8am, wanka suka yi a tare sannan suka shirya, sai suka koma Parlour domin breakfast dan tin da zu aka kawo musu, kallon ta yake yi cikin so da ƙauna mara misaltawa, nu na mata wani babban ƙofa ya yi wanda yake a gefe ya ce mata

"Ƙofan shiga Main parlour kenan ba sai kin sha zagaye na, kodan idan zaki gai da iyayena ko kina son yin hira nan za ki bi " ɗaga kai ta yi sannan ta marairaice fuska, tai magana cikin shaƙwaɓar ta.

"Ni kace min zan koma aiki amma baka faɗamin yaushe ba ne."

" Madam ke da amarya ce kibari nan da three weeks sai mu koma tare."

"Ni kade na cemin Madam banaso." sai da yayi murmushi sanann ya ce

" To Omry, ni fa wanne zaki din ga kirana dan na gaji da kira na da kike yi da kai ko Malam." Sai tin kunnansa ta kai bakin ta sannan ta ce

"Farsi."

" Awwwnnn omryty thanks, suna mai daɗi." yafaɗa yana shafa gashin kanta.

" Kai ba business kake yi ba ai ko next week ka koma kasuwan ka."

"Eh, toh ha ka dai na ce amma soon zaki dan aiki na dan yanzu ne ma nake yi na kanje kasuwa ne kawai." da ga haka suka dinga hira kwanin sha'awa.



Ramlat ce ta ɗauko abincin ta nufe ƙofar da a ke ce ta shiga, duk ka ƴan matan su ƙi kawowa sa boda wai karsu haɗu da Shuraim. Sallama ta yi har sau biyar ana shida Ramlah amarya ta fito ta na amsawa, ganin ƙawarta ta faɗaɗa murmushi a fuskanta ta na faɗin

"Naji daɗin ganinki ƴar uwa." gaisawa suka yi sannan suka zauna a parlour suna ɗan hira sai Ramlat ta ce

" Ango na barci hala, Allah ya sa ban ta kura muku ba?."

"Hmmmm to ai be zo ba, banga kowa ba ha ka na kwana da tambayoyi da yawa, shin kodai auran dole a ka yi mai." ta ƙare maganan cikin kuka, da ƙar Ramlat ta samu ta rarrasheta sannan ta ce tabar abin kar ta faɗa ma kowa ta yu akwai dalilin ƙin zuwan nasa. ƙara suka ji ana ƙoƙarin buɗe ƙafan ɗaya daga cikin sauran ƙofofin na ɗakin dan ƙofofi kusan 6 ne, sai kuma a ka yi shuru

"Kodai a ɗakinsa ya kwanta Ramlat?."

" Oho mai ni wallahi na ji ban ma son ganinsa, har ta auran banso dashi." ta faɗa ta na share kwallan Idonta, sai ji sukayi an buɗo ƙofan a fito a kan Wheelchair, da yake ta baya ya fito sai Ramlat ta miƙe da sauri ta fie tana jin Ramlat na faɗin

" Ina zakije, ki tsaya mana." ai tuni tabi ƙofar da ta shigo ta fice, direct ɗakin ladies ta shiga, be kamata mijin bestyn ta ya ganta babu hijab sai gyale shi ya sa ta fice da sauri. tana shiga ta tatta Hasty da Baby ne kaɗai a ciki za ma ta yi suna ɗan hira dan sunfi sakin jiki da ita ban da sauran wai su ba zasu kwanta da ƴar talakawa balle ma kandy halinta daban ne akan talakawa sai mai bi mata Fancy.


************* Miƙewa ta yi tanufi part din da ta kwana har ta kusa shiga tajiyo muryansa mai daɗi da taushi yana magana hakan yasa ta tsaya.

"Ina son magana da ke " abin da taji kenan, kaman ba zata dawo ba sai kawai ta juyo ta nufi in da ta ga yakai a keken sa. zama ta yi a can gefe a kan carpet bayan ta gyara zaman hijab din ta, cikin haushin sa da rashin sonsa ta furta

"Barka da safiya." sai shuru ya biyo baya kaman ba ze ɗago ba sai ya ɗago ya kalli direction din ta karaf suka haɗa idanu, da sauri

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login