Showing 27001 words to 30000 words out of 93691 words
dubara ya ke taɓa wasu waje wanda duk in da ya taɓa sauti kaɗan ne ke fita, harufa huɗu kawai yasa sai ga gurin yana rarrabewa biyu, take lungu ya bayyana a ciki aikuwa ya na shiga ƙofan ta kulle, dogon lungun ya bi sai haske walwal suka fara bayyana, cikin minti 3mnt ya isa wani ƙofan wanda hannunsa kawai ya ɗaura ajiki ya yi scanning akuwa ta buɗe ya sa kai ya shiga, be yi mamakin ganin muta ne uku na jiran shi ba, gaishe shi suka yi ya amsa da kai kawai, ama ya yi kan wani kujera wanda yake kallon na su kujerun,
"Boss yanzu na sauke video din akan sabon page din dakacye na buɗe, amma aganina hakan be da ce ba saboda za a iya bibiyan mu kuma....."
"Adamsi kai ma kasan Oga mayen computer ne so wannan ba matsala bane." cewan na gefan Adam din, sai shi ma ɗayan ya ce
"Gaskiya ka faɗa Skiddo munsan Yallaɓai ai."
" Haka ne kuma Spider." faɗin Adam, sai suka mai a hankalinsu ga ogan nasu wanda ya ta ɓa kan table din sai wannan maginin Tv nan yabayya, suka mai da hankalin su a kai.
" Gobe misalin ƙarfe 9am na safe zaku kawomin shugaban betir na ƙasarnan, koma yayane ni dai 9am ya shigo hannun ku." da kai suka amsa kawai, sanann suka dinga bincike akan abubuwa da yawa, Sai 2am suka kammala ya miƙa tsaye ya na kallonsu sannan ya ce
"Za ku iya tafiya 6hs, ya rage muku." da kai suka amsa sannan suka fita ta wani ƙofa wanda ze sa da su da ɗakin Adamsi. gyara zama ya yi ya kunna wani system din ya na kallo ko ina na gidan akwai camera wacce yasa ba tare da sanin kowa ba, baya shiga in da be dace ba dan haka abubuwa ya dinga kallo balle ma akan ƙananan sa, ya na gamasa sai ya duba na Kifaty, can ya hangeta ta na barci sai yaja videon ya koma baya anan ne ya ga duk abin da ta yi bayan ya fita, dariya ya yi ya na ce wa
" Wato ƙarya ne hmmmmm zamu haɗu gobe ai." sai kuma ya ɗauki wayansa ya tura sms ya na kallonta ta cikin Camera, saɓon na shigowa wayanta ta duba ta re da kashe wayan da suke yi da saurayin ta, ganin baybban yaya ne ya rubuto SMS yasa ta buɗe da rawar jiki. yana kallon ta yadda ya ga ta daburce sannan ta kwanta, Murmushin ya yi ya na jin daɗin yau ɗin shike nan haƙonsu ta cimma ruwa dan ta wayan ƙawar ta sa ya samo komai da komai saboda saurayinta yaron mutumin da suke hari ne, shuru ya yi sannan ya miƙe ya kashe ko ina ya koma na sa ɗakin ya kwanta ransa pesssss a zahiri amma can ƙasa akwai abubuwa da ya wa sosai wan da Idanu ba sa hange haka ƙwaƙwalwa ba ta lissafawa sannan baki ba ya furtawa.
End.
Toh fa Alƙalami ya fara zafi sosai, jinjina ga J.A.W.
[6/15, 22:28] ᑭᖇᗴTTY ՏK ✍️✍️✍️: https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIAION (J.W.A)💪
Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi.✍️
𝐑𝐀𝐒𝐇 Ɓ𝐎𝐘𝐀𝐘𝐘𝐄𝐍 𝐌𝐀𝐒𝐇𝐄Ƙ𝐈
ꜱᴀᴋɪɴᴀ ᴀʙᴅᴜʟʟᴀʜɪ
ᑭᖇᗴTTY ՏK✍️✍️
Page 19
******************* ***************
"Hello Boss." jin ba'a ce komai ba ya sa me maganan na cikin wayan ya ci gaba da maganarsa cikin girmamawa "Akwai matsala a yadda na fahimci komai, ƴan jam'iyar suna tsangwaman Aliyu Haidar duk da ya na babban matsayi, gani suke shine ƙarami a ciki dole su juya shi kuma a kan gaskiya ya ke, YAA-RASH, yanzu umarnin ka kaɗai muke jira a kan komai, sannan mun samu nasaran sato Alhaji Mansir."
"Ok" abin da ya faɗa kenan ya katse wayarsa ya na kallon Kifaty wacce ke gefansa ta na cin lunch, murmushi ya yi ya na tina duk ranan da Ramlat ta fahimci shine wannan mutum da ya ke girgiza mutanen Nigeria wato RASH dole ta rabu da shi gashi ya na so ya sosai.
" Baby yanzu pharmacy zan karanta?, na fi son low fa."
" Karki damu za ki iya, kodai mu canza kawai."
" Eh gaskiya."
"To sai ki canza amma aikin Asibiti na keso kinji."
"To." ta faɗa ba dan taso ba kawai,
**************** **************
Bayan biyu
Ɗaya abubuwa da yawa sun faru ciki har da fara zuwa makarantan Ramlah wacce ke karantan Pharmacy, dan ta ga yafi sauƙi, ta fara zuwa poly abinta in da Shuraim yasa mammata Driver ya dinga kaita da dawowa.
Ɓangaren Meerah kuwa suna ta bincike kaman tashin hankali dan RASH yanzu duk bayan sati ɗaya ze saki video na kisan wani. kowa cikin fargaba yake akan wannan mutumin, kuma mafi ya wa an fi kashe muta ne a kaduna, shi yasa jami'an ciki su kafi ya wa sosai, harta Zaki ya dawo Kaduna dan haɗuwa gurin zaƙulo wannan masheƙin amma ko makama ɗaya basu samu, sannan a ɓoye Governor Aliyu Haidar yasa an fara bincike ƙarƙashin ƙasa a kan duk wanda ake kashewa bi sa ɓoyayyen jami'a sa Sunusi, harta su Pazars abin na basu tsoro sosai yadda ake kisa kuma makashin cikin rashin imani yake aikata kisan. Ɓangaren ladies kuwa cikin matuƙar ɗar-ɗar suke da Babban yaya saboda dai-dai da wani abu suka aikata sarai yana jin cikin ƙanƙanin lokaci, shi ya sa dukkansu suka mai da hankali ga karatunsu, sananne time to time yakan shiga ɗakin su ɗan binciken karatun su. Ita ma Ramlat Badikko ta koma wata makaranta Saleem international School in da ta shiga SS 2 ta fara karatun, zuwa yanzu sun fara soyayya da Zaki tun wani zuwa da ta yi gidan ƙawarta suka haɗu ana ne ya samu har suka yi exchanging numbers, cikin ikon Allah suka fara ƙaunar juna da soyayya me tsafta, sannan suna shan chat da aminiyarta dan ko da yaushe suna online sai dai in sunje makaranta, harta Assignment idan Ramlat badikko ta kasa sai Kifayaty ta taimaka mata.
************** *****************
"Wai nikam me yasa Ya Adamsi yake miki haka ne, ya ka mata zuwa yanzu ayi magana koda ya yane, duk da nasan su Pazars suɗin dai su zasu tsaya mai."
" Hmmmmm ke dai bari Fancy na rasa me ke damunsa ko tani bayayi ma sai yasamu lokaci, kina gani rabon da muyi waya na manta ya na da waya amma number shi kullum a kashe." Khadija ta rufe idanunta jin zafin abin da Adam yabke mata, Fancy da ke fuskantanta ta sauke ajiyan zuciya ta na ce wa
" In sha Allah komai ze yi dai-dai soon, yanzu kawai kibari muhaɗu dashi, kwanda ke Sis kuna son juna, kawai wasu ɗan abubuwa ne ke hana shi, amma ni fa, hmmmm ina matuƙar son Zaki amma yaƙi ba ni fuska, har numbersa na sa mo a wayan Aunty Meerah amma a banza, Infact an cemin ya na da budurwa, hmmmmmmmm."
"Haka ne ki bari zuwa an jima idan ya dawo zamu je mu same sa kawai." dajin wannan shawaran suka tsaida cewa zasu je in ya dawo, ilai yana dawowa Karis ta shaida musu da yake a gidan ya sauka amma a ɗakunan waje saɓanin wancan zuwan, sallama suka yi tare da Knowking "Yes coming." abin da aka faɗa kenan, a hankali suka murɗa handle din suka shiga da sallama da kai ya amsa saboda waya yake yi, kallonsu ya yi cikin ƙaunarsu, sunyi kyau sosai, Kandy Black abaya tasan ya fuskan nan fayau babu make-up, ita kuwa Fancy less blue tasan ya ɗinkin riga da skit nomal, ta yi kyau dan har simple make-up ta sa Baby ta yi mata, su kuma kallon Zaki suke yi domin kayan aikinsa ne a jikin sa, sunayi masa matuƙar kyau, gawannan sajen nasa ma sha Allah, a hankalin kunnuwansu suka fara juyi musu abin da ya ke faɗi a cikin wayan
"Haba ƙauna ke ma dai kinsan bana so ko." Dam, Daram, zuciyan Fancy ta buga da ƙarfi, kallonsa ta ci gaba dayi ganin irin farin ciki da nishaɗi na mamaye sa, Cikin kullewa ta miƙe ta nufesa, gyalan da ke kafaɗarta har sai da ya faɗin, sam ba ta ji ba ta gani harta Kandy ta tsaida ta amma ina kawai nufansa tayi, hannu ta sa ta fizge wayan tare da cillar dashi kan sopan da ke right side, yariga yasan me ya kawo su, ta ke fuskanta ya haɗe annuri ciki ta ɓace, wannan ainiyin Zakin ya bayya wani tsawa daya sake mata ya sa ta tina wanene ZAKI. mutum ne shi amma mai wiyan sha'ani, cikin rawan murya ta fara magana
"Yaya Umar ka san ina son ka, ina ƙauanrka me yasa ka ke kulawa wata banza ƴar iska can......"
" Ƙeeeeee." kit ta yi shuru domin cikin ƙara ji da ihu ya yi magana kuma ya na kai hannusa saitin fuskanta amma ya tsaya dan besan ya mareta domin dole sai an kaita asibiti, harta Kandy ta ji tsoro tasan Uncle Umar be da wasa wani lokaci, durƙusawa Fancy ta yi har ƙasa tana mai fashewa da kuka gami da haɗa hannuwa ta fara magana
"Zaki wallahi ina sonka, kai ma kasa ni na kamu da soyayyan ka dan Allah ka tausaya min." jiyayi jikinsa ya yi sanyi amma be mu na a fuska ba ya ce
"Wato tsabar rashin kunya yau sai ki ka biyoni ɗakina kenan, kin faɗa min ta waya na ce miki ina da wacce nake so dan har manya sun shiga maganan, harda ke a kazo rakiya kenan." ya nuna Kandy da jikinta ya yi sanyi ta na tsaye kamar babu laka a jikinta ita ma muryanta ra wa yake yi ta ke faɗin
" Uncle Umar I'm so sorry please ba za mu sake zuwa ba."
"Shut-up." ya da ka wata tsawa sannan ya kalli Fancy ya ce "Miƙomin wayar can." ya nuna wayan da ta cillar, da sauri ta ɗauki wayan ganin har yanzu kiran na tafiya domin ba ta katse mai kira saboda baya so, yasan ta ji komai kuma ta na kusa da wayan yasa ya sa ke ce wa "bata haƙuri." da sauri ta kai wayan ƙunnenta ta furta "Ki yi haƙuri." ƙet ta katse kiran da ga can, abin da ya ɗaure mata kai shine ganin hotan ƴarinyar da kwanaki suka yi rigima da ita a cikin gidan su, miƙa mai wayan ta yi ya amsa, tsaki yaja ya shige bedroom dinsa, ya na shiga Fancy ta kalli Kandy ta ce
"Ke hotan wannan ƴar talakawan ce."
"Wace kenan?." ta tambaya dan ba ta gane wacce ta ke nufi ba, sai da ta janyo hannunta suka fita sannan ta ce
"Ƙawar matar Boss, wannan Ramlat din."
" Ke bar wasa."
"Wallahi ita ce hotan ta ne a wallpaper, yanzu ha ka muje gurun matar Boss na amsa number ta wallahi za ta sa ni." Fuuuuu suka shiga Main parlour, Aunty da Momcy ke hira suka wuce su, Knocking suka yi ba'a buɗe ba kawai suka buɗe suka shiga kansu tsaye.
END
Daga alƙalamin Pretty SK.
[6/16, 19:54] ᑭᖇᗴTTY ՏK ✍️✍️✍️: https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9ᑭᖇᗴTTY ՏK
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 ᴊᴀᴊɪʀᴛᴀᴛᴛᴜ ᴡʀɪᴛᴇʀ'ꜱ ᴀꜱꜱᴏᴄɪᴀɪᴏɴ (ᴊ.ᴡ.ᴀ)💪
ʀᴜʙᴜᴛᴜ ʙᴀɪᴡᴀ ᴄᴇ ᴅᴀɢᴀ ᴀʟʟᴀʜ, ᴊᴀᴊɪʀᴛᴀᴛᴛᴜ ɴᴇ ᴋᴀᴡᴀɪ ᴋᴀɴ ɪʏᴀ ᴀᴍғᴀɴɪ ᴅᴀ ᴡᴀɴɴᴀɴ ƙᴀꜱᴀɪᴛᴀᴄᴄɪʏᴀʀ ʙᴀɪᴡᴀ ꜱᴜ ꜱᴀᴜʏᴀ ᴛᴜɴᴀɴɪɴ ᴀʟ'ᴜᴍᴍᴀ ᴄɪᴋɪɴ ꜱᴀᴜƙɪ.✍️
𝐑𝐀𝐒𝐇 Ɓ𝐎𝐘𝐀𝐘𝐘𝐄𝐍 𝐌𝐀𝐒𝐇𝐄Ƙ𝐈
❤(。◕‿◕。)❤ [ᑭᖇᗴ𝙏𝙏𝙔 Տ𝙆] ❤(。◕‿◕。)❤
ꜱᴀᴋɪɴᴀ ᴀʙᴅᴜʟʟᴀʜɪ
Page 20
************ *********
A lokacin Ramlat zaune take suna hira da ƙawarta, har tana labarta mata, amma ba ta shedi wacece ba sai dai Kifayaty ta na tsammanin Kandy ce amma ai tana soyayya da Adam abokin Babban yaya. Jita yi an shigo ko izini babu, ɗaga ido tayi tana kallon Kandy da Fancy
" Lafiya kuka shigo mun babu sallama?."
" Lafiya ce ta kawo haka." Cewan Kandy ta na jijjiga da ga tsaye bakin ƙofa
"Okh sannunku." Ta faɗa tana typing da "to jama'ar ki sun shigo,"' sai ita Ramlat ɗin mata reply da "Hehehe, ba na kiraki Voice call." Take wayan yaɗau Ringing aiko ta amsa kiran tare da sawa a speaker ta ce
" Namesake fatan kina lafiya?."
" lafiya lau friendy, kinsan kuwa gobe za'a sa rana."
" For real ?.'
"In sha Allah."
" Allah ya sanya alkairi." Kallon su Fancy ta yi wanda sun ƙulu iya ƙuluwa kuma har ila yau suna tsaye kaman sojoji, basa son ɗaga mata murya domin Babban yaya jiya ke kaman aljani komai sa ni yake yi, tsaki Kandy ta ja ta fice, dan idan ta na kallon Ramlat ji take kaman ta kashe ta, ita kuwa Fancy matsawa ta yi gab da Ramlat ta ce
"Kifaɗa ma ƙawarki ta fita harkan Zaki, ba sa'an auranta ba ne." dariya Ramlat ta hau yi ta ciki wayan dan har yanzu yana hannun Ramlat ne, cikin ƙuluwa da fusata ta fice bayan ta yi ƙwafa sai Ramlat ta ce
"Ke ƙawata kinsan yaran nan basu da kunya balle wa'innan biyun."
"Share kawai, zan ma Zaki magana." ta ba ta amsa cikin ainiyin voice din ta ba na rigima ba,
" Bara na barki zanyima Baby abinci."
" Uhmmmm masu baby, Ya kamata zuwa yanzu muji rabo ya shiga amma ƙawata shiru nake ji, Maryam da Hajara abu ya kan ka ma." murmushi ta saki sannan tabce
" Ke ai nake jira kiyi auran sai mu jera kawai."
"Ha ba Pure white."
"Da gaske pure black" dariya suka kwashe sannan suka yi sallama da kashen kiran, ta na tina suna yara suka sa ma junan wannan sunan, ita saboda hasken ta sai a ce pure white, Ramlat kuwa Pure black, aje wayan ta yi sannan ta nufa Kitchen ta hau aiki.
************ ************
Yana kallon komai a cikin na'uransa, jiya yi ransa ya ɓaci sosai, hakan ya sa a fusace ya miƙa, sai kuma ya furzar da iska mai zafi sosai tare da sakin shu'umin murmushi ganin komai yana tafiya yadda ya tsara, a Wheelchair ya sauka ya fa tafiya har wani ƙarin lungu wanda ga ba ɗaya files ne aciki kuma step by step suke, na farko ya janyo ta re da dubawa na wani ɗan lokacin sai ya mai da, ba ya ya koma ya kalli muta ne biyun da ke zaune Spider da Skiddo ya ce
"Skiddo yadda na tsara haka komai ze tafi, babu yadda zasu gano mu domin kai ne me bincike akan mu, kawai juya musu tinanin zaka yi, amma a zahiri mu kake ma aiki." faɗin Boss sai Skiddo ya yi magana shima cikin ladabi sosai
"In sha Allah, sai dai matsalan shine ba ze yuhu na zauna a family house dinku ba, na ga wannan police din a ciki gidan nan ya ke, kar ya zargi wani abu, and matar ƙaninka ita ma police ce suna da kaifin tinani."
" Wannan ba matsala ba ne, kawai a ɗalin Adamsi za ka zauna ƙanuna kunsa ba da shi, kaga ne ai kasa mu free ba yanzu ba ku ke sato hanya ba." da "To." suka amsa, take aka tuɗo ƙofa aka shigo sun san wanene domin su kaɗai ke da ikon shiga wannan ɗakin sirrin na su a haka wannan ƙarami ne meeting na gaggawa ne kawai suke yi.
"Boss na ga ma bincike a kan pastor John Johnny, ya na zuwa church duk ranan Sunday in babu damuwa a wannan lokaci zamu iya wuff da shi."
"Okh hakan ya yi ma, kowa ya duba wayansa." take suka fiddo wayoyinsu, duk sati biyu suke canza sim, amma su na da number juna wanda su huɗu kawai ke da na juna sai wasu ƴan team din su.
"Na turo muku albashin ku, sannan Adam a tabbatar kuɗin nan ya isa in da ya da ce." Da kaiwa nan be jira godiyar su ba ya wuce, su kuwa sunata murna duk one week ake biyansu five hundred thousand, kuɗin ma yawa yake musu, cikinsu duk sun mallaki abubuwa da yawa da kuɗaɗen amma a ɓoye suna jiran lokacin da komai ze lafa ne kawai, duk da haka akwai masu yi musu aiki da yawa su dai duk 2weeks ake biyan su.
END
❤(。◕‿◕。)❤ [ᑭᖇᗴ𝙏𝙏𝙔 Տ𝙆] ❤(。◕‿◕。)❤ĎĂĞĂ ĂĹƙĂĹĂМĨМ РŔĔŤŤŶ ŚĶ
[6/19, 05:40] ᑭᖇᗴTTY ՏK ✍️✍️✍️:
.
❤(。◕‿◕。)❤ [ᑭᖇᗴ𝙏𝙏𝙔 Տ𝙆] ❤(。◕‿◕。)❤
Ka yawaita ziyarar asibiti, insha'Allah zaka zama mai yawan Godiya ga rahamomin da Allah yai maka.
True love may be hard to define,but the signs to read true love can be clearly seen in every loving relationships.
[6/24, 17:41] Ameeratul Khairy❤️❤️: https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 ᴊᴀᴊɪʀᴛᴀᴛᴛᴜ ᴡʀɪᴛᴇʀ'ꜱ ᴀꜱꜱᴏᴄɪᴀɪᴏɴ (ᴊ.ᴡ.ᴀ)💪
ʀᴜʙᴜᴛᴜ ʙᴀɪᴡᴀ ᴄᴇ ᴅᴀɢᴀ ᴀʟʟᴀʜ, ᴊᴀᴊɪʀᴛᴀᴛᴛᴜ ɴᴇ ᴋᴀᴡᴀɪ ᴋᴀɴ ɪʏᴀ ᴀᴍғᴀɴɪ ᴅᴀ ᴡᴀɴɴᴀɴ ƙᴀꜱᴀɪᴛᴀᴄᴄɪʏᴀʀ ʙᴀɪᴡᴀ ꜱᴜ ꜱᴀᴜʏᴀ ᴛᴜɴᴀɴɪɴ ᴀʟ'ᴜᴍᴍᴀ ᴄɪᴋɪɴ ꜱᴀᴜƙɪ.✍️
𝐑𝐀𝐒𝐇 Ɓ𝐎𝐘𝐀𝐘𝐘𝐄𝐍 𝐌𝐀𝐒𝐇𝐄Ƙ𝐈
☮▁▂▃▄☾ ♛ [Sakina Abdullahi] ♛ ☽▄▃▂▁☮
ᑭᖇᗴ𝙏𝙏𝙔 Տ𝙆
page 21
*********** ****************
Kandy na shiga part dinsu, ta nufi ƙofan ɗakinsu ta shiga, zama ta yi tana jin tsanar Ramlat biyun nan, babu wanda ya tambaye ta sai da Fancy ta shigo tana hawaye shine suke tambayi ba'asi sai Kandy ta faɗa musu, suna ta mamakin ƙarfin halin Fancy domin Zaki sam ba shi da wasa haka rayuwansa yake ɗan zafi-zafi ne.
"Shi ya sa na tsani talakawa har kwanda matar Boss, hmmmm samun waje, wato ta shiga ɗaula bara ta jawo ƙwarya." Cewan Besty ta na yamutsa fuska sai Beauty ta caɓe zancen da ce wa
"In da ranka kasha kallo, ta kula ranan da za ta shigo hannunmu."
" Ni ban ga wani abu a ciki ba a.i"
" Baby shut up, dan ƙanin Aunty ne ko dole ki yi magana ai." Cewan Beauty ta na hararan Baby.
"Ku dai bar maganan yanzu dai zuwa gobe za mu faɗa masu Pazars kawai."
"Gaskiya Husty ba ki da sense, wani ya ji abin nan ai mun shiga uku." Cewan Hasty sai Karis ta ce
"Ai kuwa dai wannan shine son wani ƙoshin wahala." da ga haka suka bar zance amma Fancy har 1am na dare idonta biyu, kira ne ya shigo wayarta amma baƙon number, amma ta na ji kaman Babban yaya, kiran har ya katse sai ga saƙon ya shigo ta kalla na kusan minti 5 wanda aka rubuta. "Damuwa ce ta hanaki barci, love ki ka shiga hmmmm, na ba ki 10mnt da kiyi barci kuma gobe zamu haɗu da ga Boss." Da sauri ta a jiye wayanta kwanta cikin ikon Allah barcin ya