Showing 15001 words to 18000 words out of 93691 words

Chapter 6 - RASH ƁOYAYYEN MASHEƘI. COMPLETE HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

209

wa ba."

" Mun ba ka 3weeks sannan wannan maganan ya zama secret domin ga ba ɗaya jam'iyyar zamu girgiza." kai ya ɗaga kawai ya fita ya barsu dan za su tattauna ne, part din sa ya nufa sai dai kan ya shiga yaji muryan Shuraim ya kiran shi, juyawa ya yi ya nufesa, ya sauka a wheelchair din ya hau kan kujera ya na zuwa shima yahau sai da ya ɗaura kansa a kan cinyan Shuraim ya na sauke ajiyan zuciya, Shuraim kuwa gashin kan Uncle yake shafawa a hankali alaman rarrashi, har ze yi magana sai Shuraim ya sa mai yatsa a kan bankin dan haka ya yi shuru kawai sai shi Shuraim din ya kai bakinsa kan kunnunsa ya raɗa mai " ina ta re da kai duk runtsi duk wiya, karka saɓa musu umarni ka ji ƙanina." kai kawai ya ɗaga mai.

END

Daga alƙamin pretty SK.

Ina fatan kowa yayi babban sallah lafiya. Allah ya maimaita mana. Ameen.
[6/11, 07:41] ᑭᖇᗴTTY ՏK ✍️✍️✍️: https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

💪 JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIAION (J.W.A)💪
Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi.✍️

May Allah ﷻ accept all our righteous deeds bring us endless joy, peace, and prosperity.

✨ 🌙 🕋 Eid Mubarak 🕋 🌙 ✨

𝐑𝐀𝐒𝐇 Ɓ𝐎𝐘𝐀𝐘𝐘𝐄𝐍 𝐌𝐀𝐒𝐇𝐄Ƙ𝐈

ᑭᖇᗴTTY ՏK
ꜱᴀᴋɪɴᴀ ᴀʙᴅᴜʟʟᴀʜɪ
Page 11

********* **************

RHYENO ESTATE

A tabayan gidansu gurin shuke-shuke wato Garden suke zaune, ranta a haɗe ta ke magana dan ko gaisawa basu yi ba ta zauna dan kiranta ya yi a waya ya ce tazo gurin ta same shi

" Wani kalan soyayya muke yi Yaa Adamsi? 2yrs ban ganka ba sannan baka kirana ko chat sai ta facebook muke yaɗuwa, shima sai kayi one month ba ka hau ba, dana yi ma magana sai ka wani ce Babban yaya baya barinka, ba lokaci, how zamu ci gaba da rayuwa a haka, na gaji gaskiya na gaji, rabuwa zamu yi sa bo da kai ba na kula kowa sam amma ban samun kulawa agurinka, Why?." ta na kaiwa nan ta miƙe tsaye sai Adam shima ya miƙe yasan be kyauta mata ba, domin haka ya ke mata to ya ze yi baze iya saɓa umarnin Shuraim ba, amma kafin subar nan ko ma menene ze samu ayi maganar auran na su.

" I'm sorry My Sweet kandy, Insha Allah da ga yanzu zan kasance da ke koda yaushe, kuma zan gyara, ai yanzu muna nan ba'inda zan ƙara tafiya na barki, sai kiyi saving number da ma kira ki dan sabon sim ɗi na ne."

" ni nagaji da savings numbers din ka, da munyi waya yau to ban kuma samu ka da wannan number. "

" Ki ya ƙuri mana Insha Allah komai ya huce kuma jira na ke ki kammala karatu sai muyi aure."

" Uhmmmnmmn." Zama ta yi a in da ta tashi, haka shima ya yi ya zauna, zan can hira na ƙorafi suka bari zuwa na soyayya da kewan juna, Khadijah sam ba ta fushi da Adam domin ta na son shi sosai shima haka ya na son ta. Tin lokacin ta na yarin ya idan ya zo gidan suke hira sama-sama tin a lokacin ya ke furta ma ta yana sonta sai dai kawai ta yi dariya, har ta kai lokacin da ta fara son shi, kowa na gidan sun sani amma babu wanda ya shiga harkan su, harta Babban yaya ya sani sai dai ya sa musu ido kawai.

A Parlourn kuwa sai da suka dau mintina a ha ka sai Shuraim ya ce

"Kawai ka kira su haɗa ma ka komai gobe Adam sai yaje ya amso maka." da kai ya amsa sanan shuraim ya ci gaba da magana

" Ka na da budurwa ne?." ya kuma ɗaga kai, "Wow ƙanina hakan ya yi, to yaushe za ka nunamin ita?" Sai a lokacin Uncle ya buɗe baki ya bashi labarin haɗuwar su da Meera, a fili Shuraim ya ke nuna farin cikinsa, da bashi shawaran daya je gidan su dan ƙara tabbatar mata da ya na sonta.

************ **************
KINKINAU

Muwaɗɗa Malik shine littafin da suke karantawa a masallacin, sati da lahadi ne kawai karatun, 9:30pm su ka kammala dan awa ɗaya da rabi suke yi. yanzu ma sun kammala kenan sai suka yi addu'a tare da salatin Annabi sannan kowa ta wuce, sai Ustaz kaɗai dan yana son yagama haɗa ta kadun sai ya futya, yana gamawa ya fito yakulle masjid din da mamaki yake kallon Alhaji Abdulqadir da ke jikin motansa, ƙara sa wa ya yi ya na ce wa

" Alhaji lafiya kuwa baka tafi ba, ga dare na yi fatan lafiya."

."Malam Ustaz motar ce taƙi tashi nayi-nayi, yanzu na kira driver da mechanic zasu zo."

" To ko zamu shiga ciki kafin su izo ne ?."

" Karka damu Mal.Ustaz zan shiga cikin mota na zau......"

" A'a gaskiya ba ra nayi maka iso kawai, dan ma mota ta ta na gareji ana dubamin da na kaika da kaina." bajira ya faɗi komai ba ya shige gida, murmushi Pazar Q ya yi dan yanajin daɗin karatun malamin nan, cikin ɗan lokaci ya mai iso, aikuwa suka shiga har Parlour suka zauna, Umma ta fito suka gaisa, Ramlat wacce ke Kitchen da niyyan ɗiban abinci dan yau barci ne ya ɗauka akan prayer-mat bayan tabsha maganin ciwon kai dan da shii ta dawo, Umma ta shigo Kitchen din ta na ce wa

" Abbuu ya yi baƙo ki haɗo mai abinci kikai mai, ni zan shiga ciki." da kai ta amsa mata sannan ta ajiye na ta ta shiga haɗa musu, bayan ta kammala ta daidaita hijab dinta ta kai musu, hira suke yi akan littan da aka kammala last week Umdatul-ahkam. Gaishesu ta yi suka amsa sai ta ajiye musu komai data ɗauko sai Abbu sa ta kira sauran matan suzo su gaida shi, dan Alhaji Abdulqadir Musa ƙanƙara akwai mutumci, cikin ɗan lokaci su ka shigo dukan su, gaisheshi suka yi cikin ladabi ya amsa ya na mai jin daɗin a ransa sannan ya ce

" Masha Allah Malam Ustaz, wacce za'a bani aciki ." dukkansu suka yi dariya sai Abbuu ya ce

" Ai su ukun nan an riga ka sai dai naba ka waccan." yanuna Ramlat ya na murmushi, ita ma murmushi ta yi ta ce

" To Baba sai da safe." a tare suka tashi suka wuce amma su na jin ya na ce wa

" Wai Baba ta ce min ta na ganina ɗan saurayi me jini a jiki." dariya suka yi ta yi har suka shiga ɗaki, suma Abuu hira suka ɗan yi sannan yaci abincin kaɗan ya na kammalawa aka kira da cewan sun iso,, aikuwa suka yi sallama ya wuce, har sai da ya hau mota tunkun Abbu ya kulle gidan. yana jin daɗi dan tina maganarsu ta ƙarshe da ya ce mai

" mubar wasa ba tada miji kace?."

" Eh Alhaji, su uku ne zamu aurar nanda lokaci kaɗan."

" In babu damuwa ina neman ma Babban yaro na ita, sai dai shi masaki ne ƙafarsa ɗaya ba lafiya tin wa ni faɗi daya taɓa yi shekarun baya."

" Allah sarki, ai dukkan mu muta ne kuma ba'a gama mana halitta ba, bamu san yadda Allah ze mai da mu ba nan gaba, kowa yasan ku kuna da mutumci w aye zeƙi haɗa jini daku."

" A'a kadai fara jin ta yarinyar ta wa kaji zuwa ko next week sai muyi maganan akai idan na zo Saturday, ka ga sai ka haɗa su gaba ɗaya tin da nan da 2 mounth ka ce." da haka suka bar maganan, ko da ya shiga ɗaki sai da ya labarta ma Umma ita fatan alkairi ta yi amma tanajin ba daɗi wai masaki ne, zata so itama ta auri lafiyayyen mutum kaman ƴan uwanta.


************ **************
RHYENO ESTATE

yana isa gida part dinsa ya wuce, dare ya yi dan har Aunty ta yi barci ma, shima wanka ya yi ya kwanta.

Acan ɓangaren Shuraim kuwa ya na kwance akan bed ya rufe idonsa abubuwa da yawa ya ke tinawa, a haka har Adam ya shigo, zama ya yi sannan ya fara magana

"Boss everythings is ready." sai Shuraim ya buɗe idanuwansa a hankali, sai ya kalli Adamsi ido cikin ido yana wani murmushin da ni kai na bansan fassaran ta ba sai ya ce

" Okh, wato kai ɗan soyayya kabarni ka je can kai da khadija, wai na yarinyar nan har ta san wani love?."

" Meka mai da Sweet-kandyta ......" ya katse maganan dan jin Pillow a fuskan sa.

*** "Assalamu alaikum." abinda yafaɗa kenan sai yayi shuru, kusan 2mnt suka ɗauka ahaka sai sautin muryanta mai daɗin gaske yashiga kwanyarsa.

" Wa'alaikumul salam, meke tafe dakai " tafurta tana shafa lotions ajikinta dan tin tana wanka taji wayanta nata Ringing tana fitowa ta duba amma ganin number kuma True-caller tasa Aliyu Haidar tasan shine sai da yakira sau biyar ana shida ta ɗaga,

" Bansan me zance ba amma wlh naji makamu sosai, in badamuwa kimin ƙawataccan gidan ku gobe zanzo muyi magana dan da gaske nake"

" wanda yabaka number dinnan tsaf ze kawoka gidan mu, amma banda lokaci hira gaskiya yanzu kafaɗa abinda ke bakin ka kawai"

" I love U, kuma auranki nakeson yi "

" When " saida zuciyarshi ta tsaya na wani lokaci dan jin abinda tace, har number yaƙara dubawa itace dai, saida yaseta kansa sannan yace

" Nanda wata biyu indai yamiki"

" Hmmmm yayi kazo ka nemi izini, amma bansan soyayya ban iyaba kaima na amince ma ne dan naji har raina na aminta, bansan damu da kira aƙalla duk bayan 2dys waya sau 1 yayi kuma zan baka time dan bakoda yaushe nake son kira ba."

" Na shiga uku, wlh Beauty bazan iyaba gaskiya "

" Not beauty I'm Meerah or Ramlat "

" Ohhh sorry Madam "

" Goodnight " kafin yace komai tatse kiran, dariya Zaki yasa wanda yake gedan Haidar yana cewa

" Wlh Aliyu kayi sa'a kasan Ramlah kuwa, ta tsani soyayya kuma batayi, a Abuja tayi karatu dani acan muka haɗu, ni kaɗai take abota, a duk lokacin da namiji yace yana sonta to sai anyi da gaske inba haka ba sai tace zasuyi faɗa, wani rana har dambe takeyi da wasu dayake macece me kamar maza akwai ƙarfi da brain, ga tsiwa."

" Kace nakwaso ma kaina"

" aikuwa amma akwai riƙo da addini sosai ga bin gaskiya " a haka sukaita hira abinsu har sukai barci.


Bayan wata ɗaya abubuwa dayawa sun faru daga ciki akwai sa ranan auran Uncle Aliyu da Meera, bayan iyayenshi sun je har gidan su kuma yayyan ninta sun bashi dan mahaifinta ya rasu, hakama gurin su Ustaz sunata shirin dan duka su huɗun zai auran, dan tin washe garin ranan yasami Ramlah da maganan aiko batai musuba ta amince dukda kuwa ance mata baya iya tafiya.


Zaune take tana waya da Zaki akan case din dasuke dan jiya aka ƙara sakin wani kisan gilla da RASH yayi, hankalinta ya tashi sosai domin Babban jami'in Police aka kashe

" RASH mutum saikace aljani bamusan harin saba bamusan farmakin saba, ba sheda baya anfani da kowani abu gurin sharing Videos dinsa kawai datsan gidan Televisions yakeyi, taya zamu kamashi? "

" Karki ɗaga hankalin ki nanda 1 weeks zan shigo Kaduna bikin ki, zamu tattauna kuma ya kamata kidau hutu domin kiyi dilka kinsa...." Ƙet ta kashe wayan, batasan tunawa da maganan zatayi aure ji take kaman tace ta fasa amma tinda ƙannan mahaifinta sunshiga maganar tafasa, rufe Idonta tayi tana tina kwata-kwata sau 6 suka taɓa waya da shi koya kira bata ɗauka abubuwa sunyi mata yawa, amma kullum safe, rana da dare sai ta ga saƙon sa na soyayya tin bata karantawa har tafara a yanzu ita da kanta ma take duba wayan nata ko zata ga yaturo, agogo ta kalla ganin 3:15pm yasa ta dau wayanta tashiga contact, number shi wanda ko saving batayi ba amma tahaddace ta, Kira tayi amma harta katse ba'a ɗaga ba tsaki taja har zata aje wayan sai ga kiranshi, tanson ɗagawa amma dole tajira sai da yakusa katsewa tayi accepting takai kunne, muryansa taji ya yi mata amsakuwa, sai tasamu kanta da lumshe idanu gaskiya tayi kewanka sosai.

" Madam yau kece kika kurani, Wow naji daɗi Alhamdulillah faɗamin mekike so ko nazo ki gan nine?"

" Ba komai yanzu haka uku tayi tini " sai tayi shuru annan taci gaba da cewa "banga ni bane" jitai haushin kanta yakamata sai ta katse wayan takifa kanta a kan Desk cikin 2mnt SMS yashigo, cikin sauti ta buɗe tana karantawa, ta kara ta yafi sau 10, tanata jujjuya wayarta ƙiran hot 11, tana sakin murmushin dabatasan dalilinyin saba, saƙon yafara kaman haka (Imandhayaty - pillar of my heart, a gaskiya kinsani cikin farin ciki mara misaltuwa, ashe kindamu dani nagode sosai, kikulamin da kanki zuwa dare zankira ki Please ki ɗauka, busy nashiga yau shiyasa ban turo ba). aje wayan tayi tanajin daɗi a ranta, take kuma Idanuwata su kai kan rubutun dake facing dinta wanda akasa RASH, annurin fuskarta ya ɗauke sannan ta na tambayan kanta 'waye kai ? yaushe zaka bayya? kuma a ina ? Ina nan ina jiranka............

END

Daga Alƙalamin Sk .

[6/12, 12:43] ᑭᖇᗴTTY ՏK ✍️✍️✍️: https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

💪 JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIAION (J.W.A)💪
Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi.✍️

May Allah ﷻ accept all our righteous deeds bring us endless joy, peace, and prosperity.

✨ 🌙 🕋 Eid Mubarak 🕋 🌙 ✨

𝐑𝐀𝐒𝐇 Ɓ𝐎𝐘𝐀𝐘𝐘𝐄𝐍 𝐌𝐀𝐒𝐇𝐄Ƙ𝐈
ᑭᖇᗴTTY ՏK
ꜱᴀᴋɪɴᴀ ᴀʙᴅᴜʟʟᴀʜɪ
Page 12


*********** **************
KINKINAU
Bayan wani lokaci

Su huɗun suke zaune a Parlourn Umma suna kallon wani series me daɗi na korea, sallama sukaji ana yi tare da knocking get din, Zainab da ke zaune a kujeran dake kusa da ƙofa ta fita ta na amsa sallaman, sai ga ta ta shigo ta na faɗin

" Ramlat, sahibaty ce ta zo kingant.." ai kafin ta ƙasar har Ramlat ta fita da sauri, a tsakiyar cikin gidan suka haɗu sai suka rungume juna ita da ƙawarta, sannan suka shiga Parlour gaisawa suka yi da Maryam, Hajara cikin sakin fuskan sannan suka koma ɗakinsu, bayan ta ɗauko mata ruwa mai sanyi da zoɓo ta yi mata godiya ta na ce wa

" Mama bata nan ne?."

" Eh namesake, gaskiya na ji daɗin zuwan ki, Maman Rabi ta barki kenan?. "

" Kedai bari yanzu shiri muke yi sosai balle da su Radiya suka yi aure, anko na zo siya karya ƙare, ace Sahibaty ba ta yi ankon ba ai babu daɗi ba."

" Ai in ba ki yi anko ba babu magana kinsan kece kaɗai ƙawata, sai dai class mate kawai shiyasa ni bandamu da ankon ba, ban zuwa shagali kowa nasan babu me zuwa na wa gashi saura sati biyu."

" Hmmmm haka ne ai, ni ko anko bangani ba, na manta na tambaye ki lokacin da kika zo gidan mu ko colour din na gani." ta faɗa ta na kai zoɓon bakinta

" Hmmmmmm ya yi kyau gaskiya, zan nu na miki anjima."

" Tom, yanzu dai tin da ni ce babban ƙawa yakamata nasan ango tun kafin biki takwara"

" Hmmmm ni kai na ban san shi ba Ramlat."

" Kamarya Ramlat? Badai har yanzu be zo ba?."

" Eh takwara Abbu ya ce min bayanan ne, sai ana gobe biki ze dawo kinga."

" To amma ku na waya?."

" Har yau be kirani ba gaskiya, Uhmmm be damu bane share kawai." daga nan suka sauya hira da abubuwan da zasu na biki, ita ma Ramlat badikko ta ba ta labarin yadda suka shirya da Maman Rabi, dariya suka dinga yi. sai misalin biyar na yamma 5pm ta shirya ta amsa ankon amma Ramlat Kinkinau sam taƙi amsan kuɗin ankon, a haka suka rabu cikin ƙaunar juna da cewan in tazo biki kwana biyu zata yi tako amsa mata. Hijab Ramlat ta cire tanajin tausayin ƙawarta domin ta sha wahalan rayuwa a baya amma yanzu ta ga ta canza ta yi fresh abin ta, da yake tana da kyau sai yanzu kyawun na ta keta ƙara bayyana.

******** ********* *******

Rana ba ta ƙarya sai dai uwar ɗiya taji kunya, babban masallacin juma'a USMAN BIN AFFAN MASJEED KINKINAU. misalin biyu bayan an idar da sallan Jumma'a wanda muta ne sun cika maƙil kamar kowacce Jumma'a dan bautan Allah, 2:00pm dai-dai aka aura auran muta ne sama 20 wanda aciki na jiyo an ambaci Muhammad Bashir da Hajara Abdullahi Saleh Ustaz, Muhin Sunusi da Zainab Anas Saleh, Usman Usman da Maryam Abdullahi Saleh Ustaz sai Aliyu Haidar Abdulqadir da Ramlah Musa wato Meera bi sa sadakin dubu dari biyar adalan ba ajalanba. Kabbara aka kuma yi sai kuma can naji an kuma cewa, sai Shuraim Abdulqadir da Ramlat Abdullahi Saleh Ustaz, aure ya ɗauru an gama ɗauran yau, nan ma sai kabbara ke ta tashi da ga ta ko ina, kowa a gurin fuskarsa a sake yake banda Shuraim da ke kan kekensa ya haɗe rai sosai, ya yi kyau sanye ya ke da sky blue na shadda iri ɗaya da na Aliyu Haidar. Adam da ke gefan sa ya tsugunno sai tin sa ya ma faɗin

" Dama har da kai auren?" furzar da iskan bakinsa ya yi sannan ya koma yadda ya ke cikin sakin fuska sai ya ce

" Hmmmm ban sani ba amma naji a jikina kan cewa Pazars ba zasu barni haka ba amma mubar maganan sai mun koma gida." ɗaga kai Adamsi kawai ya yi, sai ga Zaki ya ƙaraso cikin walwala, shima manya kaya ne ya sanya wanda suka mai kyau sosai, ya ce

" Ango ango iyyeee ai ni banji an ce da kai ba ma sha Allah Babban yayanmu." Shuraim be ce komai sai ya miƙa mai hannu suka gaisa. Alhamdulillah taro ya watse a masallaci bayan an ci an sha an rabar domin an yi wasan kuɗi iya kuɗin. Motoci 6 ne su ka shiga babban gidan su, suna isa muta ne ne cike aciki kowa cikin an kon wani tsadaccen leshi Black and pitch. guɗa kawai ke tashi ango Aliyu sai murmushi yake yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login