Showing 90001 words to 93000 words out of 93691 words

Chapter 31 - RASH ƁOYAYYEN MASHEƘI. COMPLETE HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

230

ce.

"Kana kusa, amma ta ina ka shigo?, ƙamshin turaren na gab da n...." Sai wai, wato mai gadi ya fito ya gyara hutan, juyowa tai ta ganshi tsaye sai ta marairaice fuska ta ce.

"Tsora ta ni za ka yi da koh."

"Mun ɓata, ba ruwa da ke."

"Shike nan, ruwan juna da juna." Sai ya matso tare da ɗago fuskan ta ta kalleshi, ƙyafa idanu ta shiga yi kaman ƴar baby, ya ce.

"Yaushe za ki girma? Yaushe idan kika ma mijin ki abu za ki ba shi haƙuri?, Yaushe ne idan ya faɗa abu ko bai miki ba za ki yi na'am da shi?."

"Ai haka nake, kaima sheda ne."

"Ke wai?."

"Garantee Nawan 🥰,, sanan me ya kamata na yi kuma ina yi, irin rayuwar matan zamanin daa akwai ni da biyayya."

"Shut-up, ai in zance ne kinfi kowa iya tsarawa kaman mai waƙe."

"Uhmmm to ni me na yi?."

"Ba ki komai ba, yunwa na ke ji."

"Sai dai ka ci break banyi girki ba wallahi."

"Dalili?." Yafaɗa ya na sakin fuskanta sai ta ce

"Yau ni kallo na sha, na manta zan yi girki ne."

"Ya yi kyau, yanzu kije kimin tuwon shinkafa miyan agushi." Waro ido ta yi sai ta kalla agogo 9:23pm, marairaice fuska ta yi sai ta ce.

"Dan Allah Baby na ma indo....."

"Tuwo na ke so, kefa akwai biyayya na san yanzu za ki min ai, rayuwar ki na burge ni komai irin na mutanen da kike yi." Ya kai nan da sigar wasa, miƙewa ta yi ta shiga kitchen, da ido ya bita dan tafiya ta ke tana bubbuga ƙafa. Tin da ta shiga ba ta fito ba har sai da ta kammala dan ma akwai komai a ƙasa, duba wayarta ta yi har 10:41pm ta yi, ɗauko tuwon ta yi wanda cin mutum ɗaya ta yi haka miyan haka. Kallo ya ke yi sai ta ajiye mai sannan ta nufa bedroom ɗin ta amma kafin ta shiga ta ji ya ce.

"Dawo ba ki kammala ba." Kaman ba zata juyo ba sai ta dawo, ta bi ta haɗe rai.

"Oyaah feed me Madam." Kaman ta kurma ihu haka tai sai ta zauna ta ɗauki spoon sannan ta fara ba shi, 4spoon ya yi ya ce.

"Na gode, na ƙoshi." Kallan tuwon ta yi dan ko kwata bai ci ba, kuka ta fashe da shi kaman an mata wani abu.

"Baby menene?."

"Gyale ni, na ma abu ka ƙi ci, kasan wahalar girki kuwa....." Sai ta ci gaba da kukan, hannu ya sa ya riƙota ya ce.

"Sorry wasa na ke miki ban na ci, jeki wanka." Miƙewa ta yi ta wuce, shikuma ya ci gaba da kallon sa dan ya ƙoshi ɗin.
END


Page 73.
******************** *****************

BAYAN SHEKARA HUDU.


_____________ Lokaci ya jaa, rayuwa ta sauya sosai, abubuwan masu daɗi da akasin haka sun faru. bara mu dubi zuwa kowani ɓangaren dan ganin wani sauyi aka samu ko akasin sa.

***** Milinium City, Rhyneo estate *******

_______ Ma sha Allah tin da ga waje na fara ganin sauyi ba na wasa ba, ko da na shiga cikin gidan haka nan ma, main Parlour na shiga, cikin Sa'a na datta kusan kowa na gidan, harda ƴam mata uku wanda sai da nayi da gaske na ga ne su, Baby, Karis, Butter, sun ƙara girma ma sha Allah kyau da cikin halitta duk ta gama bayya a jikin su, Pazars na gani wanda duk girma ya ƙara kama su sosai, ƴar yarin ya na ga kyakykywa ta fito d gudu daga wani ɗaki, ta na riƙe da bindiga na wasa, Parlour ta iso ta ce.

"Aunty kin ga twins?, Yau sai na harbi Hussain." Sai da suka yi dariya dan yadda ta yi maganan cikin hausar ta, Aunty da itama ta ɗan sauya ta kalla small Ammee ta ce.

"Du ba su dai, ba kiga Aunty's ɗin ki ba ne, gaishe su."

"Tom, ina kwana, ina kwana, ina kwana." Ta gaida su Baby dan ba ta san su ba, fiiii ta gudu ta bar gun.

"Ina ga wata Police ɗin za mu yi." Pazars Q ya faɗa yana murmushi dan sun shan drama, sai Hajiya ta ce.

"Ku shiga ku huta, zuwa anjima za suka duk sun iso." Suka amsa sannan suka shiga part ɗin su wanda sukai kewan sa sosai, shekara uku ba wasa ba, ko gida ba su waiwaya ba sai yau.


***** Air Force Base*****

__________ Idanuna ne suka sauka a kan wacce har na mance da ita wato Hafsat, riƙe ta ke da mopar ta na mopping, wayarta da ke ringing ta ɗauka ganin number tsohon mijinta ya sa ta ɗauka, bayan sun gaisa ya ce.

"Hafsatu yanzu na dawo da ga Kano, kuma Alhamdulillah ta ke su Yaya Bashir suka ɗaura mana aure." Kukan murna ta shiga yi, sai ta katse kiran, ta ma rasa ina za ta sanya kanta dan murna, tun bayan samun lafiyarta ta dawo gida, sai dai ba ta samu Maa da Dad ba duk sun koma ga Allah, cikin ikon Allah su Fatima suka tarbe ta cikin kula, haka suka fara sabuwar rayuwa duk da ta na cikin wani hali, dan ita ma Halima ta rasu, dan ciwo yaƙi ci yaƙi cinye wa. da sauri ta ake ta nufi part ɗin Fancy, knowing ta yi sai ta ji muryan Airah.

"Yes Coming." ta shiga da murnan ta ɗan a yanzu sune ƴan uwanta, sai dan gin Dad wan suke garin kano, kuma can ta tura Muktar.

Ganin yadda ta shigo ya sa Airah da Fancy kallonta sai Fancy ta ce

"Aunty Hafsat lafiya?."

"Lafiya har yanzu ba ku gama shirya wa ba?."

"Mun gama, yanzu za mu wuce, amma faɗi abin da ke bakin ki." Airah ta faɗa suna mai da hankalin su gareta.

"Yanzu Muktar ya kira ni, wai an ɗaura daga zuwa tambaya."

"Kai ma sha Allah, gaskiya na ji daɗin wannan albishir ɗin."

"Na gode Ummu-Affan (Fancy 😳)"

"Amarya, Amarya, Allah ya bada zaman lafiya, bara muyi sauri mu dawo dan akwai meeting akan shagali bikin nan."

"Hmmm Ummu-Arif kenan, to sai kun dawo." Sai ta bar ɗakin, Fancy ce ta kalla Arif da ke shan barci ta ce.

"Ummu-Arif ɗauke shi muje, kinga Affan na barci a mota, badan su Butter na a nan zan barta wallahi." Daga haka suka fita zuwa coumound, motan Airah suka hau, suka ɗau hanya, Arif Fancy ta riƙe wanda ke kama da A.A, da fari mace ta haifa sai ta koma ga Allah, ita ma a lokacin ya haifa Affan, sai bayan dan lokaci ta kuma haifan twins, mace da namiji, Arif da Anam, still bayan wata biyu macen ta rasu, yanzu dai Arif shekaran shi ɗaya da rabi, shi kuma Affan Shekara 3.........




***** K.K GRA.******
_________ Motan Husty ce akwai mai dan haka nan suka shiga, suka ɗauki hanya zuwa gida, su biyu a gaba Hasty da Husty sai bayan wanda yara biyar na gani ɗaya na barci jariri yaron Hasty Ameer, kafin shi, a rana ɗaya suka haifi twins, Hasty mata, Husty kuma maza, su ma shekaran su uku, sai kuma Hasty ta kuma haifan na miji wanda watan shi hudu da kwana biyu, su ma Hajiyar su ta rasu bayan haihuwan Ameer da sati biyu, sun sha kuka fiye da zato mutum, hatta Meerah sun fita shiga yaya ni a bayyane amma dai kowa ya san Uwa Uwace.



_________ misalin 1pm suka isa babban gidan na su, cikin murna aka tare be su, zaune suke a suna shan hira sai ga su Beasty, Beauty, Kandy, Beasty da Beauty sun haifa yara mata suma shekarun su 3, Beasty ƴarta mai suna Ramlat, Beauty kuma Maryam ta sanya ma ɗiyarta, Kandy ce kawai ba ta haihuba sai dai tana ɗauke da tsohon ciki wanda akai scanning twins ne.

Gidan ma sha Allah ko ina yara ne ƴan dugwi dugwi sai wasa suke yi, bayan sun huta Ramlat ta shigo part ɗin, tin daga nesa na hangi irin sauyawan da ta yi, ta yi wani mugun kyau, ta yi free haka ta yi ƙiba daidai. Zama ta yi suka hira sai ta kira Small Ammee, bayan ga zo ta ce.

"Kira min ƴan biyu." Da gudu ta koma haraban gidan ta kira su, da yake sune manyan a maza sun tara yara suna wasa, Ammee na zuwa suka ka mata dan dama ta sa su kuka ɗazu, duka suka mata dan su akwai cika fuska sosai, za ka za ci sun girme ta, ita kam uwar kuka sai ta fashe da kuka. A haka suka shiga main Parlour ɗin.

"Small Ammee waya ta ɓa ki.?" Kandy ta faɗa sai ta ce.

"Twins ne suka duke ni."

"Ban hana ku taɓa ta ɓa, yayar ku ce fa." Ramlat ta faɗa tana haɗe musu fuska, da da yake Hussain shine rama kunya sai ya ce.

"Mom tin da zu take dukan Hassan ni kuma ta ji ƙani, na mata gargadi (magana yaro ne) sam ba ta ji ba, shine muka mata dukka."

"Innalillahi haka ka zama Hussain." Faɗin Husty.

"Wannan ai baya jin, shi ne ya gado manyan ido ashe na rashin kunya ne." Kafin Momcy ta kulle ba ki ya ce.

"Ni kowa ma ga na, wallahi ko." Ya yi kwafa ya na barin gurin.

"Abdulraheem zo nan."ya na ji Ramlat na kiran sa ya fice.

"Hmmm wallahi za ka shigo hannu ai, Hussan ma za kaje gidan Uncle Umar ka kira Maman Triple."

"To sai na goyo ɗaya?." Smalla ta faɗa sai Hassan shima ya ce.

"Mom ni ma na ɗauki ɗaya?."

"Eh kuje." Kafin ta kuma magana har sun fice.

"Allah ya shirye ku, Butter kuje ku ɗauko mata yaran, dan Sakeenat ba iya ɗaukan jarirai uku za tai ba." Su ukun suka fita, da yake unguwan akwai tsaro su Ammee har sun shiga, a tsakar gidan suka ga Sakeenat da abin turawa wanda yara jarirai uku mata ke kwance a ciki sai aka rufe saman saboda rana. Gaisheta suka yi ta amsa sannan suka jera, ita ma sai yanzu Allah ya bata, tashi ɗaya ƴan uku mata, Airah, Amrah, Afra, koya ya yi murna balle Zaki, aikam Sakeenat ta ga masoya hatta Mama Zulaikha sai da ta zo a lokacin, ta sha gata sosai, kuma har yanzu ta na samun kulawa, ƴan aiki biyu aka kai mata, tayi arba'in dan haka ta fara fita sama sama, da ƙafan da Zaki ya mata suka shiga sai ga su a gidan su Meerah, shiga suka yi nan fa gidan ya ƙara kaurewa ya hira, ga yara masu kawo complain da masu kuka, ƴan uku ne a gidan sun sha girke girke sosai.

Misalin 5pm Meerah ta dawo a wata arniyar mota wanda Yusuf da Yunus suka siya mata, sai ta kyautar da nata wanda Haidar ya siya mata. Yanzu ba ta zuwa aiki sai lokaci lokaci takan leƙa, yau ma babban abu ne ya kaita. da farin ciki ta isa gurin matan gidan, ta zauna suka da sa hira, Small Ammee ta zo da gudu ta hau jikinta ta na ce wa.

"Police station kika je?."

"Ba sannu sai tambaya, nan naje."

"Tom nima yau zan kama Hussaini za ki kulle shi koh."

"Me ya miki?."

"Duka na, dan na harbe shi."

"Ban ha naki wasa da bindigan ruwa ba, ni wallahi na ƙosa a koma hutu, kun ishemu." Da ga nan suka sauya sabon hira, sai bayan isha'i suka watse, dan nan da sati biyu bikin three ladies, Butter lecture ne a school ɗin su, amma a Nigeria iyayen shi suke, Babu kuma wani Balarabe ne a can Saudiyya ya ke, sai Karis ita kuma a Saudiyyan suka haɗu amma a London ya ke, baban shi ɗan United States ne, mamarsa ce ƴar Nigeria.
END.



True love may be hard to define,but the signs to read true love can be clearly seen in every loving relationship


Page 74.
************* ***********
***** RASH*****

________Tin shekarun baya ƙungiyar ta bayyana, ƙungiyar Rash wanda a duk faɗin Nigeria ake magana, a yanzu ta zama group ma fi daraja sosai, bayan dogon bincika hatta shugaban ƙasa ya ba su sanya hannu akan aikin su, aikin gaskiya da gaskiya suke yi, gaba ɗaya unguwan ba mai shiga sai mai son ganin Rash, kowa na ƙasar son ganin sa suke, amma baya bayya nuwa hatta jami'an sa wanda sunfi sama da dari uku babu wanda ake ganin fuskan sa domin wani fuske suke sanya wa mai fuskan biri, gaba ɗaya fuskan ke rufewa.

Kamar kullum yau ma tawagar R.1 suka dawo shugaban ta wagan shine Damuwa R.1 (Adam), tawar Skiddo A.2, tawagar Spider S.3, sai tawagar Madaa (a cikin members ne aka zaɓe shi saboda jajirce wan shi.) Shine H.4.

Sauka sukai a jerin motoci wanda a yanzu idan sun fita har binsu ake yi, yadda kasan jami'an polices haka suke, kuma cikin sanye da uniform iri ɗaya, mutane matasa da waya suna fatan ganin su a cikin wannan group ɗin na ƙasa.

"Damusa, na za ci sai gobe za ku dawo."

"A'a Spider, ai muna gama Meeting da Tsohon shugaban ƙasan Algeriya mukai juyo."

"Okh, muma jiran Boss muke yi." Kafin ya ce wani abu sai ga Rash nan ya fito, sai da na ƙara goge idanuna sannan na kuma kallon sa, ba za ka ce Rash ɗin shekara hudun baya ba ne, saboda wannan Rash ɗin yafi wancan komai da komai, ya ƙara girma da faɗi, gemun na nasa ya cika sosai, girma da kamala sun bayyana sosai a jikin sa. ta ku ya je kamar wani namjin ɗawisu, har tsakiyar Parlour ya kawo, sannan ya zauna, Barka da fitowa suka mai sai ya ɗaga musu kai sannan ya na latsa kiran number Ramlat, bugu biyu ta ɗauka sai ya ce.

"Yau dai zan cika miki burin ki." Ban ji mai ta ce ba, sai dai murmushin da ya yi sannan ya katse kiran, kallon su ya yi sai ya ce

"Muje." Daga haka suka fito dukkan su, su hudu ne suka hau mota ɗaya, sai wasu moto biyu suka sa na su a tsakiya. Ba su tsaya a ko ina ba sai gidan su Shuraim. Gaba ɗaya mutanen gidan ne, dan yanzu masu huce wa ke niyyan tafiya da tini sun wuce amma Ramlat ta ce su jira Baban yaya. Ramlat ya kira sai ga su mutanen gidan sun fito dan ta ce su firfito. Sun dai ga motoci uku a tsakiyan gidan, hatta Zaki da Aliyu suna gida, Zaki ne ya kalla Sakeenat, murmushi ta sar mai, dan tintini ta shaida mai waye RASH.

Mutanen ciki ne suka firfito sanye da wannan fuske ga uniform mai ɗauke da tambarin Rash. Kowa zaro idanuwa suka yi dan ganin wa'innan sai Aliyu ya matso.

"Rash Members, Fatan ba wani ne ya muku abu ba."

"Eh His Excellency." Ɗaya ya faɗa. Take masu tsaron gidan suka rirrige bundugu, dan ma Ramlat ta ce idan wasu motoci sun zo banda bincike an san da zuwan su shine suka bari suka shiga.

"No, ko aje makaimai, me ke tafe da ku?." Kafin wani ya yi magana sai maza uku suka fito suma sanye da fuske ɗin, daga nan shima jagaba ya fito, a tsakiya ya tsaya, suna ganin shi suka san shine Shugaba domin shi ne da uniform kuma fusken sa da banbanci da na sauran. A cikin mamakin ƴan gidan ke kallon wanann tawagan, hannu Boss ya a kan mask ɗin ya cire. Take suka waro idanuwa ganin Babban yaya a tsaye. Mamaki da firgici ne ya bayya ga fuskokinsu.

"Babban yaya, kai ne..... RASH." Aliyu ya faɗa cikin haɗo kalmomin da ƙyar, ɗaga kai ya yi sannan ya yi taku zuwa hudu, ya ce.

"Ni ne Rash, ban so bayya muku amma Ramlat ta sanya ni, bayan yin dogon tinani na ce bara yau na bayya a gare ku." Pazars Q ne ya matso gab da Shuraim ya ce.

"Shuraim ne?, To ai Shuraim baya ta fiya..."

"Baba ni ne, Shuraim kuma Ni ne Rash."

"Dan Allah mu shiga cikin Parlour." Ba musu kowa ya koma ciki. Rash ne ya ce.

"Da fari ina neman gafaran ku, dan na ɓoye muku asalin waye ni, a gaskiya sama da shekara biyar ina wanan aiki, kafin na fara ni dama jami'i ne. Ba komai ya sa na zama Rash ba fa ce, Abokina Adam." Ya faɗa ta ke Adam ya cire fusken da ke fuskan shi, sam ba suyi mamaki ba dan sun san za su ka sance tare dama.

"A lokacin baya Adam ya na rayuwa cikin kulawa iyayen shi, wata rana aka shiga cikin gidan don yin sata, ma su satan suka kashe Maman shi da Baban shi, a lokacin muna tare da Adam, ko bayan na sauke shi a mota da ya shiga, sai yaga gidan a buɗe, take hankalin sa ya tashi, tare muka shiga ciki, sai mai abin da muka tadda ba bi kyau, an musu fashi, an sace musu abubu da waya sannan an kashe mai iyaye, mun kai ƙara amma ba doka, sai ce wa suka yi, ma su irin wanann ta'asar a ƙasar nan suna da yawa. Kun san yadda na ke ji da abokina kuwa, ina son sa sosai, ko da nake jami'i na nema shuwagan nina su shiga maganar amma kowa na taɓa sai ace na bar maganan, da ga lokacin na ke da wani nufi a ƙasar nan, bayan lokacin da na tara hujjoji sosai, na yi plan aka na zama gurgu haka na ci gaba da bincin, ina fita ƙasashen waje amma ba sosai ba, ina cikin ƙasar nan, ganin idan ban yi maganin komai da kaina ba to bazan ji daɗi ba domin a binciken na ga no abubuwa da yawa akan ƙasar nan shine na ƙudirta za ma RASH." Sai ya yi shuru sannan ya da sa.

" Cikin ɗan lokacin na haɗa da karu masu rai da lafiya, training sosai na koya musu, sannan da kishin ƙasar su, a cikin su ina da amintattu sune Sunusi da Mubarak." Take suma suka cire mask ɗin su, Beasty da Beauty suka waro idanu sosai.

"Ina fatan ban muku laifi ba." Babu wanda ya iya magana a cikin su ma sai mamaki. Ramlat ce ta nufe sa ta rungume shi, sai kuka ya kwace mata.

"Is okay, shike nan ko."

"Uhm." Sai ta sake shi take sauran ladies suma suka zaga ye shi cikin murnan. Meerah da Sakeenat ne kawai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login