Showing 81001 words to 84000 words out of 93691 words
Halima suke, dan yanzu ba sa gidan nan, amma da sa ni na kuma da yadda ta, kin san ba zan cutar da su ba, dan nima ƙannai na ne kuma yara na."
"Ina ka kaisu toh?."
" Kimin alƙawarin ba za ki tambaya kowa ba kuma ni ma kibar tambaya ta, lokaci na nan zuwa za su dawo."
"Shike nan na yadda."
END.
Page 65.
*********** ************
_____ Da idanu ta bisa har ya isa wardrobe ya sanya kayan aikin sa, sannan ya juyo ya kalleta.
" Wannan kallon fa, ko duk gajiyan suna ne?."
"Sai ka ce Naman twins."
"To ai naga duk kin gaji ne, kuma nima twins nake so gaskiya." Ya faɗa ya na ɗago fuskanta sai ta sakar mai da murmushi, sannan ta ce.
" Allah ya ba mu."
"Ameen Mu Pretty Sk, faɗa min ko a kunne ne?."
" Me ne?." Ta mai tambayan tana gyara zaman ta zuwa jikinsa.
"Kullum ƙara kyau ki ke yi, menene sirrin ne?." Dariya ta ɗan yi tana aiyana ta yadda za ta sanya ya faɗa mata abun da ta ke maradi.
" Kai ne sirrin ai, kana kula da ni sosai, sai dai na ce Alhamdulillah, Baby na Dan Allah ka faɗamin wani abu mana."
"Ina jinki."
"Waye ya tona asirina har kuka kama ni?."
" Oh Pretty Sk abu baya wuce a gunki wai......"
"uhm uhm uhm uhm."
"A'a ni kar kimin shaƙwaɓa ki hani fita, i promise idan na dawo zan faɗa miki." Murmushi ta yi sannan ta mike tsaye, tare suka yi breakfast sanna ya wuce, sai misalin 10am ta shiga gidan suna dan yin aiki, a parlour ta haɗu da Meerah, part ɗin ta suka shiga dan kaso wasu kaya.
Wanke kayan cikin nama suke yi su, Beauty,Kandy, Sakeenat da Meerah, su kuma Beasty,Hasty, da Husty suna yankan nama ne.
"Bayan Fatima sai waye mai juna biyu a cikin ku, shurun ya yi yawa fa." Meerah ta faɗa sai suka kwashe da dariya.
"Beasty, Hasty, da Husty Allah ya basu saura mu." Faɗin Kandy sai Beasty ta ce.
"A'a ba dai ni ba ko?"
"Ke mana."
"Ai kema kina da shi." Beauty ta dalla ma Beasty hararan wasa, sai Meerah ta ce
" To menene abin jin kunya dukkan mu mata ne ai, Allah dai ya raba lafiya." "Ameen" suka haɗa baki sai Meerah ta kuma ce wa.
" Kyanshi Hasty da Husty ku haifo twins rana ɗaya."
"Wallahi kam."
"Su kandy an iya bada amsa ai, saura ke da Sk ai." Sakeenat dai murmushi ta yi dan calculation ta ke yi, a yau ta ke so jin labarin Baban yaya a baki mutane hudu, Zaki, Ramlat, team of ladies da Meerah.
"Auntyn Meerah, ki ba mu labarin soyayyan ku da His Excellency, dan jiya munga love." Dariya suka sa sai Hasty ta ce.
" Gaskiya kam a bamu labari."
"Beauty ku gyara na dinga hangen Ummee ammee da kyau."
" To uwar son story." Beauty ta faɗa sai Meerah ta ce.
"Gaskiya ni bamuyi wani soyayya ba dan ban iya ba, shi kuma Yayanku Haidar, lallaɓa ni yake yi, sai bayan munyi aure ne muka sha love, wata dai ta ba mu na ta."
" Da Fancy na nan ne toh da ta bamu dan ita uwar love ce." Faɗin Hasty sai Meerah ta ce.
"Naman tweens ba tanan da ita ma ta bamu labari......."
"Tab Baban yaya ina ya iya soyayya, hatta abokinsa ba ya bari mu wani sha love balle shi ace yanayi."
"Kai Kandy, ai irinsu wallahi sunfi iya soyayya." Sakeenat ta saki murmushi dan anzo in da ta ke so.
" Ku dai barshi da sanin System." Faɗin Husty sai Beauty ta ce.
"Ke dai bari, ai wannan yadda ku kasan al'jani, da munyi abu take ya ke sani."
"Sai na tina rayuwar baya, kaman fa ya dasa mana bi diddigi, komai mukai take ya ke sani, hmmmmm munji jiki wallahi." Husty ta kaina tana tina da yadda suka kwashe da Babban yaya. Sai Sakeenat ta ce.
" Kunji daɗi kam, dan samun mai kula da mutum haka ai da daɗi...."
" Banda kalan na Baban yaya, dan dai baki san shi bane Aunty Sk, wallahi mun ci uban mu, ai Baban yaya Boss ne, shi yasa muke ce mai Boss."
"Kandy ina ranan da kika je birthday ɗin class mate ɗinkin...."
"Beauty bar tina min, hmmmm abu kaman wasa yanzu komai ya wuce."
"Haka ne, komai lokaci ne ai." Sakeenat ta faɗa bayan ta gama auna zancen su akan mizaji. Bayan sun kammala Sakeenat da Meerah suka je part ɗin Meerah dan duba Small Ammee ko ta farka, ba ta farka ba dan haka suka zauna dan su huta.
" Auntyn Meerah wai da gaske haka Babban yaya ya ke, na ganshi kaman ba zai yi zafi ba."
" Hmmmm be da zafi amma akwai tsauri akan ladies, yadda Haidar ke faɗa min ya ce sam be damuwa, matsalan sa ɗaya shine rashin zaman gida, yau yana nan gobe ya bar gun."
"Wai maybe yana yin work na shi ne?". Sk ta furta da fatan ta samu ƙarin bayani agunta.
"Eh to online business da aikin bank yake yi, na san dai zai zama mai matsayi because ya san system sosai." Daga nan suka can za hira zuwa wani daban. Bayan ɗan lokaci suka koma bakin aiki. Hajiya ce ta ɗauki yaji da ke cikin ƙaramin farin rober ta ce.
" Sasakee, ungo wannan ɗan kai ma Me jego." Murmushi ta yi dan jin yadda ta kira ta don ita ce kadai mai kiranta da haka, amsa tayi sanan ta nufa part ɗin Babban yaya, ko bayyan ta ba Ramlat ɗin sai ta ɗauki Hussain tana kallon sa.
"Wancan ya fi wannan son barci, duk time ɗin da na leƙo wannan idonsa biyu na ke gani."
" Haka suke dan ma bai yawan kuka da abin ba sauƙi."
"Aunty Ramlat kin san wai har yanzu wannan mugun na raye, yanzu na tina zan koma gidan na duba wani abu akan sa." Ta kai nan tana kallon fuskan Ramlat da ke latsa waya, yadda ta yi fata ne sai ta ga yana yinta ya sauya sannan ta ce.
"Wai Rash?."
"Abin da mamaki ko."
" Sosai ma kuwa, amma ta ya kuka sani?."
"Bincike dai, amma ba Rash ba fa, wani ne Harun da muke bincike a kansa, ɓarawo ne so an ce ya mutu ashe ƙarya ne." Take ta ɗan saki ran ta sanan ta ce.
"Wayyo, ai na za ci Rash ne, Allah ya shirya mu gana ɗaya."
" Ameen, Bara na koma kar suce na tsaya." Daga haka ta miƙa mata shi sannan ta fice..
**************** *****************
Misalin 4:23pm, a hankali ta fara buɗe idanunta, p.o.p shine abin da idanunta suka fara gani sai ta kalla gefe da gefan ɗakin, Fancy fa ke zaune ta miƙa tare da nufota ta na ce wa.
"Alhamdulillah, Alhamdulillah kin farka, Airah sannu ya jikin?." ta faɗa tana taimaka mata ta zauna da kyau. " Bara na kira Doc....." Ta katse magana ta sakamakon riƙo hannunta ta karfi Airah ta yi, sannan ta fara magana a natse kuma a hankali irin na marasa lafiya.
"No need, ki kaini gun Ramlat yanzu."
"A'a, Doctor zan kira ya ga kin fark...."
"Fatima Please, muje yanzu akwai abin da zan ce mata ne."
"Ba ki da lafiya, a ina ma kika san ta."
"Bazan iya magana ba kawai yanzu dan Allah." Take hawaye suka wanke fuskanta, cikin matuƙar da burgewa Fancy ta rungumeta sannan ta ce.
"Mu je." Da ka ganta kasan ba ta cikin isasshen lafiya, dan tafiya ma da ƙyar da take yi, a haka su lallaɓa har haraban Asibitin in da Fancy ta yi parking motarta, ko bayan sun shiga ga ɗau hanya kuka mai ciwo Airah take yi wanda ya yi mugun ba Fancy mamaki, Fancy Kan ta fita ta kira number A.A ta ce mai ya biyo bayan su. Ko a lokacin da ya fito da mamaki yaga sun shiga mota har ta bar asibitin cikin sauri ya sauka daga stairs sannan ya shiga na sa mota tare da kiran Fancy amma ba ta ɗaga ba, har kira biyar ya yi sai ya haƙura tare da ci gaba da bin su.
END
Page 67.
*************** ***************
RASH
______________ Shuraim da Adamsy ne suka sauka a mota, a hankali Adam ya ke tura shi a keke ya na mai magana cikin raɗa-raɗa.
"Boss, a halin yanzu Spider ya isa can, ya ce tawaga ta zama cikin shiri."
"Ku yi komai yadda ya da ce, zuwa 5pm zamu fita."
"Okh sir."
Tin daga ne sa ƴam matan suka yo kan Babban yaya, Kandy kuma ta ƙarasa kusa da Adam suna ɗan hira, Sakeenat da ke kusa da Meerah kallon su kawai suke kowa da abin da take aiyanawa a ranta.
"Baby kira Auntyn ku kice ta zo muyi hotan tarihi da babies." Babban yaya ya faɗa take Baby ta yi cikin gidan dan cika umarnin sa, ba su ɗau lokaci ba sai ga Ramlat ta fito sanye da cikin wani lifaya ja mai kwalliyan ɓaki, kusan ja yana haske fararen mata, take ta haska gurin dan ba ƙarya Ramlat akwai kyau mai suna kyau. Adam ne ya ɗauke su hoto harda su Aunty duk sun fito, hatta Mama Zulaikha ta zo yau ma. Bayan sun gama ne aka koma videos cikin raha suke komai. sec 1, sec 2, sec 3 zuwa sec 10, take get ɗin gidan ya buɗe motoci uku suka shigo haraban gidan, sannan mai gadi ya kulle get ɗin. Kowa ya bi motocin da ido dan ganin su waye a ciki, A.A da ya fi han zari ko motan bai kashe ba ya fito yana nufan motan Fancy da take son daidaita parking ɗin ta, a parking lot sai ɗayan motan ba ban san ta waye ba....................
(Hmmmmm bara mu ɗan huta koh, kaman duk mun gaji.............).
***************** *****************
Air Force Base
_________ Shuru babu mai motsi acikin su biyar ɗin da ke parlour, Dad wanda yake gun aiki aka kira shi ya dawo, Maa da ke zaune ta yi tagumi, Hajiya, Yunus da Yusuf suma suna zaune sunyi jugum, dan sun zo ne akan suga Hafsat sai suka riski mummunan labarin da ya sa me ta, ba musu suka yafe mata, Maa ta sha kuka akan haka dan gani ta ke koma menene laifin ta ne akan kabarin Hafsat.
"Allah ya kyauta, kuma ya yafe mana gana ɗaya, bara mu ta fi." Hajiya ta faɗa tana miƙawa, su ma twins haka, sai Dad ya ce.
"Mun gode Hajiya, Allah ya sa ka da alkhari, mun gode sosai."
"Ayya babu da muwa." Har Motan suka raka su, bayan sun koma cikin gida, Maa ta ɗauki wayan Hafsat ɗin tare da cire sim ɗin ta ɓalla, tinda hauka ya sami Hafsat take riƙe da wayarta, ɗazu kam a kaita kira Allah ya so ta ɗauka, ita ce ta musu kwatance gidan bayan sunyi waya da jami'an bakin get base shine suka samu damar shiga.....
____ "Wannan unguwa akwai kyau, ga tsaro ɗan ko ina ga sojoji nan." Hajiya ta faɗa a daidai suna barin cikin base ɗin.
"Aifa ai su a security suke, yanzu Milinium muka nufa koh?." Yunus ya tambaya dan shi ke driving sai Hajiya ta ce.
"Eh, kaimu muga yara, Hassan."
"Na'am." Yusuf ya faɗa ya na maida hankalin sa ga su ɗan waya yake latsawa, shi kuma Yunus ya juya kan motansa zuwa gidan su Babynsa.
"Karka sa abu a ranka fa, dan Allah komai ya wuce."
"Hajiya wallahi ya wuce, da ta na nan ne to sai mun shiga coat, ta sanni ta san waye ni, amma by now ya wuce."
"Yauwa yaro na."
****************** **************
Hajiya da Twins ne suka fito a cikin motan dake bayan na A.A, ya tare hanya babu daman su gyara na su parking ɗin dan haka suka fito, ganin jama'a gidan suna tsakar gida ya sa suka nufe so da fara'a. Kafin su fara gaisawa Fancy ta fito daga motarta tana ƙoƙarin zagayawa ɗaukan ɓangaren dan taimaka ma Airah.
"Matar Yaya lafiya waina." A.A ya faɗa yana isa gabanta.
"Kwada da kazo taimaka ta fito daga cikin motan, ta bi ta ruɗani da na kawota nan gidan." Ta faɗa tana buɗe murfin motan baya dan anan ta Airah ta kwanta.
Ganin kaman ba lafiya ba yasa su ka ɗan matsa kusa da Fancy suna tambayan lafiya.
"Airah mun zo ki fito." Fancy ta faɗa sai ga Airah ta fito, da fuskan A.A ta fara cin karo take fuskanta ta ƙare haɗewa, hannunta A.A ya rige ya na ce wa.
"Airah, lafiya wai? Jikin ki babu kwari, muje na maidaki hosbit......" Hannunta ta fizge tana ce wa
"Waye kai? Kyaleni."
"Waye, waye ni....." Ya faɗa da wani irin murya dan ya harbo jirgin, Airah ta warke daga cutar da ya ka mata. Kafin ya kuma magana ta nufa Ramlat da gudu ta rungumeta tana kuka ta na ce wa.
"Ra...ra..ramm..lat, Ramlat....." Sai luuu ta suma, take suka hau salati, da gyara aka ɗauke ta aka cikin gidan ta ida, A.A dai mutuwar tsaye ya yi, Fancy da Ramlat su ma kaman jikin su ya mutu murus da sauran mutanen da ke tsaye.
"Kifayaty kin santa ne?."
"A'a, ni ta tsora ta ni wallahi, Allah yasa lafiya dai." Ramlat ta faɗa tana tura Babban yaya zuwa cikin parlour.
_______ "Ƙanin miji mu je ciki." Fancy ta faɗa tana yin gaba, take ya bi bayanta, sai dai shi bai ƙarasa cikin babban parlourn ba ya tsaya cak, badan komai ba, sai dan ganin.................... (Kar naja rai koh 🤗 .)
______ sai dan ganin......... Alƙalamina ya karye gaskiya ✍️, Bara na siyo sabo....... Bye guys. Karku manta kuna tare da Pretty SK ce ✍️✍️✍️✍️✍️.
Page 68.
*********************** ********************
____________ Fuskoki biyu ya gani a guri ɗaya, saurin da fa kansa ya yi tare da furta duk kalmomin da ke bakin sa, "Lokaci ya yi." Ya furta a hankali yana ƙara ta ku zuwa in da zai zauna, gana ɗaya ya rasa sukuni sai faman bin su yake da idanu, Mama Zulaikha da Sakeenat, ba ma wacce yafi kallo kaman Sakeenat, dafa kansa yayi yana ƙaro dauriya.
_______ an samu ta farka da salati a bakinta, A.A shine kan gaba a gurin ɗagota daga kwanciyan, dan ya za ci ta koma gidan jiya ne.
"Airah, baki da lafiya, muje asibiti yanzu."
"Malam waye kai? Bar ta ɓamin hannu." Ta fizge hannunta sai Fancy ta ce.
"Airah wannan Mijin ki ne, Abdullahi ne....."
"Fatima." Ta faɗa tana miƙewa tare da nufan Ramlat da duk motsin Airah ta sa ma ido.
'Ramlat na dawo, Ramlat ɗinkin ta dawo, ƙawata ko baki gane ni bane." Ganin Ramlat bata motsa ba ya sa ta sake ta ta nufa Sakeenat ta na kuma ce wa.
"Uhmmm ya na sunan ki, ku kalla ko muna da banbanci, ke ma baki ga ne ni ba, yauwa Sakeenat, eh Sakeenat sunan ki koh." Sk ta daga kai kawai batan ta fahimci inda maganar na ta ke dosa ba.
"Naga kowa na bina da ido ne, wai lafiya kuwa kumin baya ni na gane." Ta durgushe a ƙasa tana kuka, kowa dai ido ya sa mata, A.A ne ya nufe ta ya ɗagota yana ce wa.
"Airah, natsu na ce ki...."
"Waye kai?, Waye kai?, Kar ka kuma ta ɓani na faɗa maka."
" Ko dai ta samu matsala ne a kanta?." Fancy ta faɗa cikin ɗan da burce wa take, His Excellency da Zaki suka shigo cikin main parlour ɗin, komai ya mai da idon sa ga su, take Airah ta nufi Zaki da gudu ta rungumesa ta na cewa.
"Idan kowa ya manta ni, nasan banda kai Mu A. Asad." da sauri ya raba jikin sa da na ta yana kallonta cikin mamaki, duk da A. Asad da ta faɗa ya shiga brain ɗin sa ya ce.
"Ki na hauka ne za ki ta ɓani haka, wace ce ke?." Dam Dam, ƙijinta ya buga, baya ta ja sannan ta ɗurƙushe gwiwowinta ta kafin ta fara magana taji an dafa kafaɗarta cikin sauri ta ɗago, sai suka haɗa ido da Ramlat.
" Miƙa tsaye, share hawayen ki, faɗa min a ina kika sanni?." Take kanta ya kuma sarawa sai ta dafe kan, Ramlat hannunta ta sa ta riƙon hannunta, take Airah ta kalla hannunta, a kallo ɗaya ƙirjinta ya yi mugun bugawa badan komai ba sai dan kallon hannunsu a tare da ta yi, komai kaman gizo ya ke mata, hannunta ta fizge da ƙarfi ta na kallon hannuta sannan ta janye hannunun rigarta ta na kallo take ta kalla ƙafarta nan ba ba ƙarya gani tai ta fi Ramlat haske, dan haske na ta ba ma irin na Nigeria ba ne, ita da tasan kanta a Black colour.
Babu wanda ya kuma magana sai kallonta ake yi da mamakin gaske, nema neme ta shiga yi a parlour ta na ko hangan mirror ta nufa tana kallon kanta, a kallo ɗaya sak da ta dafa ƙirjinta dan ganin halitta ta sauya fiye da tinani.
"Airah, wai lafiyan ki kuwa? Me ke faruwa ne?." Fancy ta faɗa kamar ta yi kuka, sai Airah ta kalleta ta ce.
"Fancy dole ku ka sa ga ne ni, ni kaina ban gane kai na ba, jibi jikina ya canza, dan Allah wa zai min bayani, kaina kai....kaina...." Take ta kuma zuɓewa a jikin Fancy. Innalillahi wa'inna ilaiyi raji'un.
Bayan hours 1 ɗaya.
************** **************
____________ A firgice ta buɗe idanunta tana kiran sunan Allah, sai ta ji an da fata, kallon wacce ke gefan ta tayi 'Ramlat' take ta sakar mata murmushi, ba ɗan drib ɗin hannunta ba da ta rungume ta, sai tai ta ɗaga mata hannu, Ramlat ta miƙa sannan ta zauna a gyefan gadon ta na ce wa.
" Sannu ya jikin?."
"Alhamdulillah, Pure white! What is happening to me? Why has my skin changed from black to this?" Ta faɗa tana nuna hannunta da jikinta.
"That's enough, my head is already stressed. Are you trying to say you're Ramlat?"*
*"Hmmm, my namesake... I can't remember anything clearly. Please, where is my aunt that looks like Rabi? And my father? I know they'll recognize me. Take me to them. The only thing I remember is the car I boarded yesterday on my way to Mama's family’s wedding. Do you know what happened to my skin?" Ta faɗa tana nuna hannunta."
"Ramlat ina kika shiga ne tsawon lokaci mai yawa? Sam na kasa yadda wai ke ce, sam babu alaman da ya nuna ke ce, amma naji a raina ke ce, ina zuwa." Ta furta ta na miƙewa