Showing 1 words to 3000 words out of 93691 words
Godiya ga dukkanin yabo sun tabbata ga ubangiji talikai mamallakin sammai da Kasai Allah .
tsira da amincin Allah su Kara tabbata ga fiyayen halita annabi Muhammad (s. a. w)
*godiya mara iyaka*
GA dumbin mabiya litattafaina a Duk inda kuke cikin kasar Allah.
ina matukar alfahari daku ina kaunarku kmr yadda kuke kaunata.
“I will succeed. Not immediately. But definitely.” in shaa Allah.
✽»≿━༺🌹﷽🌹༻━≾»✽
Anas b. Malik (R.A) reported that Messenger of Allah ﷺ thus told him:
*"When a non-believer does good he is made to taste Its reward in this world. And so far as the believer is concerned, Allah stores (the reward) of his virtues for the Hereafter & provides him sustenance in accordance with his obedience to Him."*
حَدَّثَنَا عَاصِمُ بْنُ النَّضْرِ التَّيْمِيُّ، حَدَّثَنَا مُعْتَمِرٌ، قَالَ سَمِعْتُ أَبِي، حَدَّثَنَا قَتَادَةُ، عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ، أَنَّهُ حَدَّثَ عَنْ رَسُولِ اللَّهِ ﷺ *"إِنَّ الْكَافِرَ إِذَا عَمِلَ حَسَنَةً أُطْعِمَ بِهَا طُعْمَةً مِنَ الدُّنْيَا وَأَمَّا الْمُؤْمِنُ فَإِنَّ اللَّهَ يَدَّخِرُ لَهُ حَسَنَاتِهِ فِي الآخِرَةِ وَيُعْقِبُهُ رِزْقًا فِي الدُّنْيَا عَلَى طَاعَتِهِ* " .
References: Sahih Muslim 2808
� ?cX僆茀$桝�欔凸W鸜竊甛厘预�,d衺n+NUm.}�櫏 葄忾g渽展家腅魖题�洄┉�9K 咕旱鹁粧穽墚Z� �驼xx�19L揣7s@熮e3i `{譜kル
بِسْمِ اللَّهِ الَّذِي لَا يَضُرُّ مَعَ اسْمِهِ شَيْءٌ فِي الَْأرْضِ وَلَا فِي السَّمَاءِ وَهُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ
[5/23, 21:56] Pretty Sk: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9
https://www.facebook.com/share/p/14pZMxnDPB/
https://www.facebook.com/share/p/19hDk5NB65/
💪 JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION💪✍️
(J.A.W)
Rubuyu baiwa ce daga Allah, jajirtattu me kawai man iy amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi. ✏️
Typing free pages..................
𝙍𝘼𝙎𝙃 Ɓ𝙊𝙔𝘼𝙔𝙔𝙀𝙉 𝙈𝘼𝙎𝙃𝙀Ƙ𝙄
Story & written
BY SAKEENAT ABDULLAHI
𝕻𝖗𝖊𝖙𝖙𝖞 𝕾𝕶✍️✍️✍️✍️✍
page 1
*********** *************
Kaduna south, Kinkinau, layin Massalacin Ustaz, unguwace ta masu wadata dai-dai misali.
Tafe take cikin shiga na mutunci, hijab ne har ƙasa sai niƙaf, kwayan idanuwanta da ya sha uban kwalli kawai ake gani a jikinta, tana isowa jikin gidan nasu sai ga Mahafinta Malan Abdullahi Saleh Ustaz yafito daga cikin gidansu, cikin ladabi ta gaishe shi
" Abba ina huni "
" lafiya lau, har an dawo makarantan ?"
" Eh Abba"
" to Allah yataimaka " sannan ya shiga massalacin dan kiran sallan magrib. da sallama tashiga cikin madaidaicin gidan nasu wanda yahaɗu balaifi. ba kowa a tsakar gidan dan haka tashiga ɗakinsu.
" Assalamu Alaikum " da kalman da tashiga ɗakin kenan, shuru ba'a amsa ba sai ta kunna globe din ɗakin take hasken lantarki ya haska ɗakin. babban ɗakine wanda yakeda gado irin na ƴan bodin guda 2 me hawa biyu, kenan guda 4, sai babban wradrobe guda biyu da madubi wanda ya sha uban kayan kwalliya. jakkanta tacire tare da cire niƙaf din tana kallon kanta a mirro, Alhamdullih ta furta tanamai kallon kyawun da Allah ya yi mata, bafara bace choculate ce sosai ga tsayin hanci da manyan idanuwa sai baƙaƙen gashin idon wanda za ka za ci tasa gashin ido ne. baza'a ce mata doguwa ba sannan baza'a kirata gajeraba daidai wadaidai tsayin nata.
" Wai kinshigo dama ?" ta tsinkayi muryan yayarsu Hajara wacce ta ɗan miƙa daga kwancen datakeyi tana murza idanuwan ta.
"Eh Aunty Hajara na dawo ashe kina sama kina barcin dai."
"Uhmmmmm ni fa kar ku dameni" wata budurwa ta furta itama daga ɗayan bed din.
"Lallaima Marry wai da ma baki daura girkin ba?" Hajara ta faɗa tana zaro idanuwa. take suka sauko suka fita da sauri harda haɗawa da gudu-gudu dan jin wasu masallanta sun fara kiran sallah kuma sunsan sallan magrib ne, sanyayyar murmushi tasaki tana mai cire hijab sannan tafita dan duba Umma kafin a shiga sallah. Babban ɗakin Umma tashiga da sallama, falon yasha kyau komai Ash and white ne, mai girma ne sosai, sannan ga kayan kallo a ɓari guda, bakowa a parlourn dan haka tanufi babban kitchen wanda ƙofansa ke ta ɓangaren yamma wanda takejin hayaniya sama-sama, su hudu ne aciki, Umma, Hajara, Maryam, sai Zainab da alaman ita ke girkin dan sai faman yanka albasa take yi.
" ai barci yafi komai agunku, kuci gaba dayi ". Umma tafaɗa tana tashi daga kujeran da take kai.
" ki ya ƙuri, wlh nama Maryam magana dan ita ce dayi shine tayi barci kuma ni bansan nima barcin ya ɗauke ni ba"
" ki ya ƙuri Umma ban jin daɗi ne shine nakwanta bansan barcin ya ɗaukeni ba, kaina ke ciwo" Maryam ta faɗa da sauri dan jin Hajara zata ɗaura mata laifi
" ya isa shi ke nan, kuje an shiga masjed" Umman tafaɗa a daƙile dan haka suke mayun barci danma zainab batada damuwa kusan koda yaushe tana Kitchen abinta
" Umma barka da yamma " sai suka juyo suka kalleta dan basusan lokacin da tashigo ba
" yauwa Ramlat ". Abinda Umman tafaɗa kenan ta huce ɗakinta, inda sabo tasaba, sam Umma bata wasa da ita irin nasauran yaran gidan. Hajara ce ta dafa mata kafaɗa tana cewa.
" Sorry Ramlat "
" ayya badamuwa, bara naje nai sallah." daga haka ta wuce fuuuu.
" Wai yaushe Umma zata canza ne akan Ramlat? gaskiya banjina daɗin haka, ace ko magana mai tsawo bazatayi da ita ba" zainab ta faɗa tare da kashe gas dan ta kammala.
" ha kane amma muci gaba da mata addu'a kawai danma Ramlat din ba ta da ruƙo a zuciya " cewan Hajara
" Allah ya kyauta " abin da Maryam tafaɗa kenan. tare suka fita ta ƙofan cikin Parlour suka shiga babban ɗakinsu mai ƙofa biyu, kowannan su ya ɗauro alwala suka gabatar da sallah cikin jam'i kamar yadda suka saba, bayan sun idar, maraja'an karatun alqur'ani suka fara cikin daddaɗan muryoyinsu, musaffa sukeyi cikin futar da hukuncin kowani harafi na tajweed, su gunna, ƙalƙada dasu iddigami bigairi gunna da sauransu, ma sha Allah kowannansu gwanine cikin rero nashi shafin.
binsu nai da kallo masha Allah, kowacce hijab ɗin jikinta ya haskata sosai, Hajara fara ce, ga dogon hanci da idanuwa daidai wadaida haka Maryam take itama dan akwai kama sosai a tsakaninsu, tsayi, launin fata da wasu abubuwa, Itako Zainab tafusu haske sai dai ita bawani tsayi garetaba tsayinsu ɗaya da Ramlat sai dai Ramlat dafisu body-shape mai kyau. kuma tafusu kyau dukda itace mai duhun cikin su, gashi muryanta yafi nasu ɗaɗi har suna so a zo ɓangaren ta dan ƙira'anta akwai daɗi da taushi, ana kiran isha suka kammala karatun tare suka gabatar da sallan isha. suna idarwa suka nufi babban parlour dan cin abinci. Umma suka samu tana cin abinci dan haka Hajara tazubo musu a babban flate suka hauci suna kallo a babban TV ɗakin, shirin Lavi da lena suke kallo a tashar Daɗin kowa TV. bayan sun kammala cin abincin suka cigaba da kallon TV sai can Umma tace
" Kun san dai lokaci nata ƙaratowa dan gudanar da shagalin bikin ku, ke Ramlat har yanzu kinƙi fitowa da saurayi a haɗa da ke a huce gun ko? "
" Umma ni banda saurayi ai ......."
" uhmmm faɗa gas..." hararan da Umma ta yima Maryam ne yasa tayi shuru tana kallon ƙasa,
" Nidai bawanan ba kije ki bincika, nasan bakya kula kowa amma ba zan yadda bakida samari ba, kodai zaki ba Abbuu zaɓi kawai daya aura miki wanda yadace, kin ga Zainab ma haka ne an ha ɗa ta da wani ɗalibin sa"
" Umma wlh na amince koma wanene ni banda damuwa, kawai bana da ce ne duk wan'inda suka zo nema na sai na same su da wani ɗabi'a na daban" kanta a ƙasa tayi maganan cikin jin daɗin yadda yau wai itace da Umma ke maganan daya shafi rayuwarta.
" shikenan zanma Abbuu magana kuje ku kwanta" daga haka suka shige ɗakin su rufewa sukayi suna dariya ƙasa-ƙasa.
" Maryam kinga ai yafi a haɗa dukkan mu kawai a huta"
" Haka ne Hajara zefi gaskiya"
" Karfa ku manta ni shekara ta 18 ne, ku tweens (Hajara da Maryam) 22yrs kuke, Ita Zee 21yrs ......"
" so what madam, oya get ready to marriage, wa ze ce ke ce ƙaramar mu bayan ki na da uban jiki " faɗin Zee tana kwanciya kan bed din ƙasan na Maryam.
" Waima ina Sagir ? dayake nemanki a islamiya ne?" Maryam ta fa ɗa tana kallon Ramlat
" wannan ai bazan iya auran shi ba, be da mutunci kar kiga yadda yake ma malaman makarantarmu, nikadai yake raga mawa saboda makarantar Abuu ne"
" Allah ya kyauta " abinda Hajara ta faɗa kenan tana ka ra waya a kunne alaman amsa kira, Zainab kam barci ne ya dauke ta, Maryam kuma ana sana'ar ta chart da Usman, Hajara kuma waya take da wanda ze aure ta Muhammad.
Ramlat kwanciya tayi ta na ta tinanin hirar ta da Umma, murmushi ta sa ki a hankali dan tinawa da rayuwar su ta da.
End
alƙalamin daga PRETTY SK..
[5/27, 18:34] Pretty Sk: https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION💪✍️
(J.A.W)
Rubuyu baiwa ce daga Allah, jajirtattu me kawai kan iya mfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi. ✏️
𝙍̀𝘼̀𝙎̀𝙃̀ Ɓ̀𝙊̀𝙔̀𝘼̀𝙔̀𝙔̀𝙀̀𝙉̀ 𝙈̀𝘼̀𝙎̀𝙃̀𝙀̀Ƙ̀𝙄̀
ᑭᖇᗴTTY ՏK
Page 2
TINANI
Malan Abdullahi Saleh Ustaz mutun ne mahaddacin alqur'ani da hadisai yana zuwa guri-guri dan ba da fatawan addini, Malamin sunna ne sosai, yana da mata ɗaya Habiba wato Umma, suna rayuwa tare cike da tausayi da kulawa, shekarun su biyar da aure Umma tahaifa 'ya mace aka sanya mata Aisha, yarinya na kai 1yr ta koma ga Allah, sun ji ba daɗi amma su barma Allah komai dan yafisu son ta, a na nan wata rana a ka kawo wata yarinya dan ta musulnta a gun Abbuu, bayan ta amsa musulunci ta zaɓa suna Aisha, Abbuu yaji ɗaɗi dan yana son ya ga mace mai suna Aisha. labarin ta aka ba Abbuu ya tausaya mata, dan an kashe mata kowa a yaƙin boko haram, sai ya nemi daya riƙe ta a gunsa aikuwa aka bashi, bayan yazo gida ya bama Umma labarin ta, 'yar gudun hijira ce wace ta rasa kowa nata, Umma ta karɓe ta hannu bibbiyu. a haka su ka ci ga ba da rayuwa suna koya mata addini. Bayan wasu watanni Umma ta buƙaci Aisha ta zaɓa wanda take so a masu zuwa karatu gun Malan don ta aure shi, a nanne ta shaida ma Umma ita dai Abbuu kaɗai zata iya aura saboda ganin kyautatawan shi gare ta. Umma da ya ke maca ce mai sauƙin kai sai ba ta sa a ranta ba duk da ba taso jin haka ba, amma da Abbuu ya dawo ta shaida mai sai ya nuna indai ita ba ta da matsala shi ke nan. taso taƙi amincewa amma ganin Aisha duk tasauya ko abinci tadena ci, hakan yasa ta yadda aikuwa aka ɗaura auran, bayan ta tare su ka ci gaba da rayuwarsu cikin jin daɗi da kula da juna. a tare Allah ya basu ciki Umma ta riga haihuwa taƙara samun mace, Abbuu ya sa mata Aisha, ita ma Aisha data haihu mace yaƙara sa Aisha, dan shi be ƙi ko yara nawa ze haifa ya sa Aisha ba, yara sun fara girma har sun fara tafiya ga su da ɓarna, wata rana Aisha na suya taji wayan ta na ringing ta miƙe ta shiga ɗakin dan ta san ƙawar ta Mardiyya ce, da suka haɗu a islamiyyan da take zuwa, tana shiga ta ɗauki wayan tare da du bawa aikam taga ita ɗin ce, kafin ta sake latsa wayan suka ji gigitaccan ihu yaran nan, da salati ta fito ita ma Umma haka, aiko man suyan doyan nan ya zube ma Aisha babba wato yarinyar Umma ta ƙone sosai ta nata shure-shure, take ta rasu dan ta ƙone sosai ita ko ɗayan Aishan gefan jikinta ne ya ƙona, dan tare su kaje gurin suna rigima. Sunyi kuka kaman me, balle A'isha wacce take ganin kaman ita ce sanadi, a nayin sati 1 ita ma Aisha ƙarama ta bita dan tin wannan ƙunan bata samu lafiya ba, rayuwa haka taci gaba da tafiya a nan ne Umma taƙara haihuwa in da tahaifo tweens mata masu kama da ita,wanda suka ci Hajara da Maryam. tare da Aisha suke rainon yaran nan har Allah ya kawo ma Aisha ita ma ta haifa mace Ramlat wacce ita ma ita ta biyo kyau din ta dan Aisha akwai kyau ba tada haske amma kyau kam akwai shi.
Lokacin da Tweens na da shekara 10 ita Ramlat ke da 7yr tare suke komai na rayuwa, rana daya aka wayi gari babu Aisha wanda mutuwarta ta girgiza kowa dan lau ta kwanta amma aka wayi gari bata (Rayuwa kenan Allah yasa mudace).
Umma dukkan su ta haɗa take rainon su, amma sam ta dena sakin jiki da Ramlat bisa rashin sanin dalilin kowanne su, a haka suka taso bayan wasu shekaru aka kawo ma Abbuu kyautan Zainab da ga ƙaninsa me yara maza ganin ita maca ce yasa ya kaita gun yayansa, tare suka taso cikin ƙaunar junan su da natsuwa dan Abbuu mutum ne mai iya tarbiyyar ko yaro na rashin ji gun Ustaz ake kawoshi kuma da yaddan Allah ze shiryu, ya raine su cikin gata da walwala dan ya na da wa da ta sosai, dukkansu iyakansu secondry sch, amma islamiyya ko wacce sai da tayi N-Bayes ( Jsce na islamiyya).
Cigaban labari
Wayar ta ne ya ɗan yi ƙara a laman saƙo ya shigo, hakan yasa ta miƙe ta janyo jakkan ta dan du ba wa, a nan ne ta ga lokaci har 11:15pm yayi, wayar ta ƙiran Spark-4 irin nasu Maryam dan wayan su iri ɗaya ne, ganin MTN ne suka turo saƙon yasa ta koma ta kwanta tarasa me za ta yi dan haka takunna data tahau Facebook dan ganin abin da ke faruwa a duniya, a haka har barci ya dauke ta.
9:35pm Malam Ustaz yashigo gidan bayan sun gama karatun zaure da sukeyi sannan yakulle get din, sai da ya tabbatar ƙofon yaranshi na waje a ƙulle yake sannan ya shiga nasu ɗakin, bayan ya yi wanka yaci abinci suka zauna suna ɗan hira da Umma a nan ne take faɗa mai yadda sukai da Ramlat, sai da ya nisa sannan yace
" Ai da ita an barta har muga abin da Allah zai nufa tin da ba ta da tsayayye"
"Haka ne amma ni na fi so dukkan su a haɗa, a dai duba Malam, sun girma ma sha Allah"
" To ai Umma sai idan mutum ya nemi da a neman mai cigiyan matan aure sai a duba a cikin ɗalibai masu natsuwa, ko ita Zainab da kika ga ni shi ya ganta ya yi magana shi ya sa, amma bamu san me Allah ze nufa ba "
" Haka ne Malam Allah yasa mu da ce" ya amsa da. "ameen" sannan suka canza hiran.
Washe gari da safe bayan ta kammala shiryawa ko breakfast ba ta yi ba ta huce ɗaya da ga cikin islamiyoyin Babanta dan koyarwa, ita kadai ke da ra'ayin koyarwa ban da sauran su dai sai aikin barcin kawai suka iya ita Zee kuma sarkin aiki.
Sai 2pm aka tashi, uban yunwa ya ga ma gala baitar da ita dan dishi dishi take gani saboda ta na da ulcer, ta zo tsallaka titi kenan wata mota ta kusa ka ɗa ta, Allah yaso an ci uban birki, Idanuwanta a rintse tana an baton Allah ta kuma tsaya cak, har taji an bu ɗe motan da uban ƙarfi an fito.
" Are u mad ? are u out of ur sense ?" cikin izza yarinyar da tafito da ga motan ta ke faɗa.
" Ki ya ƙuri kuskur...."
"shut-up, mtwwwwsssss, I hate poor people bcuz ba ku da hankali, da na bi ge ki da an ce laifi na ne, bayan ke ki ka shiga gaba na. Ramlat ganin ita ce da laifi yasa tayi ta ba ta haƙuri har ta hu ce, tsallakawa titin ta yi ta na jin ba ɗaɗi saboda wata banza ta za ge ta "Amma bakomai" abin da ta ce kenan ta na tafiya cikin natsuwarta wacce ya zama mata ɗabi'a.
END
Alƙalami daga Pretty Sk
[5/29, 18:39] Pretty Sk: https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION💪✍️
(J.A.W)
Rubuyu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi. ✏️
𝐑𝐀𝐒𝐇 Ɓ𝐎𝐘𝐀𝐘𝐘𝐄𝐍 𝐌𝐀𝐒𝐇𝐄Ƙ𝐈
story and written by
ᑭᖇᗴTTY ՏK
ꜱᴀᴋɪɴᴀ ᴀʙᴅᴜʟʟᴀʜɪ
page 3.
RHYENO ESTATE MILLINIUM CITY
Da sauri Abbas ya buɗe get din gidan, direct motan ta shiga ƙiran GLK, Budurwa ce mai ki manin 20yrs ta fito sanye da atamfa me golding wanda aka yi ma ta ɗinkin fitted gown me upon shoulder, sai gyalen kayan wanda ya ke hannunta, babban palourn ta shiga tana mai kwaɗa kiran sunan "Mom" jin shuru ya sa ta zauna ta na ɗan huci, ga ni ta yi hutar babban parlour ya ɗauke duk ka, take ma su colours su ka faraa bayyana cikin ƙawa da tsari kafin ta buɗe baki sauti me duka ya fara tashi na waƙan Happy birthday, Happy birthday, sai ga muta ne sun yo kan ta suna ihu, wasu na watsa mata ruwa wasu kuwa flowers suke watsawa, cikin jin daɗin ta miƙe ta na kallon su, ɗaya bayan ɗaya suke ta wishing na ta tare da bata kyaututtukan, Mom ta yi ma godiya dan ta san ita ce ta gayyato ma ta friends din ta da wasu ƙawayen Mom din sannan gashi ƴan gidan su sun haɗu duk kan su. Bayan ansha an ci aka watse, wanka ta shiga bayan ta fito tana kallon ɗakin nasu, gado biyu ne wanda do ga ye ne har can sama sannan akwai ta za ra sosai tsakanin ɗaya da ɗayan, sai glasses guda goma wanda suka ke wa ye bangon hagun ɗakin, ɗan madaidaicin guri ne a ta gefe da aka ƙawa tasl shi kaman ƙaramin parlour kujeru ne a za ga ye da shi, a can ta hangi mata kusan age-mate dinta su na ta hira, ɗaya daga cikin glass din gurin ta janyo sai ga shi ya buɗe irin cikin salon nan, take kayan sawa suka bayyana iri-ri, zaɓan ɗaya da ga cikin kayan gurin tayi, wani haɗaɗɗan riga da wando masu kyau ta sanya sannan ta nufe idan matan nan