Showing 81001 words to 84000 words out of 117953 words

Chapter 28 - MY ENEMY BOOK 1 HAUSA NOVEL

asmeetah   

20 May 2025

4750

ƙwayar idanuwansa ya soma yi ko zaiga mutum domin yaji kamar motsin mutum a kansa amma baiga kowa ba,
jin anata ƙiraye-ƙirayen sallah ne yasa ya tashi zaune yana dafe da goshinsa, ganin towel yayi ya faɗo daga saman kansa, cike da mamaki ya ɗauki towel da jiƙar ruwa a jiki yana jujjuya shi,
Juye²juye ya fara yi amma Babu kowa, sakin dogon numfashi yayi tareda wurgar da towel ɗin gefe ya sauƙar da zura-zuran ƙafafunsa ƙasin carpet yana shirin tashi,
Baiwar Allah tana kwance ƙasin carpet ta ƙarƙashin gadon amma sai dai bata ƙarisa shigewa ciki ba saboda gadon a matse yake da ƙasi babu yanda zatayi ta shige gaba ɗayanta,
ganin sawayensa yasa ƙirjinta bugawa da ƙarfin gaske kamar zai faso ya fito tsabar harbawar da ƙirjinta ke yi,
miƙewa yayi ya nufi toilet domin ɗaurowa alwala yana shiga kuwa tayi saurin hautsunowa a ruɗe ta miƙe tana ɗingishi tayi saurin ficewa daga cikin bedroom daman already ƙofar a buɗe take, a gurguje ta samu nasarar fita daga falon ma, a hankali take taka Benin domin ba ƙaramin buguwa tayi a ƙafar ba,
tana sauƙa public falo ta nufi kitchen kai tsaye, tana shiga ta ɗora hannayenta a saitin ƙirjinta tana fitar da numfashi daƙer, kunna ruwan fanfon sink tayi ta wanke fuskarta sannan ta tsiyayi ruwa a cup ta sha domin maƙogaronta ba ƙaramin bushewa ya yi ba, saida ta kammala hutawarta a cikin kitchen tukun ta fito falon tana takawa a hankali idonta ne suka sauƙa akan Roshan wanda yake ƙoƙarin sauƙowa downstairs shima idonsa akanta, tsayawa tayi tana tunanin marin da tayi masa Nan danan taji ba daɗi a ranta, tayi nadamar wulaƙancin da tayi masa tana maganar zuci idonta akansa, har ya ƙarasa sauƙowa baice mata komai ba shima kuma ya kasa ɗauke eyes ɗinsa akanta, suna cikin wannan halin basu san lokacin da Uncle Deen shima ya sauƙo falon ba, hannu yasa ya dafa kafaɗar Roshan tareda faɗin "my twins what's wrong with you?...."

A firgice Roshan ya juyo yana kallonsa da smile akan fuskarsa
ya ce "there's nothing my Man....."

Uncle Deen idonsa yakai kan Baiwar Allah tareda faɗin "okay that's good...."

Baiwar Allah Kai a sunkuye gudun karta haɗa Ido da Uncle Deen a gurguje ta nufi room ɗinta kafin ta ƙarasa taji muryar Abbah daga sama shima yana ƙoƙarin sauƙowa yana faɗin "lafiya kuwa Dota naga kina ɗingishi?...."

Juyowa tayi tana ƙiƙƙina idonta akan Uncle Deen wanda idonsa akan agogon hannunsa yana ƙoƙarin saita shi ta ce "am am ammm Abbah dam daman buguwa nayi ne ....."

Roshan idonsa akanta shima ya lura da yanayin tafiyarta amma sai dai ya fahimci akwai wani abu domin eyes ɗinta akan Uncle Deen suke, dasauri Roshan ya waiwaya yana kallon Uncle Deen yaga shi hankalinsa ba'a kanta yake bama, ya sake Kai idonsa kanta anan suka haɗa Ido,
Abbah yace "toh kina lura maza kinji Koh...."

Ɗaga Kai sama tayi ba tareda ta ce komai ba tayi saurin shigewa room ɗinta...

Haka suma duk suka haɗa kayuwansu suka nufi hanyar fita zuwa masallaci daman kullum haka suke tare suke zuwa masallaci, duk suna sanye da jallabiya Roshan da Razhdeen fararen jallabiyoyi ne a jikinsu shi kuma Abbah yana sanye da baƙar jallabiya ga haske dadau-dadau ta ko ina kamar rana,

Baiwar Allah zama tayi a bakin gadonta tana jin tada motarsu har suka tafi a lokacin itama ta tashi ta nufi toilet yowa alwala, tana mai jin takaicin Uncle Deen ba komai ne ya ɓata mata rai ba illah rashin yin sallar dare,
ta saba kullum zata tashi tayi sallah daga ƙarfe ɗaya zuwa uku amma yau saboda Uncle Deen bata yi sallolin ba,
da wannan takaicin tayo alwala sannan ta fito da ɗauki zureren hijab ɗinta ta zura sannan ta tsaida sallah.....



Around 9:00 Baiwar Allah da Ummy suna kitchen suna fama haɗa breakfast sai kuma Pinky a gefe guda tana wanke-wanke tana jin yanda suke hirar su amma bata sa musu baki ba sai faman tsuka take ta jerawa,
ita kuma Rukky tana falo sai gyare-gyare take da goge-goge,
Bayan wasu ɗan mintuna duk suka hallaru a dinning iya mutum biyu ne Babu Roshan da Razhdeen daman su Kai musu ake can part ɗinsu,

suna cikin yin breakfast minal ta tashi da hanzarinta ta zari handbag ɗinta domin sauri take zata fita gurin aiki, daga ita sai mommy itama ta kammala shirinta zata tafi office itama,
Ƴar Tiny kuma daman bata tsayawa yin breakfast lunch ake haɗa mata kularta a saka mata acikin lunch bag ɗinta taita tafiya,
ko wacce ta security da yake kaita gurin aiki,
Shima Abbah tashi yayi cikin shirinsa na kakin soja zai tafi headquarters domin gudanar da wasu ayyuka, kafin ya fice ya juyo yana kallon Ummy ya ce "uwar masu gida ganan Dota ki rakata gurin Roshan ya duba mata ƙafarta...."

Ummy ta amsa da "toh Abbah....."

sai gurin ya rage daga Pinky sai Rukky da Ummy da kuma Baiwar Allah,
suma Pinky da Rukky suna kammalawa suka tashi suna hararar Baiwar Allah suka bar wajen, su haushinsu Abbah yafi damuwa da Baiwar Allah akan su....

Itama Baiwar Allah tana gamawa ta fara tattara kulolin kan dinning zata Kai su kitchen Ummy ta tayata duk suka gyara wajen,
suna kitchen Baiwar Allah ta kalli Ummy sannan ta ce "Sister Ummy Dan Allah ki temaka mun ki Kai breakfast ɗin Uncle Deen ni zan Kai na Yaya Roshan ..."

Ummy ta ce "ok ba damuwa bari na miƙa masa...." ta ɗauki na Uncle Deen tayi gaba,
Ita kuma ta fara shirya na Roshan kuma daman tanaso ta same shi ta bashi haƙuri akan laifin da tayi masa ...

Ummy ce ta shiga room falon Uncle Deen da sallama a bakinta gani tayi falon wayam Babu kowa, zuwa tayi gurin dinning ta ɗora kayan abincin akai, idonta akan tsarin falon yanda ya zama, cike da mamaki take bin falon da kallon tana maganar zuci "yaushe Uncle ya chanza carpet ɗin falon? ....."

tana cikin wannan tunanin taji ya ce "what's wrong?..."

A zabure takai idonta kansa tareda faɗin "gud morning Uncle Deen....."

ba tare da ya nuna wata damuwa ba ya ce "same to you Hajia ta...."

Wani irin farin ciki Ummy tayi yau ta samu kansa daman bayan Ƴar Tiny sai Ummy waɗanda yake shiri dasu acikin yaran gidan, kuma daman sunan da yake ƙiranta dashi kenam Hajiya domin ita ɗin takwarar Hajiya Maryama ce kakarsu kenam....

idonsa akanta ganin yanda take ta sau murmushi ya ce "are you okay?...."

Dasauri ta ɗaga masa Kai tana jinjina masa,
ya ce "ok whare is her?...."
Ummy cikin rashin fahimta ta ce "who?...."

Ɗaure fuska yayi kamar bazaiyi magana ba bayan seconni ya ce "the Girl...."
Ummy gudun karta hargitso shi yasa tayi saurin hasasho Baiwar Allah nan danan ta ce "ohhh ƙafarta ne yake mata ciwo shiyasa na kawo yau ɗin...."

Goya hannayensa yayi Saman ƙirjinsa yana kallon dinning ya ce "ki ɗauki gaba ɗaya kayan abincin Nan ki koma dashi can yanda suka fita, sannan ki ce mata tazo ta right now...."

yana kaiwa Nan ya nemi guri ya zauna akan kujerar falonsa yana pressing phone nashi ..

Ummy zaro Ido tayi waje tana jinjinawa Uncle Deen tareda amsa masa cikin girmamawa ta ɗauki gaba ɗaya kayan abincin ta fice dasu,
tazo zata sauƙa downstairs taci karo da Baiwar Allah tana ƙoƙarin haurowa zata miƙi ɗakin Roshan ita kuma tana tafe daƙer,
Ganin Ummy yasa ta dakata cike da mamaki ta ce "ya naga kin dawo da kayan abincin?....."

Ummy ta ce "wallahu a'alamu yace kije yana nemanki...."

Baiwar Allah saida ƙirjinta ya buga ta zaro manya-manyan eyes ɗinta tareda faɗin "ni kuma?....."

Ummy ta ce "Kinga baya son delay fah ki samu kije...."

Baiwar Allah ta ce "shikenam ba komai, bani na hannunki ke kuma saiki karɓi na Yaya Roshan ki Kai masa...."

Ummy ta ce "kar ki koma da kayan abincin ki ajiye anam idan ya ce yana buƙata saiki dawo ki ɗauka...."
Baiwar Allah ta ce "toh shikenam...." ta ajiye kayan abincin kamar yanda Ummy tace sannan ta miƙi hanyar part ɗinsa, ita kuma Ummy ta nufi part ɗin Yaya Roshan,

Baiwar Allah shiga tayi da sallama a bakinta ta tarar dashi yana zaune ko ɗagowa baiyi ba balle ya amsa sallamarta,

Sunkuyar da kanta tayi ƙasi ta ce "gani...."

Fuska a murtuƙe ya ce "baki iya gaisuwa bane?...."
Murya a harharɗe ta ce "ina kwana...."
Baice mata komai ba sai cewa yayi "meya hanaki kawo mun breakfast?...."

kamar zatayi kuka ta ce. "ƙafata ke mun ciwo..."
ya ce "meya sameta?...."

"Buguwa nayi...." A cewarta.

Ya ce "Oh God! Shi ya hana ki kawo mun breakfast?...."

Baiwar Allah dasauri ta amsa masa tareda ɗaga masa Kai ganin ya tausaya mata,

Ya ɗago da fararen eyes ɗinsa yana kallonta ya ce "nake ga tinda ƙafar ba yankewa tayi ba ai bazai hana ki kawo mun breakfast ba Koh?....."

Baiwar Allah ɗagowa tayi tana kallonsa kamar zatayi kuka Babu bakin magana,
ya kuma cewa
"Koda ƙafarki yankewa tayi dole ki tokara da sanda ki kawo mun abinci, daga yau last warning kar na sake ganin ƙafar wata ta kawo mun abinci indai bake bace, idan kuwa ba haka ba daga ke har ita you will see what am going to do,
Yanzu kije ki ɗauko mun abinci now! now!! Before I count 1 to 5...."

Baiwar Allah juyawa tayi tana sharar hawaye ta fice, tana zuwa ta ɗauki kayan abincin a yanda ta ajiye a saman Benin,
Ɗauka tayi ta nufi ɗakinsa tana Jan ƙafar da sauri kafin ya ambaci biyar a ƙirgensa,
Da sallama a bakinta ta shige falon saida tazo tsakiyar falon ƙafarta ta sake gurmuɗewa ta faɗi gaba ɗaya kayan abincin suka watse, ga miyar Ogusi yasha tsala-tsalan naman kaji aciki duk miyar ya kife gaba ɗaya....

Baiwar Allah bata san lokacin da ta fara furta "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un,
Allahumma ajurni fi musibatin wa akhlifli khairan Minha,
Ƙalu innalillahi wa inna'ilaihi raju'un....."

Saida ya bari ta gama addu'o'inta sannan ya ɗago yana kallonta fuska a hargutse,
Ita kuma hannayenta biyu ta haɗe guri ɗaya ta ɗago dasu alamar roƙo, bakinta ne yake kakkarwa zatayi magana amma ta kasa furta komai sai kukan da take yi ....

Ya ce "ki haɗiye mun kukan Nan,
kin ci sa'a yau murnar ƙarin shekara ta kuma shekarar rasuwar mahaifiyata, bazan yi murna ba kuma bazanyi jimami ba, zan sassauta miki hukunci, abunda zakiyi shine kisa bakin ki duk ki shanye miyan da kika zubar akan carpet, sannan kizo ki mun mopping....."

Kamar yanda ya ce a hanzarce ta kifar da kanta ƙasin carpet ta soma Shan miyan Nan kamar wata Akuya,
tass saida ta shanye miyan Nan dake Allah ya temaketa iya miyar ce kawai ta zube sauran abubuwan duk akulle suke da marafansu, bayan ta kammala tashi tayi ta tattare kulolin ta fice dasu,
Daga baya ta sake dawo da abun goge-goge da bucket mai ɗauke da ruwa a ciki tazo ta fara mopping duk da goggoge wuraren da ya ɓaci,
Sannan ta sake fita da kayan aikin,
Ba jumawa ta sake shugowa da wasu kulolin abinci daban kuma du a hankali take tafe ta ƙarasa gurin dinning ta jejjera masa kayan abincin....

Shi kuwa yanata uzurin gabansa ko kallon yanda take beyi ba,
Bayan ta kammala daƙer ta daidaita tsayuwarta sannan ta ce "na kammala...."

Tasowa yayi yana Jan ƙafa kamar mai tambayar ƙasi ya ƙarasa dinning ya zauna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login