Showing 90001 words to 93000 words out of 117953 words

Chapter 31 - MY ENEMY BOOK 1 HAUSA NOVEL

asmeetah   

20 May 2025

4762

kwantar da hankalinka kar kayi fushi da ɗan uwanka, kai ma dai kasan halinsa bai kamata ka biye masa ba...."

Roshan kamar zaiyi kuka ya ce "toh Abbah ya zanyi? bazan iya juran ganin yana azabtar da ita ba, inasonta Abbah....."

Jinjina kai Abbah yayi sannan ya ce "Uhmmm! Roshan kenam ai na sani daman, tin farkon dawowarku da yanda kake shishshige mata duk idanuwana akanku yake, duk wani motsin ku na sani,
kayi haƙuri komai a hankali ake yinsa, duk abinda haƙuri bai baka ba toh rashinsa bazai baka ba ......"

A haka suka kai har sallar asuba babu wanda ya rimtsa, a falo duk sukayi sallar asuba amma basuga fitowar Razhdeen ba,

Shima Razhdeen acikin room ɗinsa yayi Sallah, yana zaune akan sallaya yaji motsin Baiwar Allah daga kan gadon sai faman juyi take, daƙer ta ɗan buɗe eyes ɗinta tana jero addu'o'i,
Ganin yanda room ɗin yake chanza haske kala-kala yasa tayi saurin buɗe idanunta sosai domin tasan ɗakinta babu irin wannan fitillu haka daban daban,
A razane ta tashi zaune tana faɗin "nashiga uku aina nake?...."

Idonta ne suka sauƙa akan Uncle Deen wanda yake kan sallaya ko kallonta baiyi ba,
A ruɗe ta ɗora hannu akai ta rausa wani irin uban ihu idanu kamar zasu faɗo....

Dasauri ya juyo yana kallonta cikin ɓacin rai,
wani irin tsawa ya daka mata agigice ta haɗiye ihun tana jan numfashi da ƙarfi....


A ruɗe Abbah da Roshan suka miƙe tsaye daga kan sallaya jin ihun Baiwar Allah,
Da gudun gaske Roshan ya nufi upstairs kai tsaye part ɗin Razhdeen ya nufa, shima Abbah bayansa ya biyo, jin har yanzu ba'a buɗe ƙofar ɗakin ba yasa Roshan fashewa da kuka yana faɗin
"Shikenam Abbah ya kasheni ya gama da rayuwata, daman nasan babu yanda za'ayi su kwana ɗaki ɗaya bai mata wani abu ba,
Abbah Razhdeen ya cuceni sannan ya cuceta na tsane shi Abbah,
I hate him! I hate him!! I hate him!!! ......"

Barin wajen yayi yana kuka ya nufi room ɗinsa shima,
Abbah tsabar takaici bai iya cewa komai ba, sai hannu yasa ya dafa jikin bango Kai a sunkuye sai faman girgiza shi yake.......



𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪.



𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔
✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦‍♀️🤦‍♀️

𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢𝐭͢ 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢

𝗗⃪𝗲⃪𝗱⃪𝗶⃪𝗰⃪𝗮⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗱⃪ 𝘁⃪𝗼⃪ 𝗺⃪𝘆⃪ 𝘀⃪𝗲⃪𝗹⃪𝗳⃪.

𝗔⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗡⃪𝗼⃪𝘃⃪𝗲⃪𝗹⃪ (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚)
𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇
𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅
👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈
𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈
👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ👈

ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ
👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt

ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ,
ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ..

𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃:

1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.

2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.

3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃.

4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼.

𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 41 to 42



꧁꧂



Kwance yake a falo kan 3 seater ya ɗora hannu akan goshinsa ido a lumshe kamar meyin Bacci,
Ita kuma Baiwar Allah tana bedroom yanda ya baro ta sai faman rera kuka take akan sallaya yanda ta idar da sallar asuba bata tashi ba har zuwa yanzu misalin ƙarfe 9 na safe,
Saida ta gama kukanta ta share tukun ta tashi ta nufi falo, a tunaninta Uncle Deen ya fita sai kuma ta tarar da shi akan sopa, ganinsa yasa gabanta yankewa, ta juma tana tsaye idonta akansa wanda ko motsi bayayi alamun yayi nisa a cikin baccinsa,
Kallon bakin ƙofa tayi nan ta fara taku a hankali ta nufi bakin ƙofa zata fice, cikin rashin sa'a tana isa ta riski ansa key a ƙofar, cikin ɓacin rai haka ta juyo tana kallon Uncle Deen kamar zata rausa ihu, zamewa tayi ƙasi ta zauna a bakin ƙofar tareda kifar da kanta kan gwiwa ta cigaba da rera sabon kuka....

kamar a mafarki yake jin ƙinƙishin kuka a hankali yake mutsil-mutsil da eyes ɗinsa har ya iddasa buɗesu gaba ɗaya, kallon yanda take zaune yayi daga bisani yaja dogon tsuka saboda hakane yasa yabar mata can bedroom ɗin amma saboda nashi ta biyo shi nan ma,
tashi yayi tareda miƙewa tsaye ya nufi waran frig ya buɗe sannan ya kalli yanda Baiwar Allah take a zaune fuska a haɗe ya ce "ke! tashi ki miƙo mun tray ɗin kan dinning can ...."

Tayi kamar bata ji shi ba kai a kife, saida yayi mata wani gigitaccen tsawa tareda faɗin "Ba magana nake miki ba?...."

A tsorace ta ɗago jiki na ɓari ta tashi ta nufi dinning ta ɗauko tray sannan ta kawo masa,
Hannu yasa ya karɓa sannan ya fara jido kayan fruits yana jejjerawa akan tray ɗin tare da Cake 🍰 da juice, ya rufe frig sannan yaje ya ajiye akan dinning, ya kalli yanda take a tsaye
Ya ce "ki zo Nam...."

Juyowa tayi ta nufi dinning itama yasa hannu ya gyara zaman kujerar tareda faɗin "zauna ga kayan breakfast....."

Girgiza Kai tayi tareda cewa "a'a na ƙoshi...."

Cikin ɓacin rai yake kallonta ya ce "kin san idan na fara dukan ki acikin ɗakin nan bamai ƙwatarki Koh?....."

Kamar zata fashe da kuka fuska ba annuri ta zauna tareda saka tray a gaba nan ta fara ɗaukan kayan fruits ɗaya bayan ɗaya tana ci, kuma daman da matsanancin yunwa ta tashi....

Shima zama yayi tareda kifar da kansa akan table ya zura dogin yatsunsa acikin sumar kansa yana caccakuɗa shi, alamun yana cikin damuwa over....

Baiwar Allah duk tana kallonsa amma sai dai ko a jikinta Ita dai tana cika cikinta ne....


Roshan gaba ɗaya ya rasa mai yake masa ciwo ajiki, abinda Razhdeen yayi masa sam baiji daɗin hakan ba, ya kasa zama guri ɗaya sai zarya yake acikin room ɗinsa, yana cikin wannan halin saiga Ummy ta shugo da sallama a bakinta tana riƙe da tray ɗin kayan breakfast, ajiye masa tayi a ƙasin bed ɗinsa domin a halin da yake ciki bazai iya zama a dinning ba,
Ummy ce ta tsaya a gabansa tareda faɗin "Dan Allah Yaya Roshan ka daina shiga damuwa haka, tinda har ba saceta akayi ba tana nan acikin gidan ai zata fito ....."

yana zubda ƙwallah ya ce "Uhmmm! Sau ɗaya naji ihunta ya daki dodon kunnena daga lokacin ban sake jin motsinta ba,
Bansan me yayi mata ba...."

Ummy cikin nuna damuwa ta ce "Yaya Roshan ka kwantar da hankalinka babu abinda ya faru, nasan Uncle Deen bazai taɓa aikata wani mummunan abu ba, inaso ka kyautata masa zato...."

Idonsa akan Ummy ya ce "shikenam insha Allahu...."

Ta ce "toh zauna muci abinci yau tare na sako mana saboda nasan idan kai ɗaya ne baza ci ba ....."

Murmushi yayi sannan ya zauna, Ummy ta fara zuba musu a plate ɗaya tareda two spoon, tana jansa da hira suna ci cikin kulawa.....

Abbah shima lamarin Razhdeen ya yi matuƙar bashi mamaki da kuma haushi, tinda yake da Razhdeen bai taɓa ɓata masa rai irin ta yau ba...


☾D☽☾A☽☾Y☽ - 5

࿙R࿚࿙A࿚࿙Z࿚࿙H࿚࿙D࿚࿙E࿚࿙E࿚࿙N࿚🤦‍♀️🤦‍♀️🤦‍♀️

A kwana a tashi yau kwana biyar kenam Razhdeen bai buɗe ɗakinsa ba,
Yana zaune a falo kan sopa sai danna computer sa yake hankali kwance,
Baiwar Allah ce ta fito daga bedroom ɗinsa tana sanye da baƙar jallabiyarsa yanda tayi wanka ya bata akan ta sanya domin kayan jikinta sunyi datti,
zuwa tayi ta durƙusa a gabansa kanta a ƙasi ta ce "Dan Allah Uncle kayi haƙuri nasan nayi maka laifi amma hukuncin nan daka ɗaukar mun yayi tsauri da yawa, na roƙe ka da girman Allah ka buɗe mun ƙofa nabar ɗakin nan, inason ganawa da Mutanen gidan, bansan me zasu yi tunani akan mu ba, kodan saboda Abbah ka temaka wannan ba ɗabi'ar ɗan musulmi bane mahaifinka na ganinka amma kana zaune da macen da ba muharraminka ba acikin ɗakin........."

Bata ƙarasa maganar ba taji da daka mata tsawa da cewar
"Enough! U are very stupid, saboda Kinga na sake miki kwana biyu shine zaki nemi ki raina Ni?....."

Baiwar Allah tana hawaye ta ce "ba haka bane Uncle amma mutanen gidan zasu wani irin bahagon tunani akan mu yau kwana biyar muna ɗaki....."

Ɗaga mata hannu yayi alamar ta dakata haka tareda yi mata wani irin kallon ƙasƙanci ya ce "wani irin tunani? akan mu? Uhmmm! Bari kiji yarinya Ni Razhdeen nafi ƙarfin nayi tarayya dake kowa ma yasan da haka saboda kinyi mun ƙanƙantar da bana ɗaukar ki a matsayin ƴa mace,
Kada ki sake yin irin wannan tunanin na gaya miki....."

Cikin ɓacin rai take kallonsa ta ce "koda banyi tunanin nan ba amma sauran mutanen zasu yi...."

Ya ce "Wait! bana son sa'insa saboda Ni nafi ƙarfin tunaninki, ki tashi ki koma bedroom na bar miki can karna sake ganin ƙafarki a yanda nake...."

idonta akansa tana huce ta miƙe tsaye ta ce "Wallahi Uncle babu yanda zanje Ni kuma yau kwanana na ƙarshe kenam a ɗakinka domin bazaiyu ka zubar mun da mutunci ba....."

Ɗagowa yayi yana kallonta cike da mamaki daƙer ya iya furta "Ni kike gayawa maganganun nan?..."

Kawar da kanta gefe tayi ko kula shi batayi ba,
tsabar takaici bai ƙara ce mata komai ba haka ya cigaba da pressing ɗin computer,
ganin ya cigaba da abinda yake yi yasa ta juya ta nufi bakin ƙafa tasa hannu tana bubbuga ƙofar da ƙarfin gaske tana magana da ƙarfi cewar
"Dan Allah Azo a temake Ni, jama'a temakoooo....."

waiwayawar da zata taga mutum sangangam a bayanta yana tsaye ya goya hannayensa kan ƙirjinsa idonsa akanta,
Saida ƙirjinta ya buga ganin shi a haka, itama tsayawa tayi tana kallonsa idonta har ya cicciko da hawaye,
hannunsa ya ware yana nuna mata hanya da cewar "zo ki wuce ciki....."
sunkuyar da kanta tayi ƙasi tana ƙoƙarin share hawaye,
Ya kuma cewa "magana nake miki..."
still kanta a ƙasi ko ɗagowa batayi ba balle tasan da ita yake, bata ankara ba taji ya saɓata akan kafaɗarsa yayi cikin bedroom da ita,
ƙoƙarin zamowa take tana tutture shi, a garin ajiye ta a kan gado ta harɗe musu ƙafafu a garin ƙwacewa, cikin rashin sa'a ya kifu a kanta duk suka doku akan gadon,
ɗan ƙara tasau jin nauyinsa akanta, gagara tashi yayi sakamakon rasa ƙwarin jikinsa, gaba ɗaya ta kashe masa jiki, tinda ya kifar da kansa akan ƙirjinta bai ƙara motsawa ba, sumar kansa gaba ɗaya ya rufe mata fuska saida suka ɗau tsawon mintuna a haka kafin daga bisani ta ɗan fara motsawa tana ƙoƙarin ture shi, sai a lokacin shima ya ankara bai san lokacin da yayi saurin sauƙa daga kanta ba yana fitar da numfashi sama-sama, kansa ne yake wani irin sarawa tinin gumi har ya wanke masa duk ilahirin jikinsa, a gigice ya yi saurin faɗawa bathroom domin sam baya juran zafi duk da sanyin A.C dake ɗakin, shi kansa bai san dalilin shigarsa cikin wannan yanayin ba, domin bai taɓa shiga wannan yanayin ba sai yau,

Ita kuma Baiwar Allah tana nan a yanda take ko motsawa batayi ba ta ƙanƙame idonta kunya ne ya lulluɓeta....


࿙R࿚࿙O࿚࿙S࿚࿙H࿚࿙A࿚࿙N࿚.
A hankali yake sauƙowa daga upstairs kamar zai kife, hannunsa yana ɗore akan saitin zuciyarsa, daƙer ya sauƙo falo wani irin hajijiya ne ya ɗebe shi yayi baya luuu zai faɗi dai-dai lokacin da Abbah ya sauƙo shima daga upstairs ɗinsa, da gudu Abbah yayo kansa yayi saurin riƙo shi tareda manna shi a jikinsa yana faɗin "Roshan! Roshan!! Roshan!!! kana lafiya kuwa?...."

Shi kuwa Roshan ba abinda yake faɗin illah "Abbah zuciyata zata fashe Abbah, Abbah tafasa take zato fashe, ka temaka mun Abbah zan mutu, zan mutuuu......"
ya ƙarasa maganar tareda fashewa da matsanancin kuka hannunsa akan ƙirji, shi kaɗai yasan halin da yake ciki,
kafin Abbah ya ankara har ya fara Aman jini, ɗayan hannun yasa yana toshe bakinsa kar jinin ya fito amma inaa abun yaci tira hannu duk ya ɓaci da jini, shima Abbah gaba ɗaya ya ɓata masa kaya da jini,
Gaba ɗaya Abbah ne ya fita hayyacinsa ganin halin da Roshan ke ciki, gaba ɗaya ya rasa ta yanda zai fara temaka masa shima Abbah kawai ya fashe da kuka, daƙer ya samu ya lalumi wayarsa a aljihu ya ciro yayi dialing call number security gidan,
Ga mutanen gidan basa nan iya Ummy ce take room ɗinsu bata san wainar da ake toyawa ba,

Sojoji ne suka shugo kusan su biyar kai tsaye nufan wajen da Abbah yake riƙe dashi sukayi, su biyu suka ɗauki Roshan Abbah yana biye

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login