Showing 108001 words to 111000 words out of 117953 words

Chapter 37 - MY ENEMY BOOK 1 HAUSA NOVEL

asmeetah   

20 May 2025

4761

going to find you a solution...."

Uncle Deen idonsa akan Marshall ya ce "Really?..."

Marshall ya amsa masa da "yeah...."

Girgiza Kai Uncle Deen ya yi can na wasu ɗan lokuta ya ce "okay! don't worry..."

Marshall cikin yanayin damuwa ya ce "kodai akan mafarkin yarinyar nan ne?...."

Ɗan buɗe eyes ɗinsa ya yi dasauri yakai ƙwayar idanuwansa kan Marshall, lokaci guda yaji kamar wanda aka jona masa shocking a jiki,
Ƴar Amana ce ta faɗo masa a rai lokaci guda kuma yaji wani sanyi a ransa wanda bai san lokacin da ya ɗan sau wata ɓoyayyar murmushi ba,

Marshall jin ya kasa bashi amsa yasa shi maimaitawa ya ce "ita ce Koh?..."

Girgiza Kai Uncle Deen ya yi tare da faɗin "I already find her...."

A zabure Marshall ya ce "Whattttttt!!!!
wai da gaske kake Major? but how comes?...."
Uncle Deen tsaya kallon Marshall ya yi ganin yanda ya firgita jin ya ce ya samo ta,
"Wait! duk wannan ruɗin na meye?..."

a hanzarce Marshall ya yo kan Uncle Deen ya zauna dab dashi fuskarsa ɗauke da fara'a
ya ce "na tayaka farin ciki Major domin wannan yarinyar ba ƙaramin wahalar dakai take ba, ina murna ne saboda matsalarka tazo ƙarshe,
You know Babban Malami ya sanar mana cewa ciwon mafarkinka bazai warke ba har sai kayi ido huɗu da yarinyar, kaga kuwa daga yanzu wannan mummunar mafarkin ka daina shi har abada,
Amma taya ka sameta?..."

Uncle Deen jin Marshall ya cika shi da surutu yasa shi cewa "oh my god Marshall! I don't know how can I explain for you, please leave me alone...."

Marshall a hanzarce ya riƙo hannun Uncle Deen yana faɗin "i want to see dis useless girl da take wahalar mana dakai..."

A firgice Uncle Deen ya juyo yana kallonsa fuska a ɗaure ba alamar wasa ya ce "WHO is the useless girl?...."

Ganin yanda yanayinsa ya sauya lokaci guda yasa Marshall cewa "it's okay am just jocking, yanzu dai tashi ka rakani gurinta in batayi Sa'a ba na harbe mata kai...."

a fusace Deen ya juyo tare da watsa masa wani irin kallo,
cikin zolaya Marshal yake cewa "am sorry sorry am just playing,
please tashi muje naga ƴar baiwar yarinya mai fitowa a cikin mafarkin jarumin jaruman sojoji...."

hannu Uncle Deen ya ɗora akan goshinsa yana bubbugawa a hankali tsabar tsananin ciwon da yake masa ga Marshall kuma yana damunsa da surutu, a hankali ya furta cewa "I'll not go anyway, am hungry and am not feeling well once...."

sauƙe numfashi Marshall ya yi tare da faɗin "okay! daman tinda naji kace baka gida nasan akwai matsala domin indai kana Nigeria baka son yin nesa da Daddy, saboda haka yasa nabi ta restaurant nayo mana shopping kayan abinci dasu fruit...."

ya ƙarasa maganar tare da miƙewa tsaye ya nufi yanda wata ƴar jaka take yasa hannu ya buɗe ya ciro wata leda mai ɗauke da take away ya ciro guda biyu da spoon a jiki, sannan ya ɗauko wata leda mai kayan fruits da juice,
yazo ya jawo ɗan ƙaramin glass table dake tsakiyar falo zuwa gaban Deen ya ɗoɗɗora kayan ciye-ciye akai,
bayan ya kammala shirya komai enough a hankali ya fara feeding ɗin Deen yana sashi cin abincin daƙer saboda a rayuwarsa ya tsani cin abincin restaurant,
a nutse suka kammala cin abincin su daga baya Uncle Deen ya taya Marshal ɗaukar jakarsa bayan ya ji kansa garau ya kaishi wani tsararren bedroom dake saman upstairs,
Dake falo biyu ne a cikin ɗaki ɗaya sai bedroom huɗu ko wanne yana saman upstairs,
two bedrooms suna upstair a falon farko sai another two bedrooms a falo na biyu,
Marshall ya sauƙa ne a falon farko saida ya zaɓi bedroom ɗaya acikin biyu dake upstairs,
Shi kuma Uncle Deen a falo na biyu yake shima yana ɗaya daga cikin bedrooms a saman upstairs,

Bayan Uncle Deen yakai Marshall bedroom ɗinsa shima sauƙowa yayi ya nufi falonsa kai tsaye upstairs ya haura ya nufi bedroom ɗinsa,
Bathroom ya shige domin yin Bathing....

Shima Marshall kafin ya shige Bathroom yayi wanka saida ya ƙira wayar Minal bugu ɗaya aka ɗauka, murya ciki-ciki ya ce "hello Beb na sauƙa a Nigeria...."

daga ɓangaren Minal kamar bazata mutu ba tsabar farin ciki tana kwance saman katafaren ƙaton gadonta tana sanye da doguwar rigar bacci marar kauri mai hannun breziyya
ta ce "honey yanzu haka kana ina?...."

ya ce "ina tare da Major a gidansa na Ƙwarimpa...."

A ɗan ruɗe ta ce "me! Uncle Deen kuma...."

Ya ce "wait kar ki damu kinsan dai Major bashi da case akan mu, daman Daddy ne baya son tarayyar mu amma kamata yayi naje na sameki a can gida...."

Cikin nuna farin ciki ta ce "okay zan zo na sameka....."
tana kaiwa nan tayi saurin katse wayar sakamakon jin motsin mutum yana nufo room ɗinta....

shima a ɓangarensa sauƙe dogon numfashi yayi tare da manna wayar a ƙirjinsa yana sakin ƙayataccen murmushi, daga bisani ya jefar da wayar saman bed ya shige Bathroom yana ɗaure da towel a kunkuminsa,
Mohandas inba gaya maka akayi ba bazaka taɓa cewa Christal ne ba saboda zubinsa da kalar ɗabi'unsa irina musulmai ga kyautatawa....


Around 3:30PM
Minal ce cikin shirinta taɗau wanka kamar zataje party, tana sanye da shadda less tasha ɗinkin doguwar riga har ƙasi, style ɗin ɗinki gaba ɗaya zigzar wuta ne daga sama har ƙasa,
tasha takalmi mai tsini blue kalar shadda less ɗinta sai sarƙa da ɗan kunne blue colour, da gyale shima blue colour, handbag shima blue, kwalliyar fuskarta kuwa kamar wanda aka tsara mata daga ƙasar waje hatta eyelashes ma blue, lips ɗinta ne kawai ya kasance red a yayinda girarta da kwallin ido da kuma eyeliner suka kasance Black colour,
sauƙowa falo tayi tana ƙamshin turare ta tarar da Pinky da Rukky da kuma Ummy da Ƴar Tiny suna kallo,
Ƴar Tiny ce ta ɗago tana kallonta ta ce "Aunty ina jaki je?..."

Harara Minal ta watsa mata ba tare da tayi magana wa kowa ba ta nufi hanyar ƙofar fita daga falon bata ankara ba taji muryar Abbah yana faɗin "ina zaki je ?...."

Dasauri ta waiwayo tana kallonsa a yayin da ya ƙarasa sauƙowa daga upstairs yana fuskantar ta tare da goya hannayensa ta gaban ƙirjinsa,
Ƙiƙƙina ta fara masa tana kai ƙwayar eyes ɗinta kan sauran yaran gidan,
A tsawace Abbah ya ce "ki buɗe baki kiyi mun magana...."

a tsorace ta ce "Abbah bikin ƙawata zanje kuma Ni ce babbar ƙawa...."

fuska a haɗe Abbah ya ce "idan zaki fita kinfi ƙarfin sanarwa cewar zaki je wani guri?...."

kai ta sunkuyar ƙasi tana wasa da yatsun hannunta,
Sai ji tayi ya ƙara cewa "wato Mohandas ya ƙira ki cewar yazo Nigeria Koh? shine zaki je ku haɗu,
toh bari kiji duk wayonku a tafin hannuna kuke, tin sauƙar Mohandas a airport na sani domin akwai ma'aikata na da yawa acan, sannan yana shiga gidan Razhdeen security gidan suka ƙira ni suna sanar mun,
na gaya miki bana son soyayyarki da Christal, bawai bana sonsa bane kawai addininsa ne banaso ki fita harkarsa na gaya miki,
saboda ku muka yanke zumunci tsakanina da mahaifinsa, mahaifinsa baya son sa dake nima kuma haka amma kun ƙi rabuwa,
Amma zanyi maganinki zan nemo miki wani ne na Aura masa ke,
kuma kada na kuskura naga ƙafarki a waje....."

Minal gaba ɗaya jin kanta take kamar ta sheƙe kanta gaba ɗaya hawaye duk ya wanke mata fuska cikin kuka take faɗin
"Abbah wallahi inasonsa...."

A fusace Abbah ya ce "kisa ya musulunta indai har kina sonsa in ba haka ba bake ba shi...."

Lokaci guda ta fashe da matsanancin kuka mai cin rai ta nufi upstairs da gudun gaske tana kuka ta haura kai tsaye room ɗinta ta nufa....

Shima Mohandas yana zaune a falo yasha kuptarsa maroon colour yasha kyau sosai ga sajen nan ya zaunu sai faman pressing phone ɗinsa yake yana jiran isowar abar ƙaunarsa,
yana cikin zaman kaɗaici saiga Deen ya fito yana sanye da baƙar jallabiyansa wanda ya tsaya masa a iya gwiwa dake jallabiyan da dogon wandonsa,
Gaban rigar yasha aikin wuta ga kayan yabi shape ɗin jikinsa gaba ɗaya, kayan ba ƙaramin masa kyau suka yi ba gasun kama jikinsa matuƙa sai kayan suka ƙara bayyanar da ƙirar ƙarfin jikinsa,
Sumar kan nan ya yi masa kyakkyawar gyara gashi a kwance lupp har ƙasin kafaɗa sai sheƙi yake yana fitar da wani irin ƙamshi na daban ga ya haɗu da ƙamshin turaren jikinsa gaba ɗaya gidan ne ya turniƙe da ƙamshi,
yana riƙe da key ɗin motarsa ya tsaya yana kallon hanyar fita a hankali yake motsa lips ɗinsa ya ce "Are you finish?..."

Mohandas tin daga kan takalminsa har zuwa kan sumar kansa yake bi da kallo sakin baki yayi gaba ɗaya Deen ya burge shi duk da kullum acikin burge shi yake amma na yanzun wanka ya ɗau sama da yawa,

Uncle Deen ganin Marshall sai ƙare shi yake da kallo yasa shi haɗa rai fuska ba annuri ya ce "bana son kallo fa, nace ka kammala?...."

Murmushi Marshall ya yi sannan ya ce "kai ɗin ne Major sai a slow, amma ina zamu je?...."

juyowa Deen ya yi yana kallonsa ya ce "ina kace na rakaka?...."

Marshall ya ce "Ohoooo na tuno, wai waran dreamer takan?
toh ai nima happiness ɗita tana nan zuwa don haka na fasa fita....."

Uncle Deen kallonsa yake cikin takaici domin shima yana muradin ƙara ganin yarinyar,
kafin Uncle Deen ya motsa baki yayi magana yaji wayar Marshall tana ringing hakan yasa ya haɗiye abinda zai furta,

Murmushi Marshall ya saki tare da faɗin "gata ta ƙira wata ƙil tana bakin gate ta iso...."

Ɗaga ƙiran yayi yaga video call ta ƙira,
ganin ta a zaune tsakiyar gado sai kuka take yasa shi tsorita a ruɗe ya ce "meya faru dake Beb?...."

tana kuka ta ce "kayi haƙuri honey Abbah ya dakatar dani...."

cikin rashin jin daɗi Marshall ya ce "taya Abbah yasa nazo ƙasar?...."

cikin kuka take faɗin "An ƙira Abbah an sanar masa zuwanka, kasan Abbah yanada mutane daga airport har gidan da Uncle Deen yake...."

A hankali ya furta "Oh my God! yanzu ya zanyi na haɗu dake? ga can gidanku akwai tsaro na musamman balle nace idan Abbah ya fita aiki nazo, ya zanyi?...."
ya ƙarasa maganar ciki ciki kamar wanda zaiyi kuka,
Uncle Deen ganin zancen su yaƙi ƙarewa yasa shi cewa "Hmmm! na tafi if you finish your madness u can follow me ....."

yayi maganar tareda nufan bakin ƙofa zai fice,
Shima Marshall ganin bazai iya juran ganin kukan Minal ba yasa shi cewa "please my wife stop dis cry I don't wanted, ina zuwa zan ƙira ki daga baya...."

yana sauƙe ƙiran ya ɗora wayan saitin zuciyarsa yana sauƙe numfashi daƙer, cike yake da damuwa amma sai dai babu mafita,
miƙewa yayi yana jan ƙafa daƙer yayi waje shima,
a cikin mota ya tarar da Deen yana zaune a driver seat, buɗewa yayi ta gefensa ya shige lokaci guda damuwa ta bayyano ƙarara akan fuskarsa,
Ganin haka yasa Uncle Deen kawar da kai gefe yana shirin karya kwana zai nufi hanyar gate,
A wannan lokacin har sukayi nisa babu wanda yayi wa kowa magana,
shi Uncle Deen bai iya rarrashi ba balle ya bashi haƙuri akan damuwar da yake ciki, shi kuwa Marshall baƙin cikinsa shine ba lallai har ya tafi yaga Minal ɗinsa ba tinda har Abbah yasan yana ƙasar, zuwa aiki ma zai iya dakatar da Minal har sai ya bar Nigeria,
Uncle Deen tinda suka fara tafiya ko sau ɗaya bai juyo ya kalli yanayin da Marshall yake ciki ba,
Da haka har suka isa yankin mabarata,
Dasauri Uncle Deen ya danna burki a dai-dai wurin cike da mamaki yake bin wajen da kallon ganin gurin ya hargutse da kiɗe-kiɗe, ga yanda mabaratan nan suka zagaye tsakiyar ƙwalta sai gurin yayi circle duk suna zazzaune sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login